2025-04-03@10:30:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 70
«Shugaban Ƙasa»:
Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na 0.5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensu, daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS). A cikin wata sanarwa haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da kudaden ne don tafiyar da al-amuran ƙungiyar. Harajin, wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani...
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za su mayar da martani cikin gaggawa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya kai shekara 40 ko sama da haka, zai iya tuna irin tarbiyyar da ya samu daga iyayensa a baya, da kuma yadda alaƙar da ke tsakanin yara da iyaye ta ke cike da girmamawa, kulawa, da soyayya. A yau, abubuwa sun canza sosai. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu Yawancin iyaye na fuskantar ƙalubale iri-iri, musamman yadda nauyin rayuwa ke ƙaruwa a kansu. Ɗaya daga cikin manyan sauye-sauyen da aka samu shi ne yawaitar mata masu aiki, ko dai a gwamnati ko a kamfanoni masu zaman kansu. Wannan sauyin yana iya shafar irin...
Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu. Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumomin Myanmar sun buƙaci ƙasashen duniya su hanzarta tura agaji, yayin da jami’an ceto ke ƙoƙarin gano mutanen da suka maƙale a cikin baraguzan gine-gine. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun tabbatar da ganin jinjirin watan Shawwal, wanda ke nuna ƙarshen azumin watan Ramadan na bana. Kwamitin duban wata na ƙasar ya bayyana cewa an ga jinjirin wata a yammacin yau, wanda ke tabbatar da cewa gobe za a fara bukukuwan Sallah. Shirye-shiryen Bukukuwan karamar Sallah Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge Mijinki Wannan na nufin cewa al’ummar Musulmi a Saudiyya za su yi bikin ƙaramar Sallah, domin kammala azumin da suka gudanar a tsawon watan Ramadan. Hukumomi sun buƙaci jama’a da su gudanar da bukukuwan Sallah cikin lumana da bin dokoki don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin...
A shekarar 1468 wanda yake mulkin Sonni Ali Shugaban Songhai ya ci wurin da yaki.Shi ba wanda yake ya saki jikinsa bane musamman ma musulmai wadanda suke da ilimin musulunci,amma wanda ya gaje shi Askia Muhammad na daya (1) wanda ya yi mulkin kasar daga shekarar( zuwa 1493–1528)ya yi amfani ne da wadanda suka yi karatu a matsayin wadanda yake tuntuva dangane da abinda ya shafi shari’a da al’amura na yau da kullum. Bayan da kasar Morocco ta mamaye ta a shekarar 1591, daga nan sai Birnin ya fara komawa baya.Aka bada umarni na kama Malamanta a shekarar 1593 saboda ana yi masu kallon basu goyon bayan abinda aka yi; an kashe wasu daga cikinsu lokacin da aka yi wani...
Yawancin wadanda suke da HNd basu samu damar tafiya aikin Yiwa kasa Hidima/Aikin Bautawa kasa wanda hakan ne kuma aka gay a kamata ayi masu adalci kan lamarin Sai dai kuma irin ci gaban da aka samu ya kawo ko samar da wata matsala ta yadda wadanda suka yi karatun suka kammala a makaranta sai ta kasance wasu daga cikinsu basu samu damar tafiya aikinyiwa kasa hidima ba saboda irin karatun da suka yi. Da yake bada ta shi gudunmawa darekatan lamurran ‘yan jaridu da hulda da jama’a ma’aikatar ilimi ta tarayya Boriowo Folasade, ya fitar da sanarwa wadda take tabbatar da gaskiyar lamarin na abubuwan da suka biyo bayan dukkan tarurrrukan da kuma ganawar da aka yi. Sanarwa ta...
Jihohin da wannan matsalar ta fi shafa sun hada da, Zamfara, Borno, Yobe da kuma Katsina, musamman duba da yadda aukuwar yawan rikice-rikice, ya tarwatsa rayuwar miliyoyin alumomin yakin da fadawa cikin kangin fatara da yunwa da kuma rashin samun wadataccen abinci. A ra’ayin mu, matsalar karancin abinci a kasar nan, ba voyayayen abu bane, musammamn duba da cewa, yawan aukuwar tashe-tashen hankula, kalubalen rashin tsaro da matsatin tattalin arziki, suna manyan hummulhaba’isin da ke janyo karancin abinci a a cikin alumma. Misali, yawan samun hare-haren ‘yan bindiga a yankin kudu maso gabas, ayyukan ‘yan bindiga daji a yankin arewa masu yamma da kuma rikice-rikicen kabilanci a sauran yankuanan, sun janyo tarwatsa miliyoyin alumomi daga matsugunan su, lalata gonakansu wanda...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa. Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya. Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa. Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro. Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
“SDP jam’iyya ce mai zaman kanta, kuma za mu ci gaba da bin tsarukanmu da dokokinmu wajen zaɓen ‘yan takara,” in ji shi. “Za Mu Fi Mayar da Hankali Kan Ci Gaban Jama’a” Shugaban jam’iyyar ya bayyana damuwa kan halin da ‘yan Nijeriya ke ciki, musamman matsalar tsadar rayuwa da rashin tsaro. Ya ce SDP ba za ta zama mafakar wasu ‘yan siyasa masu neman mulki ba tare da wani ingantaccen shiri ba. “Dole mu duba halin da ƙasa ke ciki. Tsadar rayuwa na ci gaba da ƙaruwa, mutane na fama da wahala, amma ana cewa tattalin arziki yana inganta. Dole ne a fuskanci gaskiya, a yi aiki don ci gaban jama’a, ba kawai neman mulki ba,” in ji Gabam....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Mulkin dimokuraɗiyya kamar yadda Hausawa ke cewa ‘yancin ɗan adam. A lokacin da ta ba ka damar tsayawa don a zaɓe ka kan wani muƙamin, kazalika ta ba ka damar zaɓen wanda kake so ya shugabance ka kuma ya wakilce ka. Wani abun da dimokuraɗiyyar ta bai wa al’umma dama a kai kuma shi ne na yin kiranye ga wakilan da suka zaɓa musamman idan waɗannan wakilan basa biya musu buƙatun da suka tura su a kai. Tuni dai al’ummar Kogi ta Tsakiya suka fara kaɗa ƙuri’un kiranye ga Sanata Natasha da suka aike ga Majalisar Dattawa bisa dalilai nasu na ƙashin kan su. NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a...
A cewar takardun kotun, gwamnonin suna neman a bayyana cewa, hukuncin da shugaban kasa ya zartar ya saɓa wa sashe na 1 (2), 5 (2), da 305 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima). Sun kuma kara da cewa, shugaban kasa ba shi da wani iko ko kadan na dakatar da zaɓaɓɓen gwamna da mataimakin gwamnan wata jiha a tarayyar Nijeriya bisa fakewa da dokar ta-ɓaci. Gwamnonin kuma suna kalubalantar amincewa da dokar ta-ɓaci da majalisar dokokin kasar ta yi, suna masu cewa, yin amfani da kuri’a jin ra’ayi ta baki ya saɓawa kundin tsarin mulkin kasar, saboda dokar ta ce, dole sai an samu mafi rinjayen kuri’a biyu cikin uku na dukkan ‘yan majalisar....
Sabon Kocin tawagar Super Eagles ta Nijeriya Eric Chelle, ya fara jagorantar tawagar da ƙafar dama, bayan samun nasara a wasan farko da ya jagorance ta. Chelle wanda ya zo Super Eagles watanni biyu da su ka gabata, ya jagoranci Super Eagles a wasan da su ka doke ƙasar Rwanda da ci biyu da nema a Amahoro. Wasan shi ne zagaye na biyar a wasannin neman gurbi a gasar cin kofin Duniya da za a buga a shekarar 2026, Nijeriya na matsayi na 4 a rukunin C na gasar da maki 6 a wasanni 5, sai Afrika Ta Kudu dake jan ragamar rukunin, ƙasar Benin ta biyu sai Rwanda dake matsayi na uku. Eric Chelle Ya Sake Bai Wa Ahmed...
Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka. Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya rantsar da Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya) a matsayin Mai Kula da Jihar Ribas. An rantsar da shi ne a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja a ranar Laraba. Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya fice daga gidan gwamnatin Ribas Naɗin ya biyo bayan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas da Shugaba Tinubu ya yi a ranar Talata, bayan dakatar da Gwamna Siminalayi Fubara, Mataimakiyarsa, da ’Yan Majalisar Dokokin Jihar. Bayan ayyana dokar ta-ɓacin, Tinubu ya sanar da cewa Vice Admiral Ibas ne zai jagoranci jihar na tsawon watanni shida. Yayin jawabinsa, Shugaban Ƙasa ya bayyana cewa dokar ta-ɓacin ba ta shafi ɓangaren shari’a ba,...
Dalilin wannan doka shi ne rikice-rikicen addini tsakanin Musulmai da Kiristoci a watan Satumba 2001, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 2,000. A Jihar Borno Ma An Taɓa Sanya Dokar, Amma Ba A Jihar Baki Ɗaya Ba A shekarar 2011, Shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana dokar ta-ɓaci a wasu ƙananan hukumomin jihohin Borno, Adamawa, da Yobe saboda yawaitar hare-haren Boko Haram. A 2013, Jonathan ya faɗaɗa dokar ta-ɓacin zuwa ɗaukacin jihohin Borno, Yobe, da Adamawa sakamakon tsanantar matsalar tsaro. Wannan mataki ya bai wa jami’an tsaro ƙarin iko domin dawo da zaman lafiya. Sai Kuma Jihar Ribas a Yanzu Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas saboda rikicin shugabanci...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya ce, “Shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi,” yana mai cewa mahaifinsa ya ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki da samar da dama ga matasa. Ya kara da cewa, “Shi ne kawai shugaban da ya kiyaye mutanenku a gida, tun lokacin da ya kasance gwamna har ya zama shugaban kasa. Shugaban da ya dauki matasa da muhimmanci, ya samar da dandali don...
Seyi Tinubu, ɗan shugaban kasa Bola Tinubu, ya bayyana cewa mahaifinsa shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi, yana yaba wa shugabancinsa da himmarsa wajen bunkasa rayuwar matasa. A cikin wani faifan bidiyo da ya bayyana ranar Litinin, Seyi ya furta wannan magana yayin da yake jawabi ga taron matasa a jihar Adamawa. Ya ce, “Shi ne shugaban Nijeriya mafi girma a tarihi,” yana mai cewa mahaifinsa ya ba da fifiko ga ci gaban tattalin arziki da samar da dama ga matasa. Ya kara da cewa, “Shi ne kawai shugaban da ya kiyaye mutanenku a gida, tun lokacin da ya kasance gwamna har ya zama shugaban kasa. Shugaban da ya dauki matasa da muhimmanci, ya samar da dandali don...
A cewar Dunbai, gwamnatin kasar Sin tana kara inganta alakarta da jihar Kano a fannonin samar da abinci, kayayyakin more rayuwa, ilimi, tare da kasuwanci da gwamnatin jihar. A fannin aikin gona, wakilin kasar Sin ya yi nuni da muhimmancin samar da abinci a jihar Kano, inda ya ce, jihar da ke da dimbin al’umma kamar kasar Sin, ta cancanci amfani da fasahohin zamani a fannin noma don karfafa samar da dimbin abinci. A cikin sanarwar, Mista Dunhai ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta ci moriyar damar da kasar Sin ta samar na zuba jari a Nijeriya na sama da dala tiriliyan 20, domin farfado da ci gaban masana’antu da kasuwanci. A nasa jawabin, Gwamna Yusuf,...
Ya ce, muddin ‘yan siyasan Nijeriya ba su haɗa kansu waje guda ba, ƙalubalen da suke cikin ƙasar nan za su yi wuyar kawuwa. Ya ce, akwai kuma buƙatar tunƙarar matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya. Ya ce, tuntuɓar da suka fara da gwamnan Bauchi a matsayinsa na fitaccen ɗan siyasa a Arewa kuma shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP ya yi ne ba wai don son zuciyarsu ba, illa sai don son da suke yi da cigaban ƙasar nan da nemi mafita. Ya lura kan cewa akwai buƙatar a fara magance matsalolin talauci a Nijeriya kafin a tunƙari sauran matsaloli. Ya yi fatan cewa za su ci gaba da irin wannan tattaunawar domin nema wa Nijeriya mafita. Shi...
SP Adeh ta kuma ce jami’an ‘yansanda sun ceto wasu mutanen da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a lokacin farmakin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayan ɗimbin falala da yawan samuwar ibadun da ke ƙara kusanta bayi ga Ubangijinsu, da azumin watan Ramadan ke zuwa da shi kamar yadda malamai suka saba faɗa, Hakazalika kuma a watan na zuwa da wata al’ada mai ɗimbin tarihi da ke ɗebe wa al’umma musamman na Arewacin Najeriya kewa. Wannan al’adar ita ce ta tashe da ake fara d zarar watan azumi ya kai kwanaki 10. DAGA LARABA: Yadda Zawarawa Suke Ɗanɗana Kuɗa A Watan Ramadana DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Maza da mata na gudanar da wannan al’ada ta hanyar yin shigar kwaikwayo tare da ɓatar da kama, su ringa zagayawa gidaje da kwararo-kwararo...
Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo su ba bisa ƙa’ida ba. Ya ce ana ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar an kammala za a gurfanar da waɗanda ake zargin a kotu domin su fuskanci hukunci. Idan ba a manta ba a kwanaki kaɗan da suka wuce gwamnatin Jihar Filato, ta sanar da sanya haramci kan harkokin haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba a faɗin jihar saboda...
Ya ce: “Za mu yi amfani da dandamalin Taron Kasuwanci na Faransa da Nijeriya domin isar da saƙon da Shugaban Ƙasa ke son mu isar a wannan shekara. “Wannan shekara, 2025, ita ce shekarar da za a ƙarfafa tattalin arziki da zamantakewa a Nijeriya kamar yadda Shugaban Ƙasa ya alƙawarta. Kamar yadda kuka ji a lokuta da dama, tattalin arzikin mu ya fara samun ingantacciyar nasara. Farashin abinci da ya hauhawa a baya yana sauka. “Darajar Naira na fara nuna alamun daidaituwa, kuma duk shirin gyaran tattalin arzikin da Shugaban Ƙasa ya aiwatar suna fara samun nasara, kuma da yardar Allah, za mu kai ga burin da muke nema.” Ministan ya amince da cewa kowace ƙasa da...
Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya naɗa Tsohon Shugaban Hukumar INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega, a matsayin Mashawarci kuma Mai Kula da Shirin Gyaran Noma da Kiwo na Shugaban Ƙasa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ne, ya tabbatar da naɗin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a. An kashe shugaban Lakurawa, Maigemu a Kebbi Zan sasanta Akpabio da Natasha — Ministar Harkokin Mata Shugaba Tinubu na fatan wannan naɗi zai kawo ci gaba a harkar noma da kiwo, tare da ƙarfafa yunƙurin raya ƙasa. Farfesa Jega, wanda tsohon Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano ne, ya kasance mataimakin shugaban Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Gyaran Noma da Kiwo tare da Shugaba Tinubu. Kwamitin ya gabatar da shawarwari masu...
Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta shirya buɗa-baki a Fadar Gwamnati da ke Abuja, inda ta tabbatar wa ’yan Najeriya cewa ƙasar nan na kan hanya gyaruwa nan ba da jimawa ba. A yayin jawabinta, ta jaddada muhimmancin tausayi da jin-ƙai a tsakanin rayuwar ɗan adam. Wani mutum ya yanke jiki ana salla a Masallaci, ya rasu a asibiti Dakatarwa: Har yanzu ni Sanata ce — Natasha Ta buƙaci kowa ya kasance mai aikata alheri tsakaninsa da Allah, ba don neman yabo ko amincewar mutane ba. A yayin buɗa-bakin, Farfesa Azeezat Adebayo, Shugabar Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Ilorin, ta bayyana cewa tausayi da jin-ƙai su ne ginshiƙai na kyakkyawar rayuwa a tsakanin al’umma. Ta tunatar da mahalarta...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
A ranar 29 ga watan Janairu, 2025, ƙasashen Burkina Faso, Mali, da Nijar – waɗanda suka haɗe a ƙarƙashin Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES) – sun sanar da ficewarsu daga ECOWAS. Duk da hakan, ECOWAS ta tabbatar da cewa babu wata matsala a ɓangaren sufuri da kasuwanci tsakanin ƙungiyar da ƙasashen AES, domin har yanzu ana ci gaba da hulɗa tsakanin al’ummomin yankin. Hakazalika, ECOWAS ta bayyana cewa ƙofarta a bude ta ke ga ƙasashen idan har sun shirya komawa cikin ƙungiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga...
Hukumar zaɓen ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su shirya don shiga zaɓen da ke tafe, tare da tabbatar da cewa an bi ƙa’idojin zaɓe. Haka kuma, hukumar ta yi alƙawarin gudanar da zaɓen cikin gaskiya da adalci, domin tabbatar da cewa an zaɓi shugabannin da suka cancanta a matakin ƙananan hukumomi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana kasafin kuɗin bana, wanda Shugaba Tinubu ya rattaba wa hannu kwanan nan, a matsayin tsari mai karfi da zai daidaita tattalin arziki da kwanciyar hankali a zamantakewa, da kuma cigaban ƙasa. Ya bayyana hakan ne a yayin taron da ake da Ministoci karo na uku da aka gudanar a Cibiyar Manema Labarai ta Ƙasa, Abuja, a yau. Mohammed Idris ya jaddada cewa kasafin kuɗin wannan shekarar ya mayar da hankali kan zuba jari a sassa masu muhimmanci da ke da tasiri na kai tsaye kan jin daɗi da ci gaban tattalin arzikin ƙasa. “Kasafin kuɗi na 2025 ba kawai wata takarda ta kuɗi ba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wannan mataki yana da matuƙar tasiri a siyasar Jihar Ribas, inda jam’iyyar APP ce ta lashe mafi yawan kujeru a zaɓen da aka soke. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma kara da cewa, gwamnatin jihar Kano ta bai wa ilimi fifiko, wanda Kano ce a gaba wajen ware kasafin kudi mai yawa a shekarar 2024 da 2025 a fannin Ilimi. Bugu da kari, gwamnatin ta ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi domin tabbatar da matasa sun samu ingantaccen ilimi wanda zai ba su damar yin fice a tsakanin takwarorinsu. Da yake magana tun farko, Gautier Mignot, jakadan Tarayyar Turai a Nijeriya da ECOWAS, kuma jagoran tawagar, ya bayyana cewa, sun zo Kano ne domin halartar bikin baje kolin karatu na Turai da aka shirya yi a ranar 27 ga Fabrairu, 2025 a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da...
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa shugabancinsa ya gaji bashin Naira biliyan 8.9. Ganduje ya bayyana haka ne a Abuja yayin taron Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar APC. Boko Haram sun sace mutum 2 da kayan abinci a Borno Buhari da El-Rufai ba su halarci babban taron APC ba A cewarsa, wannan bashi ya samo asali ne daga kuɗaɗen da aka kashe a shari’o’i kafin zaɓe, ƙalubalantar sakamakon zaɓe, da ƙarar da aka shigar da ’yan majalisu, gwamnoni, da na shugaban ƙasa. “Shugabancin kwamitin zartaswa na ƙasa na yanzu ya gaji bashin Naira 8,987,874,663 da kuma tari shari’o’i daban-daban,” in ji shi. Ya ƙara da cewa mai bai wa jam’iyyar shawara kan harkokin...
Shirin Rumbun Saukin zai fi bayar da da muhimmanci ne kan ma’aikatan gwamnati da dattijai masu shekaru 60 zuwa sama, inda kayan abincin za su kasance a nau’ikan ma’aunai daban-daban domin a dai-daita da bukatun iyalai da samun masu cin gajiya wanda za su yi rijista ta yanar gizo ko kuma ta cibiyoyin da aka tanada domin shirin. Danja, ya ƙara da cewa burin gwamnati shi ne faɗaɗa shirin zuwa dukkan ƙananan hukumomi 34 da ke jihar, tare jaddada himmatuwar gwamnatin Katsina na ci gaba da ɗaukar nauyin shirin domin rage matsin tattalin arziki da jama’a ke fuskanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye...
Shugabannin Jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnoni, da sauran manyan jagorori, sun gana a daren Talata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja. An gudanar da taron ne domin shirye-shiryen babban taron jam’iyyar na ƙasa da za a yi a yau a hedikwatar APC. Kamfanin Saudiyya ya haɗa kai da gwamnatin Jigawa kan noman dabino Sanata Natasha na neman diyyar N100bn wurin Akpabio Wannan shi ne taron farko da za a yi taron tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki a ranar 29 ga watan Mayu, 2023. A bara, an tsara shirya waɗannan taruka ne a watan Satumba, amma aka ɗage su ba tare da saka sabuwar rana ba. A baya-bayan nan, tsohon gwamnan Jihar Kaduna,...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya). Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar. Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da...
Mansa Mūsā, ko dai shi jikan ko kuma abokin wasan Sundiata wanda shi ne ya kirkiro Daular Mali yah au kan karagar mulkin ne a shekarar. A karni na 17 (1324),lokacin ne ya tafi aikin Hajjin wanda ya zama abinmagana saboda dalilai masu dama. Aikin Hajjin da ya tafi ne ya sa idon duniya ya bude saboda irin arzikin da Allah ya yi wa kasar ta Mali.
Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio cewa kasarsa ba za ta amince da korar Falasdinawa daga Gaza ba. Mohammed bin Zayed Al Nahyan na mayar da martani ne ga shirin Shugaba Trump na Amurka na karbe ikon Zirin bayan sauya wa al’ummar Gaza matsuguni. Shugaban na Hadaddiyar Daular Larabawa ya ce sake ginin Gaza abu ne da ya kamata a hada shi da shirin da...
Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim. Amorim zai fafata da Kocin Everton Moyes a ranar Asabar yayin da yake kokarin fitar da United daga koma bayan da ta ke fuskanta, tsohon kocin na Sporting Lisbon ya lashe wasanni huɗu ya yi rashin nasara a wasanni takwas a wasannin gasar Firimiya 12 da ya jagoranci Manche’ster United tun bayan zuwanshi a watan Nuwamba. Juma Bah: Balladolid Za Ta Kai Manchester City Kara...
Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar, ya samu fitowar masu zaɓe sosai tare da ingantaccen tsaro. Gwamna Adeleke ya yaba da yadda zaɓen ke tafiya cikin lumana, inda ya buƙaci al’umma su ci gaba da kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ko matsin lamba ba. Gwamnan Shekarar 2024: Sanata Ademola Jackson Nurudeen Adeleke An Yanke Wa Mutane 5 Hukuncin Kisa Bayan Sun Kashe Wani Bafullatani A Jihar Osun Da yake jawabi...
“Idan ba a dau matakin da ya dace akan abin da ke faruwa a DRC ba, al’amarin zai faskara. Ba batun fitar da takardar jawabin bayan taro ne kawai muke yi ba. Dole a biyo bayan hakan da wasu muhimman matakai ko tsare tsare da zasu tabbatar da cewa an gabatar da wadannan al’amura kan teburin shawara tare da nemo mafita irin wanda ya dace da Afurka don warware matsalolin Afurka.”
Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da sojoji. Gwamnati Ta Haramtawa Tankokin Dakon Mai Ɗaukar Fiye Da Lita 60,000 Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau Kauyukan a cewar dan majalisar mai wakiltar mazabar Sabon Birni ta yamma a majalisar dokokin jihar, Hon. Aminu Boza ya hada da Garin Idi, mahaifar mataimakin gwamnan jihar mai ci, Injiniya Idris Gobir. Boza ya kuma ce, Turji ya koma da...
Abiola Ne Ya Lashe Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 12 Ga Watan Yuni 1993 – Janar IBB
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu. Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da hakkin kananan hukumomi na samun kudadensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta rike kason su. Da yake jawabi bayan yanke hukuncin, lauyan kananan hukumomi 44, Barista Bashir Wuzirchi, ya bayyana matakin a matsayin nasara ga jihar Kano.
“Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa kuɗin jama’a ba su faɗa hannun jagorori marasa cancanta ba. Saboda haka, za mu ɗaukaka ƙara kuma mu ci gaba da fafutuka har sai an yi mana adalci,” in ji shi.
Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu kai kan yadda za su kula da yaronsu idan sun koma gida. Ita kuwa Hasana Lawalli cewa ta yi har mai ciki ta kawo kuma ta haihu a wannan asibiti daga bisani aka sallame su suka koma gida. Ta ce yau kuma gashi ta kawo diyata ita ma a duba ta. Dahiru Magaji shi ne mai kula da wannan asibiti ta Magama Jibia ya yi...
Ƙasashen da suke da saukin cin hanci a duniya Mafi yawan kasashen da rahoton ya nuna cewa babu yawaitar matsalar cin hanci da rashawa suna a nahiyar Turai ne. Bakwai daga cikin kasashen 10 na farko, wadanda ba su da matsalar Rasha duk a yankin Tarayyar ta Turai suke. Qasar da ta fi kowace a duniya samun maki a bangaren yaki da rashawa ita ce Denmark, wadda take da maki 90. Sai kuma Finland mai maki 88, ta uku kuma ita ce Singapore, wadda ke a kudu maso gabashin nahiyar Asiya. Ga yadda kasashen 10 na farko suka kasance: 1. Denmark – Maki 90 2. Finland – Maki 88 3. Singapore – Maki 84. 4. New Zealand – Maki 83....
Wata majiya daga CBN ta bayyana cewa idan ba tare da cikakken tantance kudi ba, babban bankin ba zai iya bude sabbin asusu ga kananan hukumomin ba.
Ya ce ya zama wajibi gwamnati ta tashi tsaye wajen farfado da darajar ilimi, ya kuma nuna damuwa bisa ganin yadda darajar ilimi take kara faduwa a kasar nan. Ya ce dole sai gwamnati tarayya da na jihohi sun hada kai wajen tafiyar da harkar karantawa a kasar nan ta yadda yaran masu karamin karfi za su sami ilimi mai inganci.
Majalisar Dokoki Ta Ƙasa Ta Amince Da Tiriliyan 54.9 Kasafin Kuɗin 2025
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon albashin, an bar malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi a baya. Sun ce sun ba shugabannin isasshen lokaci domin su cika alƙawarin da suka ɗauka amma sun kasa, don haka suka yanke shawarar ci gaba da yajin aiki har sai an biya su hakkokinsu. Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja… Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba...
Ƙungiyar malamai ta NUT-FCT da ma’aikatan ƙananan hukumomi na NULGE sun fara yajin aiki na dindin a yau Alhamis, sakamakon gazawar shugabannin ƙananan hukumomi wajen aiwatar da sabon albashi mafi ƙarancin na ₦70,000 da aka amince da shi tun Disamba 2024. Ƙungiyoyin sun koka cewa duk da cewa sauran ma’aikatan FCT sun fara karɓar sabon albashin, an bar malaman firamare da ma’aikatan ƙananan hukumomi a baya. Sun ce sun ba shugabannin isasshen lokaci domin su cika alƙawarin da suka ɗauka amma sun kasa, don haka suka yanke shawarar ci gaba da yajin aiki har sai an biya su hakkokinsu. Yadda Jami’an Tsaro Suka Fara Gyara Wa ‘Yan Jari Bola Zama A Abuja… Hukumar FCTA Ta Rufe Asibitin Da Ke Aiki Ba...
ATM da ke cikin shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan duk wani cire kuɗi na N20,000. ATM da ke wajen shalƙwatar banki: Za a caji N100 kan N20,000 da kuma ƙarin haraji har zuwa N500. Cire kuɗi a ƙasashen waje: Za a yi caji bisa ga yawan kuɗin da mai ATM ya buƙata. CBN ya ce wannan sabon tsari zai ƙarfafa shigar da sabbin ATM a faɗin ƙasa tare da tabbatar da cewa bankuna suna cajin kuɗin da ya dace.
Majalisar wakilai ta umarci kwamitocin sadarwa da harkokin cikin gida da su binciki haɗa lambar shaidar zama ɗan ƙasa (NIN) da layukan waya ba tare da izini ba da kamfanonin sadarwa ke yi. Wannan mataki ya biyo bayan ƙudirin da ‘yan majalisa Patrick Umoh da Julius Ihonvbere suka gabatar, inda aka buƙaci hukumar NCC ta ɗauki mataki kan duk wani kamfanin sadarwa da aka samu da laifi, tare da NIMC ta tabbatar da sahihancin haɗa bayanan NIN. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Trump Ya Hana Maza Masu Sauyin Jinsi Shiga Wasannin Mata Umoh ya ce wannan mataki na iya haifar da damuwa ga ‘yan ƙasa, tare da jefa su cikin hatsarin satar bayanai, da damfara,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A da akan kwashe kwanaki ana bukukuwan aure a ƙasar Hausa, kama daga kamu, zuwa sa lalle, yinin biki da zaman ajo zuwa buɗar kai da sayen baki. Sai dai waɗannan al’adu sannu a hankali suna ta gushewa. Ko mene ne dalilin wannan sauyin? NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Wannan ne batun da shirin Daga Laraba zai duba a wannan makon. Domin sauke shirin, latsa nan
Babbar Kotun Jihar Kogi ta tsige Alhaji Ahmed Muhammed Tajani Anaje daga kujerarsa ta Ohinoyi na Ƙasar Ebira. Kotun ta soke naɗin Alhaji Ahmed Muhammed ne a ranar Litinin, shekara guda bayan fara aikin basaraken. Alƙalin kotun, Mai Shari’a Salisu Umar, ya kuma dakatar da basaraken daga gabatar da kansa matsayin Ohinoyi, har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukuncin ƙarshe. Kotun ta bayar da umarnin ne bayan ƙarar da Dakta Barnabas Adeku Ojiah da wasu mutum biyu suka shigar. Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba Sun shigar da...
Ƙungiyoyin alarammomi da matasa daga jihohin Arewa sun nuna goyon bayansu a kan taron karatun Kur’ani na ƙasa da ake shirya gudanarwa a Abuja a ranar 22 ga watan Fabrairu. Shugaban ƙungiyoyin, Kwamred Murtala Mohammed Garba, wanda aka fi sani da Gamji, shi ne ya bayyana hakan a taron manema labarai a Abuja, inda ya bayyana cewa, suna yaba wa shugabannin Musulunci da suka shirya wannan taro kamar su Sarkin Musulmi, Imam Dahiru Usman Bauchi da Sheik Karibullah, da kuma Sheik Bala Lau. Yadda ake wasan ɓuya tsakanin ’yan gudun hijira da jami’an tsaro a Abuja Dangote ya karya farashin man fetur Ya ce, irin wannan taro na masu kishin Kur’ani, wanda ba a taɓa yin irinsa ba a Nijeriya,...

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba. “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama. “Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.” Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don...
Mayaƙan Boko Haram aƙalla 5,000 da suka tuba sun koma cikin al’umma da iyalansu, a cewar Cibiyar Yaƙi da Ta’addabnci na Ƙasa. Cibiyar, wadda ke ƙarƙashin Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa Kan Sha’ani Tsaro ta bayyana cewa babu ko mutum ɗaya da cikin tubabbun mayaƙan na Boko Haram da ya sake ɗaukar makami. Ta bayyana cewa gwamnatin Jihar Borno ta tabbatar cewa wata shida bayan kammala ba su horo da sauya tunanin tsofaffin mayaƙan, amma har yanzu babu labarin ko mutum ɗaya daga cikinsu da ya yi tubar muzuru. Shugabar Sashen Daƙile Rikice-rikice Masu Alaƙa da Tsattsauran Ra’ayi (PVEA) ta Cibiyar, Ambasada Mairo Musa Abbas, ce ta bayyana haka a yayin taron gwamnonin yankin Tafkin Chadi a Maiduguri, Jihar Borno. NAJERIYA...
Ya gargaɗi kamfanonin da suka samu kwangilar da su tabbatar da ingantaccen aiki, tare da jaddada cewa za a hukunta duk wanda ya kasa cika sharuɗan aikin. Sannan, ya buƙaci direbobin manyan motoci da su guji lodin da ya fi ƙarfin titin domin kare lafiyar matafiya da rage hatsari. Don haka, gwamnati za ta kafa kwamiti don tabbatar da bin doka da oda a kan titin. Kwamishinan ayyuka na jihar, Injiniya Abdullahi Umar Faruk, ya bayyana cewa kashi 40 na kuɗin aikin an riga an biya. Ya ce an biya kamfanonin kuɗin kamar haka: Kamfanin ZBBC zai shimfiɗa titin daga Dabai zuwa Mahuta (kilomita 25) a kan Naira biliyan 18. Kamfanin Habib Engineering LTD zai yi aikin daga Mahuta zuwa...
Tinubu ya gode wa shugaban Bankin Duniya, Ajay Banga, da shugaban Bankin Raya Ƙasashen Afirka, Akinwumi Adeshina, saboda ƙoƙarinsu na samar da karin wutar lantarki a Afirka. Ya kuma ce yadda masu zuba jari ke gamsuwa da shirye-shiryen gwamnatinsa ya sa aka samu jarin dala biliyan shida a ɓangaren samar da makamashi a shekarar da ta gabata. Hukumar IFC ta sanar da cewa za ta saka dala miliyan 70 domin taimaka wa ‘yan kasuwa su samar da wutar lantarki ta hanyoyin da ba sa gurɓata muhalli. Rahotanni sun nuna cewa Nijeriya na buƙatar aƙalla dala biliyan 23.2 domin inganta ɓangaren wutar lantarki da tabbatar da wadatarta ga al’umma. Taron ya samu halartar shugabannin ƙasashen Afirka da dama, ciki har da...
“Baya ga tsarin Daidaiton Jinsi, muna kuma ƙaddamar da Dokar Kare Al’umma a jihar Zamfara. Waɗannan matakai suna da muhimmanci don tabbatar da cewa tsarin zamantakewarmu yana da ƙarfi kuma ya dace da buƙatun mutanenmu, musamman ma masu rauni. “Dokar kare haƙƙin yara da dabarun aiwatar da ita sun ƙarfafa ƙudurinmu na kare haƙƙin yara da walwalarsu. A matsayinsu na ginshiƙin makomarmu, dole ne mu tabbatar da cewa yara suna cikin aminci da kulawa don cimma burinsu. “Dokar nakasassu ta jihar Zamfara ta nuna ƙudurinmu na kare haƙƙin nakasassu. Wannan na neman kawar da wariya da haɓaka damar shigarsu cikin al’umma. Mun haɗa da manyan masu ruwa da tsaki, ciki har da nakasassu, don tabbatar da jin muryoyinsu. “Saboda haka,...
Ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna (PPRO), DSP Mansir Hassan ba da aka tuntube shi har zuwa lokacin hada wannan rahoto.