HausaTv:
2025-04-23@19:46:03 GMT

Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 113

Published: 23rd, April 2025 GMT

113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi.

Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau.

///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko.

A cikin shirimmu da ya gabata mun kawo maku yadda Khalifa Uthman ya kori Abuzar Algiffari babban sahabin manzon All…(s) wanda manzon All..(s) ya yabe shi, sannan a cikin wasu  hadisansa (a) yana bayyana cewa Abuzar Algifari yana da sifofin Annabi isa (a), kamar zuhudu da hakuri da rashin yawan magana.

Wanda babu shakka Khalifa Uthman, ko bai ji duka ba, amma tabbas ya ji wasu daga cikinsu, amma ya ajiye wadannan a gefe, ya bada umurni aka kori Abuzar daga Madina, zuwa wani wuri tsakanin Makka da Madina wanda ake kira Rabazah. Inda ba zai ga wani ba, sannan wani ba zai ganshi shi.

Kuma munji sanadiyyar korarsa daga Madina, wanda kuma shi ne, don ya tsawatawa wani bayahude wanda ya musulunta bayan wafatin manzon All..(s), wanda kuma khalifa Umar da Khalifa Uthman suka jawoshi a jiki, ya na bada fatawowi a addini.

Kafin haka Khalifa yayi tambaya, yana cewa: Shin ya halatta mutum ya dauki bashi a cikin baitul mali idan ya samu daga baya ya biya? Sai Ka’abul Akhbar ya ce, yana ganin ba laifi, a nan ne sai Abuzar ya tashi a kansa, yana cewa: ya kai dan yahudawa, kai zaka fada mana addinimmu ne! A nan ne Khalifa Uthman yayi fishi, har daga karshe ya kai ga korarsa daga Madina. Zuwa Rabazah har sai yamu tu. Don haka Khalifa Uthman ya kore babban Sahabin manzon All..(s) Abuzar Algifari daga Madina zuwa wani daji har ya mutu saboda yunwa, saboda wani bayahude da ya musulnunta bayan wafatin manzon All..(s).

A cikin shirimmu na yau zamu fara magana dangane da wani sahabin manzon All..(s) Ammanr dan Yasir, wanda da shi da iyayensa    Sumayya da Yasar suna daga cikin mutane na farko da suka musulunta a Makka, kuma iyayensa sumayya da Yasir sune shahidan na farko a musulunci, ammam zamu ga yadda ya wanye da Khalifa na uku, wato Uthman dan Affan.

Da farko, tun kafin bayyanar musulunci, baban Ammar Yasir da wasu yan uwansa guda biyu sun taho Makka suna neman wani dan’uwansu, sai basu gane shi ba, sai yan’uwan Yasir biyu suka koma Yemen, amma shi yasir baban Ammar (R ) ya zabi zama a Makka, sai ya nemi wanda zai lamunce masa zama a Makka daga cikin manya manya a garin sai أبا حذيفة بن المغيرة،Abu Khuzaifa dan Mughira ya lamunce masa ya zauna a makka, tunda yana daga cikin manya manyan mutanen Makka a lokacin.

Da haka Yasir ya zauna a Makka, sannan bayan wani lokaci Abukhuzaifa dan Mugirah, ya aurarwa Yasir kuyangarsa wacce ake kira Sumayya, sai ba’a dade ba ta haifi Ammar dan Yasar, anan said an Mughira yan yentar da ita. Ba’a dage ba addinin musulunci ya bayyana suka kuma karbi kiran manzon All..(s).

A lokacinda Abujahal da kuma dan Mugira suka sami labara sai suka fara azabtar da su. An ce Abujahal yana daga cikin wadanda suka azabtar da su, kuma shi ne ya daki sumayya mahaifiyar Ammar ya kasheta, don haka sumayya ita shihiya ta farko a Musulunci, sannan Abujahal ya nufi Yasir shi ma ya kasheshi, don haka shi ne shihidi nan a biyu a musulunci. Sanna suka nufi dansu Ammar suka azabtar da shi suka tsorata shi, sannan suka bukaci ya zagi manzon All..(s) ya kuma fita daga musulunci, sai Ammar don tsoro ya zagi manzon All..sannan y ace masu ya fita musulunci. A nan suka suka kyale shi.

Amma yana koka ya je wajen manzon All…ya fada masa abinda ya faru, sai ya ce, idan sun sake cewa ka zageni ka zaga. Yace yayi haka ne don kubutar da ransa daga wadannan kafiran.

Har’ila yau bayan haka ne ayar Alkur’ani a  cikin suratul Annahal aya ta 106 ta sauka ta na tabbatar da Imanin Ammar dan yasir, inda All ..yake cewa.

{ Wanda ya kãfirta da Allah daga bãyan ĩmãninsa, fãce wanda aka tĩlasta masa, alhãli kuwa zũciyarsa tanã natse da ĩmãni kuma wanda ya yi farin ciki da kãfirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma sunã da wata azãba mai girma.} Annahal 106

Kafin iyayensa su kai ga shahada, manzon All..(s) yana wucewa ta inda aka azabtar da su, ba abinda zai iya, don kubutar da su, sai ya ce masu: Ku yi hakuri ya ku yan gidan Yasir, Lalle makomarku aljanna ce. Wani lokacin yakan cewa: Ya Ubangiji ka gafartawa yan gidan Yasir, hakika ya yi….

Har’ila yau wata aya a cikin suratul Zumur ta sauka tana yabon Ammar dan Yasir

{Shin, wanda yake mai tawãli’u sã’õ’in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: “Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?” Mãsu hankali kawai ke yin tunãni.} Azzumur 09.

Sai kuma aya ta 122 a cikin suratul An-aam inda All..T yake cewa:

{ Shin, kuma wanda ya kasance matacce sa’an nan Muka rãyar da shi, kuma Muka sanya wani haske dõminsa, yanã tafiya da shi, yanã zama kamar wanda misãlinsa yanã cikin duffai, shĩ kuma ba mai fita ba daga gare su? Kamar wancan ne aka ƙawãta wa kãfirai abin da suka kasance sunã aikatãwa.} Al-Anam 122.

Da kuma aya ta 61 a cikin surara Kassas inda All..T yake cewa

{Shin fa, wanda Muka yi wa wa’adi, wa’adi mai kyau, sa’an nan shĩ mai haɗuwa da shi ne, yanã zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan dãɗi, dãɗin rãyuwar dũniya, sa’an nan shi a Rãnar ¡iyãma yanã daga mãsu shiga wuta?} Al-kassas 61

Zamkhshari ya kawo cikin tafsirinsa kan cewa ta sauka a kan Ammr da walid.  Manzon All..(s) ya himmatu da Ammar saboda irin wahalar da ya sha a farkon musulunci da kuma bayan wafatinsa, saboda kuma ikhlasin da ga All..da manzonsa (s) da ya  gani. Yakan daukaka sha’aninsa, yana kuma fifitashi a kan wasu a wurare da dama.

Wata rana manzon All..(s) ya ga Khilid dan Walid yana daga murya yana tsawatwa Ammar dan yasir, Sai yace: Wanda yayi adawa da Ammar All..kayi adawa da shi, wanda wanda yayi fushi da Ammar All..kayi fushi da shi. Kamar yadda yazo cikin Musnat Ahmad Jz 4  shafi 89.

A wani hadisin yana cewa: Ba za’a taba bawa Ammar zabi ba, sai ya zabi mafi alkhairi. Sannan a wani hadisin yana cewa: Menen matsalarsu da Ammar ne yana kiransu  zuwa Aljanna suna kiransa zuwa wuta. Da wasu hadisan da dama dangane da falalar Ammar dan Yasir, da kuma matsayinsa a wajen manzon All..(s).  

Har’ila yau a lokacin da ake gida masallacin manzon All…(s) bayan hijira kowa na daukar ‘tubali daya daya, amma Ammar yana daukar tubali biyu biyu yana cewa : Mu musulmi muna gina masallatai.

Sannan a yakin Khandik ko gwaloli, Ammar ya kasashen baya kakada kasa daga jikinsa, don neman al-barkan wannan kasar wanda ya fadi a kan rigarsa. Halin Ammar dan yasir Kenan a tsawon rayuwar manzon All..(s), amma bayan wafatin manzon All..(s), ya luzumci Aliyu dan Abitalib (a) duk abinda yayi shi zaiyi, don haka ne yaki bai’a wa Khalifa Abubakar bayana manzon All..(s) a matsayin Khalifa, a lokacinda Aliyu (a) yaki yi masa bai’a.

Don haka ammar baya ganin wani daga cikin sahabban manzon All..(s) ya cancanci khalifanci in banda Aliyu dan Abitalib (a). saboda haka ne ya tsaya a gefen Aliyu (a) yana kafawa Khalifa Abubakar Hujja kan rashin cancantarsa, da kuma cancantar Aliyu (a) da Khalifanci.

A cikin shirye-shiryemmu na baya mun bayyana yadda Ammar dan yasir ya luzimci Aliyu (a) ya kuma yi fana’ii cikin sonsa da kuma luzumtarsa.

Amma a lokacinda al-amura suka koma hannun Khalifa Uthman, ya kuma sauya hanya, Ammar ya tsaya a gabansa, ya yi inkarin abubuwa da dama da Uthman ya aikata, a wurare da dama , daga cikinsu.

01-A lokacinda ya dauki karamin akwatin kayakin kawa da mata wa kansa, ya bawa matansa suka kawata kansu da abubuwan kawa da ke cikinsa, Imam Ali (a) yayi masa magana, ya kuma fada masa hakan bai dace ba, hakama Ammar ya bishi ya goyi bayan Amirul muminin (a).

Sai dai Khalifa bai bar shi ba, yana cewa: Ni zakayi inkari kan abinda nake yi ya kao dan…kaza..kaza…(ya zageshi). Sai ya umurci jami’an tsaronsa su kamashi su zo da shi a gabansa. Sai suka bi Ammar suka kamashi da karfi suka zo dashi gaban Khalifa, ya dake shi da kafarsa har da ya suma, sai aka dauko shi aka kaishi gidan Ummu salma matar manzon All..(s), Ammar bai farka ba, har kusan tsakiyar dare, sallolin azahar da la’asar da magariba duk sun kubuce masa. Sai ya tashi yayi Alwala yayi sallar Isha’ii. Sai an jishi yana fada: Godiya ta tabbata ga All.., ba yau ne aka fara cutar da mu a kan tafarkin All..ba.

Sannan A’isha matar manzon All..(s) ta yi fushi saboda abinda Uthman yayiwa Ammar dan Yasir, sai ta fito da gashi da da wasu kayan sawa da kuma takalma na manzon All..(s) da suke wajenta, tana cewa: Ga gashi da kaya da kuma takalman manzon All..(s) basu tsofa ba, amma ku kunyi sauran barin sunnarsa(s). A lokacinda Uthman ya ji abinda ta yi sai ya rikici, ya rasa abinda zai yi na shafe kurakuransa kan Ammar.

02-Wata rana manya-manya sahabban manzon All..(s) sun rubutawa Khalifa Uthman gargadi na cewa ya bar sunnar manzon All..(s) kuma lallai ya dawo kanta, suka rubuta sunayensu daga cikin har da Ammar dan Yasir, kuma shi ne ya kaiwa Uthman takardan Nasihar.  A lokacinda Khalifa Uthman ya karanta, ya yi fushi, yana fadawa Ammar: Wai sai kai kadai ne daga cikinsu zai gabatar mani da wannan nasihar ne?

Sai Ammar yace: don ni na fisu yi maka nasiha. Sai Uthman yace ka yi kariya ya kai dan Sumayya. Sai Ammar yace: Lalle ni dan Sumayya kuma dan Yasir ne. Sai yasa yaransa suka rike kafafi da hannayen Ammr, Uthman ya dake shi da kafafuwansa da suke cikin huffi, a kan gabansa har sai da ya suma.

03-A lokacinda Khalifa ya kori Abuzar Algifari zuwa Rabzata, har yanwa ta kashe shi, sai labarin wafatinsa ya zo madina, sai Khalifa Uthman ya ce, All..ya jikansa, sai Ammar yana wajen, sai yace: Ee All..ya jikansa ya jikammu gaba daya.

Sai Khalifa ya zagi Ammar, sai yace masa kana ganin na yi nadamar kan korarsa daga Madina ne?

Sannan ya umurci yaransa su fidda Ammar daga wajen, sannan ya bada umurni, shi ma a kore shi zuwa rabaza, inda Abuzar ya yi wafati.

Ma’aikatansa sun fara shirin korar Ammar daga Madina zuwa Rabazh, sai dangin Banu Makhzum suka bukaci magana da Khalifa dangane da shi. Sai suka shiga wajensa tare da Amirul muminina Aliyu dan Abitalib (a).

Inda yace mas. Ka ji tsoron All..! Lalle ka kori mutum bawan All…daga cikin musulmi yam utu saboda korarsa da kayi, Sannan a yanzun kana son ka sake korar wani mai kama da shi ?  sai Khalifa Uthman yayi fushi, ya ce: Ai kan kafi cancanta in kora daga Madina. Sai Imam ya ce masa. Ka gwada ka gani.

Amma sai muhajirun da dama suka taro suka yiwa Khalifa magana, mai tsanani har suka samu yi amice yiwa Ammar Afwa, sannan aka dakatar da korar.

Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu nay au sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu. Wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: Khalifa Uthman ya Ammar dan Yasir Ammar dan yasir masu sauraro

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe

Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.

 

Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.

 

Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.

 

A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan ya taimaka wajen hana barkewar rikici a yankin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamna Inuwa Ya Bayar Da Gudunmawar Naira Miliyan 10 Ga Iyalan Wadanda Hatsarin Ista Ya Rutsa Da Su A Gombe
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 112
  • Sharhin Bayan labarai: Rage Kasafin Kudin Ma’ailatar harkokin wajen Amurka da tasirinsa
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Alhassan (a) 112
  • Fafaroma Francis ya Rasu
  • Yadda ma’aikatan gidan ruwa 4 suka mutu a Bauchi
  • Gaza : Red Crescent ta yi watsi da rahoton Isra’ila kan kisan da aka yi wa jami’an agaji
  • Bikin Easter : Paparoma Francis ya yi kira da a tsagaita wuta a Gaza
  • Ambaliya ta kashe mutum 3 ta lalata hekta 10,000 na shinkafa a Neja