Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
Published: 31st, January 2025 GMT
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba.
“Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama.
“Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.”
Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don kauce wa irin waɗannan haɗurran.
Haka kuma, ministan ya jaddada damuwar Shugaban Ƙasa kan yawaitar irin waɗannan bala’o’i a faɗin ƙasar nan, yana mai cewa dole ne a ƙara wayar da kan al’umma domin daƙile aukuwar irin su a nan gaba.
Ya ce: “Abu na farko da ya kamata mu gane shi ne irin wannan bala’i yana faruwa sau da yawa a ƙasar mu, kuma Shugaban Ƙasa yana cikin matsanancin baƙin ciki. Ya kuma umarta cewa Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ta gudanar da wayar da kai da faɗakarwa, musamman a cikin waɗannan ƙauyuka, domin hana aukuwar irin hakan a nan gaba.”
A ƙarshe, Idris ya yaba da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar Neja ta yi wajen ɗaukar matakin gaggawa game da lamarin, tare da bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta umarci Ma’aikatar Harkokin Jin Ƙai da Rage Talauci tare da Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da su taimaka wa waɗanda abin ya shafa.
কীওয়ার্ড: Shugaban Ƙasa
এছাড়াও পড়ুন:
Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara
Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025.
A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita.
Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane da su ka kamu da ita.
Tare da cewa an dauki shekara da shekaru ana fama da wannan cutar a cikin kasar ta Nigeria, sai dai har yanzu babu wani ci gaba na azo a gani da aka samu na dakile wannan cuta, saboda halayyar kazanta da rashin muhalli mai tsafta.
Ana samu wadanda suke tsira daga cutar amma a lokaci daya tana kisa.