2025-04-23@19:30:50 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1223

«Ammar dan Yasir»:

    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.   Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.   A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya.   Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da umurni a kwanan baya kan aikin inganta hadin gwiwar jama’a da sojan kasar, inda ya ce, nagartacciyar hulda mai karfi tsakanin jama’a da soja fifiko ne da bangaren siyasar Sin ya jima da shi. Ya ce ya kamata a tsaya tsayin daka kan jagorancin ra’ayin gurguzu mai salon musamman na kasar Sin a sabon zamani, kuma a nace ga jagorantar jam’iyyar JKS a dukkanin fannoni, da zurfafa yin kwaskwarima, da kirkire-kirkire, da ma kyautata tsare-tsare da manufofi, har da raya aikin inganta hadin gwiwar jama’a da soja.   An kira taron rada sunan birane ko gundumomi dake taka rawar gani a wannan bangare a yau Laraba a nan birnin Beijing. Inda...
    Gwamnatin Shugaban kasa John Mahama ta tsige Gertrude Torkornoo daga mukaminta na babbar mai shari’ar kasar, bisa wasu zarge-zarge da ake yi mata, domin bayar da damar gudanar da bincike. Matakin da gwamnatin ta dauka na tsige babbar mai shari’ar ya jawo cece-kuce a tsakanin mutanen kasar. Tsohon mai shigar da kara na kasar Godfrred Yeboah Dame ya yi tir da matakin na gwamnati da ya siffata da farmaki mafi girma akan ma’aikatar shari’a a tarihin kasar.”  Ita kuwa jam’iyyar hamayya ta zargi shugaban kasa da tsoma baki a harkokin shari’ar kasar, domin nada alkalan da za su  zama masu biyayya ga jam’iyyar da take Mulki ta ( NDC). Torkornoo da ta hau mukamin nata a 2023, kuma  ta kasance...
    Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An  fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
    Matsalar tsaro ta kara tabarbare a jihohin Filato da Benuwai, inda rahotanni ke cewa, wasu da ake zargin makiyaya ne daga kasashen waje ne ke kai hare-haren kashe rayuka da kuma raba al’umma da matsugunansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Garuruwan da aka fi tsananta wa harajin sun haɗa da Gijinzama da aka tilasta musu biyan Naira miliyan 8.5, Dakolo da aka karɓi Naira miliyan 5 da buhun wake 20, sai Kibari da Kunchin Kalgo da suka biya Naira miliyan 20, Sungawa da Naira miliyan 15, da kuma Yalwa da aka tilasta su biyan Naira miliyan 2.7. Bayan rasuwar Isuhu Yellow, wani ƙasurgumin jagoran ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide ya sa harajin Naira miliyan 100 a kan ƙauyuka 23 da ke ƙaramar hukumar Tsafe. A ƙarshen makon da ya gabata kuma, mazauna ƙauyen Dankurmi a ƙaramar hukumar Maru sun fuskanci sabon harajin Naira miliyan 60. Wani mazaunin ƙauyen Dan Jibga, Muhammad Dogo, ya bayyana cewa bayan kashe mutane biyu...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
    Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
    “Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani. Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi. Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya roƙi matasa da su zauna lafiya kuma su riƙa kai rahoton duk wani abu na barazana ga jami’an tsaro, domin nemo mafita game da hare-haren da ke ci gaba da faruwa. Garba Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da makiyayan shida ke kiwo. “Da maharan suka fara harbi, ɗaya daga cikin makiyayan da ya tsira ne ya kira ya ba mu labari. Ina samun labarin, na garzaya wani shingen sojoji da ke Latiya, inda na kai rahoto. Daga nan jami’an tsaro tare da ni muka tafi wajen, mun tarar da shanun da tumakin da aka kashe,” in ji shi. Shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) da GAFDAN a jihar, Ibrahim Babayo da...
    ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila. Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila. Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP),...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025. Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025. A...
    A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’ar ta ce, “Shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar na da inganci kuma masu gamsarwa ne, don haka kotun ta samu wanda ake tuhuma da laifi kuma ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.”   A cewar mai gabatar da kara a karkashin jagorancin Lamido Abba-Sorondinki, lamarin ya faru ne a ranar 7 ga watan Janairu, 2023, a unguwar Rijiyar Zaki da ke Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga nan sai Geng Shuang ya bayyana matsayar kasar Sin don gane da hakan, yana mai cewa, kasar na matukar jajantawa al’ummun Haitian bisa halin da suka shiga. Yana mai kira ga daukacin al’ummun duniya da su ci gaba da taimakawa kasar wajen karfafa tsare-tsarenta na ikon gina kai, da rungumar tafarkin neman ‘yancin kai, da dogaro da kai, da gaggauta hawa turbar neman ci gaba na kashin kai. Yayin da hakan ke wakana, Sin za ta ci gaba da taka rawar gani tare da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki na kasar ta Haiti. (Mai fassara: Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
    A jawabin Gwamna Zulum wajen kaddamar da aikin titin, ya ce, “A ci gaba da tsarinmu na sabunta birane, a yau mun kaddamar da gina titi mai tsawon kilomita 7.1 daga tashar borno Express zuwa Molai, hadi da karin ginin gadar sama ta hudu.   “Abin da muke da burin aiwatar wa, shi ne ba don kawai kyawawan ayyuka ba, har ma don daukar nauyin ci gaban al’ummar Maiduguri, kuma ya zama dole mu fadada birnin Maiduguri.”   Gwamna Zulum ya yi kira ga yan kwangilar su tabbatar da bin ka’idojin inganci da kuma kammala aikin a cikin lokacin da aka kayyade.   “Za a kammala aikin cikin watanni goma, an bayar da kwangilar kan naira biliyan 16, kuma mun...
    A yayin ziyarar, mataimakin shugaban kamfanin LEADERSHIP Mike Okpere, ya bayyanawa uwargidan shugaban kasa irin ayyukan agaji da Kamfanin LEADERSHIP ke gudanarwa tare da yin fatan hada hannu da shirin tallafin fata na gari ‘Renewed Hope Initiative (RHI)’ da nufin karfafawa mutane 1,000 da ayyukan yi.   A cewar Okpere, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da sana’o’in dogaro da kai a sassa daban-daban na tattalin arziki da suka hada da rini, kamun kifi, dinki da dai sauransu.   Ya yi nuni da cewa, manufar ita ce a taimaka wa daidaikun mutane su samu ‘yancin cin gashin kansu da kuma zama masu amfani a cikin al’umma.   Uwargidan shugaban kasar, wacce ta yi marhabin da shirin tallafin, ta...
      Iyalan Alhaji Surajo Ilyasu Malumfashi (RADIO NIGERIA KADUNA) dana Alhaji Idris Ahmed Accama na farin cikin sanar da bikin aure na ‘ya’yansu, Muhammad Auwal Idris da Zainab Surajo Malumfashi. Za’a gudanar da bikin auren ranar Asabar, 3 ga Mayu, 2025, a Masallacin Juma’a na Dan Fodio, Dake Anguwan Sunusi, Jihar Kaduna. Za a daura auren da misalin karfe 11:00 na safe, sannan ana sa ran ci gaba da liyafa kai tsaye bayan kammala daurin auren. Iyalan suna gayyatar dangi, abokan arziki da duk masu fatan alkhairi su halarta tare da murnar wannan babban biki, wanda ke nuna sabon babi a rayuwar amarya da ango. Surajo Ilyasu Malumfashi
    Sai dai a hakika, ba dole ne kasar Lesotho, da sauran kasashen Afirka su mika wuya ga kasar Amurka, don ta ci zalinsu yadda ta ga dama ba. Kamar yadda Charles Olunaiju, wani masanin kasar Najeriya, ya rubuta a cikin wata makalarsa da jaridar Vanguard ta wallafa, kasar Amurka ba za ta samu biyan bukata a yakin ciniki da ta tayar ba, saboda dunkulewar duniya sakamakon dimbin cinikin da ake yi tsakanin kasashe daban daban, da hadewar sassan duniya da cudanyar mabambantan al’adu, wadanda aka samu bisa tushen ci gaban fasahohi, sun haifar da wani yanayi mai armashi da ba za a iya sauya shi ba.   Mista Olunaiju ya kara da cewa, a matsayin wata dabarar tinkarar rikici, kasashen...
    An kama shi ne sakamakon wani mummunan al’amari da ya faru kwanan nan, wanda ya yi sanadin mutuwar wani babban bafadan masarautar, John Ikhamate, lamarin da ya tayar da ƙura da kira na ganin an samu adalci. Gwamna Okpebholo ya tabbatar wa da jama’a cewa gwamnatinsa na da niyyar yaƙar rashin tsaro a faɗin jihar, tare da ɗaukar mataki kan shugabannin al’umma da suka gaza yin abin da ya dace a yankunansu. Ya kuma buƙaci sarakunan gargajiya da su mara wa gwamnatinsa baya wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwa da jami’an tsaro. Gwamnatin jihar ta kuma buƙaci al’ummar Masarautar Uwano da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka yayin da bincike ke gudana kan lamarin kisan. Haka...
    Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun...
    Kungiyar Hamas ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su shirya zanga-zangar nuna goyon baya ga Gaza da kuma kin amincewa da kisan kare dangi Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, ta yi kira ga jami’o’in Yammacin Kogin Jordan da su tashi tsaye wajen gudanar da gangami da zanga-zanga a ranar Talata, domin nuna goyon baya ga Gaza, da tsayin dakanta, da kuma kawo karshen kisan kiyashi. A cewar cibiyar yada labaran Falasdinu, shugaban kungiyar Hamas Abdel Rahman Shadid ya bukaci ‘yan Falasdinu gami da daliban jami’o’in Falasdinu masu ‘yanci a Yammacin Gabar Kogin Jordan da suke mamaye da su da su tashi tsaye tare da gudanar da zanga-zangar bacin rai da aka shirya za a fara a yau...
    Wannan ya kai ga aike ƙorafi zuwa ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. A baya, Shettima ya gargaɗi shugaban hukumar da ka da ya ci gaba da tafiyar da NAHCON tamkar mallakarsa ce shi kaɗai. Sai dai shugaban ya musanta zarge-zargen, inda ya bayyana cewa bai aikata komai ba da ya saɓa wa doka ko tsarin aikin hukumar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A makon da ya gabata, Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya ce gwamnatinsa za ta ɗauki sabbin matakai, ciki har da hana kiwon dare da dawo da ‘yan sintirin sa-kai domin taimakawa wajen samar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wang Yi ya ce, yana son yin aiki tare da Monday Semaya, domin aiwatar da matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da karfafa cudanya da hadin gwiwa a tsakanin sassan biyu, da daukaka zumuncin kawancen Sin da Sudan ta Kudu a bisa manyan tsare-tsare. (Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A daren yau ne shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kammala ziyarar aiki ta makonni uku a Turai, inda ya gudanar da muhawara da manyan jami’an ƙasa da ƙasa don inganta dangantakar Najeriya a fannin tsaro da ci gaban tattalin arziki. Jirgin shugaban ya sauka ne a Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja da misalin ƙarfe 9:50 na daren ranar, inda ya samu tarɓa daga manyan jami’an gwamnati, ciki har da Sakataren Gwamnatin tarayya, Sanata George Akume; Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa, Hon. Femi Gbajabiamila; Mai Ba da Shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu; Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsare, Sanata Atiku Bagudu, da Ministan Birnin Tarayya, Barrister Nyesom Wike. Zuba Jari Daga Kasashen Waje A Noman...
    Shugaban ma’aikatar shari’a ta Iran ya isa kasar China domin halartar taron shugabannin ma’aikatun shari’a na kasashen da suke mambobin kungiyar Shangai karo na 20. Hujjatul-Islami Wal Muslimin Muhsini Eiji wanda shi ne shugaban ma’aikatar shari’a ta jamhuriyar musulunci ta Iran, ya nufi kasar China a yau Litinin domin halartar taron kungiyar Shangai wanda shi ne irinsa karo na 20. Gabanin barinsa filin saukar jiragen sama na “Mehrabad” Eiji ya bayyana muhimmancin yin aiki a tare a tsakanin ma’aikatun shari’a na kasashen mambobin kungiyar Shanghai sannan ya kara da cewa: ” Taron na shugabannin ma’aikatun shari’a karo na 20 na kungiyar Shangai za a yi shi ne a garin Hangatsho, za kuma mu hatarta ne a karkashin bunkasa diflomasiyya ta...
    A yau Litinin shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya fitar da sanarwa ta nuna aljinin rasuwar Papa Roma Farancis,sannan kuma ya mika sakon ta’aziyya ga Mabiya darikar Roman Katolika na duniya. Shugaban kasar ta Iran ya rubuta cewa; Daga cikin matsaya da ta kasance fitacciya wacce Papa Roman ya dauka a lokacin rayuwarsa ita ce ta kalubalantar yadda ake take hakkin bil’adama a duniya, musamman mai dai yadda ya yi Allawadai da kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa a Gaza. Haka nan kuma yadda ya rika yin kira da HKI ta kawo karshen kisan kiyashin da take yi, da kashe mata da kananan yara. Fizishkiyan ya kuma kara da cewa; Wadannan matakan da Papa Roman ya dauka...
      Har ila yau, rahoton ya nuna cewa, yayin da adadin yabanya ke karuwa a cikin gida, kuma karuwar bukatunsu ke raguwa, akwai hasashen raguwar bukatar shigo da nau’o’in amfanin gona cikin kasar daga ketare. (Mai Fassara: Saminu Alhassan)   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Hukumar kula da kasuwannin kasar Sin ta bayyana a yau Litinin cewa, adadin kamfanoni masu zaman kansu a kasar Sin ya zarce miliyan 57 ya zuwa karshen watan Maris, wanda ya kai kaso 92.3 bisa dari na jimillar baki daya. Kazalika, a rubu’i na farko, adadin sabbin kamfanoni masu zaman kansu da aka kafa a kasar ya kai miliyan 1.979, wato karuwar kashi 7.1 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, kuma ya zarce matsakaicin ci gaban da aka samu a shekaru ukun da suka gabata. (Mai Fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wannan amincewar da kammala aikin ginin cibiyar, babban nasara ce wajen inganta harkokin kiwon lafiya, da inganta bayar da kulawa ga lafiyar al’ummar jihar Yobe.   A cikin wannan ziyarar, Gwamna Buni ya sami rakiyar Sanata Musa Mustapha, mai wakiltar Gabashin jihar Yobe, Mai Baiwa Gwamnan shawara kan Ayyuka na Musamman, Hon. Kachallah Mai Hassan, Hon. Abdu Gulani, Mashawarcin Sufuri da Makamashi, da sauran manyan jami’an gwamnati. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen Iran ya tattauna ta hanyar wayar tarho da takwarorinsa na Switzerland da Pakistan Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi wata ganawa ta hanyar wayar tarho guda biyu a yammacin jiya Lahadi tare da ministocin harkokin wajen kasashen Switzerland da Pakistan. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya gana da ministan harkokin wajen kasar Switzerland Ignazio Cassis ta hanyar wayar tarho a yammacin jiya Lahadi, inda suka tattauna kan alakar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan kasa da kasa tare da yin musayar ra’ayi a kansu. A yayin wannan tattaunawa, ministan harkokin wajen na Iran ya bayyana jin dadinsa ga rawar da kasar Switzerland ta taka a shawarwarin nukiliyar kasar cikin...
    Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ya bayyana cewa: Babban abin da suke bukata a duk wata tattaunawa shi ne a dage takunkumi Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Isma’il Baqa’i, ya jaddada cewa babban bukatar Iran a duk wata tattaunawa ita ce a dage takunkumin da aka kakaba mata ta hanyar da za ta kai ga samun sakamako mai ma’ana. Isma’il Baqa’i ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na mako-mako da yake yi a yau litinin cewa: A kwanakin baya ministan harkokin wajen kasar Iran ya ziyarci kasar Rasha, sannan ya gana da ministan harkokin wajen kasar Italiya, a gefen shawarwari ba na kai tsaye ba tsakanin Jamhuriyar Musulunci ta Iran da Amurka. Ya kara da cewa: A...
    Fadan Vatican ta mabiya darikar Katolika ta sanar da mutuwar  Paparoma Francis a yau Fadar Vatican ta bayyana a cikin wata sanarwa ta faifan bidiyo a yau Litinin cewa: Paparoma Francis, shugaban darikar Katolika dan Latin Amurka na farko, ya kawo karshen mulkin da ya yi fama da rikici, rarrabuwar kawuna, da tashin hankali a yayin da yake kokarin kawo sauyi a cibiyoyin majami’u. Cardinal Kevin Farrell ta hanyar gidan talabijin na Fadar Vatican ya shelanta cewa; Ya ku ‘yan uwa maza da mata masu daraja, tare da bakin ciki da alhini, ina sanar da mutuwar Fafaroma Francis”, da karfe 7:35 na safiyar yau (agogon gida), yana mai jaddada cewa: Francis, ya koma gidan mahaifinsa.” Fafaroma Francis yana da shekaru...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A daidai lokacin da ake tunanin samun sauƙi daga tarin matsalolin tsaro da na tada ƙayar baya a Najeriya, sai ga wasu sabbin matsalolin na ƙara kunno kai. Yayin da a wannan lokaci ake fuskantar hare-haren da ake zargin na ƙungiyar Boko Haram ne a Arewa maso Gabas, da kuma sabbin kashe-kashe a sassan jihohin Filato da Binuwai, sai kuma ga wata sabuwar ƙungiya da ake zargin ta ’yan ta’adda ce mai suna Mahmuda ta ɓulla a Jihar Kwara. To ko mene ne ya haddasa wannan koma-baya ta fuskar tsaro? Shin a ganinku, me ya sa matsalar tsaro “ta gagari gwamnatin” Najeriya? NAJERIYA A YAU: Sabbin dabarun hana matasa aikata laifi DAGA LARABA:...
    Ma’aikatan Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Bauchi guda huɗu sun rasu a yayin da suke aikin tsabtace madatsar ruwa ta Gubi. Wasu jami’ai da ke aiki a Madatsar Ruwa ta Gubi, sun bayyana cewa daga cikin mamatan har da wani uba da dansa da kuma wani wanda ke shirye-shiryen ɗaurin aurensa. “Abin ya faru ne a lokacin da suke aikin tsaftace ruwan da ake kula da ruwan da ake yi wa babban birnin Bauchi. Na samu labarin suna cikin tafki, sai suka ga wasu kifaye a cikin ruwan datti, ɗaya daga cikinsu yana ƙoƙarin kama kifi, kifin ya yi zurfi, sai ya bi shi ya mutu. “Ana cikin haka, wani abokin aikinsa da ya ga abin da ya...
    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Leicester City dake buga babbar gasar Firimiya ta kasar Ingila ta koma gasar yan dagaji ta Championship bayan da tayi rashin nasara a guda a wasanta da Liverpool. Leicester wadda ta lashe gasar Firimiya a shekarar 2016 ta samu maki 18 kacal a wasanni 33 da ta buga, ta zura kwallaye 27 yayinda aka zura mata kwallaye 73 a ragarta, Leicester ta koma gasar Championship duk da cewar akwai sauran wasanni 5 da su ka rage ba a buga ba a gasar Firimiya ta bana. Yaushe Liverpool Za Ta Lashe Gasar Firimiyar Ingila? Salah Ya Kafa Tarihi Yayin Da Liverpool Ke Dab Da Lashe Gasar Firimiya Kocin Leicester Ruud Van Nistelrooy ya karbi ragamar horarwar...
    Shugaban kungiyar Asa’ib Ahl-Al-Hak, kungiya mai yaki da yan ta’adda a kasar Iraki, ya bayyana cewa idan shugaban kasar Siriya mai ci Abu Muhammad Al-Jolani ya kuskura ya taka kasar Iraki ana iya tsare shi sabuda gwamnatin kasar Iraki tana da sammashin kama shit un da dadewa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto shugaban kungiyar Qais Al-khazali yana fadar haka a shafinsa na X a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa jita jitan da yake ji na cewa shugaban kasar ta siriya zai zo iraki a nan gaba, bai taso ba, lokacin zuwansa kasar Iraki bai yi ba saboda zarge-zargen da ake masa tun kafin ya kwace shugabancin kasar ta Siriya, akwai matsalolin doka sosai wadanda...
    Gwamnaton kasar Kongo Democradiyya ta bada sanarwan haramta jam’iyyar Josept Kabila tsohon shugaban kasar. Shafin yanar gizo na labarai, Africa News ya nakalto ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar tana bada wannan sanarwan. Labarin ya kara da cewa, Josept Kabila ya shugabanci kasar ta kwango har zuwa shekara ta 2019, karkashin Jam’iyyarsa ta ‘the People’s Party for Reconstruction and Democracy (PPRD). Daga baya Kabila ya dorawa kansa gudun hijira zuwa kasashen waje a shekara ta 2023. Bai kuma sake dawowa ba sai ranar jummar da ta gabata. Kabila dan shekara 53 a duniya, ya shigo kasar kongo daga kasar Rwanda, sannan ya je ya gana da shuwagabannin kungiyar M23 a birnin Goma, inda daga nan suke ikonsu a kan yankunan...
    Mutum ɗaya ya rasu yayin da matasan gari suka yi taho mu gama da ‘yan bindiga lokacin kai hari garin Kware a Jihar Sokoto a daren Asabar. Shaidu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin Kware, cibiyar ƙaramar hukumar Kware, da nufin aikata fashi. Mamba na ƙungiyar masu samar da tsaro ta cikin gari, Bello Mai Maciji, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun samu nasarar satar wani adadin kudi daga hannun Dan Balgore, wani sanannen mai kasuwanci a yankin. Gwamnatin Sakkwato Ta Siyawa ‘Yan Gudun Hijira Gidan Miliyan 100 ‘Yan Bindiga A Ƙarƙashin Jagorancin Turji Sun Kashe Manoma 12 A Sokoto Mai Maciji ya bayyana cewa, ‘yan fashin sun bayyana cewa suna da masaniya game da kuɗin kasuwancin...
    Ya kuma ce, kasar Sin tana adawa da duk wani nau’i na yakin karin haraji ko yakin kasuwanci. Kuma wannan ba wai don kare muradu da martabar kasar Sin ba ce kawai, har ma da kare tsarin tattalin arziki da cinikayya na kasa da kasa, tare da tabbatar da daidaito da adalci.   A cewarsa, “Idan har wata kasa ta dage kan kakaba mana yakin haraji ko kuma yakin kasuwanci, to tabbas za mu yi gaba-da-gaba da ita ba tare da tsoro ba, kuma tabbas za mu dauki kwararan matakan mayar da martani.”(Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
      A shekaru 70 da suka wuce, kasashen yamma sun yi wa taron Bandung kallon taro na kasashe matalauta, amma kuma ga irin yadda ya haifar da kyakkyawan sakamako ga mikewar kasashen. A zamanin yau, lokacin da kasar Amurka ke ta kara kakaba harajin kwastam a kan sauran kasashen duniya, muna farin cikin ganin yadda kasashe masu tasowa ke hada kansu, da rike tsaronsu da ci gabansu a hannunsu, suna kuma rungumar akidun zaman lafiya da hadin gwiwa da bude kofa don tinkarar yadda kasashe masu karfi ke neman cin zalin kasashe masu karamin karfi da ma rashin tabbas da ake fuskanta a duniya. Yau da muke waiwayen taron Bandung, za mu gano cewa, ko-ba-dade-ko-ba-jima za mu ga bayan nuna...
    Kididdigar da hukumar kula da harkokin makamashi ta kasar Sin ta fitar a yau Lahadi ta yi nuni da cewa, zuwa karshen watan Maris din shekarar da muke ciki, yawan wutar lantarki da kasar Sin ke iya samarwa ya kai kilowatt biliyan 3.43, adadin da ya karu da kaso 14.6 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara.   Daga cikin wutar lantarkin da ake samarwa, yawan wutar lantarki da ake iya samarwa bisa makamashin hasken rana ya kai kilowatt miliyan 950, adadin da ya karu da kaso 43.4 bisa dari idan aka kwatanta da na makamancin lokacin bara. Kazalika, a sa’i daya kuma, yawan wutar lantarki da kasar ke iya samarwa bisa karfin iska ya kai...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Tattaunawa da Amurka an yi ta ne cikin yanayi mai inganci da hangen nesa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya bayyana tattaunawar da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, wadda Oman ta shiga tsakani a birnin Roma na kasar Italiya, da cewa an gudanar da shi cikin yanayi mai ma’ana da hangen nesa. A cikin wata sanarwa bayan tattaunawar, Araqchi ya yi nazari kan yanayin tattaunawar, inda ya bayyana cewa: “Sun gudanar da shawarwari na tsawon sa’o’i hudu a ci gaba da zaman da aka yi a baya, kuma sun samu kyakkyawar fahimta kan ka’idoji da manufofi da dama.” Ya ci gaba da cewa: An amince da a ci...
    Mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Masu sasantawa Iran a birnin Roma suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu Ali Shamkhani mai ba da shawara ga Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi nuni da cewa: Masu gudanar da shawarwari na Iran sun tafi birnin Roma ne domin yin shawarwari karo na biyu da Amurka kan batun makamashin nukiliyar kasar Iran. Ya ce masu yin shawarwari na Iran suna da cikakken ikon gabatar da shawara kan matsayin kasarsu. Shamkhani ya yi nuni da cewa: Masu shiga tsakani na Iran suna neman cimma cikakkiyar yarjejeniya bisa ka’idoji guda tara: tsanani, samar da lamuni, dage takunkumi, yin watsi da tsarin Libya/UAE, kaucewa...
      Kasar Sin tana kara bude kofa ga kasashen waje, don haka masu zuba jari na kasashen waje za su gane wa idonsu irin damammakin da aka samar. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Labarin harin na zuwa ne kwana daya kafin cika shekara biyu da fara yakin basasar na Sudan tsakanin RSF da rundunar sojin kasar. Da yake magana da BBC a safiyar Lahadi, wani mazaunin Zamzam da ke aiki da wata cibiyar da ke tallafa wa mutane da abinci ya ce an kashe “matasa da yawa”. “An kashe masu aiki a cibiyar, haka ma an kashe likitocin da ke aikin kula da lafiya a cibiyar,” a cewar Mustafa mai shekara 34 cikin wani sakon murya ta WhatsApp. “An kashe kawuna da dan dan’uwana. An raunata mutane kuma babu magani ko asibitin da zai kula da su – suna mutuwa saboda zubar jini. “Har yanzu ana ci gaba kawo hari, kuma muna tunanin...
    Hyda ta bude kungiyar kwallon kafa ta ‘Breakthrough Football Academy’ a Kano watanni shida da suka gabata inda take da burin bai wa Kanawa dama su shiga duniyar wasanni inda a hirarta ta sashin Hausa na BBC ta ce ta zama kociya ce saboda tunanin da take da shi na taimakon al’ummar Kano bisa la’akari da irin taimakon da al’ummar Kano suka yi mata itama. Ta ce “Babban burina shi ne samun wasu daga cikin wadanda nake bai wa horo sun yi fice a duniyar kwallo.” Ta kuma kara da cewa wani karin burin nata shi ne a samu babbar kungiyar wasa ta mata zalla a Kano “Domin a Kano akwai matan da suka iya kwallon kafa amma saboda rashin...
    Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa sojansu daya ya halaka a Gaza yayin da wasu 4 su ka jikkata bayan da aka kai wa motar da take dauke da su mai sulke hari. Majiyar ta kuma ce ana ci gaba da yin fada mai tsanani a tsakanin sojojin Isra’ilan da kuma ‘yan gwagwarmaya a yankunan daban-daban na zirin Gaza. Majiyar Falasdinawa ta ce; ‘yan gwgawarmaya sun tarwatsa wata tankar yakin HKI ta hanyar tashin wani bom da aka ajiye a kan hanya. An ga jiragen yakin HKI masu saukar angulu suna jigilar daukar wadanda su ka jikkata sanadiyyar harin. A gefe daya, Falasdinawa da dama sun yi shahada a wasu hare-hare da ‘yan sahayoniya su ka kai akan yankin...
    An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    An kuma buƙaci a ci gaba da siyasa cikin fahimta da girmama juna domin amfanin Jihar Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yayin wannan ziyara har ila yau, shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, yakin cinikayya zai gurgunta tsarin cinikayyar kasa da kasa, da haifar da mummunan tasiri a kan tattalin arzikin duniya, da tarnake halaltacciyar moriyar kasashen duniya, musamman ma ta kasashe masu tasowa.   Sai dai kuma, yayin da ake fuskantar karuwar masu nuna ra’ayin kariyar ciniki a duniya, kasar Sin za ta tsaya kan kokarin tabbatar da ci gaban tattalin arziki, kuma za ta ci gaba da samar da dimbin gudummawa ga yunkurin raya tattalin arzikin duniya, in ji shugaban kasar Sin. (Bello Wang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Masu iya magana kan ce, banza ba ta kai zomo kasuwa. Mai yiwuwa hakan ne ya sa matasan da ake zargi da aikata manyan laifuffuka shiga ofishin ’yan sanda, su kuma fita ba tare da wani ya harare su ba, balle ya kama su. ’Yan sandan dai sun ce wannan wata dabara ce ta yakar aikata manyan laifuka irin su sata da fashi da makami da ƙwacen waya da fyaɗe kai har ma da satar mutane domin karɓar kuɗin fansa a tsakanin matasa. NAJERIYA A YAU: Ainihin Abin Da Ke Hana Matan Arewa Koyon Ilimin Kimiyya DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Ko yaya wannan dabara take aiki?...
    Gwoza dai tana daga cikin wuraren da Boko Haram suka mamaye a baya kafin sojoji su ƙwato ta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
     Sojojin Sudan sun sanar da kashe mayakan dakarun kai daukin gaggawa 70, ciki har da kwamandojin mayakan a birnin a El Fasher fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa A ranar Alhamis ne rundunar sojin Sudan ta sanar da kashe mayakan da jami’an dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces fiye da 70 da suka hada da kwamandojin ‘yan tawaye a shiyar kudu maso gabas da arewa maso gabashin El Fasher. Kamfanin dillancin labaran Sudan (SUNA) ya watsa rahoton cewa: A ranar Alhamis ne sojojin kasar Sudan tare da hadin da tallafin dakarun hadin gwiwa na kungiyoyin fafutuka, da hukumar leken asiri ta kasar da ‘yan sanda, suka dakile wani mummunan hari da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support...
    Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta yi nasarar kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su, a wani samame da ta gudanar cikin gaggawa tare da tabbatar da ganin an dawo da zaman lafiya da tsaro a fadin jihar.   A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Yazid Abubakar ya fitar, ya ce a ranar 16 ga Afrilu, 2025, da misalin karfe 1:45 na rana, tawagar hadin guiwa da ta kunshi jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an kare hakkin jama’a (CPG) suna sintiri a kan babbar hanyar Anka-Gummi, inda suka gano wata mota samfurin Peugeot 206 da suka yi garkuwa da su a gefen hanya.   A cewar sanarwar, ba tare...
    Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya bukaci Kiristoci da su yi tunani a kan darussa, muhimmaci, da kuma kyawawan dabi’u na makon Easter.   Gwamna AbdulRazaq a wani sako da ya aike a Ilorin, ya taya mabiya addinin kirista a jihar da ma fadin Najeriya murnar bikin Easter.   Gwamnan ya ce nasarar da Yesu Kiristi ya samu a fuskantar wahala, wanda bikin Ista ke alamta, ya kamata ya fitar da imani ga Allah da kuma yuwuwar da ba su da iyaka da ke zuwa tare da samun bangaskiya mara girgiza cikin ikonsa.   Ya yi addu’ar Allah ya sa lokacin Easter ya kawo farin ciki da jin daɗi mara iyaka ga kowane gida a jihar da kuma bayansa  ...
    Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Barr. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya mika sakon taya murna ga al’ummar kiristoci a jihar da ma sauran sassan jihar bisa nasarar kammala azumin Easter na kwanaki 40.   A madadin shugabanni da membobin majalisar ta 10, shugaban majalisar ya yaba wa mabiya addinin kirista saboda sadaukarwar da suka yi da kuma ci gaban ruhaniya a wannan lokaci mai tsarki.   Duk da haka ya yaba musu bisa sadaukarwar da suka yi a wannan lokacin kuma fatan sabunta ruhi da aka samu a lokacin Azumi ya kawo zaman lafiya, farin ciki, da wadata ga kowa.   Barr AbdulMalik Sarkin Daji, ya amince da muhimmiyar rawar da shugabannin addinin Kirista ke takawa wajen jagorantar al’ummar Nijar cewa majalisar...
    Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa za ta gudanar da atisayen harbe-harbe ga sabbin ‘yan sanda a karamar hukumar Birnin Kudu ta jihar Jigawa.   Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa, Ahmad Tijjani Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a Dutse babban birnin jihar.   Ya ce, atisayen zai fara ne daga ranar 19 ga Afrilu zuwa 11 ga Mayu 2025 a kauyen Tsohon Kafi da ke Birnin Kudu.   A cewarsa, makasudin bayar da horon shi ne don inganta shirye-shiryen gudanar da aiki, da dabarun sarrafa makamai, da kuma kwarjinin sabbin jami’an ‘yan sandan da aka dauka, a daidai lokacin da rundunar ‘yan sandan Najeriya ta himmatu wajen tabbatar da kwarewa da...
    Jami’an rundunar ’yan sandan jihar Edo sun ceto ɗalibai 10 da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Edo. An kashe ɗaya daga cikin ’yan bindigan, a yayin musayar wuta da ’yan sanda a lokacin aikin ceto, yayin da sauran suka tsere da raunukan harbi. Daily Trust ta ruwaito cewa an yi garkuwa da ɗaliban ne a ranar 16 ga Afrilu, 2025, a kan hanyarsu ta zuwa Jami’ar Babcock don taron shekara-shekara na GYC Africa. Kakakin rundunar, SP Kontongs Bello, wanda ya tabbatar da ceton, ya ce da samu rahoton sace daliban, kwamishinan ’yan sandan jihar, Funsho Adegboye, ya tura ’yan sanda na musamman tare da ’yan banga da maharba cikin daji domin ceto su da kuma...
    Shugaban ya kuma bai wa masu ruwa da tsaki a fannin cewa, ako da yaushe, kofar Hukumar ta NPA, bode take domin hadaka wacce ta zarce ta gudanar da baje koli. Dakta Dantsoho ya kara da cewa, an samar da tsarin na EPT domin a tabbatar da cewa, ana fitar da kaya zuwa waje, ta hanyar yin amfani da na’urar zamani. “Wannan na zai taimaka matuka wajen kaucewa samun jinkiri da kuma mai-maita aiki da Hukumar ta saba fuskanta a baya,” A cewar Dantsoho. Kazalika, Dantsoho ya bayyana cewa, domin a samu sauki wajen kai kaya a tsakanin masu kananan da matsakaitan sana’oi, musamman duba da cewa, tsarin na EPT, zai taimaka matuka ga guraren da ake adana kaya a...
    Wannan nasarar ta nona irin namijin kokarinda Bankin ya yi na kara habaka samar wa da kansa kudaden shiga duk da matsin tattalin arzikin da kasar nan ke fuskanta. Bugu da kari, kadarorin Bankin sun karu zuwa jimmlar kaso 47 daga Naira tiriliyan 20 a shekarar 2023 zuwa Naira tiriliyan 30, a shekarar 2024. Kazalika, abokan huddar Bankin sun karu zuwa kashi 45, wanda kudaden da suka ajiyarsu ya karu zuwa Naira tiriliyan 22 a shekarar 2024, sabanin yadda ya ke kan Naira tiriliyan 15, a shekarar baya. Duk da samun hauhawan farashin kaya a kasar, Bankin ya samu karin kudaden shigar Bankin, sun karu zuwa kashi 38.9, sabanin kashi 36.1. Bankin na da yakinin samun ribar shiyar da ta...
      Makera, Jihar Kaduna – Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rt. Hon. Yusuf Dahiru Liman, ya halarci bukukuwan Easter tare da al’ummomin Kiristoci na Gundumar Makera, inda ya bukaci su yi amfani da lokacin wajen tabbatar sa saƙon bangaskiya, yabo, da sadaukarwa da ke tattare da bikin. A jawabin da ya gabatar, Hon. Liman ya jaddada muhimmancin bikin Easter a matsayin lokaci na sabunta dogaro da Allah. Ya kuma bukaci mabiya addinin Kirista da su rungumi koyarwar hakuri, kauna, da kuma fifita bukatun wasu akan nasu. Kakakin ya kuma yi kira ga daukacin jama’ar Jihar Kaduna da su ci gaba da bunkasa zaman lafiya da juna ba tare da la’akari da bambancin addini, kabila ko ra’ayin siyasa ba, yana mai...
    Bugu da kari, saboda karancin masu sayen Kwan, musamman sakamakon matsin tattalin arziki da ake fama da shi, ana kara samun masu sayen Kwan don amfani da shi, wanda hakan ya sanya ake ci gaba da samun Kwan da ba a sayar ba. Misali, a makwanni biyu da suka gabata a garin Jos, an samu matukar raguwar farashin Kwan, inda ake sayar da shi kasa da Naira 3,900 zuwa Naira 4,000. Sai dai, a wannan makon an dan samu karin farashin, wanda ya kai daga Naira 4,200 zuwa 4,300. Daya daga cikin irin wadannan masu kiwon Kajin na gidan gona, Muhammad Bello Ibrahim, ya bayyana bacin ransa kan yadda wannan matsala ke ci gaba da faruwa. “Masu sana’ar kiwon Kajin...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kazalika, Injiniya Xie ya kara da cewa, a cikin rubu’in farko na bana, sashen masana’antu na kasar Sin ya taka rawar gani wajen samun ci gaba ba tare da tangarda ba sakamakon ingantuwar tsari da zurfafa ayyuka wajen samar da sabbin ginshikan bunkasa ci gaba mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Duk da cewa Atiku ya dage yayin tattaunawar da ya yi da manema labarai bayan ziyarar cewa ganawar ba ta batun siyasa ba ne, amma jawabin El-Rufai ya nuna karara akwai siyasa a cikin ganawar. Bayan ziyarar ‘yan adawa kwanaki kadan da na gwamnonin APC, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya isa gidan Buhari sa’o’i kadan bayan tawagar Atiku, wanda ya kara tsananta siyasa. Ya kuma ba da tabbaci ga ra’ayin cewa shugabannin jam’iyyar APC sun damu da siyasar tsohon shugaban kasar. Masu lura da al’amura siyasa sun bayyana cewa kalaman da Ganduje ya yi bayan ganawar, ya tabbatar da cewa APC na yin duk mai yiwuwa wajen tabbatar da cewa Buhari ya kasance tare da jam’iyya...
    Waɗanda suka take wa Ministan sawu a tafiyar su ne jagororin hukumomin yaɗa labarai da wayar da kai da ke ƙarƙashin ma’aikatar sa. Ya yi zama daban-daban tare da ƙwararru inda suka tattauna kan yadda za a inganta ƙwarewa da kuma kayan aiki na zamani na kafafen yaɗa labarai na gwamnatin Nijeriya.   Ya ce: “Ina sanar da ku waɗannan abubuwan ne domin jaddada ƙudirin gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ganin an samu cigaba mai ɗorewa a fannin watsa labarai a ƙasar nan.   “Wannan ne ma ya sanya muke gudanar da irin wannan taron bita na ministoci, da kuma shirin ƙaddamar da Taron Tattaunawa da Jama’a a sassan ƙasar nan nan gaba kaɗan.” Idris ya kuma...
    Sojojin kasar Yemen sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan birnin Telaviv da kuma kan jirgin yakin Amurka saboda tallafawa falasdinawa a Gaza, da kuma maida martani kan hare-haren Amurka kan kasar a jiya Alhamis. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar na Yemen Burgediya Janar Yahayah Saree yana fadar haka a yau Jumma’a ya kuma kara da cewa sojojin kasar ta yemen sun cilla makami mai linzami samfurin Zulfikar kan wani sansanin sojojin HKI a kusa da tashar jiragen sama na Bengerion dake birnin Yafa (telaviv. Saree ya kara da cewa sojojin, har’ila yau sun kai wasu hare-hare kan jiragen yaki masu daukar jiragen saman yaki na Amurka Harry Truman da kuma USS...
    Hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kaiwa lardin Hudaida ya karu zuwa 74. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar gwamnmatin kasar ta Yemen na fadar haka a yau Jumma’a ta kuma kara da cewa dukkan mutanen da suka mutu a hare-haren jiragen yakin Amurka a cibiyar man fetur na Ras Isa a birnin Hudaida fararen hula ne. babu wani mayakin kungiyar Ansarulla ko guda a cikinsu. Labarin ya kara da cewa jiragen yakin Amurka wadanda suka taso daga jiragen ruwa masu daukar jiragen sama na Amurka masu suna USS Harru Truman da kuma USS Carl a tekun red sea, sau kai hare kan ras Isa ne har sau biyu, hare na biyun ya fada ne kan...
    Wani mutum mai suna Muhammad Ma’aba daga ƙauyen Fujeregi da ke Ƙaramar hukumar Gbako a Jihar Neja, ya mutu a hannun tsohon mijin matar da yake shirin aura. Rahotanni sun bayyana cewa, wata Ƙungiya ƙarƙashin jagorancin tsohon mijin matar mai suna Alhaji Yikangi, daga ƙauyen Yikangi Chikan ne suka kai wa Ma’aba hari a tsakanin garin Saganuwa da Fujeregi. PDP ba ta shirya yin zaɓen 2027 ba – Wike Benuwe: Har yanzu ba a gano wasu mutanen ƙauyuka ba – Gwamna Alia Mazauna garin sun shaida wa Daily Trust cewa, tsohon mijin ya saki matar mai suna Fatima Suleiman sau uku, amma ya dage cewa ba za ta ƙara aure ba — ko da ta samu sabon mai neman aurenta....
    A cikin dan kankanin lokacin da wannan hukuma ta fara aiki, ta horar da matasa sama da 100,000 horo kan shirye-shiryen koyon sana’o’i daban-daban a fannonin noma, ICT, kananan sana’o’i da dai sauran su, gwamnatin jihar ta bayar da tallafi da jarin sama da Naira biliyan 1.7 ga wadannan matasa domin fara sana’o’i. Har ila yau, ya saukaka wa wadannan matasa rayuwa sa suka cancanta a cikin jihohi da tarayya. Jihar jigawa jiha ce mai girma ta kuma yi fice a fannin noma a kokarin gwamnati na inganta rayuwar al’umma ta hanyar sabbin manufofin noma da ya zama abin a yaba. Domin tabbatar da samar da wadataccen kayan aikin noma akai-akai, gwamnatin jihar ta zuba Naira biliyan 5 ga kamfanin...
    Wasu ’yan ta’adda da ake kyautata zaton ’yan Boko Haram ne sun kai hari a sabuwar unguwar Yamtake da ke Ƙaramar hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji biyu tare da wasu fararen hula da ba a bayyana adadinsu ba. Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun tabbatar da harin, inda suka ce maharan sun mamaye unguwannin ne da misalin ƙarfe 11:15 na daren Alhamis. Gwamnatin Yobe ta sayo hatsi don tunkarar kakar bana Matan da suka tsira daga Boko Haram na buƙatar tallafin musamman Ɗaya daga cikin majiyar sojojin ta ce, kafin a aike da wata tawagar sojoji daga Gwoza, maharan sun riga sun afkawa jama’a  da sansanin sojan Yamtake. “Muna jiran tawagar masu ƙarfafa musu su...
    Ita Jihar Yobe,rashin biyan sabon mafi krancin albashi da tsohon na Naira 30,000 ga Malaman makarantun ta na Firamare da Sakandare, hakan ta kasance ne saboda rashin amincewa tsakanin Kungiyar NUT da kuma Kungiyar ma’aikatan Kananan Hukumomi ta kasa (NULGE). A ma’aikatar ilimin bai daya ta Jihar Abia, bangaren Kungiyar Malaman makaranta NUT, da reshen Kungiyar kwadago ta kasa (NLC), LEADERSHIP ta Lahadi ta gano cewa har yanzu Gwamntin Jihar bata fara biyan mafi karancin albashin ba. An samu tsaikon yin hakan ne saboda niyyar ita gwamnatin ta dauki su Malaman makaranta matsyin kwararru ta cire daga tsarin albashi na ma’aikatan gwamnati,inda za ta fara biyansu da tsarin albashi na Malaman makaranta(TSS). Kamar yadda Shugaban kungiyar kwadago na Jihar NLC,Okoro...
    Jawabin shugaban majalisar, ya biyo bayan dambarwar hankalin al’ummar kasar ne, bayan shelar ranar 18 ga watan Maris da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi na ayyana dokar ta-baci na tsawon wata shida a Jihar Ribas. Matakin ya zo ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari, inda aka dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara tare da rusa majalisar dokokin jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Maimakon ya bai wa babban jami’in nasu kudin ya raba wa mutanensa, sai ya zabi rarraba musu shi da kansa”, kamar yadda wata majiya ta shaida wa wannan jarida. Sai dai, wata majiyar ta shaida wa wakilinmu a ranar Larabar da ta gabata cewa, an gayyaci ‘yansandan ne zuwa babban birnin tarayya Abuja, domin ladabtar da su. An gayyaci jami’in da sauran yaransa zuwa hedikwatar ‘yansanda da ke Abuja, domin daukar matakan ladabtarwa, in ji majiyar. Kamar yadda siginal mai dauke da kwanan wata na ranar Talata 15 ga Afrilun 2025, wadda LEADERSHIP ta samu, ya nuna cewa; ‘yansandan da shugaban tawagarsu, DSP Aliyu Adejembi, za su bayyana a hedikwatar ‘yansan da ke Abuja, domin amsa tambayoyi kan rashin da’a...
    Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta tsakiya Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran da Saudiyya za su iya magance yawancin matsalolin yankin Gabas ta Tsakiya ta hanyar dogaro da karfinsu a hade ba tare da bukatar shiga tsakani daga kasashen waje ba. Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian ya tarbi ministan tsaron kasar Saudiyya Khalid bin Salman a yammacin jiya Alhamis, wanda ke ziyarar aiki a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran dauke da wata babbar tawagarsa. Shugaban na Iran ya jaddada cewa Iran ta kuduri aniyar karfafa alakar ‘yan uwantaka a tsakanin kasashen musulmi. Pezeshkian ta kara da cewa: Saboda wata wasiyya ta...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar ba na kai tsaye ba da Amurka a birnin Roma a ranar Asabar Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya sanar da cewa zai tafi birnin Roma a ranar Asabar domin halartar zagaye na biyu na shawarwari ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai jaddada cewa sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha ya kunshi muhimman batutuwa. A cewar kamfanin dillancin labaran IRNA, Araghchi ya ce: Roma ba ita ce mai masaukin baki ba, a’a, a maimakon haka, wajen da za a yi shawarwarin, gwamnatin Oman ce ta kasance mai daukar nauyin shawarwarin ba na...
    Sojojin mamayar Isra’ila sun sake aiwatar da wani sabon kisan kiyashi kan Falasdinawa 5 a sansanin Jabaliya da ke arewacin Gaza Fararen hula 5 da suka hada da yara biyu da mace daya ne suka yi shahada, wasu kuma suka bace sakamakon harin da rundunar sojin mamayar Isra’ila suka kai kan wani gida a sansanin ‘yan gudun hijira na Tal al-Za’atar da ke gabashin Jabaliya da ke arewacin Zirin Gaza. A cewar majiyoyin yankin, gidan da aka kai harin na dangin Nasiyo ne, kuma yana dauke da ‘yan gudun hijira daga iyalai sama da biyar a cikinsa, inda harin ya turbude su a karkashin baraguzan gine-gine.
    Masu wannan fahimta sun yi imanin cewa duk lokacin da mutum ya ji baya son wani abu to a wurinshi wannan abin ba mai kyau ba ne. Haka nan kuma duk lokacin da mutum ya ji cewa ga wani abu amma shi ne ya kwanta mashi, toh wannan abin shi ne mai kyau. Babban misalin da wadannan masu ra’ayi suke jaddadawa da nanatawa a kullum shi ne cewa a lokacin da mutum ya yi tsammanin cewa wani abu na da kyau a ra’ayinshi, to idan ya je cikin wata al’ummar zai tarar da cewa wannan abin barna ko wani abin ki. Misali da shan giya, caca da sauransu. Da irin wannan nazari ne aka samar da mafi shaharan nazariyyar nan...
    Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Gombe, Bello Yahaya ya bayar da umarnin tura isassun jami’ai a fadin jihar domin samar da isasshen tsaro kafin bukin Easter, da kuma bayan bikin Easter.   Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Buhari Abdullahi ya fitar a Gombe.   A cewarsa, an tura jami’an dabarun dakile hare-hare zuwa muhimman wuraren da suka hada da wuraren ibada, wuraren shakatawa, kasuwanni, da sauran wuraren taruwar jama’a.   Ya kuma ce, kungiyoyin sintiri da jami’an tsaron cikin za su kasance a kasa domin sanya ido kan ayyukan da kuma gaggauta daukar matakin magance duk wata matsala idan ta taso.   Kwamishinan ya lura cewa rundunar...
    Rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai ta yi nasarar aiwatar da wasu hare-hare ta sama guda biyu, inda ta auka wa maboyar ‘yan ta’adda a yankin Sambisa na jihar Borno da kuma Kudancin Tumbun.   A wata sanarwa da Daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame ya fitar, ya ce harin farko ya afku ne da misalin karfe 5:30 na safe a Kollaram- sanannar tungar ‘yan tada kayar baya, a ranar 15 ga watan Afrilu, inda aka kawar da mayaka da dama tare da lalata muhimman ababen more rayuwarsu.   Farmaki na biyu kuwa ya biyo bayan da misalin karfe 3:55 na rana a garin Arra na Sambisa, bayan binciken sirri da bincike...
    Akwai kuma Sanata Adeniyi Adegbonire dan jam’iyyar APC daga mazabar Ondo ta tsakiya, Sanata Seriake Dickson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Bayelsa ta Gabas, Sanata Shehu Lawan Kaka, dan jam’iyyar APC, daga mazabar Borno ta tsakiya. Sauran sun hada da; Sanata Banigo Ipaligo dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Ribas ta Yamma, Sanata Jarigbe Jarigbe dan jami’yyar PDP, daga Koros Riba ta Arewa, Sanata Ekong Sampson dan jami’yyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom ta Kudu, Sanata Sani Bello dan jami’yyarAPC, daga mazabar Neja ta Arewa sai kuma Sanata Aniekan Bassey, dan jam’iyyar PDP, daga mazabar Akwa Ibom. Majalisar ta kafa wannan kwamtin ne, biyo bayan kudurin da Sanata Aniekan Bassey na mazabar Arewa da Gabas daga Akwa Ibom, ya gabatar mata...
    He Yongqian ta kara da cewa, bangaren Sin na fatan kokari tare da bangaren Turai, don kiyaye tsarin cinikayya bisa ra’ayin bangarori daban daban tare da kungiyar WTO a matsayin tushensa da bin ka’idojin cinikayya.   Game da bikin baje kolin kayayyakin shige da fice na kasar Sin karo na 137, wanda aka fi sani da Canton Fair dake gudana, He Yongqian ta ce, ya zuwa yanzu, masu sayayya fiye da dubu 110 daga kasashe da yankuna 216 sun halarci bikin, adadin ya karu da kashi 10 cikin dari bisa na karo na 135. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga...
    Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Fu Cong, ya bayyana a gun taron kwamitin sulhu na MDD game da yankin manyan tabkuna na Afirka a ranar 16 ga wata cewa, sakamakon ci gaba da kai hare-hare na kungiyar M23 a baya-bayan nan, ya ta’azzara yakin gabashin Kongo DRC, kuma daukacin yankin manyan tabkuna sun fada cikin rudani. Dole ne kasashen duniya su yi aiki tare kuma su hada kai don kawar da wannan mummunar yanayin cikin gaggawa.   Fu Cong ya jaddada cewa, dole ne a gaggauta tsagaita bude wuta domin hana shi ci gaba da ruruwa. Babu wata hanyar soji da za ta magance rikicin gabashin Kongo DRC, kuma tattaunawa ta siyasa ita ce kawai mafita. Dole ne...
    Ministan Wutar Lantarki, Adedayo Adelabu ya bayyana cewa kimanin ’yan Najeriya miliyan 150 ne yanzu ke samun isasshiyar wutar lantarki, yayin da miliyan 80 ke da ƙarancin wutar lantarki. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a yayin taron sabunta sassan ministoci na 2025 da aka gudanar a Abuja, inda ya yi magana tare da ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Malagi, da sauran masu ruwa da tsaki. ISWAP sun ruguza gadar Mandafuma a Borno ’Yan bindiga sun sace makiyaya 5, da shanu 1,200 a Kaduna Adelabu ya bayyana cewa ci gaban ya samo asali ne daga shigar Najeriya cikin shirin “Mission 300” – wani gagarumin ƙoƙarin haɗin gwiwa na Bankin Duniya da Bankin Raya Afirka (AfDB)...
    “Na gode Allah, babu wanda ya jikkata, kuma an kai rahoton lamarin ofishin ‘yansanda.” Ofishin yaɗa labaranta ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu, inda ya ce “ƙoƙarinta na kare gaskiya da wakiltar al’ummarta bai kamata a mayar da shi barazana ko tashin hankali ba.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Sakon jagora ga shugaban kasar Rasha yana da alaka da ci gaban kasa da kasa da na yanki Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana hakan ne a yau Alhamis a birnin Moscow na kasar Rasha cewa: Abu ne da ya dace a rubuta sakon da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya aikewa shugaban kasar Rasha dangane da ci gaban kasa da kasa da na yanki da kuma batutuwan da suka shafi kasashen biyu. Araqchi ya bayyana hakan ne a lokacin da ya isa filin tashi da saukar jiragen sama na Vnukovo da ke birnin Moscow a yau, yayin da yake amsa tambayar da wakilin IRNA ya yi masa kan...
    Mutane fiye 300 ne suka mutu a cikin kwanaki a wani kazamin fada a yankin Darfur da ke yammacin kasar Sudan Hukumar kula da ayyukan jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya ta watsa rahoton cewa: Sama da fararen hula 300 ne aka kashe a wani kazamin fada na kwanaki biyu a yankin Darfur na kasar Sudan mai fama da rikici. Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare a ranakun Juma’a da Asabar a kan sansanonin ‘yan gudun hijira biyu da ke fama da matsalar yunwa a arewacin Darfur da kuma babban birnin da ke kusa, inda rahotannin farko suka nuna cewa sama da mutane 100 ne suka mutu, ciki har da yara 20 da ma’aikatan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya bayyana cewa shiga wani yanki da ba a fahimtar yaren juna ɗauke da makamai na iya janyo fargaba da tashin hankali. “Ka yi tunanin idan wasu daga Kudu sun shigo ƙauyanku ɗauke da makamai kuma ba ku fahimtar yaren juna — za ku ji tsoro. Haka nan idan mutanenmu suka shiga yankin Kudu da makamai, su ma za a ji tsoro,” in ji shi. Rurum ya ce zai gana da shugabannin ƙungiyoyin masu farauta a jihar domin daƙile wannan ɗabi’a, ya kuma buƙace su da su nemo hanyar nema wa kansu asiri . “Wasu su tafi farauta su dawo ba tare da sun kamo ko ɓeran daji ba. Bai dace su ci gaba da haka ba. Ya kamata mu...
    Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi kakkausar suka dangane da yawaitar kashe-kashen da ake yi a jihar Filato da sauran sassan Arewacin Nijeriya, inda ya dora laifin kitsa tashe-tashen hankula da nufin tada zaune tsaye a Nijeriya. A wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, Fani-Kayode ya yi ikirarin cewa wadanda ke haddasa tashe-tashen hankula ba wai kawai ’yan tada kayar baya ba ne, a’a, wasu ‘yan kasashen waje ne da ake zargin suna shigowa Nijeriya ta kan iyakokin kasar, da nufin raba kan al’ummar kasar ta hanyar addini da kabilanci. Hadin Gwiwar Kasashen Asiya Da Afirka Na Habaka Karfinsu Na Dogaro Da Kai Da Cin Moriya Tare Yaukaka Zumunci Da Makwabta A Aikace...