2025-04-24@12:05:38 GMT
إجمالي نتائج البحث: 50

«haɗin gwiwa»:

    Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.   Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.   Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed...
    “Amfani da haraji a matsayin makami don matsin lamba da son rai yana nuni da tsarin siyasa na rashin haɗin kai da kare tattalin arziƙi da kuma zambar tattalin arziƙi. Wannan ba abu ne na adalci ba ko mai kyau – yana nufin zaman ‘Amurka da tafi kowa’ da kuma ƙaruwar ƙarfin Amurka,” in ji...
    A cewar Ministan, samun wannan ƙwarewar ya zama wajibi a wannan zamani da kowa da kowa – wato daga masana hulɗa da jama’a zuwa shugabannin kamfanoni – yake taka rawa a matsayin mai magana da yawun wani.   Idris ya ce: “Yau a wannan zamani da kowa ke zama mai magana da yawu – ko...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yanzu haka al’ummar Borno na cikin zullumi sakamakon wasu hare-haren da ake zargin ƙungiyar Boko Haram ce ta kai a wasu sassan jihar. Waɗannan hare-hare dai suna faruwa ne bayan shekaru da dama da iƙirarin hwamnati cewa an yi nasarar nakasa ƙungiyar. Ko mene ne dalilin sake...
    Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi hasashen za a yi ruwan sama mai ƙarfi da ambaliya a jihohi 30 da kuma babban birnin tarayya Abuja. Jihohin da ake fargabar fama da ambaliyar ruwan sun haɗa da: Abia, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross-Riɓer, Delta, Ebonyi, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos,...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da...
    Ya jinjina wa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro da al’umma, yana mai cewa hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen nasarar aikin. Gwamnati ta yaba da ƙwazon jami’an da suka halarci aikin kuma ta sha alwashin ci gaba da yaƙi da ‘yan ta’adda a faɗin jihar. “Za mu ci gaba da fatattakar waɗanda ke barazana ga...
    Ya kuma kara da cewa, binciken farko ya nuna cewa, da sa hannun ma’aikatan hukumar ake tafka wannan aika-aika. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Gwamnatin Jihar Borno ta nuna matuƙar damuwarta kan yadda wasu matasa ke amfani da kafafen sada zumunta na yanar gizo wajen yin kalamai masu nuna barazana da al’adunmu na rashin ɗa’a da rashin sanin ya kamata. A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar yaɗa labarai da tsaron cikin gida ta jihar Borno ƙarƙashin Kwamishinanta Farfesa Usman...
    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewar ya yanke jiki ya faɗi har aka kai shi asibiti a ƙasar waje. Ya ce wannan ƙarya ce da maƙiyansa na siyasa suka ƙirƙira don kawar da hankalin mutane. NAJERIYA A YAU: Dalilan Kamuwa Da Cutar Hawan Jini Da Hanyoyin Magance Ta...
    Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na...
    Ya ce: “Ya ‘yan uwa Musulmi na Jihar Zamfara da ma sauran wurare, ina miƙa saƙon barka da Sallah tare da taya mu murnar kammala azumin shekarar Hijira ta 1446, wannan wata mai alfarma ta kasance lokaci na sadaukarwa ga Allah (SWT).   “Yayin da muke gudanar da bukukuwan Ƙaramar Sallah, ina kira ga kowannenmu...
    Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana jin daɗin yadda shugaban ƙasar Bola Tinubu yake tafiyar da gwamnatinsa. Buhari ya ce har yanzu Tinubu bai sauya ba daga tsari da manufofin da jam’iyyar APC ta kafa wanda har ya sanya shi kansa ’yan Nijeriya suka zaɓe shi a 2015. An ga watan Sallah...
    Kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Litinin, 31 ga watan Maris, da Talata, 1 ga watan Afrilu, a matsayin ranakun hutun ƙaramar salla. Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da sakataren ma’aikatar, Magdalene Ajani, ya fitar a ranar Laraba. Ahmad Lawan ya raba tallafin N27m da buhun shinkafa 300...
    Manjo-Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Ayyuka na Musamman na Jihar Kano, ya yi murabus. Wannan dai na zuwa ne bayan shafe watanni bakwai kacal da karɓar muƙamin. Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Mustapha Muhammad ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Larabar....
    Shugaban riƙo na Jihar Ribas, Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya sanar da naɗin Farfesa Ibibia Lucky Worika a matsayin sabon Sakataren Gwamnatin Jihar Ribas. Wata sanarwa da ta fito daga Fadar Gwamnatin da ke birnin Fatakwal a wannan Talatar, ta ce naɗin ya biyo bayan nazari kan ƙwarewar Farfesan da gogewarsa a fannoni daban-daban. Za...
    Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya jaddada kudirin gwamnatinsa na sake farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu da aka daɗe da watsi da ita domin bunƙasa noman rani da nufin samar da wadataccen abinci a Kudancin Borno da ma Jihar ta Borno gaba ɗaya. Zulum ya yi wannan alkawarin ne a yayin wata ziyarar...
    Ya ce: “Ina so in sake nanata cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yake cikakken ɗan dimokiraɗiyya, yana da niyyar kare ‘yancin ‘yan Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Haka zalika, yana ƙarfafa sukar gwamnati mai ma’ana da adawa tagari saboda suna da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen ingantawa da zurfafa tsarin dimokiraɗiyyar...
    Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya.   Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta...
    Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan. A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya. Afirka ta Kudu ta...
    ’Yan kasuwa na ci gaba da neman mafita bayan karyewar farashin kayan masarufi, musamman abinci da ake ci gaba da samu, sabanin yadda aka saba fuskantar tashin gwauron zabon farashi a lokacin azumi a Nijeriya.  Farashin kayan abincin ya karye ne a lokacin da wasu ’yan kasuwar suka riga suka saye amfanin gona suka boye...
    Ya ce fim ɗin tarihin zai nuna nasarori, ƙalubale, da darussan da aka koya a wannan tafiya.   Ya ce: “Na yi farin cikin ganin ƙoƙarin da IPAC da shugabannin ta suke yi wajen ƙarfafa dimokiraɗiyya, musamman ta hanyar fim ɗin wanda zai zama wata muhimmiyar shaida ta tarihi, domin girmama jaruman siyasar ƙasar mu...
    Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ba ta soke naɗin Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba. Kwamishinan Shari’a kuma Babban Lauyan Jihar, Haruna Isa Dederi, ya bayyana cewa kotun kawai ta dakatar da aiwatar da hukuncinta har sai Kotun Ƙoli ta yanke hukunci a kan shari’ar. MC Tagwaye ya fice...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin...
    An gargaɗi mazauna da su kwana cikin shirin daƙile yaɗuwa cutar Sanƙarau a yayin da cututtuka masu alaƙa da ita suka soma bayyana a wasu ƙananan hukumomin Jihar Sakkwato. Kwamishinan Lafiya na jihar, Dakta Faruk Umar Wurno ne ya yi wannan gargaɗi haɗi da bayar da shawarar a wani jawabi da ya fitar a ranar...
    Adelaja ya jaddada mahimmancin ƙarfafa musayar bayanan sirri da haɗin gwiwar hukumomi, duba da irin kaifin basira da masu fasa-kwari ke amfani da wasu a ‘yan kwanakin nan wurin cimma muradunsu.   “Masu fasa kwauri na ci gaba da bunkasa a ayyukansu, kuma don tunkararsu yadda ya kamata, dole ne mu hada kai ta hanyar...
    A yayin bikin Ranar Mata ta Duniya, Hajiya Sa’adatu Ali Isa JC, matar Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Balanga da Billiri, ta tallafa wa mata 150 da injinan markaɗe domin su samu hanyar dogaro da kai. Da ta ke jawabi yayin rabon kayan, Hajiya Sa’adatu ta ce manufar wannan tallafi ita ce taimaka wa mata...
    Iyalan marigayi Janar Sani Abacha, sun gargaɗi Tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Babangida, da ya daina faɗin maganganun da ka iya ɓata sunan mahaifinsu. A cikin wata sanarwa da Mohammed Abacha, ya fitar a madadin iyalan marigayin a ranar Lahadi, sun musanta iƙirarin da Babangida ya yi a cikin littafinsa mai suna ‘A Journey...
    Ya ce: “Nijeriya da Chana sun kai matakin haɗin gwiwa mafi girma a tarihin dangantakar su. Wannan ne ya sa aka rattaba hannu kan yarjejeniyoyi guda goma a taron FOCAC, kuma guda biyu daga cikin su suna da alaƙa da ma’aikatar nan.   “NTA ita ce babbar tashar talbijin a Afrika baki ɗaya, tana da...
    “Ina son in nuna jin daɗina ga Babban Hafsan Sojin Sama, wanda kafin ziyarar tasa a yau, ya aiko da wata tawaga mai ƙarfi ƙarƙashin jagorancin ɗaya daga cikin manyan hafsoshi daga hedikwatar domin jajanta mana da al’ummar Zamfara. Ya aika da tawaga zuwa Zamfara a lokuta biyu daban-daban. “Ina son nanata cewa a...
    Samar da dabino zai samu sauyi mai mahimmanci a Jihar Jigawa bayan da wani kamfani daga kasar Saudiyya mai samar da dabino da gwamnatin jihar suka ƙulla yarjejeniya domin ƙara yawan amfanin gona. Ta wannan haɗin gwiwa za a kawo sababbin fasahohin zamani da irin dabino masu yawa don shigar da su cikin tsarin noma....
    Yayin da aka fara tsinkar tumatari dan rani a Kano da sauran jihohin da ke samar da tumatar a fadin Nijeriya, rahotanni sun bayyana cewa, farashinsa ya fadi sosai fiye da yadda aka yi zato, lamarin da ya jefa manoman cikin damuwa. Binciken da Jaridar Aminiya ta gudanar ya nuna cewa, a halin yanzu, ana...
    Gwamnan Kano Ya Gargaɗi Malamai Kan Sa Yara Aikin Wahala
    Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda...
    Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya tabbatar da naɗin Sarkin Yarbawan Funtuwa, Oba Alhaji Murtala Sani Adeleke a matsayin sabon Sarkin Yarbawan Jihohin Arewa 19 har da Abuja. Mataimakin Gwamnan JIhar Katsina, Malam Faruk Lawal Jobe ne ya tabbatar da naɗin a madadin gwamnan a lokacin da yake karɓar baƙuncin tawagar Sarakunan Yarbawan Arewa...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi...
    Kungiyar Tarayyar Turai EU ta yaba wa ƙoƙarin Gwamna Babagana Umara Zulum wajen farfado da harkokin rayuwar al’ummar Jihar Borno bayan tashe-tashen hankulan ’yan ta’adda da jihar ta yi fama da shi. EU ta buga misali da cibiyar koyar da sana’o’i ta Muna da ke horar da matasa musamman waɗanda rikicin Boko Haram ya shafa...
    Sarkin ya yi addu’a Allah ya jiƙansa, ya gafarta masa, kuma ya bai wa iyalansa haƙuri.
    Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.   “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan...
    Sanarwar ta kuma bayyana cewa, jami’an hukumar tsaron farin kaya daga jamhuriyar Nijar ne suka biyo wanda ake zargin ɗan bindigar ne a kan babbar hanyar Zurmi/Kauran Namoda a jihar Zamfara.   Da yake duba makaman da aka kama, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana kyakkyawar haɗin gwiwa tsakanin sojojin da gwamnatin jihar Zamfara wajen yaƙi...
    Masu ɗibar man fetur daga wata tankar mai da ta faɗi sun kai wa jami’an kashe gobara da ke hana su farmaki. Bayan faduwar tankar a cikin dare man cikinta ya fara tsiyaya, inda motar ta kama da wuta a kan babbar hanyar Ogbomosho zuwa Ilorin a ranar Laraba. Faɗuwar motar ke da wuya wasu...
    An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar...
۱