Jagoran Ya Ce: Iran Ba Ta Kallon Tattaunawan Iran Da Amurka A Matsayin Kawo Karshen Takaddama A Tsakaninsu
Published: 15th, April 2025 GMT
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata
Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya.
A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba.
Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan shawarwarin da kyakykyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata. A ƙarshen tattaunawar ne za a yanke shawarar kudurin da za a dauka, kuma a matakin farko an aiwatar da tattaunawar cikin kyakkyawan mataki.
Jagoran juyin juya halin Musulunci ya ci gaba da cewa: Ko shakka babu suna da ra’ayi sosai game da daya bangaren, amma suna da kyakkyawan fata game da kwarewar da suke da ita.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Jagoran juyin juya halin Musulunci
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Amurka Ta Yi Da’war Cewa; Ba Ta Neman Tashin Hankali Tsakaninta Da Iran
Gwamnatin Amurka ta sanar da cewa: Ba ta neman tada tashin hankali tsakaninta da Iran
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka Samuel Werberg ya bayyana cewa: Kasarsa ba ta neman kara ruruta wutar rikici da Iran, yana mai jaddada cewa har yanzu kofar diflomasiyya a bude take, duk kuwa da kakkausar murya da Amurka ta yi na kin amincewa Iran ta mallaki makamin nukiliya.
Werberg ya kara da cewa; Za su ci gaba da riko da siyasar matsin lamba da nufin dakatar da ci gaba a shirin nukiliyar Iran.
Kakakin na Amurka ya bayyana cewa, “Dole ne Iran ta nuna kyakkyawar niyyarta kafin ta yi magana kan duk wata nasara da za a samu.