2025-03-31@23:46:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1114

«Taskira»:

    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa...
    Jagoran juyin juya halin musulinci na Iran,Ayatullah Sayyid Ali Khamenei, ya bayyana cewa yau duniyar musulmi tana bukatar hadin kai fiye da ko wane lokaci. A yayin ganawarsa da jami’an tsare-tsare da jakadun kasashen musulmi yau Litinin ranar karamar sallah a Iran, Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya mayar da hankali kan abubuwan...
    Ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta gayyaci mai kula da harkokin kasar Switzerland da ke Tehran domin nuna fishi kan irin munanan ayyukan Isra’ila a yankin da kuma barazanar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Babban daraktan ma’aikatar harkokin wajen Iran Issa Kameli ne ya gayyaci jami’in diflomasiyyar na...
    A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin. Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Hare-haren da Isra’ila ta kai...
    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo. Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari. Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin...
    Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a...
    A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan...
    Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da...
    Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu. Amma a wani bangare a...
    Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta yi watsi da tattaunawa kai tsaye dangane da shirinta na makamashin Nukliya, sannan ya kara da cewa amma tattaunawa tare da masu shiga tsakani a bude take. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shugaban yana cewa tuni, mun bawa gwamnatin Amurka...
    Wani yaro dan shekara hudu da ya kira wayar salular ’yan sandan yankin Mount Pleasant a Karamar Hukumar Charleston Jihar South Carolina da ke Amurka ya ce, mahaifiyarsa ta shanye masa ‘ice cream’ dinsa kuma yana bukatar a hukunta ta, a kai ta gidan yari saboda aikata hakan. A cewar ’yan sanda yaron dan...
    Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan kasar Yemen a daren Lahadi a wasu yankuna a birnin San’aa babban birnin kasar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bada sanarwan cewa a safiyar yau Litinin ne jiragen yakin Amurkan suka kai hare-hare har  13 a kan wurare daban-daban a kasar, daga ciki har...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa, Iran ba ta shiga tattaunawa da Amurka kai tsaye ba, yana mai mayar da martini kan wasikar da shugaban Amurka ya aike mata, amma kuma ya bayyana cewa hakan zai bude kofa ga tattaunawar kai tsaye. Da yake magana a wani taron majalisar ministocin a ranar Lahadi, Pezeshkian...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Amurka na da hannu a ayyukan haramtacciyar kasar Isra’ila na yada rashin tsaro da zaman lafiya a yankin. A wata ganawa da ya yi da Hans Grundberg, wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a kasar Yemen a birnin Tehran, Araghchi ya yi Allah wadai da ci gaba...
    Sabon tsarin sayar da man fetur a Najeriya ya haifar da ƙarin farashi, inda ake sayar da kowace lita a kan Naira 930 a Legas da kuma Naira 960 a Arewa. A ranar 28 ga watan Maris, 2025, sabon tsarin ya fara aiki bayan da aka dakatar da sayar wa matatar Dangote mai a farashin...
    Minista mai kula da al’ada da yawon bude ido da kuma sana’o’in hannu na Iran Ridha Salihi wanda ya gana da jakadan Tunisiya a Iran,Imad al-Rahmani ya bayyana bukatar hanyoyin bunkasa alakar yawon bude ido a tsakanin kasashen biyu, yana mai kara da cewa: Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin kasashen biyu dangane da yawon...
    Kakakin sojan kasar Yemen janar Yahya Sari ya sanar da cewa sau uku su ka yi taho mu gama da sojojin da suke cikin jirgin dakon jirayen yakin Amurka “ Trauman” a cikin sa’oi 24. A wata sanarwa da janar Yahya Sari ya yi a jiya Asabar ya bayyana cewa; Sun kai wa jirgin dakon...
    Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a...
    Ƙungiyar Hamas ta ce tana goyon bayan komawa yarjejeniyar tsagaita wuta a Zirin Gaza, tana mai cewa za ta yi amfani da shawarar da masu shiga tsakanin suka bayar wadda za ta kai ga sakin ƙarin fursunonin Isra’ila biyar da kuma tsagaita wuta a Gaza tsawon kwana 50. Babban jami’in Hamas da baya zaune a...
    Sheikh Na’im Qasim babban sakatarin kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ya bayyana cewa JMI ce ginshikin goyon bayan al-ummar Falasdinu, kuma itace gaba-gaban a duk wani yunkuri na yentar da falasdinawa da Falasdinu daga hannun HKI da masu goya mata baya. A wani jawabin da ya gabatar a jiya Asabar, shugaban kungiyar ta Hizbullah, ya...
    An fara wallafawa ranar 13 ga Mayu, 2022 A halin yanzu al’ummar Musulmi sun yi haramar fara shagulgulan Karamar Sallar bana bayan kammala Azumin Ramadan. A kan haka ne muka rairayo muku abubuwan da malamai suka kwadaitar da Musulmai su yi a irin wannan rana ta farin ciki da godiya ga Allah bisa ni’imominsa da...
    Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa. Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015. An ga watan Sallah...
    Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da hango jinjirin watan Shawwal, wanda ke nufin kawo karshen watan azumin Ramadana. Shafin Haramain ne ya ruwaito hakan, bayan daukar awanni ana neman wata. Wannan ke nufin gobe Lahadi ne 1 ga watan Shawwal, wato ranar karamar Sallah a kasar ta Saudiyya.
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan kungiyoyin kare fararen hula da masu aikin ceto Palasdinawa a Rafah da ke kudancin zirin Gaza, tare da bayyana hakan da aikata laifukan yaki. Sojojin Isra’ila sun amince a ranar Asabar 29 ga watan Maris cewa...
    Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane 20 ne suka mutu sakamakon hatsaniyar da aka samu tsakanin sojoji da masu jerin gwanon ranar Kudus ta duniya a Abuja fadar mukin Najeriya. Hotunan faifan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar ke neman mafaka yayin da karar harbe-harbe ke kara kamari a kusa da su. An ce an...
    Hukumomi a Myanmar sun ce adadin wadanda suka mutu a girgizar kasar ya kai 1,644, yayin da wasu 3,408 suka jikkata, ye zuwa ranar Asabar din nan. Tunda farko dai mutane 1,007 ne aka sanar sun mutu sai wasu 2,389 da suka jikkata. Girgizar mai karfi maki 7.7 ta shafi Kasashen Myanmar da Thailand wadanda...
    Shahararren masanin tarihin nan na Jihar Kano, Ibrahim Ado Kurawa, ya bayyana cewa soke hawan Sallah da Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya yi tamkar wani wasan kwaikwayo ne. A makon jiya ne dai Sarki Aminu Ado ya sanar da janye hawan Sallar da ya ce zai jagoranta kan abin da ya kira...
    Majalisar Karamar Hukumar Jahun dake Jihar Jigawa ta kaddamar da rabon tallafin kayan noman rani ga manoma 300.   A jawabinsa wajen bikin da aka gudanar a Garin Darai, shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Jamilu Muhammad Danmalam yace hakan na daga cikin manufofin Gwamna Umar Namadi na bunkasa noman rani da na damina domin kawar da...
    Wadanda suka rasa ‘yan uwa ko suka jikkata sakamakon fashewar tankar mai da ta afku a Majia, Jihar Jigawa, a bara, za su karɓi Naira miliyan huɗu kowanne domin rage radadin halin da suka tsinci kansu a ciki. Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana haka a lokacin da aka fara rabon kuɗin tallafin ga waɗanda...
    Hukumar ’Yan Sandan Saudiyya, ta yi magana kan bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, wanda ya nuna wata mata tana mari wani ɗan sanda bayan ya hana ta wuce wata hanya da aka rufe. A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta ce tana bincike domin tattara dukkanin bayanai kafin...
    Wani babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Imam Ayatullahi Sayyid Aliyul Khaminae shawara kan harkokin tsaro ya bayyana cewa hare-haren ‘WaaduSsadik na III’ don maida martani kan HKI saboda hare-haren da ta kaiwa Iran a shekarar da ta gabata suna kan hanya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar...
    Gwamnatin HKI ta bukaci hukumar hukumar ayyukan leken asiri na kasar MOSAD ta nemi kasashe musamman a nahiyar Afirka wadanda zasu amince su karbi Falasdinawan da za’a kora daga Gaza. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyoyin HKI na cewa Firai ministan kasar Benyamin Natanyahu yana neman wata kasa ko kasashen nesa...
    Kwamandan sojojin ruwa na dakarun IRGC Rear Admiral Ali-Reza Tangsiri ya tunatar da gwamnatin Amurka kan cewa idan ta aikata wawta ta kaiwa cibiyoyin Nukliyar kasar zata gamu da maida martani mai tsanani. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Tansiri yana fadar haka a kan jirgin ruwa mai daukar jiragen saman yaki...
        Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta yi ala wadai da kisan gilla da aka yi wa ‘yan Arewa 16 a Uromi, Jihar Edo, a ranar 28 ga Maris, 2025.   Rahotanni sun bayyana cewa waɗanda abin ya shafa suna kan hanyarsu daga Fatakwal zuwa Kano lokacin da aka kai musu farmaki, aka...
    Babban sakataren MDD, Antonio Guterres ya yi gargadi a jiya juma’a da safe, akan abinda ya kira ‘yanayi mai  cike da damuwa da yake faruwa a cikin kasar Sudan ta Kudu. An sami tashin hankali da fadace-fadace a cikin kasar ta Sudan ta kudu a ranar Laraba da jami’an tsaro su ka yi wa mataimakin...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bakin kakakinta Dr. Isma’ila Baka’i, ta yi tir da sabbin hare-haren da HKI ta kai wa kasar Lebanon a daidai lokacin da ake bikin ranar Kudus. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen na kasar ta Iran ya bayyana cewa; Abinda HKI ta yi keta tsagaita wutar yaki ne,wanda abin a yi tir...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a nan Tehran a jiya Juma’a ya bayyana cewa; Jerin gwanon ranar Kudus tana da matukar muhimmanci a addinin musulunci, yana mai kara da cewa: Muna godewa Allah madaukakin sarki cewa, ranar kudus ta wannan shekarar ta bunkasa fiye da shekarun baya.” Haka nan kuma ya kara da cewa; Imam...
    A wannan Juma’a ce 28 ga watan Maris na shekarar 2025, aka gudanar da taruka da jerin wano na ranar Qudus ta duniya wadda ta zo daidai da ranar Juma’ar karshe ta watan Ramadan mai alfarma. An gudanar da wadannan taruka da jerin gwano ne a kasashe daban-daban da suka hada da wasu kasashen musulmi...
    Ƙungiyar Jama’atul Nasrul Islam (JNI) , ta raba kayayyaki da sauran kyatuttukan Sallah ga marayu 50 gabanin bikin Sallah ƙarama a garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno. An gudanar da bikin ba da tallafin ne a harabar makarantar sakandare ta Bulabulin da ke birnin na Maiduguri. Yadda kisan ’yan Arewa 16 a Edo ya tayar...
    Manyan Matakai Biyar Da Manoma Da Masu Zuba Hannun Jari A Fannin Aikin Noma Ya Kamata Su Yi La’akari Da Su Kamar Yadda kwararrun Suka Bayar Da Shawara: 1- Irin Kwakwar Manja Na Malesiya Bukatar da ake da ita ta Irin Kwakwar Manjan Nijeriya a duk shekara, ya kai na tan miliyan 3, inda kuma...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Esmaeil Baghaei ya ce hare-haren da sojojin Amurka ke kaiwa kasar Yemen da keta hurumin yankunanta barazana ce karara ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Juma’a, Baghaei ya yi tir da hare-haren da Amurka ke kai wa Yemen ba bisa...
    Miliyoyin al’umma daga sassa daban daban na duniya sun gudanar da jerin gwanon zagayowar ranar Kuds ta duniya wacce ta gudana yau. An dai kebance ranar ce domin nuna goyan baya ga al’ummar falasdinu, kuma ana gudanar da ita ne a ko wacce Juma’ar karshe ta watan ramadana bisa fatawar jagoran juyin juya halin musulinci...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga...
    A cewar shugabannin Ƙwadago, dole ne a sauya irin wadannan lamari don kare mutuncin tsarin dimokuradiyya a Nijeriya. Sun jaddada wahalar da dokar ta-ɓaci ta haifar wa ma’aikatan kananan hukumomi, da yawa daga cikinsu har yanzu ba su karɓi albashinsu ba. Sanarwar ta lura cewa hana albashin ma’aikata ya jefa su cikin matsin tattalin arziki,...
    A ranar Juma’a kasuwar ta rufe a cikin makon makon inda masu zuba hannun jarin, suka yi asarar Naira biliyan 166.43. Duk a cikin makon, saye da sayawar da aka yi ta shiyar ta kai ta jimlar Naira biliyan 3.281 da kuma wata shiyar ta Naira biliyan 63.517, duk a cikin hada-hada guda  60,782 da...
    Aikin na tura danyen Man, ya kai akalla tsawon kilo mita 180 wanda a tura shi, daga wajen hako shi da ke a yankin Neja Delta. danyen Man da Nijeriya ke hakowa, ya kai kasa da yawan wanda Hukumar OPEC ta iyakan ce, a watan Fabirairun  2025, wanda ya kai yawan Ganga  1,465,006 da ake...
    Ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka ana ci gaba da gudanar da jerin gwamnon ranar Kudus ta duniya a birane daban-daban na kasashen duniya. Marigayi Imam Khomeni ne ya ayyana ranar karshe ta kowane...