2025-04-15@23:07:46 GMT
إجمالي نتائج البحث: 815

«Jagoran juyin juya halin Musulunci»:

    Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi barazanar korar sojojin da ke neman kawo karshen yakin Gaza bayan sun rattaba hannu kan wasu takardu da ke nuna bukatar hakan. A bayan nan dai fiye da sojoji 1,500 na rundunar da ke kula da tankokin yaƙi ta Isra’ila, ciki har da janar-janar, suka sanya hannu kan wata takardar neman gwamnatin Isra’ila ta mayar da hankali kan dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su a Gaza, ko da hakan zai kai ga dakatar da yaƙin da ake yi a yankin Falasdinawa. Budurwar da ke rayuwa a banɗaki don gudun biyan kuɗin hayar gida HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno A cewar Jaridar Maariv a ranar Litinin, sojoji 1,525...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Ba su kallon tattaunawa tsakanin Iran da Amurka na kasar Oman da kyakkyawan fata ko ganin rashin amfaninsa kwata-kwata Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya karbi bakwancin wakilan gwamnati da dama, da wakilan majalisar shawarar Musulunci, da manyan jami’an shari’a, da jami’ai daga cibiyoyi daban-daban a yau Talata, a daidai lokacin da ake bukukuwan shiga sabuwar shekara ta hijira Shamsiyya. A yayin wannan taron, Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Tattaunawar kasar Oman na daya daga cikin ayyuka da dama da ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ta aiwatar, bai kamata mu alakanta matsalolin kasar da wadannan shawarwari ba. Ya kara da cewa: Ba su kallon wadannan...
    Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta sanar da cewa: Za a gudanar da zaman tattaunawa kan Shirin makamashin nukuliyar Iran zagaye na biyu ne a birnin Muscat na kasar Oman Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya sanar da cewa: Zaman tattaunawa zageye na biyu wanda ba na kai tsaye ba, tsakanin Iran da Amurka zai kasance ne a birnin Muscat fadar mulkin kasar Oman. Baghaei ya yi watsi da rade-radin da ake yi kan inda za a gudanar da zagaye na biyu na tattaunawar kai tsaye tsakanin Iran da Amurka, Baghaei ya ce, “Bayan tuntubar juna, an yanke shawarar cewa birnin Muscat ne zai karbi bakwancin zagaye na biyu na shawarwarin, wanda za a yi a ranar Asabar mai...
    Lauyoyin Landan suna tattara bayanai kan ‘yan Birtaniya da suka yi aiki a cikin rundunar sojojin mamayar Isra’ila Kwararru kan harkokin shari’a na kasar Biritaniya sun ce gurfanar da wasu ‘yan kasar masu takardar ‘yan kasa biyu da ke aiki a cikin sojojin mamayar Isra’ila a gaban kuliya bisa zargin hannu a tafka laifukan yaki a Gaza, zai yi tasiri ga wadanda ke tunanin shiga cikin sahunsu. Hakan ya biyo bayan gabatar da rahoto ga rundunar ‘yan sandan birnin Landan ne mai kunshe da shaidun da suka shafi ‘yan Birtaniya guda 10 da suka yi aikin soja karkashin rundunar mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da ake zargi da aikata laifukan yaki a Gaza. A cewar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai...
    Gabanin ziyarar aiki da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai yi a Malaysia, firaministan kasar Datuk Seri Anwar Ibrahim, ya zanta da manema labarai na CMG a jiya Litinin, inda ya darajanta bunkasar huldar kasashen biyu.   Anwar Ibrahim ya kuma bayyana matukar amincewa da tunanin Xi Jinping na ingiza al’adu da wayewar kan Sinawa. A ganinsa, Xi Jinping babban jagora ne dake matukar mai da hankali kan abubuwan dake shafar zaman rayuwar jama’a. Ya ce duniya na bukatar musanyar al’adu sosai don kawar da bambancin ra’ayi, ta yadda za a tabbatar da wadata cikin hadin gwiwa. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Ma’aikatar tsaron Rasha ta sanar da yin luguden wuta kan zaman taron shugabannin sojojin Ukraine a birnin Sumy da ke arewa maso gabashin Ukraine Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, ta kai hari kan wani ofishin rundunar sojojin Ukraine da ke dauke da makamai masu linzami na Iskander a yayin wani zaman taron manyan sojojin kasar a birnin Sumy, inda aka kashe jami’ai sama da 60. Ma’aikatar tsaron Rasha ta kara da cewa sojojin na Ukraine na ci gaba da amfani da fararen hula a matsayin garkuwa gare su, tare da kafa cibiyoyin soji da kuma shirya tarurruka tare da halartar sojoji a tsakiyar birni mai yawan jama’a, tare da yin nuni da cewa; Rasha ta kai harin...
    Wata budurwa ’yar kasar China ta janyo muhawara a shafukan sada zumunta bayan ta nuna masaukinta da ba a saba gani ba — banɗaki mai faɗin ƙafa 6 a wurin aikinta, wanda ta biya kuɗin China Yuan 50 kacal, kwatankwacin Naira dubu 10 da dari 533. Kowa yana ƙoƙari ya tara kudi, amma mutum nawa ne za su yarda su kwana a banɗaki don tara kuɗi? HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno Hauhawar Farashi ya ƙaru a watan Maris — NBS Wannan budurwa ’yar garin Hunan a ƙasar China, ta girgiza duniya kwanan nan, bayan ta wallafa hotunan wajen zamanta da ba a saba gani ba – wani ƙaramin banɗaki da ba a amfani da shi...
    Al’ummar Babura sun shirya gagarumin taron girmamawa domin karrama Dr. Salisu Mu’azu, bayan nada shi a matsayin Daraktan kuma babban likitan asibitin koyarwa na Rasheed Shekoni da ke jihar Jigawa, da kuma samun matsayin mamba na Cibiyar Kasa (mni). Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban Kwamitin Shirye-shirye, Rabiu Umar, ya bayyana cewa an gudanar da taron ne domin nuna godiya ga Allah da kuma murnar manyan nasarorin da Dr. Mu’azu ya samu. Ya yaba da kokarin Daraktan wajen gudanar da aikinsa da kwarewa, da kuma ci gaba da tallafa wa al’umma. A sakon da aka gabatar a madadin Mai Martaba Sarkin Ringim, Alhaji Dr. Sayyadi Abubakar Mahmoud, wanda Mai Girma Alhaji Usman Sayyadi, Babban Hakimin Masarautar, ya wakilta,...
    Hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati, ta gaza tabbatar da zargin wulaƙanta takardar Naira da take yi wa fitacciyar ’yar TikTok ɗin nan, Murja Ibrahim Kunya. A bayan nan ne EFCC ta gurfanar da Murja a gaban kotu kan zargin cewa ta ci karo da wani bidiyonta tana rawa a kan takardun kuɗi har kimanin Naira dubu 400. A ƙunshin ƙarar da EFCC ta gabatar mai lamba FHC/KN/CS/18/2025 a gaban wata Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano, ta ce laifin da take tuhumar Murja tanadi na Kundin Dokokin Babban Bankin Nijeriya CBN wanda ya haramta wulaƙanta takardar Naira ta kowace siga.  
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    ’Yan Najeriya da suka rabauta da sayen shinkafar kasar waje da Gwamnatin Tarayya ta karya farashinsa sun koka bisa rashin ingancin wata wadda ake sayarwa a Jihar Kogi. Wadanda suka sayi rukunin farko na shinkafar sun yaba da ingancinta da dandanonta, wasu kuma na korafi a kan yanayi da kuma dandanon wadda suka samu daga wani kamfani daga wata kasar Asiya. Wasu suka samu shinkafar mai matsala sun yi ikirarin samun kwari a cikinta kuma tana yin kumfa idan ana dafa ta, sa’annan idan ta nuna tana yin danko sosai, sabanin yadda aka san shinkafar kasar waje. Wani dan kasuwar shinkafar cikin gida a Najeriya ya yi zargin rukunin shinkafar da ta samu matsalar ta jima a ajiye ne kafin...
    Rahoton Kungiyar Kasashe Masu Samar da Man Fetur (OPEC) ya nuna cewa Nijeriya ta ci gaba da riƙe matsayinta na ƙasa mafi yawan samar da ɗanyen man a nahiyar Afirka a watan Maris. OPEC ta ce hakan ya faru ne duk da raguwar yawan man da ƙasar ta samar a watan da ya gabata. Sabon rahotonta na wata-wata da ta fitar a ranar Litinin ya ce yawan man da Nijeriya ta samar ya ragu zuwa ganga miliyan 1.40 a kowace rana a watan Maris, idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairu. A cewar rahoton, duk da raguwar, yawan man da Nijeriya ta samar shi ne mafi yawa a Afirka, inda ya zarce Algeria da...
    Hukumar Bunƙasa Noman Sukari a Najeriya (NSDC) ta sanya hannu kan yarjejeniyar Dala biliyan guda da kamfanin SINOMACH na ƙasar China kan bunƙasa noman rake da sarrafa shi da nufin samar da sukari da kudina ya kai metrik ton miliyan guda. Kulla yarjejeniyar wani ɓangare ne na shirin Kawancen Najeriya da China, na Gwmanatin Shugaba Bola Tinubu, da nufin kawo masu zuba jari na kimanin Dala biliyan guda a ɓangaren sukari a Najeriya. Daga cikin yarjejeniyar, Kamfanin SINOMACH zai kafa masana’antar sukari da kuma gonar rake da za su fara da samar da metrik ton 100,000 na sukari a duk shekara. Kamfanin zai kuma taimaka da kwarewarsa da kayayyakin aikinsa wajen zartar da abubuwan da suka danganci gine-gine sayayyan kayan...
    Isra’ila ta kashe Palasdinawa 17 tare da jikkata wasu 69 a cikin awa 24 a yankin Gaza, inda ta kai harin sama a wani asibiti da ke yankin Khan Younis. Ma’aikatar Lafiyar Gaza ta sanar cewa jiragen Isra’ila sun kashe wani jami’in lafiya tare da jikkata wasu tara a Asibitin Kuwaiti da ke yankin Al-Musawi da ke Khan birnin Younis da ke Gabashin Gaza. Mai magana da yawun asibitin, Saber Mohammed, ya bayyana cewa wadanda harin ya rutsa da su sun hada da marasa lafiya da kuma jami’an kiwon lafiya. Isra’ila ba ta uffan a game da harin ba a halin yanzu, amma wasu rahotanni sun nuna jami’an tsaronta sun yi awon gaba da wasu Palasdinawa 14 a yankin Yamamcin...
    Majiyar Falasdinawa a Gaza sun bada labarin kissan wasu sojojin HKI  a unguwar Shuja’iyya kusa da Gaza a jiya Litini,  inda wasu kuma suka ji rauni. Kafafen yada labarai da yahudawan da kuma larabawa sun bayyana cewa kungiyar Jihadul Islami a Gaza ta ce nayakanta masu farautar yahudawa daga nesa sun bayyana cewa suk halaka wasu yahudawa wadanda suka boye a wani gida a garin Rafah kudancin Gaza, inda suke halakasu. Sannan a sauran wuraren kuma sojojin yahudawan da dama ne  suka ji rauni. Kuma sun ga jiragen yakin masu sauran ungulu na yahudawan sun zo sun tafi da wadanda abin ya shafa. Wannan dai kadan Kenan daga hare-haren maida martanin da dakarun falasdinawan suke mayarwa ga sojojin yahudawan, tun...
    A zantawarsa ta wayar tarho da tokwaransa na kasar Kuwait, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya ce tattaunawarsa da Abdullah Ali Al-Yahya ya fi bada karfi kan al-amuran yankin Asiya ta kudu musamman tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirinta na makamshin nukliya da kuma dagewa kasar takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata. A cikin tattaunawar dai ministan harkokin wajen kasar Kuwai y ace, kasashen yankin da dama sun ji dadin ganin cewa Iran da Amurka suna tattaunawa a tsakaninsu, kuma fatansu shi ne ya zama daga karshe kasashen biyu sun cimma dai-dato don warware matsalolin da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa. Aragchi ya bayyana cewa a halin yanzu ba zamu iya fadar menen sakamakon tattaunawar ba,...
    Ministan harkokin noma na JMI Ghulan Reza Noori Ghezelji ya jagoranci wata tawagar jami’an gwamnatin kasar zuwa kasar Brazil don halattan taron ministocin noma na kungiyar BRICS da kuma tattauna al-amura masu muhimmanci wadanda suka shafi ayyukan noma a duniya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa gwamnatin JMI ta fara aiki a matsayin mamba a kungiyar raya tattalin arziki na kasashen BRICS, wacce ta zama cikekken maba a farkon wannan shekara. Ta fara aiki tare da sauran kasashen kungiyar wadanda suka kafa ta, wato Brazil, Rasha, India, China,da kuma Afirka ta kudu.. Halattar wannan taron ba kawai zai kara karfin JMI a cikin kungiyar BRICS ba, sai dai zai kara inganta matsayin kasar a fagen noma...
    Bayan da hukumar zaben kasar Gabon ta tabbatar da nasarar da Brice Oligui yayi a zaben shugaban kasa na karshen makon da ya gabata, shugaban ya gabatar da jawabinsa na farko ga mutanen kasar, inda ya bayyana masu kan cewa, babu jin dadi sai tare da wahala. Shafin tanar gizo na labarai ‘Africa News” ya nakalto shugaban yana cewa muhimman al-amuran da zai sa a gaban a shugabancin kasar sun hada da sauya tsarin tattalin arzikin kasar daga dogaro da man fetur zuwa harkokin kasuwanci,  har’ila yau zai yaki cin hanci da rashawa. Brice ya ce, ya zo ne a matsayin mai gina kasa, kuma yana son taimakon su don samun nasara a wannan gagarum,in aikin. A ranar lahadin da...
    Wani ƙazamin rikici da ya janyo salwantar rayukan fiye da mutum 50 a Jihar Filato ya tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. Aƙalla mutane 51 ne aka kashe a wasu hare-hare biyu da aka kai a yammacin Lahadi a Jihar Filato da ke Arewa maso tsakiyar Nijeriya. Mahukunta a Filato sun ce an kai harin ne a cikin daren Litinin a garin Zike da ke yankin Kwall a Ƙaramar Hukumar ta Bassa. Mai bai gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Admiral Shipi Gakji mai ritaya, ya tabbatar wa BBC cewa an kai harin ne a cikin dare, wayewar garin Litinin kuma adadin waɗanda aka kashe “ya zarce 40.” Sai dai Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar ta Filato ta...
    Kasashen turan nan guda uku da ake wa lakabi da E3, sun nuna goyon bayansu ga tattaunawar da ake tsakanin Iran da Amurka. Ministan Birtaniya mai kula da yammacin Asiya Hamish Falconer ne ya bayyana hakan inda ya ce Birtaniya tare da Faransa da Jamus na goyon bayan sasanta batun nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya. A cikin sakon da ya wallafa, Falconer ya yaba da tattaunawar da akayi a babban birnin kasar Oman na Muscat a matsayin “muhimmiyar mataki na farko.” Kuma a cewarsa “Birtaniya, tare da kawayenta na E3, a shirye suke don tallafawa tattaunawar. A cikin 2018 a lokacin mulkinsa na farko, Trump ya janye Amurka daga yarjejeniyar da aka cimma a baya kan shirin nukiliyar Iran da...
    Wani babban jami’in Hamas ya ce kungiyar a shirye take ta sako dukkan fursunonin Isra’ila da suka rage a zirin Gaza da aka yi wa kawanya, domin musanya abin da ya bayyana da ” fursunoni” da kuma tabbatar da kawo karshen yakin kisan kare dangi da ake ci gaba da yi. Kamfanin dillancin labaran AFP ya nakalto Taher al-Nunu na cewa: “A shirye muke mu sako dukkan ‘yan Isra’ila da ake tsare da su a yarjejeniyar musayar fursunoni, da kawo karshen yakin, da janyewar sojojin Isra’ila daga zirin Gaza da shigar da kayan agajin jin kai.” A halin yanzu Hamas na tattaunawa a birnin Alkahira tare da masu shiga tsakani na Masar da Qatar. Saidai, duk da haka, jami’in na...
    Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya bayyana alhininsa akan rasuwar Dr. Akbar I’itimadi wanda shi ne na farko da ya kafa hukumar makamashin Nukiliya ta Iran. Wasikar ta’aziyyar da shugaban kasa ta kunsa ta ambaci cewa:  Shakka babu hidima mai kima da wannan masanin ya yi, ya share fagen gina da ci gaban fasahar makamashin Nukiliya a Iran da kuma mayar da kasar mai cin gashin kanta a wannan fage. Har ila yau, shugaban kasar ta Iran ya mika sakon ta’aziyyarsa ga masana na Iran, da kuma iyalansa. Ya kuma yi addu’a da rokon Allah madaukin sarki da ya lullube shi da rahamarsa da kuma gafararsa, sannan ya bai wa iyalansa na hakuri.
    A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu. Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza. Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can....
    Wani babban jami’in Diblomasiyya na kasar Iran ya bada sanarwan cewa zagaye na biyu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin JMI da Amurka za’a gudanar da shi ne a kasashen Turai a ranar 19 ga watan Afrilun wannan shekara ta 2025. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin waje na JMI kan al-amuran da suka shafi siysa Majid Takht-Ravabchi yana fadar haka a jiya Lahadi a lokacinda yake gabatarwa Majalisar dokokin kasar Iran rahoto kan taron tawagar Amurka da kuma JMI a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Jami’in diblomasiyyar ya kara da cewa, a tattaunawar da ba kai tsaye ba tsakanin kasashen biyu a ranar Asabar da ta...
    Babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa na yankin tekun Farisa (PGCC) ya yi fatan alkhairi ga kasashen Iran da Amurka a tattaunawa ba kai tsaye ba a tsakaninsu dangane da shirin Nukliya ta kasar Iran na zaman lafiya wanda suka fara, a birnin Mascat na kasar Omman a ranar Asabar da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jasem Mohamed AlBudaiw yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa, kungiyar tana bukatar gidan an warware matsaloli tsakanin kasashen duniya ta hanyar tattanawa.  Haka ma tsakanin kasashen yankin. AlBudaiw ya yabawa kasar Omman da shirya wannan tattaunawar, sannan ya yi fatan tattaunawan da aka fara zai kai ga rage tada jijiyoyin wuya a yankin da...
    Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Gabon wanda kuma ya jagoranci juyin mulkin da aka yiwa Ali Bongo tsahon shugaban kasar ya lashe zaben da aka gudanar a jiya Lahadi tsakanin yan takara 7 har da shi. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News” ya bayyana cewa Oligui dan shekara 50 a duniya, shi ne babban dogarin sojoji masu tsare fadar shugaban kasar Gaban, a lokacinda ya jagoranci juyin mulkin da ya kawo karshen mulkin da yan gidan Bogo suka yi na shekaru kimani 50 a kasar. Labarin ya kara da cewa kashi 2/3 na mutanen Gabon wadanda yawansu bai fi miliyon 2.3 ba suna cikin talauci a cikin kasa wacce take da arziki mai yawa. Brice zai jagoranci kasar...
    A yau Lahadi ne shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaban kasar Indonesia, Prabowo Subianto suka yi musayar taya juna murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasashen biyu. Inda shugaba Xi ya ce, yana dora matukar muhimmanci kan raya dangantakar dake tsakanin Sin da Indonesia, kuma a shirye yake ya yi amfani da bikin cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu, a matsayin wata dama ta yin aiki tare da shugaba Prabowo, wajen kara zurfafa hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, da karfafa hadin gwiwa a batutuwan da suka shafi bangarori daban daban bisa manyan tsare-tsare, da ci gaba da inganta al’ummar Sin da Indonesiya mai kyakkyawar makomar bai daya daga dukkan fannoni, kuma...
    Jagoran juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Makiya suna cike da takaici da fushi kan ci gaban da Jamhuriyar Musulunci ta Iran take samu A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin kasar Iran a yau Lahadi, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya jaddada cewa; Ci gaban da Iran ta samu ya fusata da kuma kara takaicin masu mugun nufi kan lasar ta Iran. Yana mai bayyana cewa, tabbas akwai rauni a fannonin da suka shafi tattalin arziki da ya kamata a magance. Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya yi la’akari da cewa; Sojojin kasar suna matsayin kariya ta al’umma da kuma mafakar al’umma daga duk wani mai wuce gona da iri, sannan kuma ya jaddada...
    Kwamandan rundunar sojojin kasa ta Iran ya bayyana cewa: Nan ba da jimawa ba za a yaye labulen ire-iren makamai na musamman da Iran ta mallaka Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran Birgediya Janar Kiomars Heidari ya yi nuni da shirin rufe kan iyakar kasar da ke gabashin Iran, yana mai cewa: Wannan ba kawai wata katanga ba ce mai tsayin mita 4, saboda an tanadar da ita ce da nau’o’in makamai masu kwaloluwar ci gaba na zamani a duniya, wannan shiri an gudanar da shi ne tsawon shekaru hudu kuma za a kammala shi nan da shekaru uku masu zuwa. Kwamandan rundunar sojin kasa ta Iran ya jaddada haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar a...
    Jiragen saman yakin mamayar Isra’ila sun kai farmaki kan asibitin Baptist da ke birnin Gaza, lamarin da ya janyo dakatar da aiki a cikinsa Wakilin gidan talabijin na Al-Alam Mohammed Al-Balbisi ya ruwaito cewa: Jiragen saman yakin sojojin mamayar Isra’ila sun yi ruwan bama-bamai a wasu gine-gine na asibitin Baptist, da suka hada da ginin sashin kula da marasa lafiya cikin gaggawa da kuma motocin daukar marasa lafiya da wasu sassa da tantuna da ke ba da hidima ga wadanda suka jikkata. Ya yi nuni da cewa da sanyin Safiya yau Lahadi, sojojin mamayar Isra’ila sun harba makamai masu linzami da dama kan wadannan gine-gine lamarin da ya tilastawa marasa lafiya da likitoci ficewa daga asibitin tare da fakewa a...
    Sakamakon gazawar shugabanci, bayar da tallafi na neman zama wani bangare a tarihin dimokoradiyyar Nijeriya, inda gwamnatocin jihohi da ’yan majalisu da sauran ’yan siyasa suke amfani da shi wajen cusa wa ’yan kasa ra’ayinsu na siyasa. A duk lokacin da al’umma suka koka a kan wani mummunann yanayi da ya hada da matsin tattalin arziki da gobarar tankar mota da ambaliyar ruwa da gobara, abin da yake biyo baya shi ne gwamnati ta raba tallafin shinkafa da sauaran kayan abinci, tamkar shinkafa ita ce maganin duk wata matsala. A wasu lokutan, a kan raba babura masu kafa uku da dabbobi a matsayin tallafi. Makudan kudaden da gwamnatoci suke kashewa da sunan bayar da tallafi, inda ba a ganin tasirin...
    Matainakin shugaban kasar kasar Iran na farko Mohammad Reza Aref ya bayyana cewa, daukewa Iran takunkuman zalunci wadanda kasashen yamma suka dora mata na daga cikin asalin hakkin kasar da aka tauye. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Aref yana fadar haka a jiya Asabar, ya kuma kara da cewa, kasar Iran ba zata manta da hakkin kasar wanda Amurka ta take tun farkon nasarar juyin juya halin kasar shekaru 46 zuwa yanzu ba, amma duk da haka sun bata damar tattaunawa.  Yace: Muna son mu nunawa duniya kan cewa har yanzun muna hakuri, amma ba zamu taba manta da zaluncin da aka yi mana ba.   Mataimakin shugaban yana maganar ficewar kasar Amurka daga yarjeniyar JCPOA da...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esma’ila Bagaei ya godeawa ministan harkokin wajen kasar Omman kan yadda ya shirya ya kuma gabatar da tattaunawa tsakanin JMI da Amurka a birnin Mascat da kuma kai kawon da yayi a  tsakanin bangarorin biyu. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Bagaei yana bayyana haka a wani sakon da ya aika a cikin shafinsa na X  a jiya Asabar, ya kuma aika da sakon ne a dai dai lokacinda ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi yana kan hanyarsa ta dawowa Tehran, bayan tattaunawar. Ya kuma kara da cewa yana fatan Badr bin Hamad Al Busaidi zai ci gaba da wannan kokarin a ranar Asabar mai zuwa inda bangarorin biyu zasu...
    Jiragen yakin Amurka sun kai sabbin hare-hare kan wasu yankunan a kasar Yemen a safiyar a jiya Asabar, wadanda suka Baida Sa’ada da kuma Hudaidah wadanda sune sake zafafa yaki a ciki kasar na baya-bayan nan. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labarai na kasar ta Yemen na fadar cewa jiragen yakin kasar ta Amurka sun kai  hare-hare har 5 a kan makarantar koyon sana’o’ii na Al-sawma  da ke lardin  Al-Bayda a jiya Asabar . Labarin ya kara da cewa makarantar ita ce babbar makaranta a yankin, kuma cibiyar ilmi mafi girma. Har’ila yau labarin ya bayyana cewa jiragen yakin kasar ta Am,urka sun kai hare-hare har guda 3 a kan garin Al-Sahleen daga cikin...
     Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa ” Amnesty International”  ta bayyana cewa, rundunar kai daukin gaggawa ta “RSF” ta bautar da mata da kuma cin zarafinsu. Kungiyar ta yi tir da abinda rundunar ta “RSF” ta yi akan mata da su ka manyanta da kuma ‘yan mata a tsawon lokacin yakin na Sudan da har yanzu bai zo karshe ba. Wani sashe na rahoton kungiyar ya yi ishara da yadda wannan rundunar da take fada da sojojin kasar Sudan ta tarwatsa mutane daga gidaje da matsugunansu a fadin kasar. Ita kuwa Hukumar dake kula da ‘yan gudun hijira ta MDD ( UNHCR) cewa ta yi da akwai yan kasar ta Sudan fiye da 100,000 da suke neman yin...
    Ya soki masu ra’ayin cewa dimukradiyya wani sharadi ne na ci gaba, yana mai cewa “karya ne” shi akwai wata kasa da ta ci gaba a karkashin tsarin dimukradiyya?. Burkina24 ta nakalto cewa “Babu wata kasa da za a iya bayyanawa da ta ci gaba a dimukradiyya. Ya ci gaba da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da sadarwa, bayyanawa, da kuma fahimtar da mutane mene ne juyin juya hali. Traore ya yi fice wajen yanke shawarar ce bayan hayewarsa a matsayin shugaban kasar da ke yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 37 da haihuwa wanda ya hau karagar mulki a watan Satumban 2022 ta hanyar juyin mulkin da ya hambarar da shugaban kasar na wucin gadi Paul-Henri Damiba kwanan nan...
    Tsohon ɗan wasa, kuma tsohon mai horas da ’yan ƙwallon Super Eagles ta Najeriya, Christian Chukwu ya rasu. Christian Chukwu ya rasu ranar Asabar yana da shekara 74. Fashewar bam a mota ta kashe mutum takwas a Borno An kashe Uba da ’ya’yansa biyu a ƙauyen Filato Christian Chukwu ne kyaftin ɗin tawagar Super Eagles lokacin da Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) ta 1980. Dakta Olusegun Odegbami, tsohon ɗan wasan Najeriya kuma abokin Chukwu, ya tabbatar rasuwar mai ban tausayi a saƙon da ya wallafa ta manhajar sada zumunta X. “Na samu labarin cewa tsakanin ƙarfe 9:00 zuwa 10:00 na safiyar yau Asabar, Christian Chukwu, MFR, wanda aka fi sani da Chairman abokina kuma abokin wasana,...
    Jami’an lafiya a Gaza, sun ce akalla mutane 1,563 ne aka kashe tun bayan da Isra’ila ta koma kai farmaki a Zirin tun daga ranar 18 ga watan Maris, yayin da al’amuran jin kai ke kara ta’azzara a Gaza. Adadin mutanen da suka mutu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun bayan da Isra’ila ta karya yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kungiyar Hamas ta Falasdinu a watan jiya ya zarce 1,560 a cewar jami’an kiwon lafiya. A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar yau Asabar, ma’aikatar lafiya ta Gaza ta ce hare-haren Isra’ila sun kashe akalla mutane 21 a cikin sa’o’i 24 na baya-bayan nan. An kashe mutane 50,933 tare da raunata 116,045 tun farkon yakin a watan...
    Kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa na fatan nasara ga tattaunawar Iran da kuma Amurka. Kasar Iraki ta bayyana fatan tattaunawar za ta aifar da kwanciyar hankali a yankin Ministan harkokin wajen Iraki ya bayyana goyon bayansa ga tattaunawar tsakanin Iran da Amurka, yana mai bayyana fatan Bagadaza na ganin cewa hakan zai samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen Iraki ta fitar ta ce “Hussein ya karbi bakuncin mataimakin ministan harkokin wajen Iran Saeed Khatibzadeh a ranar Juma’a a gidansa da ke birnin Antalya na Turkiyya. Sanarwar ta kara da cewa “a yayin ganawar, an tattauna dangantakar da ke tsakanin kasashen dake makobtaka da juna da kuma hanyoyin karfafa...
    Isra’ila ta ce ta karbe iko da wata muhimmiyar hanya a zirin Gaza a wani mataki da ya yanke gaba daya yankin kudancin Rafah mai yawan jama’a daga sauran yankunan Falasdinawa da aka yiwa kawanya. A cikin wata sanarwa da Isra’ila ta fitar yau Asabar ta ce dakarunta sun yi wa Rafah kawanya gaba daya tare da samar da “yankin tsaro” a can. Sanarwar da ministan harkokin soji na gwamnatin Isra’ila Katz ya fitar ta ce sojojin sun karbe ikon “Morag axis, wanda ke ratsa Gaza tsakanin Rafah da Khan Yunis.” Katz ya kuma yi kira ga Falasdinawa da su fara kaura zuwa yamma, yana mai gargadin cewa nan ba da jimawa ba za a kara kaimi da fadada ayyukan...
    Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya ce kasashen wamma suna son kebe kansu da fasahar nukliya a tsakaninsu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Muhammad Eslamu shugaban hukumar AEOI yana fadar haka a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa kamfanin makamashin nukliya na kasar Iran ya kafa a kasar Iran kuma ba wanda ya isa ya kauda shi. Sabanin abinda kasashen yamma suke so na hana sauran kasashen duniya mallaka fasahar nukliya, da kuma dogara da su kadai, su bada abinda suka ga dama ko  su hana gaba daya. Ya ce JMI ta wuce wasu kasashen yamma a ayyuka da kuma sani da sarrafa makamashin Uranium, wanda ya tada hankalin wadannan kasashe, kuma suke...
    Shugaban hukumar yan gudun hijira na MDD Filippo Grandi wanda ya ziyarce sansanonin yan gudun hijira na kasar Sudan a Chadi ya bayyana cewa akwai bukatar kasashen duniya su taimaka don kula da bukatun yan kasar sudan wadanda suke gudun hijira a kasar Chadi. Grandi ya kara da cewa akwai bukatar agaji da gaggawa zuwa kasar Chadin da kuma sauran kasashen da suke daukar nauyin yan gudun hijira na sudan. A halin yanzu dai ana ganin mutane kimani 20,000 ne suka rasa rayukansu, sannan wasu da dama suka ji rauni sannan wasu kuma suka zama yan gudun hijira.
    Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a Kaduna. Atiku ya samu rakiyar tsofaffin gwamnoni da suka haɗa da tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da wasu jiga-jigan ’yan siyasa. An gano gawar makiyayi da ƙwato shanu a Filato Boko Haram: Zulum ya yi ganawar sirri da Shugabannin sojoji Kamar yadda aka wallafa bidiyon ziyarar a Shafin Atiku na Facebook, an rubuta cewa sun ziyarci Buharin, kuma sun sha dariya. “A matsayina na Wazirin Adamawa, na tsaya domin gudanar da shagungulan Sallah a Adamawa, inda na wakilci Sarkin Adamawa, Lamiɗo Fombina a wasu shagulgulan. “Yau kuma na kai ziyarar...
    Kudin biyan bashin cikin gida na shekarar 2024 ya kai naira tiriliyan 5.97, wanda hakan ke nuna karin kashi 14.15 cikin 100 daga naira tiriliyan 5.23 da aka samu a shekarar 2023. Karuwar ana danganta shi da karuwar kudin ruwa da karin lamuni na cikin gida. Nijeriya dai ta kashe dala biliyan 4.66 (kwatankwacin naira tiriliyan 7.15 kan farashin canjin naira 1,535.32/$1), wanda hakan ya nuna karuwar kashi 167 cikin 100 daga naira tiriliyan 2.57 da aka samu a shekarar 2023. Yawan kudin biyan basussuka na waje yana da nasaba da hauhawar farashin ruwa a duniya da kuma faduwar darajar naira, lamarin da ya sa bashin dala ya yi tsada wajen aiki. Duk da yawan kudin basukan da ke kan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Idan masu ajiya a Bnkin suka ajiye akalla Naira 10,000 a Asusun ajiya na Bankin ko kuma a cikin Lalitar ajiyarsu ta Bankin a kalla a cikin kwanuka 30, hakan ya nuna cewa, sun tsallake zamowa Zakarun samun damar lashe kyaututuka a wata daya, inda kuma za su shiga gasar zagaye ta karashe. Kazalika, a cikin kowanne wata daya, mai ajiyar zai iya zamaowa a cikin rukunin Zakaru 70, inda kowanne mai ajiya daya a Bankin, zai iya karbar Naira 100,000. Har ila yau, a cikin watanni uku kuma, kowanne mai ajiya daya a Bankin na Stanbic IBTC, da ya fito daga yanki bakwai da ake yin kasuwanci, zai lashe Naira miliyan daya, inda kuma a zagayen gasar na karashe...
    Sanata Oluremi Tinubu yt gana da sarakunan Taraba, ta kuma ba da gudummawar naira miliyan 50 don tallafa wa mata 1,000, da kayan aiki dubu 10,000 ga ma’aikatan lafiya   Uwargidan shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Bola Ahmed Tinubu, ta bukaci shugabannin gargajiya da su marawa shirin ta na sabon fata ta hanyar wayar da kan jama’a game da shirye-shiryen kiwon lafiya da ke gudana a fadin kasar.   Misis Tinubu ta yi wannan roko ne a Jalingo, babban birnin jihar Taraba, yayin wata ganawa da sarakunan gargajiya a ranar Alhamis, wanda aka gudanar a dakin taro na uwargidan gwamnan jihar.   Uwargidan shugaban kasa, Sen. Oluremi Bola Ahmed Tinubu da ta isa filin jirgin saman Danbaba Suntai a ranar Alhamis...
    Fira ministan HKI Benjamine Netanyahu ya yi suka cikin fushi saboda Fira ministan kasar Mark Carney  Canada ya bayyana cewa abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi dai Fira ministan kasar Canada Mark Carney wanda ya halarci taron yankin neman zabe a garin Calgary, yayin da wani daga cikin mahalarta, ya daga murya da karfi yana fada wa Fira ministan cewa, Abinda yake faruwa a Falasdinu kisan kiyashi ne. Shi kuwa Mark Carney ya amsa mas ada cewa; Ina da masaniya, kuma shi ne dalilin da ya sa kasar Canada ta daina sayar wa da Isra’ila makamai. Sai dai kuma kwana daya bayan abinda ya faru, fira ministan na kasar Canada ya lashe amansa inda ya bayyana cewa,...
    Kazalika, a wani binciken kwanan baya na gama gari kan yawan alummar kasar, ya gano cewa, kaso 53 na wasu matasan kasar, a kullum suna rungumar wannan dabi’ar. Sai dai, muna sane da cewa, wasu ‘yan Nijeriya, na kallon yin cacar tamkar wata aba ce, ta nishadi kawai, amma wasu bincike sun bayyana cewa, wani dan bangere na mutanen da ke yin cacar ne kawai, ke samun a cacar, inda akasarin sauran, ke tabka asarar kudadensu da suka zuba a cikin cacar. An dai jima ana yin caca a kasar, wadda a shekarun baya, ake yi mata wani kallon kan abinda bai dace ba, kamar dai yadda Coci ta alakanta ta, a matsayin hanyar yin arzikin dare daya Idan za...
    Sojojin kasa na kasashen Iran ta Armenia sun fara atisayen soje na hadin guiwa a tsakaninsu, don kyautata tsaro na kan iyakar kasashen biyu na kuma tsawon kwanaki biyu. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran ne suke jagorantar wannan atisayen. Da nufin hana fasa korin muggan kwayoyi da kuma sulalewar yan ta’adda suka kan iyakokin kasashen biyu. Burgediya Janar Sayyid Mortaza Mira’in babban hafsan  sojojin kasa na IRGC ya bayyana cewa, wannan atisayennn   yana nuna irin yadda sojojin IRGC suke da shirin kare kasar daggga duk wata barazana. Da kuma abota da kyautata makobtaka da kasashe mmmakobta. Labarin ya kara da cewa ana gudanar da rawan dajin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Yobe ta samu gagarumar nasara a ƙoƙarinta na yaƙi da miyagun laifuka, inda ta cafke wasu fitattun mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane. Waɗanda aka kama sun haɗa da: Babaro Baushe mai kimanin shekara 40 da Umaru Dau’a, mai kimanin shekara 25 da suka fito daga ƙauyen Askuwari a ƙaramar hukumar Tarmuwa a ranar 9 ga Afrilu, 2025. Gwamnatin Kano ta tura tawaga zuwa Edo kan kisan mafarauta Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi A takardar sanarwar da kakakin rundunar ‘Yan sandan Yobe, SP Dungus Abdulkareem ya fitar ya ce, hedikwatar ’yan sanda reshen Dapchi da misalin ƙarfe 0500hrs, 9 ga Afrilu, 2025, ta cafke waɗanda ake zargin, ’yan ƙungiyar...
    Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci wata tawaga zuwa Jihar Edo domin binciko gaskiyar abin da ya faru game da kisan mafarauta ’yan asalin jihar a ƙauyen Uromi. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne, ya umarci a kafa wannan tawaga, wacce ta ƙunshi manyan shugabanni irin su Sarkin Rano, Kwamishinonin ma’aikatu da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Bunkure. Ruwan sama ya lalata gidaje da yawa a Kebbi Yadda Tinubu ya taimaka wa ’yata ta samu aiki a NUPRC — Buba Galadima “Manufarmu a bayyane take – bincike, tattaunawa da bayar da shawarwari masu ɗorewa. “Wannan ba kawai yawon neman gaskiya ba ne, har ila yau ƙoƙari ne na kawo zaman lafiya, domin hana sake faruwar irin wannan tashin...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakchi ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badr Abdelatty, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi yankin. Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da Masar sun yi magana ta wayar tarho da yammacin ranar Laraba, a cewar shafin Telegram na kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran. Araqchi ya jaddada muhimmancin daukar matakin hadin gwiwa da kasashen yankin domin gaggauta dakatar da laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke aikatawa, da kuma tsagaita bude wuta a zirin Gaza, lamarin da ya ce yana da matukar muhimmanci wajen warware wasu rikice-rikice a yankin yammacin Asiya. Jami’an biyu sun bayyana matukar damuwarsu kan yadda ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin, sakamakon ci gaba da kai...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ba shi da wata adawa da Amurkawa masu zuba jari a kasar. “Muna maraba da masu zuba jari.” amma ba tare da tauye mutunci ko tsaron kasa ba. Har ila yau kalaman nasa sun sake tabbatar da kin amincewar da Iran ta dade tana yi na yin watsi da shirye-shiryen mallakar makamin nukiliya, wanda kasashen yammacin duniya ke zarginta da neman bama-baman nukiliya. “Muna shirye don yin shawarwari, ba kai tsaye ba. Ba mu amince da su ba. Dole ne a yi tattaunawa bisa mutunta juna inji shugaban kasar ta Iran. “Ba mu taba kera bama-bamai na nukiliyaba, ko a baya,...
    Gwamnatin Washington ta sanar da kakabawa Iran sabbin takunkumai kan shirinta na nukiliya an zaman lafiya, a matakin da Amurka ke ganin shi ne kawai hanyar matsin lamba kan Iran domin ta mika wuya game da shirint ana nukiliya. Takunkumin, wanda ma’aikatar baitul malin Amurka ta sanar a jiya Laraba, ya shafi hukumomi biyar da kuma wani mutum guda da ke Iran, saboda abin da sashen ya bayyana a matsayin goyon bayan shirin nukiliyar Iran. Baitul malin na Amurka ya ce bangarorin da aka laftawa takunkumin na baya baya nan sun hada da Hukumar Makamashin Nukiliya ta Iran (AEOI) da ta karkashinta, Kamfanin Fasaha na Centrifuge na Iran. Sakataren baitul malin kasar Scott Bessent ya bayyana a cikin wata sanarwa...
    Manchester City na nace kan buƙatar ɗanwasan tsakiya na Newcastle da Brazil Bruno Guimaraes, mai shekara 27, yayin da take shirin rabuwa da ɗanwasanta na Belgium Kevin de Bruyne, mai shekara 33. (UOL esporte – in Portuguese) Chelsea a shirye take ta biya fam miliyan 102 kan ɗanwasan Real Madrid da Brazil Rodrygo, mai shekara 24. (Fichajes – in Spanish) Manchester City na nazarin taya ɗanwasan tsakiya na AC Milan da Netherlands Tijjani Reijnders, mai shekara 26, kan tsakanin fam miliyan 42 zuwa fam miliyan 51 duk da ya sabunta kwangilar shi har zuwa 2030. (Calciomercato – in Italian) Ana sa ran Everton za ta rasa ɗanwasan bayanta na Ingila Jarrad Branthwaite, mai shekara 22, yayin da Manchester United da Tottenham ke hamayya...
    Lauyan kare hakkin bil’adama Femi Falana SAN ya yabawa jihar Kano bisa yadda take tafiyar da harkokin shari’a.   Falana ya bayyana hakan ne a yayin wani taron karawa juna sani ga masu gabatar da kara kan ingancin gudanar da shari’ar laifuka da Kurawa Hussein And Associates tare da hadin giwar Ma’aikatar Shari’a ta Kano suka shirya, wanda aka gudanar a otal din Bristol Kano.     Falana ya yabawa jihar Kano bisa amincewa da dokar hukumar kula da laifuka ta FIDRA a shekarar 2019 tare da zama jiha ta farko da ta soke tuhumar da jami’an ‘yan sanda ke yi na aikata laifuka.   Ya kuma jaddada bukatar masu gabatar da kara su samar da na’urori na zamani da...
    Bisa umarnin haramcin, za a dakatar da duk wasu huldodin fitar da hajoji daga kasar Sin zuwa wadannan kamfanoni nan take. Kazalika, a cewar ma’aikatar cinikayyar ta Sin, idan akwai wata bukata ta wajibi, dole ne sassan da za su gudanar da wata hulda mai alaka da hakan su tabbatar sun nemi izni.   Ban da haka kuma, ma’aikatar ta ce kasar ta kara sunayen wasu kamfanonin Amurka 6, cikin jerin sassan da ba za a iya dogaro da su ba.   Ma’aikatar wadda ta bayyana hakan a Larabar nan, ta ce kamfanonin su ne Shield AI, da Sierra Nevada Corporation, da Cyberlux Corporation. Sai kuma Edge Autonomy Operations LLC, da Group W and Hudson Technologies.   Tun daga karfe...
    Wasu ’yan bindiga sun nemi a ba su Naira miliyan 100 kafin su sako wani fasto da suka yi garkuwa da shi a Jihar Kaduna. Faston, mai suna Samson Ndah Ali, mai shekaru 30, yana aiki da cocin Evangelical Church Winning All (ECWA) da ke Mararaba Aboro, a Ƙaramar Hukumar Sanga. Mutanen da suka saba ba ni abinci yanzu na neman taimako — Obi ’Yan bindiga sun mamaye garuruwa 64 a Filato — Gwamna Mutfwang An sace shi da misalin ƙarfe 1 na daren ranar Litinin, lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidansa. Faston ya fara aiki a cocin ne ƙasa da makonni biyu kafin wannan lamarin ya faru. Sakataren cocin, Yusuf Ambi, ya ce yana tare da Faston a...
    Assalamu alaikum masu sauraro barakammu da war haka, sharhin bayan labarummu zai yi magana dangane da ‘Siyasar Amurka ta fara yakin kudaden fito tsakaninta da China da kasashen Turai da sauransu. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///.. A ranar laraba 2 ga watan Afrilun da muke ciki ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fidda jadawalin kudaden fito ga dukkan kayakin da suke shigowa Amurka daga wadannan kasashen, daga ciki har da kasashen Turai da kuma kasar Chaina, ya zuwa yanzu dai kasar china ta maida martani da kashi 34% na kayakin Amurka da suke shigowa kasar China, sannan Amurka ta kara maida martani ga kasha 104 kan kayakin kasar china masu shigowa Amurka, sannan kasashen turai da dama...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan ya bayyana cewa JMI ba zata taba jada baya a kan shirinta na makamashin Nukliya ba, kuma yayi allawadai da duka wani shiri na kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar Hare-hare. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana fadar haka a taron raya ranar Nukliya ta karo karo na 19 a wanda aka gudanar a nan Tehran. Shugaban ya kara da cewa, Iran bata neman yaki da kowa, amma zata maida martani kan duk wata takala daga HKI ko Amurka. Ya ce Iran ba zata amince wani ya hana mutanen kasar amfani da fasahar da All..ya hore masu ba. Ya kuma kara jaddada cewa JMI bata neman mallakar makaman Nukliya. A rana irin ta yau ce...
    Kungiyar tarayyar Turai ta yi maraba da tattaunawa tsakanin Amurka da JMI dangane da shirinta na makamashin Nukliya, tare da kara jaddada cewa hanyar diblomasiyya kadai ta rage don warware wannan matsalar. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a halin yanzu dai kungiyar tarayyar ta Turai ta na ci gaba da takurawa JMI da takunkuman tattalin arziki, masu  tsanani, a lokaci guda tana fadar cewa hanyar Diblomasiyya ce kadai ta rage wajen warware matsalar shirin makamashin nukliya na kasar Iran, wanda ya tabbatar da fuska biyu na kasashen na Turai. Labarin ya kara da cewa, wani mai magana da yawun kungiyar ta EU wanda kuma baya son a bayyana sunansa, ya fadawa kamfanin dillancin labaran IRNA...
    Sojojin kasar Yamen sun bada sanarwan maida martani ga hare-haren jiragen yakin kasar Amurka a kan kasar na baya-bayan nan, kuma zasu ci gaba da kai hare-haren kan wadannan wurare har zuwa lokacinda za’a kawo karshen yaki a Gaza. Tashar talabijin ta presstv a nan Tehran ta nakalto kakakin sojojin kasar Yemen Burgediya Janar Yahyah Saree yana fadar haka a yau Laraba . Ya kuma kara da cewa, a wannan karon sun yi amfani da jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa, kan wasu wurare masu muhimmanci a birnin Yaffa (tel’aviv). Haka ma sun cilla wasu makaman kan jirgin yaki mai daukar jiragen sama na Amurka wato USS Harry Truman dake arewacin tekun red Sea. Kafin haka dai jiragen Amurka...
    Jiragen yakin HKI sun kashe akalla mutane 38 a wurare daban-daban a zirin Gaza, kuma mafi yawan wadanda ta kashen yara kanana ne. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdinawa a Gaza na cewa da sassafe jiragen yakin sun kaiwa wani gidan Bene a unguwar shujaiyya na wajen garin Gaza inda a nan take suka kashe falasdinawa kimani 30 sannan wasu da dama suka ji rauni. Sai kuma a kan sansanin yan gudun hijira na Nusairat jiragen yakin HKI sun kashe muatne akalla 8 wanda ya kawo jimillar wadanda aka kashe zuwa lokacin bada wannan labarin zuwa 38. Wasu da dama sun ji rauni. Raunukan wasu yana da hatsari mai yuwa yam utu nan gaba. Sannan...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina al’umma mai kyakkyawar makomar bai daya tare da kasashe makwabta, da kuma kokarin bude sabon babi na ayyukan da suka shafi kasashe makwabtan kasar Sin.   Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin kolin soja na kasar, ya bayyana hakan ne a taron koli kan ayyukan da suka shafi kasashe makwabta, wanda aka gudanar a birnin Beijing daga ranar Talata zuwa Laraba. (Mai fassara: Mohammed Yahaya) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki...
    Amurka za ta iya janye sojoji 10,000 daga Gabashin Turai, kamar yadda rahoton NBC News ya bayyana. A shekarar 2022, tsohon shugaban Amurka Joe Biden ya tura karin sojoji 20,000 zuwa yankin bayan Rasha ta kai hari Ukraine. A ranar Talata, NBC ta ruwaito cewa jami’ai shida daga Amurka da Turai sun tabbatar da tattaunawa kan rage yawan sojojin da aka tura, inda aka fi mayar da hankali kan rage adadin a Romania da Poland. Shugaba Donald Trump yana kokarin kawo karshen yakin Ukraine da aka shafe fiye da shekaru uku anayi tun bayan hawansa mulki, amma har yanzu bai cimma nasarar warware matsalar ba. Ya sha sukar NATO, yana mai jaddada cewa ya kamata Turai ta dauki karin nauyi...
    Ministan Lafiya, Farfesa Muhammad Pate ya bayyana cewa, sama da likitoci dubu 16 sun fice daga Nijeriya a cikin shekaru biyar zuwa bakwai da suka gabata zuwa wasu ƙasashen duniya don ci gaba da aiki cikin ingantaccen yanayi. Farfesa Pate ya bayyana haka ne a wurin taron horas da Ƙungiyar Likitocin Afrika da ya gudana a birnin Abuja a ranar Talata. Nijar ta ayyana Hausa a matsayin yaren ƙasa DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa ‘Matar Bahaushe Ba Ta Iya Kiran Sunan Mijinta’ Ministan ya bayyana cewa, ana ci gaba da samun wani adadi mai yawa na ƙwararrun likitocin da ke da burin fita zuwa wasu ƙasashen duniya aiki, suna fakewa da matsalolin tattalin arziƙi da rashin kyawun yanayin aiki...
    Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya yi martani ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump na baya-bayan nan game da yiwuwar tattaunawa da Iran kai tsaye, inda ya yi karin haske kan matsayar Tehran, kamar yadda jaridar Washington Post ta kawo. Araghchi ya bayyana imaninsa cewa irin matakan da Iran ta dauka a baya-bayan nan dangane da wannan tattaunawa wani babban yunkuri ne na diplomasiyya. Ya fayyace cewa sabanin wasu fassarori da aka yi a baya-bayan nan a game da batun tattaunawa tsakanin kasashen biyu, inda ya ce kokarin bayyana ra’ayi ne na gaskiya da bude hanyar diflomasiyya. Dangane da kalaman Trump da ya yi a ranar litinin, Araghchi ya bayyana cewa Iran a shirye take domin ganin an cimma...
    Adadin wadanda suka yi shahada a zirin Gaza ya karu zuwa 58 a cikin ‘yan sa’o’i da suka gabata, yayin da wasu 213 suka jikkata sakamakon kazamin harin bam da Isra’ila ta kai a yankin. Jiragen yakin Haramtacciyar Kasar Isra’ila sun kai hari kan fararen hula da gidajensu, a ci gaba da luguden wutar da suke yia  kan fararen hula a yankuna da dama na Gaza. Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da samun sabbin adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da Isra’ila ke kai wa zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda adadin shahidai ya kai 50,810 yayin da adadin wadanda suka jikkata ya kai 115,688. Adadin wadanda suka raa...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali.  “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa.  “Daga shekaru uku baya zuwa yanzu a hankali zaman lafiya ya fara dawowa Borno, amma lamarin ya sauya a ‘yan kwanakin nan,” in ji shi Zulum...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun kaka da kakanni an san Hausawa  da kawaici da kunya da kuma girmama na gaba da su. Mai yiwuwa wadannan dabi’u ne suka sa matar Bahaushe ba ta iya hada ido da mijinta, balle ta kira shi da sunansa na yanka. To amma a zamanin yau ba abin mamaki ba ne a samu matar aure ta kalli kwayar idon mijinta, ta kuma kira shi da sunansa na yanka. NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta A kan wannan al’ada – asalinta da alfanunta da dalilan sauyawarta – shirin Daga Laraba na wannan makon za iyi nazari. Domin...
    Li Qiang ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, kasar Amurka ta sanar da kara buga harajin kwastam ga dukkan kasashe abokanta na cinikayya ciki har da Sin da Turai, wanda mataki ne da bangare daya ya dauka, da ba da kariya ga cinikayya, da cin zarafin tattalin arziki. Ya ce, kasar Sin ta dauki matakai don tabbatar da ikon mulkinta da moriyar samun ci gaba cikin aminci, kana da tabbatar da ka’idojin cinikayya da adalci a duniya. Ya kara da cewa, ya kamata Sin da Turai su kara mu’amala da juna, da bude kofa ga juna don tabbatar da yin ciniki da zuba jari cikin ‘yanci, da kiyaye tsarin samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata, ta...
    Gwamnan Borno, Babagana Umara Zulum, ya bayyana damuwa kan hare-haren da kungiyar ‘yan ta’addan Boko Haram suke kai wa manyan sojoji a baya-bayan nan. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da yake jagorantar taron kwamitin tsaro da aka gudanar a zauren majalisar, gidan gwamnati, Maiduguri, yana mai cewa jihar na fuskantar barazanar komawa cikin tashin hankali. Ma’aikatar Jin-ƙai ce kan gaba wajen wawure kuɗin gwamnati — Tsohon Minista Kisan Isuhu Yellow: ’Yan bindiga sun kai harin ɗaukar fansa “An gurgunta matsugunan soji da dama musamman a garuruwan Wulgo, Sabongari, Wajirko da sauransu. Alamu na nuna ‘yan ta’adda sun fara nasara akanmu. Don haka wannan abu ne mai matuƙar muhimmanci da muke buƙatar tattaunawa. “Daga shekaru uku baya...
    Duk da wannan zullumi da ake ciki, a kwanakin baya, kasar Sin ta tattauna da wasu kamfanonin Amurka sama da 20 cikinsu har da Tesla, inda ta kara ba su tabbacin cewa, za ta ci gaba da bude kofarta ga kamfanonin kasashen waje da aiwatar da gyare-gyare a gida. Wannan shi ake nufi da babbar kasa mai sanin ya kamata, mai kuma la’akari da moriyar sauran kasashe maimakon moriyarta ita kadai.   Idan Amurka na ganin matakanta za su danne ci gaban wasu kasashe, su kuma bata fifiko a duniya, to ta yi kuskure, domin yanzu ta budewa duniya ido, kuma kasashe da ma kamfanoninsu, za su koma ne ga inda suka tabbatar da cewa za su samu moriya, kuma...
    Gwamnatin kasar Aljeriya ta dakatar da duk zirga-zirgin jiragen sama daga kasar Mali da kuma zuwa kasar saboda abinda ta kira keta hurumin sararin samaniyar kasar. Shafin yanar giza na watsa labarai “Africa News” ya nakalto tashar talabijin ta kasar Aljeriya na fadar haka a daren Lahadi. Kafin haka dai matsalolin sun tashi tsakanin kasashe yanken Sahel 3 Niger,  Mali da Burkiya faso kan kakkabo jirgin saman yaki wanda bai da matuki wanda ya keta sararin samar kasar ta Aljeriya a makon da ya gabata, wanda ya sa kasashen uku suka janye jakadunsu daga kasar. Gwamnatin kasar Mali dai bata yi magana a kan wannan matakin da gwamnatin kasar ta Aljeriya ta dauka ba. Sai dai dakatar da zirga-zirgan jiragen...
    Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ta yanke wa wani shahararren mai sana’ar gyaran fuska, Abdullahi Musa Huseini, wanda aka fi sani da Amuscap, hukuncin daurin watanni shida a gidan yari saboda yin likin da takardun Naira a lokacin bikin aurensa. Mai Shari’a S.M. Shu’aibu ya yanke wa Huseini Amuscap hukuncin ne bayan ya amsa laifinsa da ake tuhumar sa, wanda ya saba wa sashe na 21(1) na Dokar Babban Bankin Najeriya (CBN) ta shekarar 2007. Takardar tuhumar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 6 ga Disamba, 2024, a Cibiyar Bikin Ali Jita da ke Kano, inda aka ga angon a wani bidiyo yana yin kari da Naira dubu dari a takardun Naira dubu daya-daya...
    Wani magidanci ya shiga hannun hukuma bayan da ya lakada wa ’yarsa mai shekaru 27 duka har lahira a yankin Ojo da ke Jihar Legas. Kakakin ’yan sandan jihar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa rundunar ta cika hannu da magidncin ne bayan ya yi aika-aikan a ranar 3 ga watan nan na Afrilu. Hundeyin ya ce makwabta ne suka kwarmata wa Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke yankin Okokomaiki, bayan mutumin ya kashe ’yar tasa ya kuma binne ta a cikin harabar gidansu. Jami’in ya ce ““Bayan samun rahoto jami’anmu suka ce suka gano kabarin, suka tono gawar aka gudanar da bincike,” shi kuma yana hannun hukuma yana amsa tambayoyi. Mali, Nijar, da Burkina Faso sun janye jakadunsu daga Algeria...
    Shugaban Iran Masoud Pezeshkian ya ce kasarsa ta yi imani da tattaunawa, amma ba a karkashin wulakanci da kaskanci ba.” Ya jaddada cewa Iran ba ta neman yaki, ko tada zaune tsaye, ko kuma mallakar makamin nukiliya, yana mai kira ga kasashen duniya da su amince da hakan. Pezeshkian ya bayyana hakan ne a yammacin Lahadin da ta gabata, yayin wata ganawa da wakilan jam’iyyun siyasa da manyan kungiyoyi a kasar, inda ya tattauna batutuwan da suka shafi sauye-sauyen harkokin mulki, da manufofin harkokin waje, da kalubalen tattalin arziki da zamantakewar kasar. Da yake magana game da kalubalen gudanar da harkokin mulki, shugaban na Iran ya bayyana cewa, ba za a iya cimma gyara halayen kungiyoyi da bangarorin gwamnati ta...
    A safiyar jiya litinin an kashe wani dan jarida Bafalasdine da wani matashi tare da raunata wasu da dama a lokacin da jirgin Isra’ila ya kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida a kusa da rukunin likitocin Nasser da ke Khan Younis a kudancin Gaza. Wakilin Al Mayadeen ya ruwaito cewa dan jarida Hilmi al-Faqawi da wani matashi mai suna Yousef al-Khazindar sun yi shahada, yayin da wasu ‘yan jarida da suka hada da Ahmed Mansour, Hassan Islayh, Ahmed al-Agha, Mohammed Fayek, Abdullah al-Attar, Ihab al-Bardini, Mahmoud Awad, da Majed Qudaih, suka samu raunuka a tashin bam din. Kungiyar Kafafen Yada Labarai ta Falasdinu ta yi Allah wadai da wannan harin da Isra’ila ta kai a kan tantin ‘yan...
    A wani mataki na mayar da martani da nuna fishi, kasar Aljeriya ta yi wa jakadunta a kasashen Mali, da Nijar kiranye, tare da jinkirta aikewa da jakadanta a Burkina faso, bayan da kasashen guda uku na kawacen sahel suka dau irin wannan matakin domin goyan bayan Mali, bisa takadamar dake tsakaninta da Aljeriya biyo bayan kakkabo jirginta marar matuki. Haka zalika ma’aikatar tsaron kasar Aljeriya ta sanar da rufe sararin samaniyarta ga dukkan jiragen da ke zuwa kasar Mali”, ba tare da bayar da wani karin bayani ba, wanda ke nuni da cewa jiragen farar hula na kasuwanci da kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa su ma abin ya shafe su. Takaddama dai ta yi zafi tsakanin Aljeriya...
    A Isra’ila dubban masu zanga-zanga ne suka fito kan titunan birnin Tel Aviv a wata sabuwar zanga-zangar kin jinin gwamnati a daidai lokacin da firaminista Benjamin Netanyahu ya gana da shugaban Amurka Donald Trump a birnin Washington. Masu zanga-zangar a ranar Litinin sun yi Allah wadai da manufofin Netanyahu, ciki har da yunkurinsa na korar manyan jami’an tsaro da na shari’a na gwamnatin. Sun kuma yi Allah wadai da sake dawo da yakin kisan kare dangi da ake yi wa al’ummar Gaza. Iyalan ‘yan Isra’ilar da aka yi garkuwa da su a Gaza su ma sun shiga zanga-zangar, inda suka bukaci a kawo karshen yakin da kuma kulla yarjejeniyar tabbatar da sakin mutanen da aka kama. Kungiyar dai ta ce...
    Aƙalla mutane biya ne suka mutu, 19 suka yi munanan raunuka a dalilin hatsarin mota da ya rutsa da su a Kasuwar Damagum da ke kan babbar hanyar Kano-Maidugri a Jihar Yobe. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi. Saudiyya ta sanya wa masu Umarah wa’adin ficewa daga ƙasar Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Wani da lamarin ya faru a idonsa, ya shaida wa Aminiya cewa, gudun wuce sa’a da wani direban bas ke yi ne ya janyo hatsarin, inda ya afka wa mutanen da ke tsaye a bakin titi ana tsaka da cin kasuwar. “Direban ya ɗauko fasinjoji ne zuwa Damaturu, kuma da alamu Potiskum ya  nufa,” in ji shi. Kwamandan hukumar kiyaye haɗura...
    Gwamnatin Saudiyya ta ayyana 1 ga watan Dhul Qada, wadda za ta yi daidai da 29 ga watan Afrilu, a matsayin ranar ƙarshe da duk wani baƙo da ke ƙasar da zummar aikin Umarah da ya fice daga ƙasar. Sanarwar da ma’aikatar aikin Hajji da Umarah ta Saudiyya ta fitar ta ce ta ɗauki matakin ne domin fara gudanar da shirye-shiryen aikin Hajji mai zuwa. Gobara ta laƙume ƙauyuka a Borno Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 30 a Kongo Cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce ranar 15 ga watan Shawwal, da ya yi daidai da 13 ga watan Afrilu, ita ce ranar karshe da masu shiga ƙasar domin aikin Umrah za su daina shiga, sai dai a fita. Ma’aikatar ta...
    A wannan Litinin ɗin ce anga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi na neman a jingine ta. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da...
    Ministan harkokin wajen Iran Sayyid Abbas Arakci ya bayyana cewa, Iran ba ta kin zama teburin tattaunawa, amma ba za ta zauna gaba da gaba da Amurka ba, yana mai kara da cewa; Har ya zuwa yanzu ba a yi wata tattaunawa gaba da gaba a tsakanin Iran da Amurka ba. Ministan harkokin wajen na Iran wanda ya gabatar da jawabi a gaban  kwamitin siyasar waje na majalsar shawarar musulunci ta Iran ya gabatar da rahoto akan hali na karshe da ake ciki dangane da batun tattaunawa da Amurka. Arakci ya kuma fadawa kwamitin cewa; Mu ma’abota diflomasiyya da tattaunawa ne, amma za mu tattauna da Amurka ne ba kai tsaye ba,kuma duk da hakan ma har yanzu ba mu...
    Ƙasar Saudiyya ta musanta batun da ake yaɗawa cewa  ta sanya Najeriya a jerin ƙasashen da ta hana biza. Sanarwar da aka yaɗa a kafofin sadarwa ta bayyana cewa daga ranar 13 ga Afrilu, Saudiyan za ta daina bai wa ƙasashen Masar, India, Pakistan, Morocco, Tunisa, Yemen da Aljeria bizar aiki, ta ziyara, da ta yawon buɗe idanu. Lakurawa sun kashe ’yan sa-kai 13 a Kebbi HOTUNA: Zanga-zangar adawa da gwamnatin Tinubu ta ɓarke a Abuja da Legas “Rashin yin biyayya ga wannan tsarin ka iya jawo haramta shiga kasar sawon shekaru biyar” a cewar sanarwar. Sai dai Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta bayyana wa manema labarai cewa waɗannan sabbin dokokin sun takaita ne ga lokacin aikin hajji....
    Jami’an ‘yansanda a gundumar Maitama da ke Abuja sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka yi kira ga gwamnatin da ta dauki matakan gaggawa kan tabarbarewar tattalin arziki da kuma zargin ‘yansanda na cin zarafin al’umma a kan ikirarin dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo. Zanga-zangar da kungiyar ‘Take-it- Back Movement’ da kungiyoyin fararen hula suka shirya a fadin kasar ya zo daidai da ranar bikin ranar ‘yansanda ta kasa a dandalin Eagle Square da ke Abuja. Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas Ya Kamata A Yi Adawa Da Kama Karya A Tabbatar Da Adalci LEADERSHIP ta tuna cewa, hukumomin ‘yansanda sun yi gargadi...
    Ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaraɗiyyar Congo ya kashe aƙalla mutane 30 tare da haddasa ɓarna mai tarin yawa. Ruwan saman ya janyo tsaiko wajen gudanar da al’amura a babban birnin tare da katse zirga-zirgan ababen hawa a kan titin Kinshasa, wanda ya taso daga tsakiyar birnin zuwa filin jirgin sama. A gundumar Debonhomme da ke gabashin ƙasar, ruwan ya laƙume motoci da dama, lamarin da ya tilastawa wasu mazauna ƙasar yin  hijira a yayin da wasu suka yi amfani da kwale-kwale kamar yadda jam’in kamfanin dillancin labaran AFP ya shaida. Wasu daga cikin waɗanda abun ya shafa, sun maƙale a saman gidajensu bayan da ruwan ya mamaye matakalar shiga gidanjensu. Bugu da...
    Kasashen Mali, Nijar da kuma Burkina faso dake hade a kawancen Sahel na AES, sun sanar da kiran jakadunsu a Aljeriya domin tuntuba. A wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar Mali a yammacin jiya Lahadi, kasashen uku sun sanar da kirawo jakadunsu domin tuntuba bayan da Aljeriya ta kakkabo wani jirgi marar matuki na kasar Mali a farkon wannan wata. Aljeriya dai ta kakkabo jirgin sojojin na Mali marar matuki a cikin daren ranar 31 ga Maris zuwa 1 ga Afrilu, matakin da kasashen uku sukayi tir da shi. A cewar gwamnatin Algiers, jirgin mara matuki da ake magana a kai ya shiga cikin kasar ne, saidai sojojin Mali sun tabbatar da cewa jirgin bai shiga...
    Iran ta bakin kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar, Esmail Baghai, ta ce nahiyar turai sun tafka kure na tarihi, ta hanyar goyon bayan Isra’ila ta hanyar yin watsi da sammacin kama Benjamin Netanyahu. Esmail Baghai ya bayyana haka ne a cikin wani sako a asusunsa na X, bayan ziyarar aiki da Netanyahu ya kai kasar Hungary duk da sammacin kame shi da kotun ICC ta bayar kan laifukan yaki da cin zarafin bil adama da gwamnatinsa ta yi a zirin Gaza. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya ce : Sammacin kame jami’an gwamnatin Isra’ila da kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ta yi na nuni da yadda duniya ke nuna bacin rai kan kisan kiyashi, laifukan yaki, da...
    Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya bayyana cewa adadin ma’aikatan yada labarai da aka kashe a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Zirin tun daga watan Oktoban 2023 ya kai 210 bayan kashe dan jarida Helmi al-Faqawi. Al-Faqawi na cikin akalla mutane biyu da suka mutu a lokacin da jiragen yakin Isra’ila suka kai hari kan wani tanti na ‘yan jarida kusa da wani asibiti a Khan Younis da sanyin safiyar ranar Litinin din nan. Akalla mutane bakwai ne kuma suka jikkata a harin. A cikin wani rahoto da aka buga a ranar 1 ga Afrilu, Cibiyar Watson ta ce yakin da Isra’ila ta yi a Gaza ya kasance mafi muni ga ma’aikatan yada labarai da aka yi rikodin kuma...
    Zanga-zangar adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ɓarke a wasu manyan biranen Nijeriya da suka haɗa da Abuja da Legas da kuma Fatakwal. Zanga-zangar wadda wata ƙungiyar gwagwarmaya ta Take It Back ta shirya na gudana ne duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi. Mutanen da Sanƙarau ta kashe sun kai 151 — NCDC Sojoji biyu da gomman ’yan ta’adda sun rasu a artabu a Borno A Abuja, babban birnin Nijeriya, fitaccen ɗan gwagwarmaya, Omoyele Sowore da lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Deji Adeyanju ne ke jagorantar zanga-zangar duk da yunƙurin ’yan sanda na hana su rawar gaban hantsi An kuma hangi masu zanga-zangar ɗauke da alluna da kwalaye masu ɗauke da rubutun bayyana buƙatunsu a...
    Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari kauyen Izge da ke Ƙaramar Hukumar Gwoza a Jihar Borno, inda suka kashe sojoji tare da rasa mayaƙansu da dama. Rahotanni na cewa harin ya auke ne da misalin karfe 1:00 na ranar Lahadi a lokacin da ’yan ta’addan suka mamaye sansanin sojin Nijeriya da ke garin Izge. Zanga-zangar da za mu yi babu gudu babu ja da baya — Take It Back An sayar da kare mafi tsada a duniya Wata majiyar tsaro ta tabbatar wa Aminiya cewar wani soji mai muƙamin Kyaftin da kuma Kofur na daga cikin waɗanda suka kwanta dama, yayin da sojoji suka yi nasarar hallaka mahara da dama a yayin arangamar. Shugaban ƙaramar...
    Ƙungiyar Take It Back ta ce zanga-zangar da za gudanar a yau babu gudu babu ja da baya domin nuna adawa da dokar ta-baci da aka sanya a Jihar Ribas da kuma abin da ta kira cin zarafin bil’adama da kuma amfani da dokar ta’addancin yanar gizo ba bisa ka’ida ba. Wannan dai na zuwa ne a yayin da rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya. Rundunar ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai...
    Rafael Grossi shugaban hukumar makamashin nukliya ta duniya (IAEA) ya bayyana cewa JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana dukkan kayan aikin da ake bukata,  da kuma fasahar kera makamin idan tana bukatar yin hakan.   Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Grossi yana fadar haka a wata hira da yayi da tashar talabijin ta Agentina a yan kwanakin da suka gabata. Ya kuma kara jaddada cewa a halin yanzu JMI bata da makamin Nukliya, sai dai tana da abinda ake kira “sinadarin Uranium da ta gasa, wanda yawansa zai iya samar da makaman nukliya har zuwa 6-ko 7, amma dai bata kera makamin ba. Abinda tambaya a nan itace tunda hukumar ta tabbatar da cewa...
    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Southampton ba za ta buga gasar Firimiya Lig na badi ba, bayan da su ka koma gasar yan dagaji ta kasar Ingila, Southampton ta yi rashin nasara a hannun Tottenham Hotspur wanda kuma shi ne ya yi sanadiyar da Southampton ta koma gasar Championship ta kasar Ingila. Hakan ya sa ta kasance kungiya ta farko a tarihin gasar da ta koma baya (relegation) bayan buga wasanni 31 kacal, Southampton ta samu maki 10 a wasanni 31 an zura mata kwallaye 74 a raga sannan kuma ta zura kwallaye 23 kacal a bana. Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya Manchester United Na Son Lashe Firimiya A Shekarar 2028 Ramsdale tsohon mai tsaron ragar...
    Babban bankin kasar ya lura da cewa wannan raguwar ya samo asali ne sakamakon faduwar farashin danyen mai na Bonny Light na Nijeriya, wanda ya fadi zuwa dala 75.66 kan kowacce ganga daga dala 82.23 a zango na uku na shekarar 2024. Bugu da kari, karin fitar da danyen mai daga ganga 1.33 kowace rana zuwa 1.43 ya taimaka wajen sanya sashin mai a matakin ci gaba na dan kadan a maimakon yin kasa sosai. A gabaki-daya, sashin mai ya taimaka da kaso 00.7 cikin 100 na ci gaban tattalin arziki cikin gida (GDP) a tsawon wannan lokacin. “Vangaren da ba na mai ba wanda ya samu tagomashi, ya samu saurin havaka da kaso 3.69 idan aka kwatanta da na...
    Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance. An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dala Amurka 769,000 kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 177 dubu dari 615 da 840 daga wani babban kantin da ke Millenia a birnin Orlando da ke Jihar Florida a Amurka a ranar 26 ga Fabrairu. A cewar sashen ’yan sanda na Orlando, Glider ya dauki matakin da ba a saba gani ba na haɗiye ’yan kunnayen da ya sace. A cewar rahoton ’yan sanda da kafar yada labarai ta...
    Hotunan faifan bidiyo da ke fallasa kisan da sojojin mamaya na Isra’ila suka yi wa likitoci 15 a Rafah, ya tilastawa “Isra’ila” ja da baya kan labarin da ta kirkiro, tana mai cewa karyar da ta yi “ba da gangan ba ce”. An kara da’awar kuma daga baya an karyata ta ta hanyar shaidun bidiyo, gami da cewa motocin daukar marasa lafiya ba su da haskensu na gaggawa, kuma sojojin Isra’ila sun shiga wuta. Rahoton sojojin Isra’ila daga baya ya yi ikirarin cewa sojojin na Isra’ila sun boye gawarwakin da motocin daukar marasa lafiya a karkashin yashi “don hana namun daji cinye su.” Wannan tsari dai ba a saba gani ba ne ga dakarunsu na aikata kisan kiyashi tare da...
    Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya, David Lammy, ya soki matakin Isra’ila na hana wasu ‘yan majalisar dokokin Birtaniya biyu shiga ƙasar, yana mai cewa matakin bai dace ba kuma abin damuwa ne. Tsarewa da hana ‘yan Majalisar Wakilan Birtaniya biyu da ke cikin tawagar ‘yan majalisa zuwa Isr’aila shiga cikin ƙasar, abin da ba za a amince da shi ba ne, bai dace ba, kuma babban abin damuwa ne,’ in ji Sakataren Harkokin Waje David Lammy, a cikin wata sanarwa a ranar Asabar.” Lammy wanda ya bayyana cewa Birtaniya tana tuntuɓar ‘yan majalisar domin ba su goyon baya, kuma ya bayyana wa hukumomin Isra’ila ƙarara cewa “ba haka ake yi wa ‘yan Majalisar Dokokin Birtaniya mu’amala ba.” “Abin da gwamnatin Birtaniya...