2025-03-21@19:41:02 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2326
«hare haren da»:
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

An Zabi ‘Yan Kasar Zimbabwe Kuma Mace Ta Farko A Matsayin Shugabar Shugabar Kwamitin Wasannin Olympic
‘Yar kasar ta Zimbabwe Kiristy Coventry ta zama mace ta farko daga fito daga nahiyar Afirka,kuma mace da za ta rike shugabannin hukumar wasannin Olympic. An zabi Kirsty ‘yan shekaru 41 ne a yayin kada kuri’a ta sirri da aka yi da ‘yan takara 7 su ka yi gogayya. An yi zaben ne ne a yayin taron hukumar ta Olympic karo na 144, a birnin Costa, Navarino a kasar Greece a jiya 20 ga watan nan na Maris. Gabanin zabenta dai , Kirsty ta kasance wacce ta zama gwarzuwa ta iyo har sau biyu a wasannin Olympic. Za ta fara aikin nata ne na shugabancin hukumar wasannin Olympic a ranar 23 ga watan Yuni, da za ta gaji Thomas Bach...
Sun kuma bayyana cewa, wajibi ne gwamnati ta mayar da hankali wajen inganta manyan makarantun da ake da su na tarayya da kuma jihohi, ta hanyar samar da wadatattun kudade, inganta abubuwan more rayuwa da kuma tabbatar da ganin ma’aikatan jami’i’on, sun samu horo na musamman da suke bukata da kuma tallafa musu. Wani mai ba da shawara a kan harkokin binciken ilimi a Jami’ar Abuja, Humphrey Ukeaja, ya gano wasu damammaki da kalubale iri-iri da aka samu kwanan nan. Masanin ya yi nuni da cewa, rashin samun wadatattun kudade a fannin ilimi a Nijeriya, ya zama wani babban al’amari. “Idan kuna son yin wannan sauyi misali, mayar da jami’i’o’i zuwa na gwamnatin tarayya, har yanzu a kwai ayar tambaya,...
Sojojin Sudan sun sanar a yau Juma’a cewa sun kwace iko da fadar shugaban kasa dake tsakiyar birnin Khartum, bayan da su ka kori mayakan rundunar kai daukin gaggawa. Majiyar ta ce, sojojin na Sudan sun fara da kutsawa cikin fadar shugaban kasar ne, ta mashigar gabas,bayan da su ka kashe mayakan rundunar kai daukin gaggawa da dama,yayin da wasu da dama su ka gudu zuwa cikin kasuwar dake kusa. Bayanin da sojojin na Sudan su ka fitar ya kunshi cewa; Mun murkushe mayakan Duqlu, ‘yan ta’adda a tsakiyar birnin Khartum da kuma kasuwar Larabawa da ginin fadar shugaban kasa da sauran ma’aikatu.” Har ila yau majiyar sojan na Sudan ta ce,su kuma yi nasarar rusa makamai da motocin yakin...

Cibiya Mai Fafutukar Kare Hakkokin Falasdinawa “Global 195” Ta Shelanta Farautar Sojojin HKI Da Su KaTafka Laifukan Yaki
Cibiyar ta “ Global 196” ta bakin babban shugabanta ta sanar da cewa a cikin watanni 18 da su ka gabata, ta tattara bayanai akan laifukan yakin da Isra’ila ta tafka a Gaza.” Haka nan kuma cibiyar mai matsuguni a Birtaniya ta ce, ya zuwa yanzu ta tattara da dalilai da su ka dace da ka’idojin shari’a a kotunan manyan laifuka na kasar. Har ila yau cibiyar ta ce, bayan kammala tattara bayanai a zango na farko, za kuma ta bude shafi na gaba domin kara samun wasu bayanan da za su tabbatar da cewa an yi wa Isra’ilawan hukunci a cikin kasashen duniya, musamman masu dauke da zama ‘yan kasashe biyu. Wani shiri da wannan cibiyar take da shi,shi...
Jaridar “Yediot-Ahranot” ta buga wani rahoto da yake kunshe da gargadi daga jami’an sojan mamaya akan yadda ake samun koma baya na sojojin sa-kai saboda da dalilai mabanbanta. Daga cikin dalilan da jaridar ta bijiro da su da akwai gajiya da yaki na lokacin mai tsawo da HKI ta shiga, sai kuma matsaloli na tattalin arziki da kashe kudade masu yawa wajen kula da su. Haka nan kuma manyan jami’an sojan mamayar sun bayyana yiyuwar rusa rundunar sojan sa-kai din saboda babu wadanda su ka dace su jagorance ta, ga kuma tsadar tafiyar da rundunar kamar yadda jaridar ta “Ahranot” ta bayyana. Ita kuwa jaridar “Financial-Times” ta bijiro da tata majiyar da take cewa; Yakin da ba shi da ranar...
Sai dai, bisa ladabi da girmamawa ga masarautu, Gwamna Bala Muhammad ya amince da roƙon ɗage Hawan Daushe. Duk da haka, gwamnatin ta nuna damuwarta kan yadda ba a tuntuɓe ta ba kafin yanke wannan shawara. Ta kuma jaddada cewa za ta ci gaba da aiki tare da sarakuna domin kyautata zamantakewa da ci gaban jihar. Ga mutanen da wannan ɗagewa ta shafa, gwamnati ta fahimci damuwarsu, amma ta yi alƙawarin ɗaukar matakan da suka dace a nan gaba don kauce wa irin wannan matsala. Gwamnan ya yi fatan jama’a za su yi bikin Sallah cikin lumana da farin ciki. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Wata gobara da ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Munna Albadawi da ke ƙaramar hukumar Jere a Jihar Borno, ta lalata wasu gidaje 10 tare da salwantar da rayuwar yaro mai shekara 7 mai suna Abubakar Gargar. A cewar shugaban sansanin, Babangida Mahmud gobarar ta tashi ne da misalin ƙarfe 3:00 asubahin safiyar ranar 20 ga watan Maris, 2025, inda gobarar ta laƙume kayayyakin abinci da tufafi da dai sauran kayayyaki. Taƙaddama: An kama wanda ya daɓa wa matarsa wuƙa ta mutu ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Wanda kawo yanzu ba a tantance adadin asarar da ta haifar ba baya ga salwantar rai guda. Hukumar kashe gobara ta Jihar Borno tare da haɗin...
Rundunar ‘yan sandan Jihar Legas ta sanar da kama Mista Peter Dike da ake zargi da kashe matarsa a gidansu da ke Unguwar Oke-Ira Ilogbo Eremi, Marogbo. Rundunar ’yan sandan a ranar Alhamis ta bayyana cewa wanda ake zargin ya daɓa wa matarsa wuƙa har lahira a lokacin da suka yi ƙazamin faɗa da ya ɓarke a gidan nasu sanadin taƙaddama a ranar Laraba. ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe Shahararren ɗan kasuwa Nasiru Ahali ya rasu a Kano Wannan mummunan al’amari ya ƙara dagula al’amuran tashin hankali a cikin gidan ma’aratan da ya kawo sanadin mutuwar matar aure. A watan Oktoban 2024, an kuma kama Motunrayo Olaniyi da laifin daɓa wa amaryarsa, Olajumoke wuƙa har...
A halin yanzu, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da wasu ƙungiyoyin jin-ƙai sun tura wakilansu don duba girman ɓarnar da gobarar ta haifar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
An yi taron tattaunawar kasa da kasa mai taken “Sin a lokacin bazara: More damammakin da take samarwa a duniya” a birnin Havana dake kasar Cuba, a ranar 19 ga wannan wata, inda shugaban CMG Shen Haixiong da jakadan Sin dake kasar Cuba Hua Xin suka gabatar da jawabi. Mahalarta taron fiye da dari sun tattauna kan damammakin da tsarin zamanantar da al’ummar Sinawa na Sin ke samar wa kasar Cuba da yankin Latin Amurka. Har ila yau, duk dai a wannan ranar, an yi taron tattaunawar a birnin Doha dake kasar Qatar, inda shugaban CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabi ta kafar bidiyo. Kana, mahalartar taron sun tattauna kan samun bunkasa mai inganci da damammakin da Sin ta...
Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani jami’in Hukumar kiyaye haɗɗura ta ƙasa (FRSC) Nathaniel Terwanger Kumashe a ƙauyensa da ke ƙaramar hukumar Tarka a Jihar Benuwe. An samu rahoton cewa wanda aka yi garkuwan ya taso ne daga Makurdi sansaninsa, domin halartar jana’izar ɗan uwansa da ya rasu a lokacin da aka ɗauke shi zuwa wani wuri da ba a san inda yake ba. Nasiru Ahali Shahararren masanin masana’antu a Kano ya rasu Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP Wani kawun wanda aka yi garkuwan, tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Benuwe shawara kan harkokin sufuri, Cif Yimam Aboh, ya shaidawa manema labarai a Makurdi ta wayar tarho cewa an ɗauke jami’in, Insfekta Kumashe a...
Kwamishinan ‘Yansandan ya yaba wa jami’an da suka gudanar da wannan aiki, inda ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar Kano. Dukkanin waɗanda ake zargi suna cikin bincike a sashen binciken laifuka na CID, kuma za gurfanar da su gaban shari’a bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Allah Ya yi wa Alhaji Nasiru Ahali, Shugaban Kamfanin Mainasara & Sons, rasuwa. Marigayin wanda yake shahararren masanin masana’antu ne ya rasu yana da shekara 108. Sojoji sun ceto mutum 84 da ’yan bindiga suka sace a Katsina Kotun ƙoli ta tabbatar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP A cewar majiyoyin na kusa da iyalan marigayin ɗan kasuwar ya rasu ne a wani asibiti da ke Kano a daren ranar Alhamis. Ana girmama Ahali a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan masanin asalin masana’antu a Kano. Ya yi ƙoƙari ya kafa tsarin kasuwanci na yau da kullun. A tattaunawarsa da Daily Trust a shekarar 2018, marigayi Ahli ya bayyana cewa sana’arsa ta haɗa da buga littattafai, bugu takardu, masana’antar bulo, sana’ar...
Ya nemi wadanda har zuwa yanzu ba su dawo da fom dinsu ba da hoto da su gaggauta yin hakan domin su samu biza daga kasar Saudiyya Arabiyya. Shugaban ya nemi maniyyatan da su bai wa hukumar cikakken hadin kai domin samun nasarar gudanar da aikin hajjin cikin nasara da kwanciyar hankali. Bayanai sun yi nuni da cewa wadanda suka fara ajiye kudin kujeru amma ba su kammala biya ba su na da zabin ko su amshi kudadensu ko su bari a asusun hukumar har zuwa aikin hajjin badi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
Dakarun Sojin Najeriya sun kuɓutar da mutum 84 da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a Ƙaramar Hukumar Kankara a Jihar Katsina. Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Nasir Mu’azu, ya bayyana cewa sojojin runduna ta 17 tare da tallafin jiragen yaƙi sun kai farmaki maɓoyar ’yan ta’adda da ke yankin Sanusi Dutsin-Ma da tsaunukan Pauwa. ’Yan bindiga sun sace shugaban kasuwar kayan miya ta Akinyele a Oyo Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira Ya ce a yayin farmakin dakarun sun kashe wasu daga cikin ’yan bindiga sannan suka kuɓutar da waɗanda aka sace. Daga cikin mutanen da aka ceto, akwai maza bakwai, mata 23, da yara 54. Kwamishinan...
Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa. Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci. Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a An bayar da...
Kotun Tarayya da ke Lokoja, Jihar Kogi, ta bayar da umarnin dakatar da Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC) daga karɓar kowace buƙatar da aka gabatar domin fara shirin kiranye ga Senata Natasha Akpoti-Uduaghan daga Majalisar Dattawa. Haka kuma, kotun ta hana ma’aikatan INEC, da wakilansu, ko duk wani wanda ke da hannu daga karɓar ko yin aiki da kowace buƙata da ke ɗauke da sunayen ƙarya daga mutanen mazaɓar Kogi ta tsakiya, sannan ta hana gudanar da kowanne zaɓe ko taro kan lamarin har sai kotu ta yanke hukunci. Kwamitin Majalisa Ya Yi Watsi Da Ƙorafin Da Natasha Ta Shigar A Kan Akpabio Majalisar Dattawa Ta Dakatar Da Sanata Natasha Na tsawon Watanni 6 Saboda Rashin Da’a An bayar da...
Sai dai, a yayin da yake yanke hukuncin; mai shari’a Omotosho, ya yanke hukuncin cewa, ya yi watsi da karar tasu da suka shigar saboda rashin cancanta. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Kotun Ƙoli ta yanke hukunci tare da tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin halastaccen Sakataren Jam’iyyar PDP na Ƙasa. Anyanwu, wanda na hannun daman Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ne, ya shafe lokaci yana takun-saƙa da Sunday Ude-Okoye kan wannan matsayi. Tinubu ya ba ni riƙon Ribas don wanzar da zaman lafiya — Ibas Kwankwaso ya yi Allah-wadai da ayyana dokar ta-ɓaci a Ribas Ude-Okoye ya samu goyon bayan wasu ɓangarori na jam’iyyar PDP bayan Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Enugu ta tabbatar da naɗinsa, biyo bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ta tsige Anyanwu. Sai dai, a ranar Juma’a, wani kwamitin alƙalan Kotun Ƙoli guda biyar, ya yanke hukunci cewa rikice-rikicen shugabanci a cikin jam’iyya al’amari ne na...
Jagoran jam’iyyar adawa ta NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya soki Majalisar dokoki ta 10 a Nijeriya bisa amincewarta da ƙaddamar da dokar ta ɓaci (State of Emergency) a Jihar Ribas da kuma dakatar da gwamnan jihar da mataimakinsa da majalisar dokokin jihar daga aiki ta hanyar shugaban ƙasa Bola Tinubu, yana mai cewa ‘yan majalisar sun zama kamar ƴan amshin Shata. Kwankwaso, wanda ya riƙe muƙamin gwamnan jihar Kano sau biyu, ya ga baiken wannan mataki na majalisar, in da ya ce yayi kama da irin kuskuren da ‘yan majalisar tarayya suka yi a lokacin majalisa ta uku (Third Republic), wanda ya haifar da soke zaɓensu na ranar 12 ga Yuni, 1993. Ya bayyana cewa ƴan majalisar ya kamata...
Shugaban Riƙo na Jihar Ribas, Ibok Ibas, ya ce Shugaba Bola Tinubu, ya naɗa shi ne domin dawo da zaman lafiya a jihar, wadda ke fama da rikicin siyasa. Da yake jawabi a wani shirin talabijin a daren Alhamis a Fatakwal, Ibas ya bayyana naɗin nasa a matsayin matakin da ya dace don kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya ɗauki kusan shekaru biyu. Farashin fetur na iya tashi bayan Dangote ya daina sayar da mai a Naira Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Ya ce rikicin ya hana ci gaban gwamnati, tare da haifar da matsalar tsaro da koma bayan tattalin arziƙi a jihar. “A matsayina na ɗan yankin Neja Delta, na fahimci damuwar mutanenmu. Rashin tabbas a...

Shugaba Bola Ahmed Tinubu A Tarayyar Najeriya Ya Bada Umurnin A Gudanar Da Bincike Kan hatsarin Daren Laraban da Ta Gabata A Abuja
Shugaban tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bada umurnin a gudanar da bincike don gano abinda ya hadda hatsarin day a faru a kan gadar Karuk an titin Abuja Keffi a daren Labaran da ta gabata, wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane da kuma jikatan wasu. Jaridar Premium Times ta nakalto shugaban kasar yana fadar haka tabakin mai bashi shawara kan al-amuran watsa labarai Bayo Onanuga a jiya Alhamis. Shugaban ya bayyana alhininsa ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu da kuma fatan murmurewar wadanda suka ji rauni. Ya kuma bukaci a gaggauta gudanar da bincike don sanin abinda ya haddasa hatsarin day a kai da wannan asarar, don daukar matakan hana aukuwar irinsa nan gaba.
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan, a sakonsa na karshe ga Iraniyawa a shekara ta 1403 na kalandar Iraniyawa, ya bukaci mutanen kasar su hada kai don kaiwa ga manufofin kasar, wadanda suka hada da bunkasar tattalin arziki, da kauda tsadar rayuwa da kuma rashin bawa makiya damar cutar da kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana fadar haka a jawabinda na ‘Nuruz’ ko sabon shekara ta 1404 wanda ya shigo yau. Pezeshkiyan ya bukaci All…ya yi rahama ga shuwagabannimmu da muka rasa a shekaran da ta kare, wadanda suka hada da Shahid Ibrahim Ra’isi da abokan tafiyar, da sharing maso gwagwarmaya a ciki da wajen kasar, wadanda suka hada da shahidan Lebanon Falasdin Siriya da...
Dubban dubatan mutane masu goyon bayan magajin garin Istambul a kasar Turkiya ne suka fito kan titunan birnin inda suke bukatar gwamnatin Urdugan ta sake shi. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa mutane suna ganin Ekrem Imamoglu, dan takarar shugaban kasa ne a zaben shugaban kasa mai zuwa kuma mai yuwa ya kara shugaban Urdugan a zaben, saboda yawan magoya bayansa a kasar, musamman a birnin Istambul. Labarin ya kara da cewa Imamoglu mutum ne wanda yake da karbuwa a cikin mutanen kasar, wanda kuma ana ganin mai yuwa ya kada shugaba Urdugan a zaben shugaban kasa mai zuwa. Don haka ana ganin gwamnatin Urdugan ta sa aka kamashi, tare da zargin cin hanci da rashawa,...
Jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a gabaci da kuma kudancin kasar Lebanon wanda yak eta yarjeniyar zaman lafiyan da HKI ta cimma da kungiyar Hizbullah mai lamba 1701 ta shekara ta 2006. Tashar talabijin ta Presstv anan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Lebanon na cewa, jiragen yakin HKI sun kai hare-hare kan bayan kauyen taraya a gundumar ba’alabak, cikin lardin Ba’alabak Hermel, da kuma kan garin Shaara kusa da garin Jenta a dai dai kasar tsaunuka da ke yankin. A kudancin kasar Lebanon kuma jiragen yakin HKI sun jefa makamai masu linzami har guda 4 a kan yakunan Jibaa da Snaya Kafafen yada labaran HKI sun tabbatar da wannan labarin sun kuma nakalto sojojin kasar suna...
Sojojin kasar Yemen sun cilla makami mai linzami samfurai Balistic kuma Hypersonic kan birnin Yafa kusa da Telaviv a cikin HKI karo na biyu a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Harin dai yana daga cikin manya-manyan hare-haren da sojojin na Yemen suka kai kan HKI tun bayan sake komawa yaki tufanul Aksa. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar ta Yemen Burgediya Janar Yahya Saree yana bada sanarwan kai harin, a jiya Alhamis ya kuma kara da cewa, hari mai kyua wanda ya dace da tallafawa Falasdinawa a Gaza. Saree ya kammala da cewa matukar sojojin HKI sun ci gaba da kissan kiyashin da suke yi a Gaza
Ya ce: “Ina so in sake nanata cewa Shugaban Ƙasa Tinubu, wanda yake cikakken ɗan dimokiraɗiyya, yana da niyyar kare ‘yancin ‘yan Nijeriya kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. Haka zalika, yana ƙarfafa sukar gwamnati mai ma’ana da adawa tagari saboda suna da muhimmiyar rawa da suke takawa wajen ingantawa da zurfafa tsarin dimokiraɗiyyar mu. “Ina kuma tabbatar da cewa wannan gwamnati za ta ci gaba da kare ‘yancin ‘yan jarida da samar da yanayi mai kyau ga aikin jarida a Nijeriya. Gwamnatin nan tana da yaƙinin cewa ‘yancin ‘yan jarida yana da muhimmanci wajen inganta nagartar shugabanci, gaskiya, da ci gaban ƙasa.” Ministan ya yi amfani da damar taron don taya Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Nijeriya...
Hukumar jin dadin alhazai ta jihar Kano ta ce ta samu nasarar kammala rijistar maniyyata aikin hajjin bana 3,155. Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Alhaji Lamin Danbappa, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis a Kano a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar gudanarwar Hukumar Shige da Fice a ofishinsa. Danbappa ya bayyana cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shirye da suka hada da kwasa-kwasan horas da aikin hajji, da takardu da kuma tattara kayanai. “Yanzu haka hukumar ta fara bayar da biza ga maniyyatan da suka yi rijista. Ya yabawa gwamnatin jiha bisa yadda take ci gaba da tallafawa kokarin hukumar na ganin an gudanar da aikin Hajji cikin sauki. ...
An yi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su hada kai da sauran masu ruwa da tsaki a harkar rage karuwar amfani da magungunan ba bias ka’ida ba a tsakanin matasa. Babban Daraktan Kula da Lafiya (CMD,) a Babban Asibitin Neuro-Psychiatric na Tarayya, Budo Egba, Jihar Kwara, Dokta Issa Awoye, ya yi wannan kiran ne a cikin jawabinsa mai taken, Sakamakon Neuropsychiatric na Maganganun Magani: Ra’ayin Clinical a taron masu ruwa da tsaki na Kwara na biyu kan Kariya da Sarrafa miyagun kwayoyi, wanda aka gudanar a Ilorin. A cewarsa an samu karuwar noma da fataucin miyagun kwayoyi a kasar, musamman a tsakanin matasa. Ya jera magungunan da aka saba amfani da su sun hada da...
Cibiyar Bincike Kan Harkar Noma (IAR) tare da hadin gwiwar Hukumar Yada Sakamakon Bincike da Wayar da Kan Manoma ta Kasa (NAERLS), Jami’ar Ahmadu Bello Zaria, sun shirya taron kwana guda a Kaduna domin masu ruwa da tsaki kan aikin bunkasa noman dawa a Najeriya. Taken taron shi ne: “Gabatarwa da Tattaunawa Kan Amfanin Sabbin Nau’ikan Dawa Masu Jure Sauyin Yanayi Domin Rage Talauci da Inganta Abinci a Najeriya.” Daga cikin manyan abokan aikin akwai Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika (ECOWAS), Kungiyar Manoman Dawa da Masara ta Najeriya, da Tarayyar Turai (EU), da sauransu. A jawabin sa, Mataimakin Daraktan NAERLS, Farfesa Muhammad Musa Jaliya, ya ce babban burin taron shi ne tabbatar da dorewar sabon...
Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hafsat Uba Sani, ta raba kayan abinci da tufafi ga marayu, mabukata da malamai a Hayin Na’iya dake Kaduna. An gudanar da taron ne a makarantar Ummul Muminina Hafsat Islamic Academy da ke Hayin Na’iya, Kaduna. Hajiya Hafsat Uba Sani, wacce Hajiya Aisha Idris Maman ‘Yan Uku ta wakilta, ta jaddada bukatar ganin masu hali su tallafa wa talakawa da mabukata a cikin al’ummarsu. “Uwargidan gwamnan ta yi imanin cewa marayu da mabukata suna bukatar soyayya, kulawa da tallafi kamar kowane yaro,” in ji ta. “Wannan shiri ba wai kawai don samar da abinci da tufafi ba ne; yana nufin nuna musu cewa ana kaunarsu kuma ba a manta da su ba.” “Muna...
Gwamnatin Jihar Yobe ta kafa cibiyoyin bayar da abinci 85 domin samar wa almajirai abinci a dukkanin Ƙananan Hukumomin 17 na jihar, a lokacin azumin Ramadan. Sakataren zartarwa na Hukumar Ilimin Larabci da Addinin Musulunci ta Jihar Yobe, Malam Umar Abubakar ne, ya bayyana hakan a wata hira da Daily Trust a ranar Alhamis. Sanƙarau ta kashe mutum 55 saboda rashin tsafta a Kebbi Dabarun Rabauta Da Kwanaki 10 Na Ƙarshen Ramadan “Muna bai wa makarantun Tsangaya 85 kayan abinci 85, biyar a kowace Ƙaramar Hukuma, inda muke ciyar da almajirai tsakanin 300 zuwa 400 a kowace makaranta,” in ji shi. Ya ƙara da cewa Gwamna Mai Mala Buni ne, ya amince da wannan shiri domin tallafa wa yara marasa...
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya bayyana cewa, Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martani ga wasikar shugaban Amurka Donald Trump a cikin kwanaki masu zuwa ta hanyoyin da suka dace. Araghchi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi kai tsaye a gidan talabijin na Jamhuriyar Musulunci ta Iran (IRIB) jiya Alhamis. Araghchi ya kuma lura cewa a wannan karon, ci gaban ya zo tare da wani yunkuri na diflomasiyya daga Amurkawa, ciki har da wasika da bukatar yin shawarwari. Ya kuma bayyana cewa manufar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a bayyane take. “Ba za mu shiga tattaunawa kai tsaye karkashin matsin lamba, barazana, ko karin takunkumi.” A cewar Araghchi, tilas ne a gudanar da shawarwari...
Gwamnatin Isra’ila ta sanar da korar shugaban hukumar liken asiri ta cikin gidan kasar Ronen Bar, wanda Firaministan kassar Benjamin Netanyahu ya ce bai gamsu da kwarewarsa ba hasali ma ba’a yarda da shi. “Gwamnati baki daya ta amince da shawarar Firaminista Benjamin Netanyahu na kawo karshen wa’adin” Ronen Bar, wanda zai bar ofis idan aka nada magajinsa ye zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, in ji ofishin Firayim Minista a cikin wata sanarwa. Rashin gamsuwa da aikin na kokaren shugaban hukumar ta Shin-bet, ta fito fili a baya bayan bayan bayannan da suke fitowa game da harin kungiyar Hamas na ranar 7 ga watan Oktoban 2023. Ronen Bar, wanda aka nada a watan Oktoba 2021 na wa’adin shekaru biyar,...
Iran ta yi Allah wadai da Kwamitin Sulhun na MDD na rashin tabaka komai wajen dakatar da ayyukan Amurka da Isra’ila wanda Iran din ta bayyana da abin kunya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da munanan hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan kasar Yemen da kuma yadda gwamnatin Isra’ila ke ci gaba da kai wa Falasdinawa hari a zirin Gaza, tare da yin Allah wadai da rashin daukar wami mataki daga kwamitin sulhu na fuskantar wadannan munanan ayyukan. Esmaeil Baghaei, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana matukar na dama kan yadda ake kashe fararen hula da suka hada da mata da kananan yara da ba su ji ba...
Shugaba Kaïs Saïed na Tunisiya ya kori firaministan kasar Kamel Madouri, da aka nada a watan Agustan da ya gabata yayin wani gagarumin garanbawul a majalisar ministocin kasar a daren jiya Alhamis. Wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce an maye gurbin firaministan kasar Madouri nan take inda aka maye gurbinsa da Sarra Zaafrani Zenzri, ministar kayan aiki. Sanarwar ta ce sauren mambobin gwamnatin zasu ci gaba da aikinsu. Garan bawul na shugaban kasar ta Tunisia a baya baya nan shi ne na ranar 6 ga watan Fabrairu inda ya sallami ministan kudinsa Sihem Boughdiri Nemsia da tsakar dare, tare da maye gurbinsa da alkalin kotun Michket Slama Khaldi.
Martanin da Fadar Shugaban Kasar ta mayar, ya biyo bayan nuna damuwa a kan matakin da Majalisar Dokokin Amurka ta dauka na amincewa da takunkumin da aka kakaba wa Nijeriya, bisa zargin kashe Kiristoci. Da yake goyan bayan wannan matsaya, Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa (CAN) reshen Arewa, Rabaran Yakubu Pam ya bayyana a baya bayan nan cewa, abubuwan da suke faruwa na musgunawa Kiristoci, su yi matukar raguwa. Har ila yau, ya bayyana ci gaban da aka samu, musamman a bangaren wariya ko nuna banbanci ga Kiristoci, wajen mallakar filaye; domin gina Coci-coci da kuma batun tilasta barin addinin da kuma aurar da yara ‘yan mata Kiristoci. Kazalika, gwamnati ta sake nanata kudirinta na ci gaba da karfafa addinai...
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya yi caccaki Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ayyana dokar ta-baci a Jihar Ribas. Kwankwaso ya ce matakin da Tinubu ya ɗauka ya saɓa doka kuma barazana ne ga dimokuraɗiyya. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe NAJERIYA A YAU: Illar Sare Itatuwa Ga Sauyin Yanayi Da Lafiyarmu A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Kwankwaso ya gargaɗi cewa irin wannan matakin na iya kafa mummunan misali da kuma illata dimokuraɗiyya a Najeriya. Kwankwaso, ya ruwaito yadda rikicin siyasa da ya haifar da soke zaɓen 1993, inda ya jaddada cewa ‘yan majalisa su daina ɓata lokacinsu kan abubuwan da ba su dace ba. “Majalisa tana...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tsawon lokaci, hukumomi a duniya suna gudanar da taruka don nemo hanyoyin daƙile ɗumamar yanayi kan irin illar da ke haifar wa rayuwar al’umma. Ɗumama ko sauyin yanayi yana barazana ga duniya, yana haifar da sauye-sauye da masana ke cewa zai iya tsananta idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba. NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ke Hana Wasu Teloli Cika Alƙawari NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Ɗaya daga cikin matsalolin da masana suka gano shi ne sare itatuwa ba tare da dasa sabbi ba, wanda ke illa ga muhalli. Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazarin illar sare itatuwa ba tare da...
Ramadan lokaci ne da ke hada kan iyalai da al’ummomi a fadin duniyar Musulmi. Lokaci ne da masoya ke haduwa tun daga lokacin sahur har zuwa buda-baki, ta hanyar kasancewa tare domin cin abinci mai gina jiki. A wannan lokacin, ba a yin abinci don nishadi kawai, lokaci ne na inganta rayuwa da bayar da labarai na nishadantarwa da zumunta da kuma jin dadin kasancewa tare. A cikin wannan labari mai ban sha’awa na MAGGI mai taken Labarin Ramadan, wasu mata biyar sun yi tafiya ta tsawon wata guda don samar da sauye-sauye, inda suka gano hadaddun girke-girke na sada zumunta da ke da alaka da samar da labarai masu jan hankali, har guda shida. Tare da wasu jaruman wasan...
Wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi awan gaba da kayayyakin wata mota ɗauke da kayan abinci na Hukumar abinci ta duniya (WFP) a garin Gubio, yayin da take kan hanyarta ta zuwa Damasak a Jihar Borno. Majiyar leƙen asiri ta shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da Aminu Malam Umar direban wata babbar mota ƙirar Iɓeco ya tsaya a gefen titi. ’Yan adawa sun shirya ƙalubalantar Tinubu a zaɓen 2027 – Atiku Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe Yayin da motar ta tsaya a gefen titi ba tare da kula daga jami’an tsaro ba, wasu da ba a san ko su waye ba...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

Hukumar Alhazai Ta Jihar Kaduna Ta Bukaci Taimakon NAMA Don Gudanar Da Aikin Hajjin Bana Cikin Nasara
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta roƙi Hukumar Kula da Sararin Samaniyar Najeriya (NAMA) ta ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar gudanar da aikin Hajjin bana. A ziyarar ayarin hukumar ƙarƙashin jagorancin Sakataren Gudanarwa, Malam Baba Mohammed Rufa’i, wanda ya wakilci Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ta kai ziyara ga jami’an NAMA a Filin Jirgin Sama na Hassan Usman Katsina da ke Kaduna. A yayin ziyarar, Malam Salihu Abubakar ya yaba wa NAMA bisa gudunmuwar da take badawa wajen nasarar hajjojin da suka gabata, inda ya roƙi irin wannan haɗin gwiwa a bana. Ya jaddada muhimmancin samun ingantattun hanyoyin sufuri tare da roƙon NAMA ta tabbatar da samar...
(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tsohon mataimakin shugaban Nijeriya, Atiku Abubakar ya bayyana cewa yanzu haka ’yan adawar siyasa a ƙasar nan a shirye suke su ƙalubalanci shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Tun bayan da ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, Atiku ya riƙa yin taro da ’yan adawa don neman karɓe mulki daga hannun jam’iyya mai ci. Gobara ta ƙone gidaje tare da asarar dukiya a Gombe Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Da yake jawabi ga manema labarai tare da wasu ’yan adawa a zauren taro na ‘Yar’adua Center da ke Abuja a ranar Alhamis, Atiku ya ce an yi taron ne don sake samar da wasu ‘yan adawa kafin babban...
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Mao Ning ta bayyana cewa, kakaba haraji da sauran shingayen kasuwanci ba za su amfani kowa ba, kuma suna matukar haifar da illa ga samar da wadatar tattalin arzikin duniya, da tafiyar da shi cikin kwanciyar hankali. Jami’ar wacce ta bayyana haka a yau Alhamis yayin wani taron manema labarai, ta ce kasar Sin za ta ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje, da nuna goyon baya ga ka’idojin ciniki cikin ‘yanci, da tsarin kasuwanci a tsakanin bangarori daban-daban, da karfafa samun moriyar kasa da kasa ta fuskar tattalin arzikin da ya hade kowa da kowa, da neman bunkasa ta bai-daya, tare da samar da moriyar juna da dukkan...
Wannan hazaka, da hangen nesa na kasar Sin, sun ci gaba da zama ginshiki na ingiza jagorancin dukkanin manufofin kare hakkin bil Adama a duniya, kana hakan zai ci gaba da zama muhimmiyar gudummawar kasar Sin ga duniya, a bangaren kare hakkin rayuwa da walwalar daukacin al’ummar duniya.(Saminu Alhassan) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
“Wannan mataki na dokar ta-ɓaci wata dama ce ta kare rayuwar al’umma, tabbatar da tsaron muhimman kadarori, da dawo da tsarin mulkin dimokuraɗiyya,” in ji Tinubu. Shugaba Tinubu ya buƙaci dukkanin ɓangarori su mara baya ga ƙoƙarin dawo da zaman lafiya a Jihar Ribas tare da jaddada ƙudirin gwamnatinsa na bunƙasa tattalin arziƙi da haɗin kan ƙasa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata gobara mai muni ta laƙume gidaje uku a unguwar New GRA, a birinn jihar Gombe, a ranar Laraba inda ta bar iyalai cikin rashin matsuguni tare da asarar dukiya ta miliyoyin Naira. Waɗanda abin ya shafa sun koka kan rashin damar ceto komai daga kayan su, kuma yanzu haka suna neman tallafin gaggawa domin sake farfaɗowa daga wannan masifa. ‘Za a fara biyan Naira 77,000 ga masu yi wa ƙasa hidima daga Maris’ Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati Gobarar wadda ta tashi da rana tsaka, ta yi saurin yaɗuwa zuwa gidaje uku, inda ta ƙone su kurmus. Hukumomin yankin har zuwa yanzu ba su bayyana ainihin dalilin tashin gobarar ba, yayin da waɗanda abin...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira ga lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin, da ya mayar da hankali kan karfafa samar da ci gaba mai inganci, da warware tarnakin tafakkuri, da aiwatar da gyare-gyare da kirkire-kirkire, da kokarin ci gaba da azama, da daukar matakai masu inganci, da kuma kafa sabon tushe na ci gabansa a kokarin zamanantar da kasar Sin. Shugaba Xi, wanda har ila yau yake babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojin kasar, ya bayyana hakan ne yayin rangadin da ya kai lardin a ranakun Laraba da Alhamis din nan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni...
Masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), za su fara jin daɗin sabon alawus ɗin gwamnatin tarayya na N77,000.00 wanda aka sake duba shi da za a fara biya daga watan Maris, 2025. Babban Darakta Janar (DG) na NYSC, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu ne ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga masu yi wa ƙasa hidima a babban birnin tarayya, a ofishin NYSC na shiyya ta 3 da ke Wuse Zone 3 Old Parade Ground a yankin Garki a ranar Alhamis. Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas ya isa gidan gwamnati ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Ya sanar da masu yi wa ƙasar hidima cewa ma’aikatar kuɗi ta sanar da...
Tun lokacin da Donald Trump ya hau mukaminsa na shugaban kasar Amurka a watan Janairu na bana, sau da dama gwamnatinsa ta dauki matakan kakaba harajin kwastan kan abokan cinikinta. A ganinsa, matakan za su tilasta kamfanoni da su maido da tsarin samar da kayayyaki zuwa Amurka, matakin da zai gaggauta bunkasuwar masana’antun kasar. Ko abin ya tafi kamar yadda Trump ya yi tsamani? Alal hakika, manufofi marasa dorewa da gwamnatin Trump ta dauka na illata amanar Amurka, har ma hakan ya yi ta dakushe kwarin gwiwar masu zuba jari na ketare da na kamfanonin cikin gidan kasar. Babban mizanin wasu muhimman hannayen jarin Amurka ya yi matukar raguwa kwanan baya, abin da ya shaida damuwar masu zuba jari a...
A shekarar 2004, lokacin da Olusegun Obasanjo ya ayyana dokar ta-ɓaci a Filato, matakin ya fuskanci suka daga jama’a da ɓangaren shari’a. Masana doka da ‘yan siyasa sun yi Allah-wadai da matakin da Tinubu ya ɗauka, inda Dokta Reuben Abati ya bayyana shi a matsayin “laifi da za a iya tuhumar Tinubu a kai”. Ya ce Shugaban Ƙasa ba shi da ikon rushe zaɓaɓɓun shugabanni na jiha. Bugu da ƙari, Sambauna ya caccaki yadda Gwamnatin Tinubu ke nuna bambanci wajen raba wa matasa tallafi. Ya ce: “Seyi Tinubu ya bayar da kayan abinci a Arewa a matsayin tallafi, amma a Kudu yana bayar da tallafin kuɗi domin mutane su dogara da kansu wajen bunƙasa kasuwanci. Wannan nuna bambanci ne da...
Mece ce Dokar Ta-ɓaci? Dokar ta-ɓaci tana bai wa shugaban ƙasa damar ɗaukar matakan gaggawa a wani yanki na ƙasa idan ana fuskantar barazanar tsaro ko zaman lafiya. Sai dai kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi cewa dole ne a bi tsari na doka kafin a aiwatar da hakan. Mece Ce Ma’anar Wannan Mataki A Ribas? Ayyana dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas yana nufin Gwamnatin Tarayya ta ƙwace ikon jihar, kuma hakan na iya kawo cikas ga harkokin siyasa da ci gaban jihar. Masana doka da ‘yan adawa na ganin cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulki, kuma yana iya zama wata hanya ta take haƙƙin masu mulki da aka zaɓa a jihar. Tun bayan ɗaukar wannan mataki,...
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya taya al’ummar Iran murnar zagayowar lokacin bukukuwan Nowruz na sabuwar shekarar hijira shamsiyya da ake amfani da itya a hukumance a kasar Iran. Ayatullah Khamenei ya bayyana hakan ne a wani sako da ya aikewa al’ummar kasar ta gidan telebijin na murnar shiga sabuwar shekara ta Farisa a yammacin wannan Alhamis. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya jaddada bukatar gwamnati da al’ummar kasar su ci gaba da zuba jari don karfafa azamarsu wajen tunkarar takunkumai na zalunci da masu girman kai na duniya suka kakaba ma kasar. Ayatullah Khamenei ya jaddada cewa samar da kayayyaki na samun bunkasuwa ne idan aka ba da tallafin jari mai karfi. Jagoran ya kuma...
Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta yi Allah wadai da sake dawo da hare-haren wuce gona da irin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza tare da yin kira da a dauki matakin gaggawa na kasashen duniya domin dakile wadannan laifuka. Kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta yi Allah wadai da sake kai hare-haren bama-bamai a yankin zirin Gaza da yahudawan sahyuniya suka yi, lamarin da ya janyo hasarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Sheik Muhammad bin Abdulkarim Issa, babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta duniya, ya yi Allah wadai da zaluncin gwamnatin sahyoniyawa, wanda hakan...
Dakarun Falasdinawa sun mayar da martani ga kisan kiyashin da Isra’ila ke yi wa fararen hula bayan sake dawo da yakin Isra’ila a kan al’ummar Gaza, inda suka harba rokoki zuwa Tel Aviv. Al-Qassam Brigades, reshen soji na kungiyar gwagwarmayar Islama ta Hamas, ta sanar a wannan Alhamis cewa, ta yi ruwan makamai masu linzami samfurin M90 a kan birnin Tel Aviv, a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashi da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ke yi kan fararen hula a zirin Gaza. Sojojin mamaya na Isra’ila sun tabbatar da cewa sun gano wasu rokoki guda uku da aka harba daga Gaza zuwa tsakiyar Falasdinu da suka mamaye, tare da jin karar makamai a sararin samniyar Tel Aviv, Gush Dan, da...
’Yan Najeriya na iya fuskantar karin farashin man fetur bayan da Matatar Man Dangote ta bayyana cewa ta daina sayar wa ’yan kasuwa man fetur a kudin Naira. Matatar, wacce ke siyan danyen mai da Naira bisa yarjejeniyar gwamnati, yanzu ta koma sayan danyen mai da dalar Amurka. An kirkiro yarjejeniyar siyan danyen mai da Naira ne domin rage tsadar mai. Bisa ga wannan yarjejeniya, Kamfanin Man Fetur na Kasa (NNPCL), yana da alhakin samar wa Matatar Dangote gangar danyen mai a kowace rana 385,000, domin ta tace ta kuma sayar da shi a farashin Naira. Sai dai rashin cika alkawari daga NNPCL ya sa yarjejeniyar ta gaza dorewa. Wata majiya ta bayyana cewa, “NNPCL bai cika alkawarin da ya...
Sabon Gwamnan riƙon ƙwarya na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-ete Ibas (mai ritaya), ya isa jihar domin ci gaba da aiki. Ibas ya isa filin jirgin saman Fatakwal da misalin ƙarfe 11:25 na safiyar ranar Alhamis inda ya samu tarba daga manyan jami’ai da jami’an tsaro. ’Yan Boko Haram 7 sun miƙa wuya ga sojojin MNJTF a Borno Majalisar wakilai ta amince da dokar ta-ɓaci a Ribas Sabon Gwamnan, tare da rakiyar Kwamishinan ’yan sandan jihar, Olugbenga Adepoju da mataimakin babban sufeton ’yan sanda na shiyya ta 16, nan take suka wuce gidan gwamnati da ke Fatakwal. Tuni dai Ibas ya isa gidan gwamnati inda wasu jami’an gwamnati suka zagaya da shi harabar gidan. A yanzu haka yana ganawar sirri...

Fashewar Tankar Man Fetur: Rundunar ‘Yansanda Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 6, Motoci 14 Sun Kone A Abuja.
Rundunar ‘yansandan babban birnin tarayya Abuja ta tabbatar da mutuwar mutane shida a fashewar tankar man fetur da ya afku a yankin Karu da ke Abuja a daren Laraba. Rundunar ta kuma ce motoci 14 ne suka kone a mummunan hatsarin. Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutane 84, Sun Kashe ‘Yan Ta’adda 3 A Katsina Cikar NUJ Shekaru 70: ‘Yan Jarida Abokan Hulɗa Ne Wajen Aza Kyakkyawar Makoma – Gwamnan Gombe Kakakin rundunar ‘yansandan, SP Josephine Adeh, wanda ya bayyana hakan a ranar Alhamis, ya bayyana cewa, rundunar ta yi matukar jimamin hatsarin motar da ya afku a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin karfe 6:58 na yamma kafin gadar Nyanya. Ta kuma ce, ofishin hukumar na Karu ya samu...
Majalisar Wakilai ta amince da ayyana dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas. Majalisar ta yanke wannan shawara ne a ranar Alhamis, ta hanyar kaɗa ƙuri’a da baki, inda ’yan majalisa 243 suka halarta. Muhimman ayyuka 8 a goman ƙarshe na Ramadan Fashewar Tanka: Asibitoci sun cika da mutane a Abuja A matsayin wani ɓangare na matakan dokar ta-ɓaci, majalisar ta bayar da shawarar kafa kwamiti domin dawo da zaman lafiya a jihar. Hakazalika, majalisar za ta karɓi ragamar gudanar da ayyukan Majalisar Dokokin Jihar Ribas na tsawon watanni shida. Me Ya Sa Aka Ayyana Dokar Ta-ɓaci? Matakin ya biyo bayan rikicin siyasa da ya ƙi ya ƙi cinyewa a Jihar Ribas. Shugaba Tinubu ya yanke...
A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su: Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul...
A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su: Yadda Teloli Ke Cin Kasuwa A Azumin Bana Fursunoni 100 na neman afuwa a Kano Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya sawwaka. Neman daren Lailatul Kadar: Mutum ya dage wajen kirdado da neman dacewa da daren Lailatul...
Darakta mai kula da al-amuran mata da kuma kare hakkin bil’adama a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, Forouzandeh Vadiati, ta hadu da jakadan kasar Jamus a nan Tehran da kuma mataimakin jakadan kasar Burtania a Tehrana a ma’aikara. Inda ta bayyana masu bacin ranta da yadda kasashen biyu suka shigar da wata daftari ta tuhumar Iran da abinda ya shafi hakin mata da a hukumar kare hakkin bil’adama ta MDD. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Vadiati yana zargin Berlin da kuma London na shiga cikin al-amuran cikin gida na JMI. Sannan ta tunanatar da kasar Jamus kan abinda ta aikata na bawa Sadam Hussain makaman guba a yakin shekaru 8 da suka fafata da kasar ta...
Yan tawayen M-23 na kasar Kongo wadanda suke samun goyon bayan gwamnatin kasar Ruwanda sun kara nosawa zuwa gaba a mamayar da sukewa gabancin kasar ta Kongo. Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa yan tawayen sun kama garin Walikale a jiya Laraba kuma a halin yanzun sun kokarin zuwa sauran garuruwa a yankin. Labarin ya kara da cewa wannan labarin na zuwa ne a dai dai lokacinda shuwagabanninkasashen Kongo da Rwanda suke kira ga bangarorin biyu su tsagaita budewa juna wuta su kuma dawo kan teburin tattaunawa. Wani mazaunin garin walikale ya fadawa reuters yana jin karar bindigogi a garin Nyabangi wanda yake kusa da inda yake. Janvier Kabutwa yace, yan tawayen sun afafatawa da sojojin Gwamnati da kuma...
Rahotannin da suke fitowa daga yankin Gaza na kasar Falasdinu da aka mamaye sun nuna cewa, a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata Falasdinawa 71 ne suka yi shahada a yayinda wasu da dama suka ji rauni. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a wannan karon jiragen yakin HKI da jiragen ruwan yake daga tekun medeteranina sun cilla wuta kan garuruwan Beit –Lahia, Rafah da kuamKhan Yunus inda suka kashe da dama ko suka kaisu ga shahada. Labarin ya kara da cewa sojojin yahudawan sun sake mamayar yankin Netzarim wanda ya raba arewa da kudancin zirin gaza a yau Alhamis. Ya zuwa yanzu yawan falasdinawa da suka yi shahada ya kai 49,547 tun...
Sojojin kasar Yeman sun bada sanarwan cilla makamai masu linzami kan tashar jiragen sama ta Bengerion a birnin Tel’aviv na HKI a daren jiya laraba don tallafawa falasdinawa a gaza wadanda sojojin HKI suke kashewa bayan yi masu kofar rago ta shigo da abinci da abinsha cikin yankin na kimani wata guda. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Burgedia Janar Yahya Saree, kakakin sojojin kasar na fadar haka a safiyar yau Alhamis ya kuma kara da cewa sojojin sun yi amfani da makami mai linzami samfurin Falasdin-2 mai saurin fiye da saurin sauti, wato Hypersonic don kai wannan harin. Tashar jiragen sama mafi girma a HKI dai ita ce ta Bengerion dake tazarar kilomita 20 daga...

Mutane Fiye Da 30 Ne Suka Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Dawkar Gas Ta Yi Bindiga A Abuja Na Tarayyar Najeriya
Mutane fiye da 30 ne aka tabbatar damutuwarsu a jiya Laraba a Abubja babban birnin tarayyar Najeriya sanadiyyar bindigan da wata motar daukar iskar gas ta yi a kan gadar Karo da misalign karfe 7:15 a jiya Laraba. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa hatsarin na jiya ya aukune a dai dai lokacinda direba wata motar dakon mai ta Burma kan wasu ababen hawa a kan gadar Karu dake kan hanyar Abuja-Keffi, sannan ta yi bindiga wanda ya tarwatsa wuta kan motocin da ta tsarewa hanya da dama daga cikin motocin su kuma da wuta kuma mazauna cikinsu sun kasa fita. Ya zuwa yanzu dai jami’an kwana-kwana da kuma majiyar asbitoci a Asokoro da Asbitin kasa...
A cewar Kwamishinan, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’adda a kauyukan Malori da Matalawa, inda suka kara tura su cikin tsaunukan. Mua’zu ya ci gaba da bayanin cewa, yayin da jami’an tsaron suka isa sansanin Sanusi Dutsin-Ma, sun yi nasarar tarwatsa jama’arsa tare da kashe ‘yan ta’adda uku, yayin da wasu da dama suka gudu da raunuka. Bayan haka, sojojin sun ceto mutane 84 da aka yi garkuwa da su da suka hada da maza bakwai, mata 23, da kananan yara 54 da aka tsare a sansanonin ‘yan ta’addan. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don...
Ƙungiyar bada agaji ta Civil defence a zirin Gaza ta ce hare-hare ta sama da Isra’ila ta kai cikin dare sun yi sanadin mutuwar mutum aƙalla 50 ciki harda yara ƙanana. Hamas wadda zirin Gaza ke ƙarƙashin ikonta ta ce ta yi alla wadai da farmaki ta kasa na sojoji Isra’ila kuma ta bayyana shi a matsayin abinda ya saɓawa yajejeniyar tsagaita wuta na watanni biyu. Rahotanni sun ce hare-haren da Isra’ila ta kai tun ranar Litinin wanda ya kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta da Hamas, sun shafi wata makaranta da ake tsugunar da waɗanda suka rasa muhalansu. Tun da farko Ministan tsaron Isra’ila, Isreal Katz ya gargaɗi almummar Gaza akan cewa za a lalata...
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci daukacin masarautun Jihar hudu da su fara shirye-shiryen Bikin Sallah Daba domin ganin jama’a da maziyarta sun ji dadin bukukuwan Sallah. Wannan umarni na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, bayan wani taron buda baki da suka yi da sarakunan gargajiya a dakin taro dake gidan gwamnatin Kano. A cewar sanarwar, gwamna Yusuf ya jaddada cewa al’ummar jihar na zurfafa kallon al’adar sanya sabbin tufafi a ranar Sallah, tare da yin jerin gwano don shaida wa sarakunan su a kan doki, da kuma yin musabaha. Don haka, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta...
Aƙalla mutum 55 ne suka rasu sakamakon ɓarkewar cutar sanƙarau a ƙananan hukumomin Jega, Gwandu, Aliero, Bunza, da Birnin Kebbi da ke Jihar Kebbi. Hukumar Lafiya ta Jihar ta tabbatar da ɓullar cutar bayan gwaje-gwajen da aka yi a Abuja. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Shugaban Dattawan Arewa ya ajiye sarautar Magajin Rafin Zazzau Sakataren Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kebbi, Dokta Nuhu Koko, ya bayyana cewa a Gwandu ne aka fi samun waɗana suka rasu, inda mutum 25 suka rasu, sai Jega da ke 16, sannan Aliero ke da mutum 14 da suka mutu. Yawancin waɗanda suka rasu sun ɗauka cewa zazzaɓin cizon sauro ne ke damunsu, wanda hakan ya sa ba su garzaya...
Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi rangadi a birnin Lijiang na lardin Yunnan dake kudu maso yammacin kasar Sin da yammacin jiya, inda ya ziyarci lumbunan samar da furanni masu aiki da sabbin fasahohi na zamani da tsohon garin Lijiang, don fahimtar yadda ake raya aikin gona na musamman mai la’akari da yanayin wurin, da yadda ake gaggauta karewa da amfani da kayayyakin al’adu na tarihi da aiwatar da ra’ayin dunkulewar al’umomin Sinawa. Lambun renon furanni mai aiki da fasahar zamani na Lijiang na da fadin hekta 73.3, wanda ya hada aikin shuka da sufurin furanni da yawon bude ido tare, kuma ya habaka aikinsa zuwa harhada man furanni da samar da busassun furanni da sarrafa abinci mai hade...
Sabon kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori, ya sha alwashin yin aiki da gaskiya domin inganta tsaron rayuka da dukiyoyi. CP Bakori ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar hukumar dake Bompai Kano. CP Bakori, wanda kwanan nan ya karbi mukamin kwamishinan ‘yan sanda na 47 a jihar, ya ce daga cikin abubuwan da ya sa a gaba sun hada da magance ‘yan daba da kuma laifuka. CP Bakori ya bayyana matsalar ‘yan daba, fadan daban, satar wayar hannu, da shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa. Sabon Kwamishinan ya jaddada muhimmancin aikin ‘yan sandan al’umma, da nufin karfafa alaka tsakanin jami’an tsaro da jama’a. Nadin na...
Dakarun Sashe na 2 tare da hadin gwiwar sojojin sama na rundunar hadin gwiwa ta Operation Fansan Yamma sun ceto mutane 101 da aka yi garkuwa da su a fadin Kankara a jihar Katsina da Shinkafi a jihar Zamfara a ranakun 17 da 18 ga watan Maris 2025. A cewar sanarwar mai Magana da aywun rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubukar Abdullahi ya bayyana cewa, a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda 10 a wata arangama da suka yi a gundumar Faru da ke karamar hukumar Maradun. Ta ce an fara kai farmakin ne a jihar Katsina, inda sojoji suka kai farmakin a kan ‘yan ta’addan a babbar filin Pauwa da ke karamar hukumar Kankara. “Hakan ya...
Wata gobara da ta tashi da sanyin safiya ta kone wani shago a wani gini mai daki 13 da ke rukunin gidajen Ile-Lodo a cikin garin Etan a karamar hukumar Ekiti a jihar Kwara. A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle ya fitar, ya ce bayan an samu tashin gobarar ta kira motar kashe gobara da ma’aikatanta sun isa wurin da gaggawa domin shawo kan gobarar, wadda ta kone wani shago a gaban wani gini mai daki 13. A cewarsa duk da tsananin gobarar, jami’an kashe gobara sun yi taka-tsan-tsan, inda suka dakile tare da kashe wutar kafin ta bazu zuwa wasu gine-ginen da ke kusa. Sanarwar ta bayyana cewa...
An dakile fashewar wata babbar tankar mai a Sokoto bayan da jami’an tsaro da jami’an kwana-kwana da masu bayar da agajin gaggawa suka yi gaggawar kai dauki bayan da tankar ta kife a hanyar Gagi-Nakasari a karamar hukumar Sokoto ta Kudu. Wani shaidan gani da ido, Magaji Shanono ya shaidawa gidan rediyon Najeriya cewa tankar mai dauke da lita dubu arba’in da biyar na man fetur, ta wuntsila ne a lokacin da take kokarin shiga shatatalen Nakasari, inda ta zubar da mai. Duk da cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sakataren gwamnatin jihar Sokoto Muhammad Bello Sifawa ya halarci wurin da lamarin ya faru, domin ganin abin da...
Gwamnatin jihar Kebbi, ta tabbatar da mutuwar mutane 56 a sakamakon barkewar cutar sankarau a jihar inda 25 a Gwandu, 16 a Jega, 14 kuma suka mutu a kananan hukumomin Aliero na jihar. Da yake zantawa da manema labarai, babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar, Dakta Nuhu Koko, ya ce an samu jimillar mutane 653 da ake zargin sun kamu da cutar a kananan hukumomi biyar da suka hada da Aliero, Jega, Gwandu, Birnin Kebbi da Bunza. A cewarsa, samfurorin da aka aiko da kuma tabbatarwa daga cibiyar bincike, yanzu jihar ta san yadda take magance cututtukan sankarau. Ya kara da cewa, an aika samfurori 17 zuwa dakin gwaje-gwaje na kasa da kasa da ke Abuja...
Jakadan Amurka a Najeriya, Richard Mills Jr, ya ziyarci mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Bamalli domin ingantawa da karfafa hadin kan al’adu. Jekadan ya ce Amurka ta jajirce sosai kan alakar da Najeriya ya kara da cewa; ‘ muna so mu zurfafa shi kuma mu ƙarfafa shi.” A cewarsa, hanyar da ta fi dacewa wajen zurfafa wannan alaka ita ce ta haduwa irin wannan da za mu ji ta bakin juna. “Ina sa ran jin ta bakinku kan abubuwan da kuke yi na karfafa hadin kan addini a tsakanin al’umma, damar ilimi da kuma damar yin aiki ga jama’ar ku. “Abin da Amurka za ta iya yi don haɓaka ƙarin alaƙa da kuma matakan da...
Ya kuma nuna jin daɗinsa da irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Kwamared Alhassan Yahayan, inda ya ce an ɗora ƙungiyar kan kyakkyawan turbar da ya kamata don ta ci gaba da taka rawar gani wajen bunƙasa aikin jarida a Nijeriya. Yahaya ya jaddada cewa akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin gwamnatin Jihar Gombe da ‘yan jarida, yana mai bada tabbacin cewa wannan kyakkyawar alaƙa da haɗin gwiwa za su kasance ginshiƙin gudanar da mulki a jihar. “Mu a Jihar Gombe muna alfahari da daɗaɗɗiyar dangantakar da muka ƙulla da ‘yan jarida; ‘yan jarida abokan aikinmu ne masu ƙima a fagen kawo ci gaba, kuma muna ci gaba da jajircewa wajen ganin sun ci gaba da yin aiki...
Sojojin Amurka sun kai sabbin hare–hare kan kasar Yemen a safiyar yau Alhamis inda suka lalata gine-gine a garuriwa Al-Hudaida da kuma Sa’ada. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban kasar Amurka Donal Trump kafin haka ya na fadar cewa, sai ya shafe kungiyar Ansarullah wacce take iko da kasar Yemen daga doron kasa. Tun ranar Asabar da ta gabata ce sojojin Amurka da Burtaniya wadanda suke da jiragen yakinsu a cikin tekun maliya da wasu wurare a yakin suka fara kaiwa kungiyar hare-hare saboda goyon bayan ga HKI. Kafin haka dai kungiyar Ansarullahi ta bawa HKI kwanaki huda ta kawo karshen kofar ragon da ta yiwa falasdinawa kimani miliyon biyu a gaza, inda suka hana shigowar...

A Jiya Laraba Ce Iran Take Bukukuwan Cika Shekaru 78 Da Kwatar Kamfanin Man Fetur Na Kasar Daga Hannun Turawan Burtaniya
A ranar 19 ga watan Maris na ko wace shekara ne mutanen Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da ranar da mutanen kasar tare da taimakon gwamnatin lokacin suka sami nasarar kwace kamfanin haka da sarrafa man fetur na kasar, daga hannun wani kamfanin mai na kasar Burtaniya suka maida shin a kasa. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya ce , wannan rana abin alfakhari ne ga mutanen kasar, don bayan haka ne kasar ta sami ikon kawo ci gaban tattalin arzikin kasar da kuma shimfida harsashen samun yencin kasar daga hannun kasashen yamma wadanda suka mamaye bangarori da dama a cikin al-amuran kasar. A ranar 19 ga watan Maris na shekara ta 1951 ne, wato shekaru 78...
Asibitin Ƙasa da Asibitin Asokoro da ke Abuja sun cika maƙil da mutanen da suka jikkata sakamakon fashewar tankar gas da ta auku da daren Laraba a gadar Karu. Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7:14 na dare, bayan wata babbar mota ɗauke da gas ta yi hatsari, tare da faɗawa kan wasu motoci da ke kan gadar, lamarin da ya haddasa gobara. Sarakunan Kano su kimtsa wa hawan sallah bana — Abba Fubara ya magantu bayan ayyana dokar ta ɓaci a Ribas Rahotanni sun nuna cewa an rasa rayuka da dama, yayin da mutane da yawa suka samu munanan raunuka. Shugaban Sashen Ɗaukar Matakan Gaggawa na Hukumar Kula da Harkokin Gaggawa ta Ƙasa (FEMA), Mista Mark Nyam, ya...
Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin Gaza ta bada sanarwan cewa mutanen Gaza ba za su taba barin kasarsu ba, da son ransu ko da karfi zuwa wani wuri ba, sai zuwa birnin Qudus babban birnin kasar Falasdinu. Tashar talabijin ta Presstv ya nakalto kungiyar na fadar haka a jiya Laraba. Ta kuma kara da cewa duk abinda HKI da babbar kawarta Amurka zasu yi don fiddasu daga kasarsu ba zai kai ga nasara ba da yardar All… Tun shekara 1948 ne kasar Burania a lokacin, wacce ta mamaye kasar Falasdinu ta mikawa yahudawan Sahyoniyya kasar Falasdinu, sannan suka kara mamayar kasar bayan yakin shekara 1967. Inda yahudawan suka mamaye har da gabacin birnin Qudus sannan sun ginawa yahudawa...

Mutane Da Dama Ne Ake Jin Tsoron Sun Rasa Rayukansu A Lokacinda Motar Daukar Gas Ta Yi Bindiga A Kan Gadar Karu A Birnin Abuja
Asbitoci a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya wadanda suka hada da Asbitin kasa da kuma na Asokoro duk a ciki suke da wadanda suka ji rauni, ko sun mutu bayan da wata motar daukar gas ta yi hatsari a kan gadar Karu a tsakiyar birnin Abuja a jiya Laraba da misalign karfe 7:14 na yamma. Jaridar Daily Trust ta Najeriya ta bayyana cewa wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar muta ne 6 sannan wasu da dama sun ji rauni sanadiyyar hatsarin. Labarin ya nakalto Mr Mark Nyam mai kula da al-amuran gaggawa na hukumar NEMA ta kasa ya bayyana cewa hatsarin ya auku ne a lokacinda direban motar daukar gas ya burma cikin wasu ababen hawa a kan gadar Karu...
Wasu ’yan bindiga sun kai hari Kasuwar Kayan Miya ta Akinyele, kusa da Ibadan, Babban Birnin Jihar Oyo, inda suka sace Shugaban Kasuwar, Alhaji Usman Yako. Bayanan da muka samu daga shugabannin kasuwar sun nuna cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, jim kadan bayan an idar da sallar Magriba. Ƙungiyoyin ƙwadago sun buƙaci Tinubu ya mayar da Fubara kan kujerarsa Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Mataimakin Shugaban Kasuwar, Alhaji Abdul’aziz Abdulwasi’u (Dan Kashi), ya tabbatar da faruwar lamarin. “Bayan na koma gida domin shan ruwa, sai yarona ya kira ni ta waya ya shaida min cewa wasu mutane ɗauke da bindigogi sun shigo kasuwa suna harbe-harbe. “Sun tilasta Shugaban Kasuwa...
Shugaban kwamiti na musamman dangane da yaki a Ukrai ya bayyana cewa kasar Rasha ta aikata laifukan yaki a yakin da take fafatawa a kasar Ukraine shekaru uku da suka gabata. Shafin yanar gizo na Labarai, Africa News’ ya nakalto Erik Mose ya na fadar haka a taron kwamitin da yake jagoranra danagen da yaki a Ukraine a birnin Geneva a jiya Laraba. Mose a fadawa kwamitin mai mutane 47 kan cewa, ya sami shaidu wadanda suke tabbatar da cewa a cikin shekaru uku da suka gabata gwamnatin kasar Rasha ta azabtar da wasu yan kasar Ukraine wadanda ta kama a yankuna guda 3 na Ukraine da ta kwace, kuma jami’an tsaron rasha sun azabtar da su, wasu kuma an...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau, mutane da dama sun fahimci muhimmancin koyan sana’a wajen dogaro da kai, maimakon dogaro da aikin gwamnati ko na kamfani. Sai dai ana zargin wasu masu masu sana’ar hannu, musamman teloli, da rashin cika alƙawari. NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya A mafi yawan lokuta, ana samun matsala da su, musamman a lokutan bukukuwa, inda suke kasa kammala ɗinkin kayan da aka ba su ko suka yi alƙawari. Shirin Najeriya A Yau, zai yi nazari kan dalilan da suka sa teloli ke kasa cika alƙawari da yadda hakan ke shafar kwastomomi. Domin sauke...

Alakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Bisa Daidaito Tsakanin Sin Da Amurka Za Ta Amfanar Da Kamfanonin Duniya
Alakar tattalin arziki da cinikayya bisa daidaito da aminci kuma mai dorewa tsakanin Sin da Amurka ta dace da muhimman muradun kasashen biyu, kuma za ta amfanar da kamfanoni a duk duniya, a cewar mataimakin ministan cinikayya Wang Shouwen yayin wata ganawa da Ramon Laguarta, shugaban kamfanin PepsiCo a ranar Talata. Da yake karin haske kan yadda kasar Sin ke da karfin gwiwar cimma burinta na bunkasa tattalin arzikinta na shekarar 2025 da aka gabatar a cikin rahoton aikin gwamnati, Wang, kuma wakilin harkokin cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin, ya bayyana cewa, wasu jerin tsare-tsare da kasar ta bullo da su na fadada bukatun cikin gida, da sa kaimi ga inganta tsare-tsaren yin sayayya za su samar...
A dunkule, ayyukan da wadannan kamfanoni za su gudanar sun kunshi samar da wadataccen takin zamani da fasahar noma ta zamani, da dabarun sarrafa takin gargajiya da fasahar kiwo mafi dacewa da jihar. Haka nan, kawancen nasu zai hada har da amfani da fasahohin zamani wajen kyautata sha’anin tsaro, da harkokin sufuri da bangaren hidindimun jama’a, da sauran dabaru da tsare-tsare na kwarewar aiki da za a samar a jihar. Hakika wannan kawance zai fa’idantar sosai saboda yadda yankin na arewa ya kwashi tsawon wasu shekaru yana kaka-ni-ka-yi da matsalolin dake tarnake ci gabansa sakamakon mummunar matsalar tsaro musamman ma a jihar Zamfara wadda ta zama babbar tungar ’yan bindiga. Kwararru a fannin sha’anin tsaro, sun sha nanata cewa matukar...
LEADERSHIP ta tattaro cewa, kuɗaɗen an turasu ne ga Abubakar da Sambo inda su kuma suka miƙa tsabar kuɗaɗen ga wasu agent-agent da makusantan gwamnan. An kuma gano cewa da fari Abubakar da ke gudanar da BDC ya tsallake sharaɗin beli amma an sake cafke shi. A lokacin da aka tuntuɓi kakakin EFCC Dele Oyewale kan wannan lamarin, ya tabbatar da batun kamun. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Tankar dakon man fetur ta kama da wuta a hanyar Karu zuwa Nyanya dake birnin tarayya Abuja, lamarin da ya haifar da wata mummunar gobara da ta rutsa da motoci da dama, inda ake fargabar mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da dama a yammacin ranar Laraba. Har zuwa yanzu dai ba a tantance musabbabin fashewar tankar man ba. Cikakken bayani na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp

An Gudanar Da Tarukan Tattaunawa Na Kasa Da Kasa Masu Jigon “Sin A Yanayin Bazara” A Turkiya Da Colombia
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ƙungiyoyin Ƙwadagon Najeriya, NLC da TUC, sun yi Allah-wadai da matakin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya ɗauka na sanya dokar ta-ɓaci a Jihar Ribas. Ƙungiyoyin sun soki dakatar da Gwamna Siminilayi Fubara, mataimakiyarsa, da ’yan majalisar dokokin jihar. Goman Ƙarshe: Dama ta ƙarshe ga mai neman rahamar Allah Matatar Dangote ta dakatar da sayar da fetur a Naira A wata sanarwa da suka fitar ranar Laraba, ƙungiyoyin bitu sun bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sashe na 2 da 305 na dokar 1999 da aka yi wa kwaskwarima. Sun ce wannan mataki ne da ka iya tauye ikon zartarwa, tare da zama barazana ga dimokuraɗiyya a Najeriya. A ranar Talata ne, Shugaba Tinubu...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni daga Gaza na cewa hare haren Isra’ila a baya bayan nan sun yi sanadin shahadar mutane kusan 1,000 a baya bayan nan wanda ke nuna irin girman barnar da gwamnatin sahayoniyan ke aikatawa a zirin. Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce sabon danyen aikin da Isra’ila ta yi ya kai ga kashe akalla mutane 970 cikin sa’o’i 48. Wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta kasar ta fitar ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ta kaddamar a ranar Talata, sun yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 970. Wasu rahotanni na daban ce mutane 356 ne suka mutu a harin da aka kai ta sama, a cikin sa’a huda sannan akalla Falasdinawa 1,000 ne suka samu raunuka. Wani...
Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmaeil Baghaei, ta yi kakkausar suka ga sabbin hare-haren da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza, yana mai bayyana su a matsayin “ci gaba da kisan kiyashi da share wata al’umma a yankin da aka yi wa kawanya. Baghaei ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar, sa’o’i bayan harin da Isra’ila ta kai a zirin Gaza, wanda ya yi sanadin mutuwar daruruwan Falasdinawa da suka hada da mata da kananan yara. Ya ci gaba da cewa, Amurka ce ke da alhakin kashe-kashen da ake yi a Gaza, yana mai cewa, ana kai hare-haren na Isra’ila ne da tare da goyan bayan Washington. Baghaei ya kuma yi kira ga...
Rundunar sojin Isra’ila ta sanar a ranar Larabar nan da cewa, ta kaddamar da hare-hare ta kasa a tsakiya da kudancin zirin Gaza, biyo bayan hare-haren wuce gona da iri kan yankin Falasdinu. Sanarwar ta bayyana cewa, sojojin sun karbe iko tare da fadada shi zuwa tsakiyar hanyar Netzarim, da nufin fadada yankin tsaro da samar da wani bangare na raba tsakanin arewaci da kudancin Gaza. A halin da ake ciki kuma, ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz, ya yi gargadin karshe ga Falasdinawa a zirin Gaza, inda ya bukaci da su sako Isra’ilawa da suke garkuwa da su, su kuma kawar da kungiyar Hamas, a cewar wata sanarwa daga ofishinsa. “Idan ba a sako dukkan mutanen Isra’ila da aka yi...