Duniyarmu A Yau: Shiri Kasashen Yamma Na Kashe Dukkan Falasdinwa A Gaza
Published: 25th, April 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gbaata wadanda suka shafi siyasa, tsaro tattalin arziki zamantakewa da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu.
///… Madalla, masu sauraro shirimmu nay au zai yi Magana dangane da Yakin da Amurka take yi a tekun maliya kan kasar Yemen da kuma yadda kasashen yamma suke son su fitar da kwararru daga cikin zirin gasa don amfani kansu sannan su ga kashe dukkan Falasdinawa da suke yankin.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya bada labarin cewa, aikin sojen da gwamnatin shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fara a tekun red sea kan kasar Yemen, don amintar da jiragen Ruwan kasuwanci na HKI a cikin Tekun, ya zuwa yanzu bai kai ko in aba, kuma ya kasa samun nasar. Wato har yanzon jiragen Ruwan kasuwanci na HKI har da na Amurka sun kasa wucewa cikin tekun maliya saboda hare-haren da mayakan Huthi na kasar Yemen suke kai masu.
Mujallar labarai ta Amurka, mai suna ;Foreign Policy, ta bayyana cewa dukkan hare-haren da jiragen yakin amurca suke kaiwa kan sojojin kasar Yemen, da kuma gwamnatin coton kasa ta kasar Yemen basu yi tasirin da zai sa suka daina kaiwa jiragen Amurka da HKI na kasuwanci wucewa ta tekun ba makonni 5 da fara yakin.
Banda haka wasu matsalolin sun bayyan wadanda suka Sanya tababa kan idan har gwamnatin Trump zata sami nasara a kan huthawa a wannan yakin, inji mujallar.
Mujallar ta kara jaddada cewa, gwamnatin kasar Amurka ta kasa maida tekun Maliya ko re sea, amintacce ga jiragen kasuwanci na HKI da Amurka. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya kara da cewa kuma babu wata alama kan cewa zata cimma wannan manufar nan kusa.
Har’ila yau kamfanin dillancin labaran FP ya kara da cewa, dokar hana jiragen HKI da Amurka wucewa da tekun maliya da kuma mashigar ruwa ta Suiz na kasar Masar, ya zuwa yanzu ta jawowa kasashen biyu asarar dalar Amurka billiyon guda.
Gwamnatin kasar Yemen ta bayyana cewa idan Amurka ta kuskura ta shiga rigimar kasar Yemen da kasashen yankin, to kuwa zata kara yawan hare-haren da take kaiwa HKI da kuma jiragen yakin Amurka a yankin.
A wani labarin kuma, masana sun ce wanda shi ne yaki mafi girma wanda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya shiga tun bayan dawowarsa fadar White House a farkon wannan shekarar, amma ma’aikatan tsaron kasar Amurka da kuma cibiyar yada labaran yaki ta Amurka (CENTACOM) basu bayyana kome dangane da yadda yakin amurca a kasar Yemen yake tafiya. In banda nuna hotunan jiragen yaki suna tashi daga sansaninsu da ke kan jiragen Ruwan yaki a cikin Tekun Red Sea.
Wani abin damuwa jiragen yakin Amurka basa tashi daga sansanoninsu kan wadannan jiragen ruwa guda biyu sai da dare. Alhali an tsarasu ne, don aiki dare dara, watakila suna taka tsan-tsan ne, da kasar China, wacce mai yuwa Amurka zata fafata da su nan gaba ko kuma a kasar Taiwan.
Banda hakan, a halin yanzu sake bude tekun maliya ko red Sea don jiragen kasuwanci nan kusa, yana da wuya, saboda yakin kasuwancin da shugaba Trump y afara da kasashen duniya da dama.
A halin yanzu yawan jiragen ruwa dauke contenoni, masu bin ta tekun ya ragu kwarai. Saboda kudaden fiton da Amurka ta dorawa kasashen China da sauran kasashen duniya ya rage harkokin kasuwanci a duniya gaba daya. Kuma banda haka a halin yanzu mafi yawan jiragen Ruwan kasuwanci sun Fifita bin ta kasar Afrika ta kudu saboda yakin da ke faruwa a tekun na Maliya, ko da kuma basa daga cikin kasashen da kasar Yemen ta hana wucewarsu a cikin tekun.
Tun ranar 25 ga watan Maris na wannan shekara ne, shugaban kasar Amurka ya fara yaki da kasar Yemen don tallafawa HKI, kan dokar hana jiragen kasar da kuma masu zowa kasar wucewa ta Tekun na Red Sea. Hare-haren dai sun kashe daruruwan mutane, mafi yawa fararen hula a cikin kasar ta Yemen. Amma gwamnatin kasar Amurka bata taba bayyana asarorin da ta yi a yakin da take fafatawa da kasar Yemen ba.
A dayan bangaren kuma, a manufarsu ta tallafawa Falasdinawa wadanda sojojin HKI takewa kisan kiyashi a Gaza, sojojin kasar Yemen sun ci gaba da kai hare-hare a cikin HKI, wato a kan birnin Yafa, ko (telaviv, da makamai masu linzami safurin bilistic, sannan sukan kai hare-hare kan katafaren jiragen yakin Amurka, kuma sansanonin jiragen yaki wadanda suke cikin tekun Maliya da kuma tekun Indiya.
Banda haka ya zuwa yanzu sojojin yemen sun kakkabo jiragen yaki ko kuma masu lekin asiri, wadanda ake sarrafasu daga nesa wato Drone samfurin MQ 9 na kasar Amurka 20 ya zuwa yanzu.
A wani labarin kuma wata kungiyar kare hakkin bil’adama mai suna ‘the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor’ ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da Kuma HKI na fitar da kwararru daga kasar Falasdinu don amfana da su.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto shugaban kungiyar (EMHRM) Ramy Abdu yana fadar haka, a ranar Talatar da ta gabata, ya kuma kara da cewa, awai wani shiri wanda ofishin jakadancin kasar Faransa dake birnin Qudus tare da hadin kai da HKI suka fara gudanarwa, don zakulo masana, kwararru a fannonin ilmi daban -daban a cikin Falasdinawa a Gaza, su fiddasu daga yankin don amfanina da ilminsu nan gaba. Rahoton ya kara da cewa, wadannan kwarrarun sun hada da duk wanda yake da digiri na uku wato PHD a ko wani fanni na ilmi, da likitoci,injiniyoyi, masna tarihi, da kwararru a ayyukan bincike na tarihi da sauransu. Sannan su aiwatar da Shirin share zirin Gaza daga dukkan Falasdinawa mata da yara da sauransu daga Gaza.
Rahoton ya kara da cewa wannan Shirin yana da marhaloli guda biyar, kuma tuni yahudawa sun fara aiwatar da su a hankali a kuma boye. Abdu ta kara da cewa wannan Shirin dai ya sabawa dokokin kasa da kasa, kuma kasar Faransa tana iya fuskantar sharia idan ha rya tabbata tana da hannu a cikinsa.
Abdu ya kara da cewa, abinda HKI ta kasa samu da makamanta a Gaza, zata kai gareshi da wannan Shirin, tare da amfani da kungiyoyin kare hakkin bil’adama. Kuma mataki na farko shi ne, hana abinci da Ruwan sha da sauransu shiga zirin gaza, wanda hakan zai samar da yunwa a cikin falasdinawa a Gaza, sannan ya kai ga dan karamin cuta zata kashesu, sannan wadanda suka ji Rauni a hare-haren da HKI take ci gaba da kaiwa a yankin ba zasu taba warkewa ba har sumutu.
Sannan mataki nag aba shi ne wargaza tsarin kiwon lafiya a gaza, rusa asbitoci kissan likitoci wadanda basu sami damar fiddasu daga yankin ba, wanda hakan zai kara saurin mutuwarsu, saboda kananan cutukktuka zasu kashesu, sannan babu likitocin da zasu kula da su.
Jaridar kasar Burtaniya (Middles east Eye) ta kasar Burtania ta yi ishara da wannan shirin, inda ta bayyana cewa, Shirin na da marhaloli 5, kamar yadda muka fada, kuma marhala ta karshe itace karsa falasdinwa da suka rage, sannan daga baya su fara marhala ta kafa dokoki wadanda zasu tabbatar da yankin Zirin Gaza, a matsayin bangare na HKI.
Tun bayan fara yakin Tufanul Aksa ne, a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023, yahudawan Sahyoniyya suka fara tunanin fidda dukkan Falasdinawa a Gaza, don yankin ya zama ta yahudawa zalla, haka ma yankin yamma da kogin Jordan.
Jaridar ta Middle east eye, ta kara da cewa a halin yanzu an fara aiwatar da wasu daga cikin wadannan marhaloli kamar yadda kowa yake gani, a halin yanzu an kusan watanni biyu da hana shigowar abinci a cikin Gaza, kuma alamun yanwa sun fara bayyana a cikin falasdinawa a Gaza, musamman a cikin yara. Don haka wannan halin zai ci gaba harm ai yuwa ya kai ga yawan falasdinawa da suke mutuwa a Gaza, saboda yunwa da Rashin rafiya fa karancin jami’an jinya sai ya wuce adadin da sojojin yahudawan suke kashewa a ko wace rana da makamai.
Yahudawan suna fatan idan sun kai ga marhala ta 5 bukatarsu zata biya, kuma babu wani bafalasdine da zai rage a zirin Gaza a lokacin da suka kai ga wannan marhalan.
Kafin haka dai shugaban kasar Amurka Donal Trump ne ya fara gabatar da wannan shawarar da korar Falasdinawa daga Gaza, amma duk da haka ba shi ne da tunanin hakan tun asali ba. Wannan tunanin tana daga cikin manufofin yahudawan Sahyoniyya tun asalin kafa HKI da sunan samar da kasa mai tsarki da yahudawa zalla.
Banda hala labarin ya kara da cewa idan har wannan Shirin bai kai ga biyan bukata ba, suna da wani shiri na daban, wanda suna ganin zai kammala wanda aka fara. Don Shirin ya fi hatsari kuma yafi muni ga Falasdinawa. Wannan dai Shirin shiri mafi muna da kisan kare dangi a karni na 21TH.
Ya zuwa yanzu dai falasdinawa fiye da dubu 52 ne sojojin yahudawan suka kashe, mafi yawa daga cikinsu mata da yara ne, sannan wasu fiye da 112 ne suka ji Rauni. Banda haka sojojin yahudawan sun hana shigowar abinci da Ruwan sha da magunguna da sauran bukatun Falasdinawa a gaza, fiye da wata biyu da suka gabata.
Masana kan rikicin gabas ta tsakiya dai suna ganin za’a dade ana wannan rikicin, amma daga karshe ko ba dade ko ba jima, wannan kasar yahudawa kan kasar Falasdinu ba zai ci gaba da kasance a wannan yankin ba. Musamman ganin cewa al-amarin Falasdinawa kuma, bai takaita da larabawa da yahudawa ba.
Al’amarin ne wanda ya shafi dukkan kasashen duniya, kuma ko wace kasa a duniya tana da ra’ayi kan rikicin. Daga ciki kasar Afirka ta kudu ta shigar da kara a kotun ICC kan cewa HKI tana aikata kissan kiyashi a Gaza, kuma har kotun a karon farko tun bayan kafuwar kasar ta fidda sammacin kama firai minitan HKI da kuma tsohon ministansa na yaki Galant.
Banda haka da dama daga mutanen kasar Amurka da kasashen yamma, musamman daliban jami’o’ii suna fitowa zanga-zanga don yin allawadai da gwamnatin kasar Amurka wacce ta kasance babban mai tallafawa HKI da makamai, sannan sun dora laifin ci gaba da yaki a gaza, kan gwamnatin kasar ta Amurka.
Sannan a matakan da gwamnatin kasar Amurka take dauka don hana daliban jami’o’ii zanga zanga a jamimi’o’insu, ya zuwa yanzon an kama dalibai da dana an kulla wasu kuma har gurfanar da su a gaban kotuna tare da tuhumarsu da kin abinda suka kira samawa. Ko yahudawa.
Har’ila yau a kasar ta Amurka gwamnatin gwamnatin kasar ta bata visar zaman a kasa ko kuma Green Card na daliban jami’o’ii daban daban har fiye da 300. A kasashen Turai musamman ingila da Faransa sun dauki matakai da dama na murkushe dalibai da sauran mutanen kasashen masu goyon bayan Falasdinawa.
Kasar Jamus tana ci gaba da daukar matakai kan masu goyin bayan Falasdinawa a kasar. Ta kori yan jarudu da damad aga ayyukansu saboda goyon bayan Falasdinawa. Kuma suna daukar wasu matakan don dakile duk wanda yake goyon bayan Falasdinu a kasar.
A kasar Amurka wata ma’aikaciyar kamfanin sadawar ta google ta hau kan babban darectan bangaren sadarwa ta AI Dr Musfafa, inda take zarginsa da tallafawa HKI da fasahar Ai ko kirkirerren kwakwalwa a yayin da take fafatawa da Falasdinawa.
Masu sauraro a nan zamu dasa aya a cikin shirimmu na yau sai kuma wata fitowa idan All..ya kaimu wassalamu alaikum wa rahamatullahi wa barakatuhu.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: gwamnatin kasar Amurka shugaban kasar Amurka Falasdinawa a Gaza Falasdinawa a gaza falasdinawa a Gaza dillancin labaran ya kara da cewa ya zuwa yanzu jiragen Ruwan a kasar Yemen A halin yanzu jiragen yakin wannan Shirin a halin yanzu hare haren da kasuwanci na jiragen yaki tekun maliya masu sauraro da sauransu
এছাড়াও পড়ুন:
Sojonin Yemen Ta Kakkabo Jiragen Yakin Amurka Wadanda Kimarsu Ya Dalar Amurka Miliyon $200 A Makonni 6
Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal.
Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar ta Yemen, kuma duk da cewa suka tashi fiye da kafa 40,000 a sama, amma sojojin yemen suna iya kakkabosu.
Wannan yana zuwa ne a dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donar Trump ya kara umurnin a kara yawan hare-haren da ake kaiwa kasar ta Yamen.
Mafi yawan hare-haren da suke kaiwa yana kasa mata da yara da kumalalata kamfanoni da kuma cibiyoyin samar da ruwa ko ajiyar makamashi ne .
Don haka hare-haren basa kaiwa ga makaman sojojin kasar Yemen wadanda suke karkashin kasa kuma nesa daga inda makaman Amurkka zasu samesu.
Amurka dai ta fara yake da Yemen ne don tallafawa HKI kan hare –haren sojojin yemen kanta tun baya sake dawoda yakin dofan al-aksa.