Wasu sarakunan gargajiya na ta’ammali da ƙwayoyi — Obasanjo
Published: 16th, March 2025 GMT
Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya nuna damuwarsa kan yadda sarautar gargajiya ke rasa martabarta a ƙasar nan.
A cikin sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future’, ya bayyana cewa yanzu akwai masu laifi, ’yan daba, da masu safarar miyagun ƙwayoyi da suka zama sarakuna a wasu yankuna na Najeriya.
“A yau, akwai ’yan daba, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane da ake kira sarakuna,” in ji Obasanjo.
“Wannan abu ne mai matuƙar ban takaici, kuma yana daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya.”
Ya ce dole ne a dawo da mutunci da ƙimar sarautar gargajiya domin tana taka rawar gani a ci gaban ƙasa.
Har ila yau, ya gargaɗi shugabanni cewa idan ba su magance matsalolin da jama’a ke fuskanta ba, hakan na iya haifar da rikici a nan gaba.
“Idan gwamnati ba ta saurari kokensu ba—musamman matasa da suka fusata—to nan gaba abubuwa ba za su yi kyau ba,” in ji shi.
“Waɗanda suka hana a samu sauyi cikin lumana, za su gamu da sauyi ta hanyar tashin hankali.”
Obasanjo ya ƙara da cewa idan shugabannin Afirka suka yi watsi da wannan gargaɗi, hakan na iya haddasa rikici a nahiyar gaba ɗaya.
“Yin watsi da wannan gargaɗi kamar yin rawa ne lokacin da gidanka ke ci da wuta,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: gargadi Miyagun ƙwayoyi Najeriya Sarakunan Gargajiya
এছাড়াও পড়ুন:
Baffa Bichi da Barau Jibrin sun gana a Abuja
Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi da tsohon Kwamishinan sa ido da tantance ayyuka Muhammad Diggol sun gana da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau I. Jibrin a Abuja.
Taron ganawar wanda ya haɗa sauran masu ruwa da tsaki, ya mayar da hankali ne kan samar da ci gaba a Jihar Kano da kuma ciyar da ƙasa gaba.
MC Tagwaye ya fice daga APC zuwa SDP Wata mata ta faɗa ruwa ta mutu a LegasA wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Barau ya wallafa hotunan ganawar da aka yi tare da bayyana muhimmancin haɗin gwiwa wajen samun ci gaba mai ɗorewa.
“Ci gaban jiharmu da ƙasa a kodayaushe yana kan gaba a ajandarmu, za mu ci gaba da haɗa kai da sauran masu ruwa da tsaki domin ciyar da jiharmu da ƙasa gaba,” in ji shi.
Aminiya ta ruwaito cewa taron na daga cikin ƙoƙarin da shugabannin siyasa ke yi na yin cuɗanya da manyan mutane a ci gaban Jihar Kano da kuma yin aiki da manufa guda domin samun ci gaba.