2025-04-16@04:42:27 GMT
إجمالي نتائج البحث: 815
«Jagoran juyin juya halin Musulunci»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, ya ce ya bayar da hayar ɗaya daga cikin gidaje uku kacal da ya mallaka domin sayen abinci. Buhari ya faɗi hakan a yayin wani taro na jam’iyyar APC da aka gudanar ranar Litinin a Fadar Gwamnatin Katsina. Tsohon Shugaban Ƙasar ya ce duk da ya shafe shekaru takwas a kan madafan iko, bai yi amfani da kujerar mulki wajen azurta kansa ba. “Nijeriya ƙasa ce mai wuyar sha’ani ta fuskar jagoranci amma galibin ’yan ƙasar ba su fahimci hakan ba. “Ba za a taɓa fahimtar irin sarƙaƙiyar da ke cikin riƙo da akalar jagoranci ba da ma ita kanta Ƙasa Nijeriya sai mutum ya tsinci kansa a kan madafan iko. “A yanzu na ƙara...
A yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar ta samu ci gaba mai inganci wajen zurfafa raya zamanantarwarta a cikin “yanayoyi masu sarkakiya da kalubale” a tsakanin watanni 12 da suka gabata. Ya furta hakan ne yayin gudanar da wata kasaitacciyar liyafar maraba da sabuwar shekara ta kasar Sin. Ana Shirin Kiranye Ga Ɗan Majalisar Da Ya Bar Kwankwasiyya Hisbah Ta Ceto Ƴanmata 16 Daga Hannun Masu Safarar Mutane A Kano Shugaba Xi wanda har ila yau shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC) kuma shugaban kwamitin tsakiya na sojojin kasar ya kara da cewa, “a cikin shekarar dabbar Dragon, mun nuna kuzari da ruhi mai karfi na iya aiwatarwa. Mun...
Jagoran juyin juya halin Musulunci: An murkushe dukkanin daidaito a gaban mutanen kudancin Lebanon Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana abin da ya faru a kudancin kasar Lebanon a matsayin murkushe dukkanin daidaito na siyasa da lissafin abin duniya. A cikin wani rubutu a dandalin “X”, Ayatullahi Sayyid Khamenei ya nuna cewa an murkushe wadannan daidaito a gaban mutane masu aminci da aminci a kudancin Lebanon. Jagoran juyin juya halin Musulunci ya yi la’akari da cewa: Al’ummar kudancin kasar Labanon ba su damu da sojojin yahudawan sahayoniyya da suka yi kaca-kaca da su ba, suna kuma kai rayukansu zuwa fagen fama da rashin son kai da kuma dogaro da alkawarin Ubangiji.
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun kera wani jirgi maras matuki ciki mafi girman da suka Sanya masa suna “Gaza” A jiya Lahadi, a gefen atisayen soji mai taken “Manzon Allah Mai Girma na 19” da aka gudanar da gwajin makamansu, sun samu nasarar gwajin sabon jirgin sama maras matuki ciki mai suna “Gaza” wanda ake daukansa a matsayi mafi girman jirgin saman maras matuki ciki da zai iya yin luguden wuta mafi girma da tsanani, jirgin yana cin dogon zango kuma shi ne mafi girma da Iran ta kera wajen kai farmakin da zai jefa bama-bamai 8 akan wurare 8 a kasa. Jirgin Gaza maras matuki (wanda ake kira Shahed 149) shi ne jirgi mara matuki...
Kwamandan runduna ta 1 ta sojojin Najeriya Gusau, Birgediya Janar Opurum Timothy, ya baiwa al’ummar jihar Zamfara aniyar rundunar sojojin Najeriya wajen ci gaba da aiki tukuru domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a karshen taron rundunar sojojin Najeriya ta yammacin Afirka WASA 2024 da aka gudanar a Gusau. Kungiyar WASA wani taron ne na shekara-shekara da rundunar sojojin Najeriya ke shiryawa domin murnar dimbin al’adun gargajiya na wannan kasa mai girma. Taron na shekara-shekara yana tattaro Jami’ai, Sojoji, da iyalansu a cikin annashuwa don bikin da kuma nuna ƙarshen ayyukan shekara. Janar Opurum wanda ya jaddada kudirin rundunar na kawar da...
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta bayyana cewa: Tun a shekara ta 2000 al’ummar Lebanon suka tabbatar da cewa su ne jagororin gaskiya a kan tafarkin nasara Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta fitar da wata sanarwa a jiya Lahadi, inda ta jaddada cewa: Daidaiton sojoji da al’umma da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke kare kasar Lebanon daga ha’incin makiya ba wai kawai tawada ne a takarda ba, don haka sun daurawa kasashen duniya karkashin jagorancin kasashen da suke daukar nauyin yarjejeniyar da aka cimma alhakin take hakki da laifuffukan makiya yahudawan sahayoniyya tare da tilasta mata ficewa gaba daya daga yankin Lebanon. Tun daga shekara ta 2000 har zuwa yau, lamarin ya ci gaba da maimaita kansa, domin al’ummar...
Wata nakiya ta fashe a Sabon-Pegi da ke Ƙaramar Hukumar Mashegu a Jihar Neja, lamarin ya yi sanadiyyar mutuwar wata mata da kuma jikkata wasu mutum shida. Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi, 26 ga watan Janairu, 2025, da misalin ƙarfe 7:30 na safe. An gurfanar da masoyan da suka kai wa malami hari a Kano Kotu ta ɗaure matashi shekara 2 kan satar wayoyi a Kano Ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wasu nakiyoyi da wani mutum ya ɓoye a wajen domin aikin haƙar ma’adinai. Lamarin ya yi sanadin lalacewar gidaje kusan 12 a yankin, inda ya jefa al’umma cikin tashin hankali. Fatima Sadauki ta rasa ranta...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi wanda ya jagoranci tawagar yan siyasa da kuma tattalin arzikin kasarsa zuwa birnin Kabul babban birnin kasar Afganistan, a yau Lahadi sun tattauna al-amura masu muhimmanci tsakaninsu da kuma yanking aba daya. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa ministan ta hadu da tokwaransa na rikon kwarya Amir Khan Muttaki a birnin Kabul inda suka tattauna al-amura da suka shafi kasashen biyu. Wadanda suka hada da al-amuran kan iyakokin kasashen biyu, tsaro, ruwa da hakkin ko wace kasa kan ruwan da ke kwarara daga kasar Afganistan zuwa kasar Iran. Da batun miliyoyin yan kasar Afgansitan wadanda suke rayuwa a kasar Iran na shekaru kimani 50. Ministocin biyu sun tattauna al-amura...
Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Gaskiya a Harkokin Jama’a (SERAP), ta maka Shugaba Bola Tinubu da Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), a kotu kan karan kudin kiran waya da data zuwa kashi 50. NCC ta amince da karin, wanda ya sa kudin kiran waya ya tashi daga Naira takwas zuwa 16.5 a minti daya, yayin da kudin sayen data 1G ya tashi daga Naira 287.8 zuwa Naira 431.25. Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Ƙungiyoyin da za su fafata da juna a Copa del Rey Shi kuwa kudin aika sakon kar ta kwana ya tashi zuwa Naira shida daga na hudu da ake biya a baya. SERAP, ta ce wannan karin an yi sa...
Isra’ila ta sako Falasɗinawa 200 daga cikin waɗanda take riƙe da su a kurkuku kamar yadda yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da ƙungiyar Hamas ta tanada. Wannan dai na zuwa ne bayan da Hamas ta saki rukuni na biyu na ’yan Isra’ilar da ta yi garkuwa da su — wasu sojojin Isra’ila mata da Hamas take riƙe da su tsawon watanni. Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda A wata sanarwa da hukumomin gidan yari na Isra’ila suka fitar sun ce: “Bayan kammala dukkanin abubuwan da suka wajaba a gidajen yarin da kuma amincewar hukumomi an saki dukkanin ’yan ta’addan daga gidajen yari na Ofer da Ktziot,” kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na...

CMG Ya Gabatar Da Bidiyon Dandanon Shagalin Murnar Bikin Bazara Na Kasar Sin A Amurka Da Myanmar Da Indonesia Da Habasha Da Faransa Da Jamus Da Paraguay
Bugu da kari, a ran 25 ga watan kuma, CMG ya gabatar da wannan bidiyo a kasar Jamus, inda gidajen sinima na manyan biranen kasar ciki har da Berlin da Frankfurt, da Dresden da kuma Dortmund da sauransu, suka watsa wannan bidiyo. Kazalika, a ran 24 ga watan, a birnin Asuncion, hedkwatar kasar Paraguay, an fara watsa wannan bidiyo a manyan allunan dake titunansa har tsawon kwanaki 7 masu zuwa a jere. Wannan shi ne karon farko da aka watsa irin wannan bidiyo a wannan kasa dake kudancin nahiyar Amurka. An ba da labari cewa, UNESCO ta shigo da bikin bazara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato Bikin Bazara cikin jeren sunayen dake wakiltar kayayyakin al’adun gargajiya na tarihi...
Wakilin babban rukunin gidajen rediyo da talibijin na kasar Sin (CMG) kwanan nan ya tattauna tare da shugaban kasar Sri Lanka Anura Kumara Dissanayake, wanda ya kawo ziyara kasar Sin a karon farko tun bayan hawansa mulki. Da yake magana game da nasarar da kasar Sin ta samu na zamanantar da kanta, Dissanayake ya bayyana cewa, yawan al’ummar kasar Sin ya kai kusan kashi daya bisa biyar na al’ummar duniya, amma kasar Sin ba ta da kashi daya bisa biyar na albarkatun duniya. Ya ce Kasar Sin ta dage kan bin hanyar ci gaba da ta dace da ita, kuma kasar ta samu ci gaba, jama’arta kuma suna rayuwa da aiki cikin kwanciyar hankali. Ya ce, ina ganin yin nazari...
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya bukaci masu tsara manufofi a fannin ilimi a Najeriya da su dauki kwararan matakai don magance gibin da ke tattare da zamantakewa da al’adu da ababen more rayuwa da manufofin da ke haifar da yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a kasar. Shugabar ofishin UNICEF na Kano, Rahama Rihood Farah, ne ya yi wannan kiran a wani taron manema labarai na bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025. Ya yi nuni da cewa, Jihohin Kano, da Jigawa da Katsina suna da adadin yara miliyandaya da dubu dari takwas da sittin da uku, da dari biyu da bakwai (1,863,207) da ba sa zuwa makaranta a matakin firamare, da...
Dan takarar zaben maye gurbin Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar Mazabar Chikum da Kajuru a jam’iyar APC Arc Sani A Abbas Sardaunan Chikum ya nada kwamitin mutane 7 domin raba tallafin karatu ga daliban yankin sa su 100 da suke karatun kimiyya da fasaha a manyan marantun Gwamnati. Wannan wata manuniya ce game da kudurin Arc Sani Abbas na karfafa matasa ta bangaren ilimin don gobe su tayi kyau. Babban aikin wannan kwamitin shi ne tantance daliban da suka cancanci amfana da wannan tallafin musamman wadanda babu ke barazanar hana su karatu. Wanda yin haka zai taimaka wajen tallafa musu su nemi ilimi don cike gibin da ake samu ta wannan bangaren. Wannan tallafin kadan ne daga cikin irin...
Shugaban Amurka Donald Trump ya zayyana wani ra’ayi mai manufar tsarkake zirin Gaza. Trump na mai cewa yana son aikewa da Falasdinawa daga yankin zuwa kasashen Masar da Jordan “na dan lokaci” ko kuma “a cikin dogon lokaci”. don samun zaman lafiya. Ana dai ganin tamakar Trump na kwatanta yankin Falasdinu da “wurin rushewa nan gaba” bayan watanni 15 na yakin da Isra’ila ta kadamar kan Gaza.