Aminiya:
2025-04-24@11:45:53 GMT

Ƙasashen AES sun kafa gidan rediyo don yaƙar farfagandar turawa

Published: 24th, April 2025 GMT

Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso, ƙarƙashin inuwar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES), sun sanar da shirinsu na ƙaddamar da gidan rediyo na haɗin gwiwa.

Ƙasashen guda uku, waɗanda duk a halin yanzu suke ƙarƙashin mulkin soja, sun jaddada cewa sun kafa gidan rediyon ne da nufin daƙile farfagandar ƙasashen waje da kuma isar da “ingantattun bayanai na gaskiya” ga ’yan ƙasarsu.

Sanarwar tasu ta kasance bayan ƙaddamar da gidan talabijin ɗinsu na intanet na haɗin gwiwa da suka yi a watan Disamba na 2024, wanda suka bayyana a matsayin dandamali da aka samar domin “yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”

Baya ga waɗannan ayyukan watsa labarai, a baya ƙungiyar ta nuna sha’awarta ta kafa kamfanin jiragen sama na yankin da kuma bankin saka hannun jari, wanda ya ƙara nuna jajircewarsu ga haɓaka haɗin kai da ci-gaba a tsakanin ƙasashe mambobin AES.

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Amfani Da Kafofin Sada Zumunta Wajen Haɓaka Kasuwanci Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya

A watan Janairu na 2025 ne  ƙasashen uku da suka kafa ƙungiyar ta AES, suka sanar da ficewarsu a hukumance daga Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS).

Makonni uku da suka gabata, ƙasashen da ke ƙarƙashin mulkin sojoji, sun ɗora harajin shigo da kaya na kashi 0.5 bisa ɗari a kan kayayyaki daga ƙasashen ECOWAS.

Harajin ya shafi duk kayayyakin da suka shigo daga ƙasashen ECOWAS zuwa kowace daga cikin ƙasashen uku, banda kayan agajin jin kai.

Wannan tsarin ya yi karo da shirin ECOWAS na tabbatar da zirga-zirgar kayayyaki a tsakanin mambobinta da ƙasashen AES duk da ficewarsu a hukumance daga ƙungiyar a watan Janairu.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ECOWAS haɗin gwiwa Nijar

এছাড়াও পড়ুন:

Hargitsi A Filin Wasan Kwallon Kafa Tsakanin Al-Ahly Tripoli Da Al-Suwaihli A Kasar Libiya

Munanan abubuwan da suka faru na zubar da jini bayan wasa tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli a Libya

A kusa da filin wasa na birnin Tripoli an ga abubuwan na zubar da jini bayan wasan da aka yi tsakanin Al-Ahly Tripoli da Al-Suwaihli, lokacin da wasu motocin ma’aikatar harkokin cikin gida ta gwamnatin hadin kan kasa suka bindige magoya bayanta da gangan.

Shaidun gani da ido sun bayyana cewa bayan an kammala wasan ne wata mota dauke da makamai ta kutsa cikin wurin da jama’a ke cunkoso, inda suka bi ta kan wasu matasa, lamarin da ya haifar da firgici da hargitsi. An kuma ji karar harbe-harbe a wurin, lamarin da ya ta’azzara lamarin tare da jikkata wasu da ke wajen.

Majiyoyin lafiya sun tabbatar da cewa an mayar da wani matashi dan shekara ashirin zuwa wani asibitin da ke kusa da birnin wasanni, inda aka bayyana halin da yake ciki da mawuyaci. Har yanzu ba a fitar da kididdigar adadin wadanda suka jikkata a hukumance ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Congo Da M23 Sun Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Wuta
  • Jirgin Farko Daga Minna Zuwa Abuja Ya Nuna Haɗin Gwiwar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi – Minista
  • Ba ‘Yan Nijeriya Ne Ke Kai Mana Hare-hare A Benuwai Ba – Gwamna Alia
  • Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya
  • CONMEBOL ta buƙaci a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta 2030
  • ECOWAS Zata YI Taro A Ghana Don Tattauna Batun Niger, Mali Da Burkina Faso
  • Hargitsi A Filin Wasan Kwallon Kafa Tsakanin Al-Ahly Tripoli Da Al-Suwaihli A Kasar Libiya
  • Tsakanin Kafa Shingaye Da Gina Gada: Yadda Matakan Amurka Da Sin Suka Bambanta Sosai
  • Abubuwan da suka sa Fafaroma Francis ya yi fice a duniya