2025-02-22@15:37:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1157

«gargadi»:

    Manufar ita ce a kawo karshen wannan tashin hankalin ta hanyar adalci, mai dorewa, wace dukkanin bangarorin da abin ya shafa za su aminta da ita” in ji Rubio ga menema labarai, duk da cewa babu jami’an Yukiren ko na Turai a wurin tattaunawar. A wani labarin kuma, shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya shaida wa...
    Kocin Manchester United Ruben Amorim ya bayyan cewar Kocin ƙungiyar ƙwallon kafa ta Everton David Moyes ba mutum ne wanda za a raina iyawarshi a harkar kwallon ƙafa ba, David Moyes ya na yin aiki mai kyau na farfado da Everton fiye da yadda na ke yi cikin ƙanƙanin lokaci a Old Trafford inji Amorim....
    Aƙalla mutum 12 — ciki har da mata huɗu da maza takwas — sun riga mu gidan gaskiya a sanadiyyar wani mummunan haɗarin mota da ya auku a kan hanyar Lapai zuwa Agaie da ke Jihar Neja. Wani da lamarin na safiyar wannan Asabar ɗin ya faru a kan idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Premier League ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu Eberton da Man United Premier League ranar Laraba 26 ga watan Fabrairu Man United da Ipswich English FA Cup ranar Lahadi 2 ga watan Maris Man United da Fulham.
    Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke, ya kaɗa ƙuri’arsa a zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a faɗin jihar a ranar Asabar. Gwamnan ya isa rumfar zaɓensa da ke Sagba/Abogunde, Ƙaramar Hukumar Ede, inda aka tantance shi kafin ya kaɗa kuri’arsa. Zaɓen, wanda ake gudanarwa don zaɓen sabbin shugabanni a ƙananan hukumomi 30 na jihar,...
    Sadiq S. Abacha, ɗan Tsohon Shugaban Mulkin Soji na Najeriya, Janar Sani Abacha, ya bayyana mahaifinsa s matsayin mutum mai nagarta duk da sukar da ake yi masa har yanzu. A wani rubutu da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Sadiq, ya ce an jima ana cin amanar mahaifinsa, amma tarihi zai yanke masa hukunci...
    Mai ba da shawara ga kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tabbas za a aiwatar da harin daukan fansa na “Alkawarin Gaskiya na 3” Mai ba da shawara ga babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Ibrahim Jabbari ya jaddada cewa: Tabbas za a gudanar da...
    Kungiyar Hizbullahi ta bayyana cewa: Ba su yarda kasar Lebanon ta mika kai ga haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka ba Mataimakin shugaban majalisar zartaswar kungiyar Hizbullah Sheikh Ali Damoush ya jaddada cewa: Ba zasu amince kasar Lebanon, mai cin gashin kanta ta kasance karkashin dokar haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka a karkashin matsin lamba da...
    Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila ya ba da umarnin tsananta kai hare-hare kan yankunan yammacin gabar kogin Jordan biyo bayan hare-haren bama-bamai da aka kai a birnin Tel Aviv Fira ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bada umarnin kai hare-haren wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijira na Tulkaram da ke...
    “Idan ba a dau matakin da ya dace akan abin da ke faruwa a DRC ba, al’amarin zai faskara. Ba batun fitar da takardar jawabin bayan taro ne kawai muke yi ba. Dole a biyo bayan hakan da wasu muhimman matakai ko tsare tsare da zasu tabbatar da cewa an gabatar da wadannan al’amura kan...
    Bayan shekaru 47, Faransa ta janye daga sansanin sojinta mafi girma a kasar Ivory Coast A hukumance Faransa ta mayarwa kasar Ivory Coast babban sansanin soji da ta mamaye kusan shekaru hamsin a kusa da birnin Abidjan, a wani bangare na yarjejeniyar da kasashen biyu suka kulla. Filin tashar jiragen ruwa na Port Bouet, wanda...
    Saudiyya Za Ta Haramta Shan Giya Lokacin Gasar Kofin Duniya
    Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Sibil Difens (NSCDC), a Jihar Yobe, ta kama wasu mutum 17 da ake zargi da satar kayayyakin lantarki, na’urorin sadarwa a jihar. Kwamandan rundunar, AS Dandaura, ya tabbatar da kamen a Damaturu, Babban Birnin jihar, inda ya ce an gano wuraren ajiya uku da ake amfani da su don ɓoye...
    Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana cewa ƙarin kuɗin makarantar Jami’ar Jihar Gombe (GSU) da kashi 120 cikin 100 ya zama dole domin tabbatar da ɗorewar ingancin ilimi a jami’ar. Gwamnan ya bayyana haka ne yayin rantsar da kwamitocin gudanarwa na manyan makarantu da hukumomin gwamnati, inda ya jaddada cewa kuɗaɗen makaranta na...
    Ana matukar bukatar jami’an ilimi saboda kuwa sune suke da alhakin tabbatar dukkan tsare tsaren ilimi da manufofi ana amfani da su kamar yadda ya kamata.Suna aiki da Shugabannin makarantu da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da dalibai suna msaun nagartaccen ilimi. Hakanan ma jami’an ilimi ma na bukatar su rika gabatar da...
    Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta ca zata saki ‘yan Isra’ila shida yau Asabar a matakin karshe na yarjejeniyar tsagaita wuta ta farko da ta cimma da Isar’ila. An kuma tsara Isra’ila za ta saki fursunonin falasdinawa Falasdinawa 602 a wannan Asabar a musayar wacce ita ce ta bakwai tun cimma yarjejeniyar a ranar 19...
    Iran ta jadadda anniyarta ta karfafa alaka da kasashen Afrika, kamar yadda ma’aikatar harkokin wajen kasar ta tabbatar. A cikin wani sako da ya aike ta shafin X a ranar Juma’a, kakakin ma’aikatar, Esmaeil Baghaei, ya yi tsokaci kan ganawar da aka yi a ranar Alhamis tsakanin mataimakin shugaban kasar na farko Mohammad Reza Aref...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Tawagogi na ci gaba da isa Beirut, domin halartar jana’izar tsohon sakataren kungiyar Hezbollah ta Lebanon mirigayi Sayyid Hassan Narsrallah. Iran, ma ta sanar da aikewa da wata babbar tawaga zuwa kasar ta Lebanon domin halartar jana’izar shahiddan Sayyid Hasan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine. A gobe Lahadi ne za a gudanar da jana’izar wadannan...
    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar...
    Shugabannin kasashen Larabawa sun tattauna kan batun Gaza dama halin da ake ciki  yankin. Bisa gayyatar Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman,  an gudanar da taron ‘yan uwantaka na yau da kullun a birnin Riyadh a ranar Juma’a inji kamfanion dilancin labaren kasar na SPA. Taron ya samu halartar sarki Abdullah II...
    Gwamnatin Jihar Yobe, ta rattaba hannu kan kwangilar gina gadar sama da titin ƙarƙashin ƙasa a tsakiyar garin Damaturu, Babban Birnin Jihar, kan kuɗi Naira biliyan 22.3. Wannan wani mataki ne na ci gaba a ƙoƙarin gwamnatin samar wa al’umma ababen more rayuwa. Sanata Katung ya damu kan yadda wasu ta’azzara ta’addanci a kudancin Kaduna...
    Arangama Tsakanin NLC Da Gwamnatocin Soji Ga duk mutumin da yai duba na tsanaki ga hakikanin manufofin samar da wannan kungiya ta NLC, la-budda, wajibi ne a rika samun sa-toka-sa-katsi tsakaninta da gwamnatoci musamman irin na Soja. Ba kawai gwamnatocin soja ba, da tafiya ta kara nikatawa kamar yadda za a gabatar nan gaba cikin...
    Sanata Sunday Marshall Katung, mai wakiltar Kudancin Kaduna a Majalisar Dattawa, ya bayyana damuwarsa kan yadda wasu mazauna yankin ke taimaka wa miyagu wajen aiwatar da ayyukan ta’addanci. Da yake magana a taron manema labarai na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Kudancin Kaduna (SKJF) a Zonkwa, hedikwatar Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf, Sanata Katung, ya jaddada cewa...
    Karamar hukumar Birnin Kudu dake Jihar Jigawa ta ce za ta dauki nauyin dalibai ‘yan asalin yankin su 80 da ke kwalejin Ilmi ta tarayya ta Jama’are a Jihar Bauchi, da kwalejin fasaha ta Dutse da kuma kwalejin fasahar sadarwa ta Kazaure. Shugaban Karamar Hukumar, Dr. Muhammed Uba Builder ya bayyana haka ga manema labarai...
    Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Taimakawa Shirye-shiryen Zabe A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya
    Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ƙasa (TCN), ya bayyana cewa wasu yankunan Abuja za su fuskanci katsewar wuta a ƙarshen mako saboda aikin gyara da za a yi wa na’urorin lantarki. A wata sanarwa da kamfanin ya fitar a ranar Juma’a, ya ce ana yin wannan aikin ne na shekara-shekara, kuma za a gudanar da...
    Ƙasurgumin fitaccen shugaban ‘yan Bindiga, Bello Turji, ya ƙaƙaba harajin Naira miliyan 22 a wasu ƙauyuka huɗu na jihar Sokoto, kan kashe ɗaya daga cikin mutanensa a wani samame da sojoji suka yi a yankin. Acewar mutanen yankin, wannan harajin, yana matsayin diyya ga makaman da suka bace yayin artabun da mutanensa suka yi da...
    Bugu da kari, ministan ya ce bana lokaci ne na Afrika, duba da cewa za a gudanar da taron kolin G20 a nahiyar Afrika a karo na farko tun bayan da AU ta zama cikakkiyar mamba. Ya ce ya kamata a saurari kiraye-kirayen nahiyar, a kuma yi la’akari da damuwarta, kana a taimakawa ayyukanta da...
    Daftarin Sin Ya Samar Wa Kamfanoni Masu Jarin Waje Damammaki Masu Kyau
    Ma’aikatan Gidan Rediyon Tarayya (FRCN) da na Hukumar Gidan Talabijin ta Najeriya (NTA) da suka yi ritaya, sun bayyana jin dadinsu kan karin haske da Ministar Kudi ta yi game da wadanda za su ci gajiyar Naira Biliyan 758 da aka amince da su don biyansu kudaden fansho da suke bi. A tsokacin da suka...
    Fitaccen dan jarida na Amurka wanda  Patrick Heili ya yi hira da shi ta  Podcast, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son ya ci gaba da zama akan kujerar mulki har abada. Hirar da Thomas Friedman ta mayar da hankali ne akan salon mulkin Donald Trump da yadda yake son sauya yadda...
    Wanda ya jagoranci sallar juma’a a yau a birnin Tehran  Hujjatul-Islam Wal Muslimin Muhammmad Hassan Abu Turabi Fard, ya ce; makiyan jamhuriyar musulunci ta Iran suna magana da sauti daya,yayin da juyin juya halin musulunci na Iran ya hada kasashen Lebanon,Yemen, Falasdinu,Iraki da wasu kasashen musulmi. Limamin na Tehran ya kara da cewa, lokaci ya...
    Kungiyar wasan Kareti ta Iran ta zama ta daya a nahiyar Asiya, yayin da Iraki ta zo ta biyu sai kuma Tajikistan ta uku. An yi wannan gasar ne ta Asiya a garin Calus dake Arewacin Iran wanda ya sami halartar kasashe da dama. Daga cikin kasashen da su ka shiga gasar wasannnin da akwai...
    Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai  hada kasashe da dama na yankin. ‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu...
    A kasar Malaysia an bude yin kira da a yanke kere-keren kamfanin Elon Musk saboda goyon bayan da yake nuna wa Donald Trump da siyasarsa ta son korar Falasdinawa daga Gaza. Mutanen kasar ta Malaysia ne suke amfani da kafofin sadarwa na al’umma wajen yin kira da a yanke mu’amala da motocin da kamfanin na...
    Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke ya ce ya sha alwashin cewa zaɓen ƙananan hukumomin da za a yi a jihar a gobe Asabar zai gudana kamar yadda aka tsara. Gwamnan ya bayyana hakan ne a matsayin martani kan shawarar da ministan shari’a na Najeriya, Lateef Fagbemi, wanda ya buƙaci gwamnatin jihar ta dakatar da yunƙurin...
    A yau Jumma’a ne jirgin saman da kasar Sin ta kera samfurin AS700D mai amfani da makamashin lantarki ya kammala tashinsa na farko cikin nasara, wanda ya nuna sabon ci gaban da kasar ta samu a sashen samar da kayayyakin sufurin jiragen sama masu amfani da makamashi mai tsafta a fannin tattalin arzikin jirage masu...
    Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, ya bayar da umarnin dakatar haƙar ma’adanai a faɗin jihar daga ranar 21 ga watan Fabrairu, 2025. Ya yanke wannan shawara ne saboda ayyukan haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida wanda ke da alaƙa da laifuka da suka shafi ta’addanci, satar mutane, da fataucin miyagun ƙwayoyi. Najeriya ta taɓarɓare bayan mulkin...
    Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin...
    Dan takarar shugaban ƙasa a Jam’iyyar Leba (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce Najeriya ta daɗa taɓarɓarewa fiye da lokacin da tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida ya bar mulki a shekarar 1992. Obi ya bayyana haka ne a lokacin da yake tsokaci kan ƙaddamar da littafin tarihin Babangida da...
    Shirin karfafa karatun mat (AGILE), ya fara horar da Malamai 20 na kwanaki 3 domin gudanar da shirin ba da ilimi na zamani mai suna dama ta biyu ta samun ilimi. “Second chance education bangaren” a Kano. Shugabar Bangaren Aikin, Miss Hafsat Adhama, ta bayyana haka a wajen taron cin abincin rana da aka gudanar...
    Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Legas ta bayar da umarnin a ƙwace Dala miliyan 4.7 da Naira miliyan 830 da wasu kadarori da dama da ke da alaƙa da tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) Godwin Emefiele. Da yake yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Yellim Bogoro, wanda a baya ya...
    Rundunar ’Yan Sandan Jihar Borno, ta daƙile wani yunƙuri da ’yan bindiga suka yi na sace wani mutum a Sabon Garin Lassa da ke Ƙaramar Hukumar Askira Uba. Rundunar ta kuma cafke wasu mutum uku tare da ƙwato wata bindiga ƙirar gida a hannunsu. Babban mai kai wa Bello Turji makamai ya shiga hannu NAJERIYA...
    daya daga cikin masu sana’ar a yankin Yashin Tuwo a karamar Hukumar Karim-Lamido a jihar, Mallam Dauda Adamu, ya tabbatar da wannan kalubalen da masu sana’ar ke fuskanta a jihar, inda ya sanar da cewa, lamarin ya tilasta wasu masu sana’ar rungumar aikin noma da kama wasu sana’oin daban, domin samun kudaden shiga. “A baya...
    Jami’an Tsaro a Jihar Sakkwato, sun kama babban mai yi wa Bello Turji safarar makamai, mai suna Hamza Suruddubu. Rahotanni sun bayyana cewar ana zarginsa da yi wa wasu maharan safarar makamai a jihar. An tara Naira 16 a taron ƙaddamar da littafin IBB Ba ni da hannu a kisan Dele Giwa — Janar Babangida...
    Sun ci gaba da cewa, tattalin arzikin ya karu zuwa kaso 3.5, a zango na uku a 2024, daga kaso 3.2 a zango na biyu a 2024. A cewarsu, Nijeriya ta samu wannan nasarar ce, saboda tsaurara tsare-tsaren hada-hadar kudade, inda kuma fannin da bai shafi Man Futur na kasar ba, ya bayar da gagarumar...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhafa barakammu da  sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau, shiri wanda yake kawo maku labarai masi muhimmanci a wannan makon wadanda suka hada da wadanda suka shafi siyasa tattalin arziki zamantakewa tsaro na sauransu, da fatana masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu...
      Tarkon Dark Web: Wasu yara na iya fada cikin rukunin yanar gizo da ke da hadari.   Dabara Da Yaudara A Wasanni (Gaming Scams): Wasu yara na fuskantar barazana a cikin wasannin da suke bugawa online. Yadda Za A Kare Yara Daga Wadannan Barazanar Iyaye su lura da abin da yaran su ke yi...