2025-04-25@13:32:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3133

«wannan Shirin»:

    “Saboda ragin farashin litar man fetur da Dangote ya yi ne. Gidan man yana da tsohon mai da ya saya a farashin da ya fi wannan, kuma ba zai sayar da shi a asara ba.   “Wannan dalilin ne ya sanya muka rufe gidajen man tun ranar Talata. Da yiwuwar mu bude nan gaba.”   Kazalika, wani ma’aikacin gidan man, ya tabbatar da cewa suna ‘yan wasu gyare-gyare ne amma za su sake budewa. Ya kuma ce, gidan man zai fara sayar da man fetur ga jama’a a ranar Talata kan kudi naira 910 a kowace lita.   Rahotonni sun tabbatar da cewa sauran abokan huldar matatar man Dangote, kamar su AP, Ardoba, da Optima, sun yi ta sayar wa...
    Kungiyar Shugabannin Arewa (NEF) ta zargi Shugaba Bola Tinubu da nadin mukaman gwamnati ba tare da daidaito tsakanin yankunan Nijeriya ba, wanda ta ce yana fifita yankin Kudu maso Yamma a kan sauran yankuna shida na kasar. Mai magana da yawun kungiyar, Farfesa Abubakar Jiddere, a cikin wata sanarwa a yau Juma’a a Abuja, ya bayyana cewa nadin da aka yi sun karkata ne wajen goyon bayan Kudu maso Yamma, yayin da sauran yankunan suka samu kadan ko kuma aka danne su. Gazawar Gwamnatin Tinubu Ce Ke Haddasa Zubar Da Jini A Filato – Ƙungiyar Dattawan Arewa Rurum Ya Shawarci Mafarautan Arewa Da Su Daina Zuwa Kudu Farauta  NEF ta bayyana cewa wannan lamari ya sabawa tsarin hadin kan kasa,...
    Farfesa Ibrahim Amos, wani Malamin cocin Katolika, ya samu ‘yanci daga hannun masu garkuwa da mutane a Jihar Kaduna, bayan an sace shi a ranar Alhamis, 24 ga Afrilu, 2025, daga gidansa a St. Gerald Quasi Parish, Kurmin Risga, ƙaramar hukumar Kauru. Wani shugaba a ɗariƙar dake Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya tabbatar da sakin farfesan a cikin wata sanarwa da aka mikawa manema labarai. Ya bayyana cewa Farfesa Amos ya dawo lafiya jiya Alhamis ɗin da aka sace shi, amma bai bayyana yadda aka sake shi ba ko sun biya kuɗin fansa ba. Tinubu Ya Kaddamar Da Ci Gaba Da Aikin Titin Abuja Zuwa Kaduna  2027: Dalilan Da Suka Sa ‘Yan Siyasa Ke Tururuwar Zuwa Gidan Buhari A Kaduna...
    Ofishin jakadancin kasar Iran a kasar Netherlands ta yi watsi da zargin da gwamnatin kasar takewa JMI na kokarin aiwatar da kashe-kashe har guda biyu a shekarar da ta gabata. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran tace Ofishin jakadancin Iran da ke Netherlands  ta fidda wannan sanarwan ne a jiya Alhamis. Ta kuma kara da cewa, kasar Iran wacce ta fi ko wace kasa a duniya fama da yan ta’adda, ba za ta yi kokarin kasashe wani a wani wuri ba. Sanarwan ta bayyana cewa wannan al-amarin siyasace ta tsakanin jami’an siyasa na kasar ta Netherlands  don neman amincewar masu kuri’a. Kafin haka dai wata cibiyar ayyukan tsaro ta kasar Netherlands  mai suna AIVD ta bada rahotomta na shekara...
    Sojojin kasar ayemen sun kakkabo jiragen yaki na kasar Amurka wadanda ake sarrafashi daga nesa a kan kasar Yemen, da dama wadanda kimarsu ya kai dalar Amurka miliyon $200 a cikin makonni 6 kacal. Tashar talabijin ta Pressstv a nan Tehran ya bayyana cewa wadan nan jiragi suna aikin leken asiri ne a kan kasar ta Yemen, kuma duk da cewa suka tashi fiye da kafa 40,000 a sama, amma sojojin yemen suna iya kakkabosu. Wannan yana zuwa ne a dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donar Trump ya kara umurnin a kara yawan hare-haren da ake kaiwa kasar ta Yamen. Mafi yawan hare-haren da suke kaiwa yana kasa mata da yara da kumalalata kamfanoni da kuma cibiyoyin samar da ruwa...
    Irin wannan zanga-zangar, ta sha ban-ban, da irin wadda ake gudanawar a kasashen da suka ci gaba kuma suke gudanar da mulki, irin na Dimokiradiyya, kamar da kasar Amurka, Birtaniya, Isara’ila da sauransu.   Sashe na 40, na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 da aka sabunta, ya bai wa ‘yan kasar ikon haduwa a waje guda su kuma yi hudda da sauran jama’a.   Kazalika, sashe na 11 na yarjejeniyar nahiyar Afirka, da ke magana kan ‘yancin ‘bil’Adama, wanda ita kanta Nijeriya ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniyar na barin ‘yan kasar su gudanar da zanga a cikin lumana.   Amma sai dai, abin takaicin duk da ‘yancin na wannan sashen, mahukunta Nijeriya, suna yawan take wannan ‘yancin, kan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki guda huɗu da suka kafa muhimman hukumomi domin ƙarfafa tsarin gudanarwa na jihar da kuma haɓaka ci gaba mai ɗorewa. Waɗannan dokokin za su samar da Hukumar Kare Hakkokin Jama’a ta Jihar Kano (KASPA), Hukumar Kula da Tallace-tallace da Rubuce-rubuce ta Jihar Kano (KASIAA), Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa da Zamani ta Jihar Kano (KASITDA), da kuma Hukumar Bunƙasa Ƙananan Kasuwanci da Matsakaita ta Jihar Kano (KASMEDA). Gwamna Abba, ta bakin mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana muhimmancin waɗannan dokokin wajen ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, tallafa wa ƙananan kasuwanci, tsara tallace-tallace, da inganta kare hakkin jama’a da samar da ayyuka. Ya jaddada cewa waɗannan hukumomi za...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na duniyarmu a yau shiri wanda yake kawo maku labarai masu muhimmanci a makon da ya gbaata wadanda suka shafi siyasa, tsaro tattalin arziki zamantakewa da sauransu, inda muke masu Karin bayani sannan daga karshe mu ji ra’ayin masana dangane da su da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu. ///… Madalla, masu sauraro shirimmu nay au zai yi Magana dangane da Yakin da Amurka take yi a tekun maliya kan kasar Yemen da kuma yadda kasashen yamma suke son su fitar da kwararru daga cikin zirin gasa don amfani kansu sannan su ga kashe dukkan Falasdinawa da suke yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na...
    Raguwar kudin a hannun mutane na iya zama wani bangare na kokarin rage matsin lamba kan hauhawar farashin kayayyaki da samun daidaiton tattalin arziki.   Baya ga raguwar kudade a hannun mutane, ajiyar a bankin CBN ya karu zuwa naira biliyan 28.52 a watan Maris na 2025, daga naira biliyan 27.57 a watan Fabrairun 2025. A watan Janairun 2025, ajiyar ya kai naira biliyan 27.43.   A halin yanzu, ajiyar ko-ta kwana ba ta canza ba a naira miliyan 284.36 a cikin watanni uku.   Ajiyar banki yana nufin kudaden da Babban Bankin da bankunan kasuwanci ke rike da shi don tabbatar da hada-hadar kudade a cikin bangaren banki. Ci gaba da karuwar ajiyar bankuna wata alama ce ta kokarin...
    Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa zaɓen 2027 zai kasance ne kai tsaye tsakanin Shugaba Bola Tinubu da ’yan Najeriya da gwamnatinsa ta jefa su cikin mawuyacin yanayin rayuwa. Shugaban riƙo na PDP, Umar Damagum, ya jaddada cewa zaɓen “Tsakanin Jam’iyyar APC ne da ’yan Najeriya,” yana mai nuni da wahalar da talakawa ke fuskanta a ƙarƙashin mulkin APC. Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su haɗa kai don magance abin da ya kira “wahalar da aka kawo mana da gangan.” Damagum ya kuma yi tsokaci kan sauya sheƙar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da tsohon Gwamna, Ifeanyi Okowa, tare da mambobin majalisar zartarwarsu, zuwa jam’iyyar APC mai mulki. ’Yan bindiga sun kashe ango, sun sace amarya a Nasarawa NAJERIYA...
    A kokarinta na ganin an gudanar da jarrabawar hadin gwiwa ta hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB, gwamnatin jihar Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na watan Afrilun 2025.   An dauki wannan matakin ne bayan nazari da tuntubar masu ruwa da tsaki, a kokarin baiwa daliban jihar Kano damar rubuta jarabawarsu ba tare da wata matsala ba.   A wata sanarwa da Daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar muhalli da sauyin yanayi, Ismail Garba Gwammaja ya fitar, ya ruwaito kwamishinan yana cewa.   “Dakatar na da nufin hana duk wani cikas da zai iya kawo cikas ga aikin jarrabawar da kuma tabbatar da cewa ‘yan dalibai za su iya zana jarabawarsu ba tare da wani shamaki...
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa na shirin bayar da gudunmawar kashi 50 na shinkafar da Najeriya ke bukata nan da shekara ta 2030.   Ya bayyana haka ne a lokacin da yake karbar tawagar hukumar tattara kudaden shiga da kasafi (RMAFC) karkashin jagorancin shugaban kwamitin inganta kasafin kudi da kasafin kudi, Ambasada Desmond Akawor, yayin ziyarar ban girma da suka kai a gidan gwamnati dake Dutse.   Ya bayyana cewa, suna noman shinkafa sau biyu a shekara, inda ya nuna cewa, a shekarar 2024 kadai, sun noma sama da hekta 200,000 na shinkafa.   Ya yi nuni da cewa, a bana, suna son noma sama da hekta 250,000 wanda a shekarar 2030, burinsu ya kai kadada...
    Gwamna Dauda Lawal ya amince da nadin Amirul Hajj karkashin wani kwamiti don sa ido kan ayyukan Hukumar Alhazai ta Jiha a Saudiyya don tabbatar da bin ka’idojin gida da na Saudiyya gaba daya a duk lokacin gudanar da aikin Hajjin 2025.   Sakataren gwamnatin jihar, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai Sulaiman Ahmad Tudu ya raba wa manema labarai, ya ce kwamitin zai fara aiki cikin gaggawa.   A cewar sanarwar, mambobin kwamitin sune mai martaba Sarkin Maradun a matsayin shugaban tawagar yayin da Alhaji Habibu Balarabe aka nada a matsayin Sakatare.   Sauran wakilan sune Sulaiman Adamu Gummi, Bello Isah Almufty,...
    Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, ya bayyana cewa duk waɗanda ke son barin jam’iyyar PDP su tafi yanzu, domin a bai wa masu kishin jam’iyyar damar sake gina ta. Saraki ya fitar da wannan bayanin ne a martani ga yawan sauye-sauyen jam’iyya da ake yi a PDP, ciki har da ficewar Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya koma jam’iyyar APC. Saraki ya bayyana cewa ya samu kiran waya daga mambobin jam’iyyar da dama da kuma matasa masu goyon bayan dimokuraɗiyya, suna nuna damuwarsu game da barin jam’iyyar PDP, musamman ma a sashin jihar Delta. A cikin sanarwar, Saraki ya jaddada cewa yana da muhimmanci jam’iyyar ta kasance da mambobi masu cikakken kishin gaskiya fiye da yawan mambobin da...
    Assalamu alaikum masu sauraro sharhin bayan labarammu zai yi magana a kan ‘wani makircin da kasar faransa ta kullawa falasdinawa a gaza’ don su amfana da kwararrunsu’ wanda ni tahir amin zan karanta. ///… Shugaba kungiyar kare hakkin bil’adama masi suna [the Euro-Mediterranean Human Rights Monitor] ta fallasa wani shiri tsakanin gwamnatin kasar faransa da HKI na fitar da kwararru da kuma masana falasdinawa da suka rage a Gaza, zuwa wajen yankin, kafin HKI ta fa wani gagarumin kissan kiyashi a yankin kashe falasdinawa da suka rage a yankin. Kamfanin dillancin labaran Parstoday na kasar Iran ya nakalto Ramy Abdu shugaban kungiyar na fadar haka, ta kuma kara da cewa, offishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Qudus da aka...
    “Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    ”Wannan lokaci ne na bakin ciki, kuma a cikin irin wadannan lokutan ne kuka san wadanda ke kulawa da ku da gaske.”   Ribadu ya bayyana cewa Gwamnatin Bola Tinubu ta gaji tashin hankali da ke fama da shi a kasar nan, kuma tana aiki tukuru don gyara abubuwan da suka lalace.   Ya ce, “Na zo nan ne don in jajanta muku da sauran mutanen kirki na Benuwai kan asarar rayuka da aka yi da kuma tabbatar muku da cewa muna tare da ku.   “Benuwai jiha ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya. Ta kasance daya daga cikin jihar da ake samar da abinci a kasa, ita ce ta farko wurin samar da abinci, kuma muna alfahari da hakan....
    Bankin Duniya ya yi hasashen cewa talauci a Najeriya zai ƙaru da kashi 3.6 cikin ɗari a cikin shekaru biyar masu zuwa, ciki har da shekarar zaɓe ta 2027. Wannan hasashe yana ƙunshe ne a cikin rahoton Bankin wanda aka fitar a lokacin taron bazara na Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya (IMF) da ake yi a birnin Washington, D.C., a ƙasar Amurka. Rahoton ya jaddada cewa duk da wasu nasarorin da aka samu a harkokin tattalin arziki a kwanakin baya, musamman a ɓangaren da ba na man fetur ba a cikin rubu’i na ƙarshe na shekarar 2024, matsalolin da suka shafi dogaro da albarkatun ƙasa da kuma raunin ƙasa na iya kawo cikas ga ci gaba. A cewar...
    Kasar faransa ta jaddada anniyar na ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar iran. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Faransa ya bayyana a ranar Alhamis cewa, Faransa na ci gaba da jajircewa wajen ganin an warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye take ta ci gaba da tattaunawa da Tehran. A yayin taron manema labarai na mako-mako a birnin Paris, Christophe Lemoine ya jaddada cewa: “Muna ci gaba da jajircewa wajen warware matsalar nukiliyar Iran ta hanyar diflomasiyya, kuma a shirye muke mu ci gaba da tattaunawa da Tehran.” Wannan bayanin na zuwa ne bayan da ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araghchi ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na X cewa, Tehran a shirye ta ke...
    Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) ta yi watsi da bukatar Isra’ila na soke ko kuma ta dakatar da sammacin kama firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da tsohon ministan harkokin sojin kasar Yoav Gallant. A cikin wata sanarwa da ta fitar, kotun ta ICC ta ce ta amince da daukaka karar da Isra’ila ta shigar na sake duba hurumin kotun kan laifukan da aka aikata a yankunan Falasdinu. A watan Nuwamba 2024, kotun ICC ta bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministansa na harkokin soji, Yoav Gallant, bisa laifukan cin zarafin bil’adama da laifukan yaki da suka shafi kisan kare dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a zirin Gaza. Hukuncin ya tilastawa dukkan...
    ’Yan bindiga sun kashe wani sabon ango, sun kuma yi wani gaba da amaryasa bayan kwanaki 11 da ɗaura aurensu a wata unguwa a Jihar Nasarawa. Ganau sun shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun kai hari gidan sabbin ma’auratan ne da misalin ƙarfe karfe 11:00 na dare ranar Laraba, inda suka harbe angon har lahira, sannan suka tafi da matar zuwa wani wuri da ba a sani ba. Name(required) Email(required) Website Message Submit Lamarin ya faru ne a ƙauyen Akaleku, da ke Ƙaramar Hukumar Obi ta Jihar Nasarawa, a kan hanyar Lafia zuwa Makurɗi. Ma’auratan, Mista da Misisi Alu Anzaku, an ɗaura aurensu ne a ranar 12 ga Afrilu, 2025. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Aisha ba wai mawaƙiyar amshi ba ce kawai a wajen Rarara ba. Sun yi matuƙar shaƙuwa da juna, kuma mu da muka san su ba abin mamaki ba ne don an ce za a yi wannan aure,” in ji majiyar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya kara da cewa, “Za mu gwabza yaki, idan yakin ya zama dole, amma kofofinmu a bude suke idan Amurka tana son a tattauna,” kana ya ce, Sin na neman hawa teburin tattaunawa da yin shawarwari ne kawai bisa daidaito, da mutuntawa da kuma samun moriyar juna. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Najeriya ta amince kuma ta sanar cewa za a bai wa mahajjatan ƙasar kuɗin guzirinsu a hannu maimakon amfani da kati ko kuma asusun banki. Hakan ya biyo bayan tsoma bakin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya yi wanda ya roƙi shugaba Bola Tinubu a madadin maniyyatan ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON. Ficewar Kawu a jam’iyyarmu zai kawo zaman lafiya – Shugaban NNPP na Kano An kori lakcara kan neman lalata da ɗaliba matar aure Hukumar NAHCON a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Abdullahi Saleh, ta dage cewa ɓullo da hada-hadar kuɗi ta amfani da kati zai shafi shirin hukumar na gudanar da ayyukan hajjin 2025. Shugaban ya damu matuƙa da cewa amfani da katin banki na dole da...
    Sabbin ‘yan sama-jannatin da aka tura, za su gudanar da gwaje-gwaje da bincike game da yanayin rayuwa a sararin samaniya, da kimiyyar karamar fizgar kasa ko jazibiyya (micro-gravity physics) da sabbin fasahohin sararin samaniya.   Kazalika, za su kuma yi tafiye-tafiye mabambanta a sararin samaniya don kakkafa shingayen kariya daga baraguzai da tarkacen sararin samaniya, da kuma girkewa da dawo da na’urorin da aka makala a wajen tashar.   Ya zuwa yanzu dai, ‘yan sama jannatin kasar Sin 26 ne suka yi nasarar zuwa sararin samaniya. (Abdulrazaq Yahuza Jere). Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    Bugu da kari, masharhanta da dama na ganin karin harajin fito ba zai warware matsalar da Amurkan ke ciki ba. Ko shakka babu idan Amurka na son ta tunkari wannan kalubale bisa gaskiya, sai ta sauya tsarin ilimi, ta kuma bunkasa fannin kirkire-kirkirenta, da daga martabar masana’antu, da zuba jari na dogon lokaci a fannin, ba wai matakin jeka-na-yika na gajeren lokaci, irin wannan na baiwa kasuwa kariyar cinikayya ba.   A daya hannun kuma baya ga illar da wannan kare-karen haraji ya haifar, matakan kasashen da lamarin ya shafa na ramuwar gayya na iya haifar da hauhawar farashi na gaggawa, da jefa tattalin arzikin sassa daban daban cikin halin komada, a maimakon fatan da gwamnatin Amurkan ke yi na...
    Jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullah sayyid Ali Khamnei wanda ya gabatar da jawabi dangane da zagayowar ranar shahadar Imam Ja’afar Assadiq ( a.s) ya bayyana cewa: Tafarkin Imaman Ahlul-Bayti (a.s) ya kasance na gwgawarmaya da jajurcewa, kuma koyarwarsu ta ginu ne akan mandiki da kafa dalili. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya ce; rayuwar Imam Ja’afar Assadiq           (  A. S ) ta ginu ne akan tafarkin koyar da ilimin addinin Allah, wacce ta kasace mai cike  da abin mamaki. Jagoran juyin musuluncin na Iran ya siffata mutanen Gaza da Lebanon da cewa suna tafiya ne akan wannan tafarki na Imaman shiriya.
    Jiragen yakin Amurka sun kai jerin hare-haren a kan biranen San,a,Sa’adah da kuma Hudaidah na kasar Yemen. Kamfanin dillancin labarun “Saba’a” na kasar Yemen ya nakalto cewa sojojin na Amurka sun kai hare-hare har sau uku a dutsen Naqam, wanda  yake gabashin birnin San’aa. Kamfanin dillancin labarun na “Saba’a” ya kuma ce, jiragen yakin Amurka din sun kai hare-haren ne a tsakanin marecen jiya Laraba da kuma safiyar yau Alhamis. Daga cikin wuraren da aka kai wa harin jiya da marecen da akwai Sahlin dake karamar hukumar Ali-Salim. Sau 6 Amurkan ta kai wa yankin hare-hare. Da safiyar yau Alhamis kuwa jiragen yakin na Amurka sun kai hare-hare a gundumar Sa’adah. Wasu yankunan da su ka fuskanci hare-haren su ne,...
    Ban da haka, yadda gwamnatin Trump ba ta da tabbas a kan manufofinta na haraji yana kuma ba kasashen duniya mamaki. Ba a jima ba da gwamnatin Amurka ta sanar da matakinta na harajin ramuwar gayya a kan kasashen da ke ciniki da ita, sai kuma ga shugaba Trump ya sanar da dage harajin a kan wasu kasashe na kwanaki 90. Kuma kashegari sai aka ji ya yi barazanar cewa, in dai ba a kai ga cimma daidaito a shawarwari ba, to, Amurka za ta maido da harajin. Ban da haka, gwamnatin Amurka ta kuma yi gyara ta ba-zata a kan dokokinta na haraji, inda ta cire harajin ramuwar gayya a kan kayayyakin lataroni da suka hada da wayar salula...
    Ya buƙaci jama’a da su ci gaba da tallafa wa jami’an tsafta domin tabbatar da tsaftar muhalli a jihar. Aikin tsaftar muhalli na wata-wata, wanda ake yi a ƙarshen kowane wata, ana dakatar da zirga-zirgar ababen hawa na wasu awanni domin tsaftace muhalli a faɗin Kano. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ya ƙara da cewa IEDs guda biyu da aka gano an birne su ne yankunan ƙaramar hukumar Hong, kuma an fashe su. Morris ya kuma ce ‘yansandan sun ceto wasu da aka sace guda shida tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro. Ya jinjina wa jami’an tsaron da suka taka rawar gani wajen wannan aiki, kuma ya tabbatarwa da jama’a cewa rundunar za ta ci gaba da ɗaukar matakai don tabbatar da tsaro a jihar. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ce a yanzu jihar na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi zaman lafiya a Najeriya. Ya ce, a matsayinsa na babban jami’in shari’a da tsaro a Jihar Yobe, yana da haƙƙin ganin an bi doka don tabbatar da cewa jihar ta samu zaman lafiya. An kama mata 2 na ƙoƙarin sayar da ƙananan yara da aka sace An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin karɓar lambar karramawa da aka yi masa shi da wasu shugabnnin da Ƙungiyar Inganta zaman lafiya ta “Peace Building Development Consult” (PBDC) ta yi musu. Gwamnan wanda ya samu wakilcin babban lauya kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Imo ta kama wasu mata biyu a lokacin da suke yunƙurin sayar da wani yaro ɗan shekara huɗu da aka yi garkuwa da shi a Owerri kan kuɗi Naira miliyan 2.7. An yi garkuwa da yaron ne a Abuja a lokacin da yake tallan kayan miya, sannan aka kawo shi Owerri a sayar da shi kafin a sa’ar kuɓutar da shi daga masu son sayar da shi. An fara raba wa almajirai tabarma da gidan sauro a Yobe Na ba ku wata 1 ku murƙushe ’yan ta’adda — Olukoyede ga sojoji Waɗanda ake zargin sun haɗa da Joy Ugwu daga garin Idah ta jihar Kogi, da Rosella Michael daga garin  Zamba da ke Abuja, yayin da...
    Hukumar Ilimin Larabci da Musulunci ta Jihar Yobe (AISEB) ta fara rabon tabarmi da gidajen sauro ga almajirai a fadin jihar. Sakataren Zartarwa na hukumar, Malam Umar Abubakar ya cen tabarmi da gidajen sauron tallafi na daga cikin kokarin da gwamnati ke yi na inganta walwala da rayuwar almajiran makarantun tsangaya a fadin jihar. A cewarsa, shirin ya yi daidai da umarnin da gwamnatin jihar ta ba hukumar na tabbatar da kulawa da kuma tallafa wa yara almajirai. Ya bayyana cewa an tsara rabon ga ɗalibai 100 a kowace karamar hukuma cikin kananan hukumomin Jihar 17, wanda za a fara daga makarantun Goni Yahaya da Goni Muhammad Tsangaya da ke Damaturu. Ya ƙara da cewa, kayayyakin za su taimaka wa...
    Hukumar lura da gidajen bashin ma’aikatan gwamnatin tarayya (FGSHLB) ta sanar da cewa ta fara tattara jerin sunayen ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya amma ba su biya bashin gidajen da suka karɓa ba. Shugabar sashin sadarwa da hulɗa da jama’a na FGSHLB, Ngozi Obiechina, ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Alhamis a Abuja, inda ta ruwaito cewa shugabar hukumar, Salamatu Ahmed, tana cewa wannan matakin yana nufin dawo da dukiyoyin da aka yi rance daga ma’aikatan da suka yi ritaya amma ba su kammala biyan bashin ba. Rashin Tsaro: Gwamnatin Neja Ta Saka Dokar Zama A Gida A Minna Gina Al’umma Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya: Jigon Ziyarar Xi A Kudu Maso Gabashin Asiya Salamatu...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran Ta bayyana cewa; Kakaba takunkumi kan kasarta ya sabawa ikirarin Amurka na yin shawarwari da ita Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi kakkausar suka kan matakin da Amurka ta dauka na kakabawa wasu gungun mutane masu alaka da bangaren makamashi, man fetur da iskar gas da kuma wasu mutane da dama masu fafutuka a shirin nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran na lumana takunkumi. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Baqa’i ya bayyana manufar takunkuman da Amurka ta kakabawa al’ummar Iran da cewa; A fili take nuna kyama ga masu yanke shawaran Amurka kan al’ummar Iran da kuma nuna rashin mutunta doka da hakkin dan Adam ne. Ya kara da cewa: Dogaro...
    Jami’in kasar Yemen ya jaddada cewa: Kwanaki masu zuwa za su aiwatar da abubuwan mamaki da za su ba abokan gabanmu mamaki! Daraktan sashin yada labarai na fadar shugaban kasar Yemen Zaid Al-Gharsi ya jaddada samun gagarumin ci gaba a karfin sojojin kasar Yemen musamman a fannin fasaha da makamai. Ya yi nuni da cewa, kasar Yemen na gab da samar da sabbin makamai da za su bai wa kowa mamaki. A cikin wata hira da tashar talabijin ta Al-Alam, Zaid Al-Gharsi ya yi magana game da irin goyon bayan da kasar Yamen ke ba wa yankin Zirin Gaza, inda ya yi nuni da mahimmancin hare-haren soji kai tsaye kan makiya ‘yan sahayoniyya tare da jaddada fifikon karfin kasar Yemen...
    Munanan azabtarwa kan fursunonin Falasdinawa a gidajen kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila da suka hada da fyade da dangogin azaba Rahoton da Hukumar Kula da Fursunoni Falasdinawa dakungiyar Fursunonin Falasdinawa da aka saka daga gidan kurkukun haramtacciyar kasar Isra’ila sun fiyar da rahoton hadin gwiwa a yau Alhamis, 24 ga watan Afrilun shekara ta 2025, da ya kunshi munanan shaida daga fursunonin Zirin Gaza da ke tsare a gidan yarin Negev da sansanin Ofer na gwamnatin haramtaciyar kasar Isra’ila. Rahoton ya bayyana yadda ake ci gaba da yin fyade da cin zarafi ga wadanda ake tsare da su a Gaza. Wanda ake tsare da shi a sansanin Ofer ya bayyana cewa da gangan masu gadin sansanin suke kara radadin yadda wanda...
    Sabuwar gwamnatin Siriya tana kara matsa lamba kan bangarorin ‘yan gwagwarmaya domin Isra’ila ta janye daga wasu yankunan kasarta Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da tura kayayyakin soji zuwa tsaunukan Dutsen Harmon, yayin da suke hanzarta gina abin da suka kira “Katangar tsaro.” Har ila yau, sun karfafa wuraren tsaro da suka kafa a cikin yankunan Siriya, a cikin abin da gwamnatin Isra’ila ta kira “yankin da ke da kariya,” wanda ya hada da mamaye wasu sassan garuruwan Quneitra da Dara’a. Majiyoyin cikin gida a garin Nawa da ke cikin karkarar Dara’a na cewa, mahukuntan kasar Siriya na ci gaba da daukan matakan matsin lamba, ta hanyar shugabannin kabilu da kwamandojin ma’aikatar tsaro a Dara’a, na tilastawa bangarorin da...
    Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, ’yan kasuwa 1,000 za su samu jarin fara aiki na Naira 150,000 kowannensu, da nufin sauya akalar kasuwancin su zuwa sana’o’i na zamani a faɗin Jihar Zamfara.   A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa bayan hawansa mulki, gwamnatinsa ta bullo da shirye-shiryen ƙarfafawa da dama tare da samar da damarmaki don cimma manufofinsa na ceto.   “Waɗannan tsare-tsare ba wani kebantaccen abu ba ne, wani ɓangare ne na babban burinmu wajen samar da jihar Zamfara mai albarka don haɗa abokan hulɗa don magance ɗimbim matsalolin zamantakewa da tattalin arziki. “Yawancin tsare-tsare na rage raɗaɗin talauci da wannan gwamnati ta bullo da su sun yi tasiri ga rayuwar dubban ‘yan jihar, ƙudirin...
    Gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da ƴan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda sun amince su dakatar da faɗa a gabashin ƙasar har sai an kammala tattaunawar sulhu da ke gudana a halin yanzu wanda Qatar ke shiga tsakani. Wannan dai ita ce yarjejeniyar sulhu ta baya-bayan nan tun bayan da ƴan tawayen suka ƙara kai farmaki a gabashin ƙasar inda hukumomi suka ce an kashe mutane 7,000 tun daga watan Janairu. A ranar Larabar da ta gabata ce, ɓangarorin biyu suka ba da sanarwar yin aiki tare don samar da zaman lafiya, bayan shafe sama da mako guda suna tattaunawa, wanda suka ce an gudanar cikin aminci tare da mutunta juna. A watan da ya gabata, shugaban ƙasar...
    Ma’aikatar yada labarai ta jihar Kano tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Radiyo da Talabijin ta kasa NBC sun shirya taron yini biyu ga masu fafutukar siyasa da masu sharhi kan harkokin yada labarai.       Taron na da nufin tsaftace harkar siyasa da inganta fahimtar juna tsakanin ‘yan siyasa a jihar.   An zabo mahalarta taron ne daga jam’iyyun siyasa daban-daban da gidajen rediyo a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.   A nasa jawabin, kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa, a karshen taron, mahalarta taron za su fahimci ladubban da suka shafi harkokin siyasa.   Ya yi Allah wadai da karuwar kararrakin batanci da sunan...
    Babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya ba da umarnin ga rundunar sojin Najeriya da ta fatattaki ‘yan bindigar da ke addabar al’ummar kananan hukumomin Baruten da Kaiama na jihar kwara da Borgu da ke dajin Kainji a jihar Neja cikin wata guda.   A jawabin da ya yi wa dakarun rundunar soji bataliya ta 22  a Sobi Ilorin, Oluyede ya ce sojojin Najeriya ba za su bari tashin hankalin yankin arewa maso gabas ya rikide zuwa arewa ta tsakiya ba.   A cewarsa nauyi ne da ya rataya a wuyan sojojin Najeriya su kare martabar yankunan kasar.   Shugaban hafsan sojin ya ce dole ne a fatattaki ‘yan bindigar daga yankin Najeriya nan da wata guda.  ...
    Kujeru dubu daya da dari hudu da bakwai ne aka ware wa hukumar jin dadin Alhazai ta jihar Taraba domin maniyyata bana.   Babban Sakataren Hukumar mai barin gado Umar Ahmed Chiroma ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai kan matakin da ake na shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana na 2025 ba tare da tangarda ba.   Aikin Hajji daya ne daga cikin rukunnan Musulunci guda biyar kuma Musulmin muminai na gudanar da aikin Hajji a kowace shekara akalla sau daya a rayuwarsu.   Chiroma ya ce hukumar ta kai wani mataki na ci gaba ta fannin shirye-shirye kamar yadda hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta bayar, inda ya ce sama da maniyyatan jihar...
    A hukumance gwamnatin tarayya ta ayyana filin jirgin saman Bola Ahmed Tinubu dake Minna a matsayin mafita ga jiragen dake sauka Abuja.   Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan a yayin bikin kaddamar da jirgin saman na Overland Airways a filin jirgin sama na BAT dake Minna.   Festus Keyamo ya ce ana shirin daukar matakan da suka wajaba kamar su kwastam, shige da fice, ‘yan sanda, NDLEA da sauran su don sarrafa fasinjoji idan filin jirgin Abuja ya samu matsala.   Gwamnan jihar Neja Mohammed Umar Bago wanda ya yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa ci gaba da goyon bayan da yake baiwa jihar, ya bayyana cewa wannan nasara wani kokari ne na hadin...
    Shi dai filin jirgin saman, wanda gwamnatin Umaru Bago ta gina a Jihar Neja, an raɗa masa sunan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.   Jirgin kasuwancin na farko mallakin kamfanin Overland Air mai lamba 5N-CCN ya sauka ne da misalin ƙarfe 1:32 na rana.   Cikin fasinjojin akwai Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, Minista Mohammed Idris, tsohon Gwamnan Neja Dakta Babangida Aliyu, Ƙaramin Ministan Harkokin Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, da wasu manyan jami’an gwamnati.   Ministan ya yaba wa Shugaba Tinubu saboda samar da yanayin da ya bai wa filin jirgin damar fara aiki, yana mai cewa hakan na nuna jajircewar Shugaban Ƙasa wajen inganta ababen more rayuwa a faɗin ƙasar.   Haka kuma, Ministan...
    Muƙaddashin Shugaban Jam’iyyar PDP na Ƙasa, Ambasada Umar Damagum, ya umarci jami’an jam’iyyar da su yi karɓi Arch. Setonji Koshoedo a matsayin mukaddashin sakataren jam’iyya na ƙasa. Gwamnonin PDP, a taron da suka yi a Ibadan, Jihar Oyo, sun amince da Koshoedo a matsayin mukaddashin sakatare har sai lokacin da shugabannin shiyyar Kudu maso Gabas za su zaɓi cikakken sakatare wanda Kwamitin Zartarwa na Ƙasa (NEC) na jam’iyyar zai amince da shi. Kotun Ƙoli, a hukuncin da ta yanke kan wanda ya cancanci ya riƙe muƙamin tsakanin Sanata Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye, ta ba jam’iyyar ikon yanke shawara kan shugabanninta. Sai dai a wata takarda da Alhaji Gurama Bawa, jami’in gudanarwa na mukaddashin shugaban jam’iyyar ya fitar, ta ce...
    “Akwai wasu bincike da ake gudanarwa domin kamar yadda muka sani, an sanar da cire tallafin man fetur ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023, amma an dauki lokaci kafin a cimma wannan kudurin. A halin yanzu, wani bangare na biyan basussukan da ake bin NNPC, daga kasafin kudin gwamnati ake tanada”.   Ya kara da cewa, babban aikin da ke gaban NNPCL shi ne bunkasa hako danyen mai da kuma samar da karin kudaden shiga – a takardun Dala zuwa Asusun Tarayya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko...
    Babban Hafsan Sojin Ƙasa na Najeriya, Laftanar-Janar Olufemi Oluyede, ya ba wa dakarun rundunar wa’adin wata guda su fatattaki sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta Mahmud a da ta ɓulla a Jihar Kwara. Oluyede ya ba da wannan umarnin ne a lokacin da yake jawabi ga sojojin a ziyarar da ya kai Barikin Sobi da ke Ilorin, babban birnin jihar. “Daga wata mai zuwa, ba na son in ƙara jin mostin waɗannan ’yan ta’addan a yankin Dam ɗin Kainji,” in ji babban hafsan sojin. Ya umarce su da su kawar da ’yan ta’addan daga ƙananan hukumomi biyun da suka addaba, yana mai jaddada cewa yana son a kammala aikin cikin wata mai zuwa. Nijar, Mali da Burkina Faso sun kafa gidan...
    Amurka ta kai wasu sabbin hare-hare ta sama a Yaman, a daidai lokacin da kasar Larabawar ke ci gaba da nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza. Gwamnonin Sana’a da Sa’ada su ne wuraren da Amurka ta kaddamar da sabbin hare-hare a safiyar Alhamis. A birnin San’a, jiragen yakin Amurka sun kai hare-hare 6 a yankin Barash da ke gabashin Dutsen Nuqum. Har ila yau Amurka ta kai hari a unguwar Al-Jarf da ke gabashin gundumar Sha’ub ta lardin Sana’a. A arewa maso yammacin kasar, an kai wasu hare-hare 6 ta jiragen yakin Amurka a yankin Sahlin da ke gundumar Al Salem a gundumar Sa’ada. Har ila yau, Amurka ta kai wasu jerin hare-hare ta sama kan lardin Al-Hudaidah, inda...
    Aljeriya sun kori fiye da bakin haure 1,100 zuwa Nijar a rana guda, al’amarin da ba a taba ganin irinsa ba. Bakin hauren da hukumomin Aljeriyar suka bayyana da basa bisa ka’ida, an kora su a cikin hamadar sahara a ranar Asabar din da ta gabata, Inda sukayi tattaki zuwa kan iyakar kasar Nijar, kasar da dubban bakin haure ke bi domin zuwa Libya da Aljeriya domin isa Turai. Wannan dai shi ne karo na farko da aka kori bakin haure da dama daga kasar Aljeriya a lokaci guda. A cewar kungiyar ‘Alarme Phone Sahara’ ta Nijar da ke taimakawa bakin haure a cikin hamada, an kori mutane 1,140 a lokaci guda, adadin da ba a taba ganin irinsa ba....
    Jamhuriyar Musulinci ta Iran,  za ta karbi bakuncin taron farko na kasa da kasa kan kare hakkin bil adama a Gabas ta Tsakiya. Shugaban Hukumar Al’adu da Sadarwa ta Musulunci Mohammad Mehdi Imanipour ya bayyana cewa, za a gudanar da taron farko na kasa da kasa kan batun kare hakkin bil’adama kan Gabas ta Tsakiya a lokaci guda a Tehran, Qom da Isfahan daga ranar 28 ga Afrilu zuwa 2 ga Mayu. Hakkin dan adam na daya daga cikin batutuwan da suka fi muhimmanci a cikin al’ummomi, saidai a baya bayan nan wasu gwamnatoci sun yi watsi da yancin dan adam gaba daya. Mohammad Mehdi Imanipour ya ce “A yau, misali karara na take hakkin bil’adama shi ne kisan kiyashi...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun zamanin kaka da kakanni ake gudanar da ƙananan sana’o’i, waɗanda al’umma ke dogaro da su don biyan buƙatunsu na yau da kullum. Irin waɗannan sana’oi sun haɗa da saƙa, jima, fawa, suyan ƙosai ko masa da dai sauransu. A da can masu waɗannan sana’o’i sun dogara ne da masu wucewa a bakin hanya don siyar da hajojinsu ko kuma waɗanda suka samu a yayin da suka ɗauki tallar kayan sana’ar tasu. Sai dai a wannan zamani masu waɗannan sana’o’i na fuskantar barazana daga wurin ’yan zamani ’yan bana bakwai da suka shigar da zamani ciki suke neman kwace musu ragama ta hanyar amfani da kafofin sada zumunta wajen tallata hajojinsu. NAJERIYA A...
    Sanarwar ta kara da cewa, Shugaban tawagar ‘yan fashin, Baba-Beru ya samu munanan raunuka, wanda daga baya ya rasu a Asibiti.   “An garzaya da dukkan wadanda suka samu raunuka zuwa Asibitin kwararru na Murtala Mohammed da ke Kano, inda Baba-beru ya rasu a lokacin da ake jinyarsa, amma jami’an ‘yansanda an sallame su bayan sun gama jinya,” in ji sanarwar.   Rundunar ‘yansandan ta ce Baba-Beru, mazaunin Kofar Mazugal a karamar hukumar Dala, na cikin jerin sunayen wadanda ake nema ruwa a jallo kafin faruwar lamarin.   Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Ibrahim Bakori, ya yabawa bajintar jami’an da suka dakile yunkurin ‘yan fashin tare da jaddada aniyar rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.  ...
    Jami’in ya kara da cewa, kasar Sin ba ta son gwabza yakin kasuwanci da karin harajin kwastam, amma kuma ba za ta rungume hannu ta zuba ido ba idan yakin ya kaure, yana mai nuni da cewa, idan har Amurka ta zabi fafata yakin kasuwanci, Sin za ta sha damarar yakin har sai ta ga abin da ya ture wa buzu nadi. Sai dai kuma duk da haka, ya ce idan Amurka na son a tattauna, Sin za ta bar kofarta a bude domin yin hakan.   Bugu da kari, dangane da batun yadda a baya-bayan nan kafafen yada labarun kasar Panama suka soki Amurka kan yin katsalandan da nuna babakere a kasashen yankin tsakiyar Amurka, musamman a kasar ta...
    Na uku, ba da ra’ayin samun tsaro kafada da kafada, inda aka jaddada cewa, ya dace kasa da kasa su yi fatali da ra’ayin nuna wa juna fito-na-fito, kana, su fuskanci dimbin kalubalen tsaro cikin hadin-gwiwa. Na hudu wato na karshe, tallata ra’ayin tabbatar da tsaro mai dorewa, wato a maida hankali kan dorewar tsaro na wani dogon lokaci. Alal misali, yayin da ake daidaita rikicin wani yanki, bai dace a dogara kan matakan soja kadai ba, ya kamata a nemo mafita tun daga asalin rikicin. Wannan shawarar tsaron da shugaba Xi Jinping ya gabatar, ta samu amincewa sosai daga mutanen kasa da kasa, inda ya zuwa yanzu, ta riga ta samu goyon-baya daga kasashe da yankuna da kungiyoyin kasa...
    Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu a Majalisar Dattawa, Abdurrahman Kawu Sumaila ya tabbatar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP zuwa APC. Sumaila ya tabbatar wa Aminiya ficewarsa a wani saƙon kar ta kwana, bayan wallafa wa a shafinsa na Facebook. Majalisun jihohi sun buƙaci a kawo ƙarshen matsalar tsaro Gwamna da jiga-jigan siyasa a Delta sun fice daga PDP zuwa APC “Gaskiya ne na koma APC. Damuwata a ko yaushe ita ce walwalar al’ummar mazaɓata,” in ji shi. Sanatan ya jaddada cewa matakin da ya ɗauka na sauya sheƙar ya yi shi ne domin inganta rayuwar al’ummar mazaɓarsa, da kuma tabbatar da ci gabansu mai dorewa. Kawu dai ya daɗe da raba gari da tafiyar Kwankwasiyya da NNPP da ya...
    Da yake jawabi a fadar Mai Tangele (Sarkin Billiri), Danladi Sanusi Maiyamba, ya bayyana lamarin da matukar bakin ciki tare da fatan samun makoma mai kyau ga wadanda suka rasu, ya kuma warkar da wadanda suka samu raunuka da gaggawa.   Daga nan sai Gwamna Inuwa ya sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan 2 kowanne ga iyalai biyar da suka rasa rayukan ‘yan uwansu, wanda ya kai adadin zuwa Naira miliyan 10.   Ya kuma yi alkawarin biyan kudaden jinya ga wadanda ke karbar magani a Asibitocin jihar.   A yayin da yake godiya, Sarki Maiyamba ya ce, hatsarin na Easter ya girgiza daukacin masarautar Tangale, amma ya amince da matakin da gwamnatin jihar ta dauka, wanda ya ce hakan...
    A yau Laraba, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana cewa, yake-yaken karin haraji da kasuwanci ba su haifar da komai illa tauye halastattun hakkoki da muradun dukkan kasashe, tare da kawo cikas ga tsarin ciniki tsakanin bangarori daban-daban, da kuma yin tasiri mara kyau ga tsarin tattalin arzikin duniya.   Yayin ganawarsa da shugaban kasar Azabaijan Ilham Aliyev, shugaba Xi ya yi bayanin cewa, kasar Sin tana da muradin yin hadin gwiwa tare da kasar Azabaijan wajen kiyaye tsarin kasa da kasa a karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da tabbatar da tsarin kasa da kasa bisa dokokin da aka amince da su a duniya, da yin tsayuwar daka wajen kare halastattun hakkoki da muradu, da kare daidaito da adalci...
    Asusun bayar da lamuni na duniya ( IMF) ya yi gargadin cewa rashin tabbataci da Karin kudin harajin Amurka ya haddasa zai iya kawo tsaiko a cikin harkokin cinikiyya ta duniya. Sanarwar wacce babban jami’in ttatalin arziki na Asusun bayar da lamunin na duniya Pierre -Oliver-Gourinchas, ya bayyana ta kara da cewa; Za a iya samun karuwar hargitsi a cikin harkokin tattalin arzikin na duniya da dama yake fama da matsala. Jami’in ya yi bayani ne  bayan sake yin hasashe akan ci gaban tattalin arzikin duniya, wanda aka fitar a cikin rahoto a ranar Talatar nan. Asusun bayar da lamunin ya yi hasashen cewa tattalin arzikin duniyar zai bunkasa da kaso 2.8 % a cikin 2025, da hakan yake nuni...
    Kungiyar da take wakiltar Iran a wasannin Taekwondo na duniya a kasar Sin, ta sami lambobin yabo 8 a ranar farko da bude gasar ta kasa da kasa. An  fara wasannin na Tikondu a garin Tayan dake kasar China wanda shi ne karo na 7 da kuma ‘yan wasa 491 daga duniya suke gasa. Daga cikin lambobin yabon din da tawagar ta Iran ta lashe da akwai gwala-gwalai 4, azurfa 3 da kuma tagulla.
    Ministan harkokin wajen Iran wanda ya ziyarci kasar China, ya bayyana cewa, tattaunawa da mahukunta wannan kasa ta yi kyau, kuma ba da jimawa ba, shugaban kasar Iran zai kai Ziyara can kasar. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci bayan ganawa da takwaransa na China ya ce; Na yi doguwar ganawa da ministan harkokin wajen China, wacce take mai muhimmanci, kuma kusan dukkanin bangarorin da suka shafi alakar tsakanin kasashenmu biyu mu ka tattauna, haka nan kuma batutuwa da su ka shafi siyasar kasa da kasa.” Arakci ya kara da cewa; Da akwai fahimtar juna a tsakaninmu, musamman abinda ya shafi batun makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, da tataunawar da ake yi da Amurka.” Haka nan kuma ya...
    Hukumar lafiya ta duniya  (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar. Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci. Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan. Haka nan kuma ta  yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar. A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar...
    Ƙungiyar shugabannin majalisun jihohin Nijeriya ta yi tur da matsalolin tsaron da suka addabi jihohin Filato, Borno, Binuwai, Neja, da kuma Kwara a baya-bayan nan. Ƙungiyar ta buƙaci gwamnatocin jihohi da na tarayya da su ɗauki matakan gaggawa domin daƙile bala’in da jihohin a kwanan nan suka tsinci kansu a ciki.  Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a Ibadan da ke Oyo mai dauke da sa hannun shugabanta, Adebo Ogundoyin. Ya bayyana cewa kashe-kashen dubunnan al’ummar da ba su ji ba, ba su gani ba ya janyo musu asarar gidajensu, da dukiyoyinsu, yana haifar...
    Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori da wasu jiga-jigan ‘yan siyasa na jihar sun sun sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Daga cikin jiga-jigan da suka sauya sheƙa har da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa, shugaban jam’iyya, da sauran masu ruwa da tsakin jam’iyyar reshen jihar. Abin da ya sa na bi sahun mahaifiyata a Kannywood — Maryam Intete Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya Sanarwar ficewar ta su ta zo ne bayan kammala taron sa’o’i shida da suka gudanar a gidan gwamnatin jihar, kamar yadda sanarwar da Sanata daga jam’iyyar, James Manager, ya bayyana. “Duk wani dan PDP na jihar har da gwamna, da tsohon gwamna Okowa, da shugaban majalisa, da shugaban jam’iyyar, da duk ciyamomin ƙanannan hukumomi...
    Gwamna Oborevwori, wanda ya samu nasara a zaben gwamna na 2023 a karkashin jam’iyyar PDP, ya samu tarba daga manyan jami’an APC. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bugu da kari, kasar ta samar da cibiyoyin kula da lafiyar mata da kananan yara 3,081, baya ga likitocin yara da na mata a fadin kasar da yawansu ya kai 373,000. Kana fiye da kashi 90 cikin dari na cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a yanzu sun mallaki kayan aiki da sassan kula da lafiyar yara masu inganci.   Ba a cikin kasarta kawai take kokarin inganta kiwon lafiyar mata da kananan yara ba, har ma da kasashen duniya, domin kwararrun likitocin Sin da aka tura don ba da agaji a kasashen waje sun gudanar da ayyukan kula da lafiyar mata da yara a kasashe da yankuna 44, ciki har da wasu kasashen Afirka. A cikin 2024 kadai, tawagogin...
    Ba wannan ne karon farko da ake zargin wasu ‘yan ƙasashen waje da kai hare-hare a Nijeriya ba. A baya an yi zargin cewa ƙungiyoyi kamar Lakurawa da ke kai hare-hare a jihohin Sakkwato da Zamfara, sun samo asali ne daga ƙasashen waje. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    113-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko. A cikin shirimmu da ya...
    112-Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na kissoshin rayuwa shiri wanda yake kawo maku kissiso da suka zo cikin alkur’ani mai girma ko kuma cikin wasu littafan wadanda suka hada da littafin dastane rastan, ko kum littafin mathnawi na maulana Jalaluddeen rumi. Ko kuma cikin wasu littafan da fatan masu sauraro zasu kasance tare da mu a cikin shirimmu na yau. ///… Masu sauraro idan kuna tare da mu a cikin shirimmu da ya gabata, a kuma cikin sirar Imam Al-hassan limami na biyu daga cikin limamai masu tsarki daga iyalan gidan manzon All..(s), kuma da na farko ga Fatimah diyar manzon All..(s), sannan jikansa na farko. A cikin shirimmu da ya...
    Maryam Abubakar, ɗaya ce daga cikin jaruman masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood ’yan ƙalilan da suka yi nasarar bin sahun iyayensu a harkar fim. Matashiyar jarumar, wadda aka fi sanin ta da Maryam Intete a masana’antar, ta yi bayani a kan matsayinta na wadda iyayenta suka suka a cikin cikin harkar fim. Mahmuda: Sabuwar ƙungiyar ’yan ta’adda ta ɓulla a Nijeriya DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa A wannan tattaunawar, jarumar ta yi bayani game da gogewarta da yadda ake samun daukaka a Kannywood, da wasu abubuwa game da ita kanta da iyayenta, da kuma sana’ar fim da dai sauransu. Wace ce Maryam Abubakar? An haife ni ne a Kano kuma a nan na girma....
    Wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira Mahmuda tana ci gaba da kafuwa da ƙara ƙarfi tare da addabar jama’a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Ilesha Baruba da Kemaanji da Kaiama da Baruten na Jihar Kwara. Bayanai sun ce ’yan ƙungiyar sun sami mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke makwabtaka da dajin har ma da wasu sassa na Jihar Neja. DAGA LARABA: Dalilan Rashin Wutar Lantarki A Wasu Jihohin Arewa CONMEBOL ta buƙaci a faɗaɗa Gasar Kofin Duniya ta 2030 Bayanai sun ce ko a Juma’ar da gabata sai da mayaƙan suka kashe wasu fulani huɗu, ɗan sa-kai da wani saurayi mai shekaru 19....
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa; Iran ba za ta taba gudanar da shawarwari kan tsaronta ba A cikin jawabinsa na shirye-shiryen shirin zaman taron Carnegie kan manufofin nukiliya na kasa da kasa da aka soke a yanzu, ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa kamfanonin Amurka za su iya cin gajiyar damar dala tiriliyan da tattalin arzikin Iran ke samarwa kuma kasuwar Iran za ta iya farfado da masana’antar nukiliyar Amurka da ta tsaya cak. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana ta shafinsa na Twitter a takaitaccen jawabin da aka shirya yi a taron manufofin nukiliya na kasa da kasa na Carnegie, yana mai jaddada cewa, “Iran sam ba ta da niyyar yin...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: China da Rasha abokan hulda ne na tushe ga Iran bisa kyakkyawan tsari Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana kasashen China da Rasha a matsayin abokan huldar na tsari a kan tubalin manyan tsare-tsare ga Iran, kuma ya dace kasashen uku su ci gaba da tuntubar juna a fannoni daban daban. A yayin da ya isa birnin Beijing, yayin da yake amsa tambaya game da makasudin ziyararsa a kasar China a jajibirin shawarwarin da ba na kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, Araqchi ya bayyana cewa: Kasashen China da Rasha abokan hulda ne na kut-da-kut da Iran. Sun kasance tare da Iran a lokutan wahala, kuma abu ne mai...
    Al’ummar Gaza sun bukaci kasashen duniya da su tilasta daukan matakin shigar da kayan agaji cikinsu Al’ummar Falasdinawa a Zirin Gaza sun yi kira ga hukumomin kasa da kasa da na Larabawa da su tilasta shigar da kayan agaji cikin yankin, duba da munanan bala’in jin kai da al’ummar yankin ke fuskanta. A cikin wata sanarwa da ya fitar, Akif al-Masri, kwamishinan hukumar koli ta al’amuran da suka shafi Falasdiwa a Gaza, ya ce: “Matsalar yunwa tana barazana ga rayuwar dubban daruruwan mutanen Gaza,  yana mai cewa: Mafi yawan gidaje kusan babu kayan abinci, kuma iyalai ba za su iya samun abincinsu na yau da kullum ba.” Al-Masry ya tabbatar da cewa: Sojojin mamayar Isra’ila sun ketare dukkan iyakokin kasa...
    Adadin Falasdinawa da suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da irin sojojin mamayar Isra’ila kan Gaza ya kai shahidai 51,266 Ma’aikatar lafiya ta Falasdinu ta sanar da cewa: An isar da gawawwakin shahidai 26 da kuma wasu 60 da suka jikkata a asibitocin zirin Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata. Ma’aikatar ta bayyana a cikin wata sanarwa a jiya Talata cewa adadin wadanda suka yi shahada da wadanda suka jikkata tun ranar 18 ga Maris, shekara ta 2025 ya kai shahidai 1,890 da kuma jikkata wasu 4,950 na daban. An tabbatar da cewa adadin wadanda suka yi shahada a sakamakon harin ta’addancin ‘yan sahayoniyya ya karu zuwa shahidai 51,266 da jikkatan wasu 116,991 tun daga ranar 7 ga...
    Wani rahoton kare hakkin bil adama ya tabbatar da aikata manyan laifuka a gabar tekun Siriya tare da yin kira da a kare fararen hula Kwamitin da ke bin diddigin kare hakkin bil adama a kasar Siriya karkashin jagorancin dan gwagwarmaya Haitham Al-Manna, ya fitar da wani cikakken rahoton take hakkin dan Adam mai shafuka 72 da ke kunshe da jerin munanan laifukan da aka yi wa fararen hula a gabar tekun Siriya, yana mai bayyana shi a matsayin “neman shafe wata al’ummar daga kan doron kasa a kan tubalin sabanin Mazhaba”. Rahoton wanda masu fafutuka 12 suka shirya, ya zo ne bayan kisan kiyashin da aka fara a ranar 6 ga Maris. Rahoton ya yi nuni da wani tsari...
    “Yaron ya kuma ce akwai lokacin da ta ba shi wani lemun tsami da yake zaton an saka wani abu a ciki kafin abin ya faru. Ya bayyana cewa ta sha maimaita wannan aika-aikar a kansa,” Wakil ya ƙara da bayani. Wakil ya ce a yayin bincike, wadda ake zargin ta amsa laifin da ake zarginta da shi. Ya ce za a ci gaba da tantance bayananta, sannan a gurfanar da ita a gaban kotu bayan kammala bincike. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Wutar lantarki ta zama tamkar gwal a wasu sassan Arewacin Najeriya, inda a wasu yankuna aka ba da rahoton samun ta sa’o’i biyu kawai a rana, wasu kuma ba sa samun ko daidai da dakika ɗaya. Masu ƙananan sana’o’i suna kallon rayuwarsu da kasuwancinsu suna durƙushewa yayin da kayan sana’arsu suke lalacewa saboda rashin wuta. NAJERIYA A YAU: Matsayin Mataimakin Shugaban Ƙasa A Tsarin Mulkin Najeriya? DAGA LARABA: Dalilan Ɓaraka A Tsakanin Iyayen Riƙo Da Ƴaƴan Riƙo Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne a kan wannan matsala da yadda take taɓa rayuwar al’umma da hanyoyin magance ta. Domin sauke shirin, latsa nan
    Hukumar Alhazai ta Nijeriya NAHCON ta sanar da soma jigilar maniyyatan bana zuwa Saudiyya daga ranar 9 ga watan Mayu yayin da take tabbatar da kammala shirye-shirye aikin Hajjin bana. Hukumar ta bayyana hakan ne bayan wata ganawa da shugabanta da wakilan majalisar gudanarwa suka yi da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima. An daƙile yunƙurin juyin mulki a Burkina Faso Abubuwa 5 da ya kamata ku sani kan mutuwar Fafaroma Francis Mataimakin shugaban kasar ne ya gayyaci shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman da wakilan sashen gudanarwa zuwa ganawar a ofishinsa domin sanar da shi inda aka kwana game da shirye-shiryen aikin hajjin. “Mun yi masa bayani game da shirye-shiryenmu a Makkah da Madina da Arafa kuma ya gamsu, har...
    Iran ta sanar da dage tattaunawar da aka shirya gudanarwa yau Laraba tsakanin tawagar kwararu ta kasar da kuma na Amurka a kasar Oman a wani bangare na ci gaba da tattaunawar da ake tsakanin kasashen biyu kan shirin nukiliyar Iran na zaman lafiya. Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya bayyana cewa, an dage tattaunawar ta matakin kwararru tsakanin Iran da Amurka kan cikakkun bayanai na fasaha na yiwuwar maye gurbin yarjejeniyar nukiliyar shekarar 2015, wadda aka shirya yi a yau ranar Laraba, zuwa ranar mai zuwa 26 ga watan Afrilu. Esmaeil Baghaei ya bayyana cewa, za a gudanar da taron a daidai lokacin zagaye na gaba na tattaunawar tsakanin jagororin tawagogin guda biyu. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi...
    Kungiyar Hezbollah, ta Lebanon ta yi tir da kakkausan lafazi da kisan da gillar da Isra’ila ta yi wani jigonta Sheikh Hussein Atoui, wanda ya yi shahada a ranar Talata, yayin wani hari da jiragen yakin Isra’ila a kusa da garin Damour na birnin Beirut. Shugaban ofishin hulda da muslunci na kungiyar Hizbullah Sheikh Abdul Majid Ammar ya yi kakkausar suka dangane da kisan gillar dan gwagwarmayar, yana mai cewa abin takaici ne da makiya Isra’ila suka yi. Sheikh Hussein Atoui shi ne shugaban Dakarun Al-Fajr, reshen Jamaa Islamiya (Kungiyar Musulunci) masu dauke da makamai, dake kawance da kungiyar Hamas. Shugaban ofishin hulda da muslunci na kungiyar Hizbullah ya yi kira ga gwamnatin Lebanon da ta dauki matakai masu nagarta...
    Gwamnatin Amurka ta kakabawa kamfanonin kasar Iran sabbin takunkumi, duk da tattaunawar da ake yi kan shirin nukiliyar.   Ofishin kula da kadarorin waje na ma’aikatar baitul malin Amurka (OFAC) ya sanar a cikin wata sanarwa jiya Talata cewa, ya kara sunan wani dan kasuwa dan kasar Iran, Seyyed Assadollah Emamjomeh da kamfaninsa cikin jerin takunkumin da aka kakabawa Iran bisa zarginsu da hannu wajen fitar da danyen mai da iskar gas a Iran. Amurka ta yi zargin cewa Emamjomeh da mukarrabansa ne ke da alhakin jigilar danyen mai na iran da aka kiyasta ya kai daruruwan miliyoyin daloli zuwa kasuwannin kasashen waje.      Ma’aikatar Baitulmali ta Amurka ta yi zargin cewa kamfanin Emamjomeh ya fitar da dubunnan kayayyaki daga...
    ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa. Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila. Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila. Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP),...
    Hukumomin Burkina Faso sun sanar da cewa sun dakile wani sabon yunkurin juyin mulki, da aka shirya daga Abidjan babban birnin kasar Ivory Coast. Ministan tsaron Burkina Faso Mahamadou Sana ne ya fitar da cikakken bayani kan juyin mulkin da bai yi nasara ba, ya kuma kara da cewa ana fargabar sake yunkurin tayar da zaune tsaye. Ministan tsaron Burkina Faso, Mahamadou Sana, ya bayyana a gidan talabijin na kasar cewa hukumomin kasar sun dakile yunkurin juyin mulkin da aka yi wa hukumomin gwamnati. An dai shirya juyin mulkin ne a ranar 16 ga watan Afrilu tare da kai farmakin hadin gwiwa a fadar shugaban kasa. Sanarwar da aka fitar a hukumance ta ce jami’an leken asiri sun kame mutane...
    Guo Jiakun ya kara da cewa, kasar Sin ta kiyaye amfani da tsarin kimiyya da babu rufa-rufa a ciki mai baje komai a faifai, tare da nuna goyon baya da kuma shiga cikin kokarin da kasashen duniya ke yi na gano ainihin inda cutar ta samo asali.   Ya bukaci Amurka da ta daina siyasantar da lamarin, da amfani da batun gano asalin cutar a matsayin makami, kana ya nemi Washington ta guji yin kafar ungulu ga wasu kasashe, da dora wa wasu laifi, da yin watsi da tababar da ake ta nunawa a game da ayyukanta masu nasaba da cutar. Kazalika, ya jaddada bukatar ganin Amurka ta warware matsalolin da kasashen duniya suka nuna damuwa a kai tare da...
    Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sanata Kashim Shettima ya bayyana farin cikisa bisa da shirye-shiryen da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa NAHCON, ta gudanar ya zuwa yanzu, domin aikin Hajjin shekarar 2025. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman ne ya bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin tattaunawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan da ya jagoranci membobin hukumar ta NAHCON domin gabatar wa Mataimakin Shugaban Ƙasa bayanai kan shirye-shiryen aikin Hajjin 2025. Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ne ke sa ido kan ayyukan NAHCON, kuma Hukumar ta shaida wa Sanata Kashim Shettima cewa an kammala dukkan shirye-shiryen da suka wajaba domin fara aikin Hajjin 2025 da jigilar mahajjata zuwa ƙasar Saudiyya daga ranar 9 ga Mayu, 2025. A...
    Sahun farko na Alhazan Najeriya zai tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayun 2025. Hakan na kunshe ne a cikin bayanin bayan taro da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, ta yi da Shugabannin Hukomomin Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihohi a  ranar 22 ga watan Afrilun 2025. Manufar taron ita ce tantance matakin shirin da kowace Hukumar Alhazai ta Jiha ta kai. Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa harkar Hajji na cikin matakin karshe na shirye-shirye kafin fara aikin Hajjin shekarar 2025. Ya bukaci jihohi da su sanar da NAHCON matsayin da...
    Gwamnatin mulkin soji a Burkina Faso ta ce hukumomi leƙen asiri sun daƙile wani yunƙurin kifar da gwamnatin a cikin watan Afrilu. Ta ce an aka kitsa juyin mulkin ne domin haifar da ruɗani a kasar ta yammacin Afirka. Gwamnatin ta ce an gano waɗanda suka shirya juyin mulkin daga makwabciyarta Ivory Coast. Shugaban gwamnatin rikon kwarya Ibrahim Traore Kaptin ɗin soja wanda shi kansa ya hau shugabanci ne ta hanyar juyin mulki a 2022 ya sha zargin ƙasar Ivory Coast da bai wa masu adawa da shi mafaka.
    Ana kallon Cunha a matsayin wani da zai iya bayar da gudunmawa wajen dawo da Manchester United kan ganiyarta, Cunha ya kasance wanda ya fi zurawa Wolverhampton kwallaye a raga a kakar wasa ta bana inda ya zura kwallaye 16 a dukkanin gasa.   United na shirin fuskantar gogayya daga kungiyoyi da dama na gasar Firimiya kan Cunha, inda Liverpool, Arsenal, Chelsea da Newcastle duk sun kasance suna zawarcin dan wasan gaban a bana. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A jawabin Gwamna Zulum wajen kaddamar da aikin titin, ya ce, “A ci gaba da tsarinmu na sabunta birane, a yau mun kaddamar da gina titi mai tsawon kilomita 7.1 daga tashar borno Express zuwa Molai, hadi da karin ginin gadar sama ta hudu.   “Abin da muke da burin aiwatar wa, shi ne ba don kawai kyawawan ayyuka ba, har ma don daukar nauyin ci gaban al’ummar Maiduguri, kuma ya zama dole mu fadada birnin Maiduguri.”   Gwamna Zulum ya yi kira ga yan kwangilar su tabbatar da bin ka’idojin inganci da kuma kammala aikin a cikin lokacin da aka kayyade.   “Za a kammala aikin cikin watanni goma, an bayar da kwangilar kan naira biliyan 16, kuma mun...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A safiyar jiya Litinin ce Fafaroma Francis mai shekaru 88 ya koma ga mahaliccinsa, bayan da ya yi fama da mutuwar ɓarin jiki da kuma bugun zuciya, kamar yadda Fadar Vatican ta sanar. Shugaban na mabiya ɗariƙar Katolika ya shafe makonni 5 a asibiti a farkon wannan shekara, sakamakon harbuwa da cutar limoniya, amma ya koma gida a watan da ya wuce, bayan da ya samun sauƙi. An sanya dokar hana fita ta sa’o’i 12 a Neja Hanyoyin da za a magance rikicin Filato — Masana Fadar Vatican ta tabbatar da cewar a ranar Asabar ne za a gudanar da jana’izar Fafaroma Francis a majami’ar St. Peter’s Basilica. A safiyar Talatar nan ce dai fadar Vatican ta saki hoton Fafaroma...
    Brigadier General Ali Mohammad Naeini, kakakin dakarun dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar ya bayyana cewa dakarunsa a shirye suke fiye da ko wani lokaci wajen kara kan iyakokin JMI daga makami. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran Naeini yana fadar haka a yau Talata a wani taro da kafafen yada labarai a nan Tehran. Ya kuma kara da cewa a dai-dai lokacinda kasar ta cika shekaru 46 na nasarar juyin juya halin musulunci a kasar dakarun na IRGC suna cikin shirin da basu taba irinsa ba don kare kan iyakokin JMI. Kafin haka, a farkon wannan watan jami’an gwamnatin JMI sun bayyana cewa kasar tana cikin shiri mai kyau na kare kan iyakokin kasar mai tsarki,...
    Kungiyar raya tattalin arziki ta kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta fara taro a kasar Ghana don tattauna al-amura da suka shafi kasashen Niger Burkina Faso da kuma Mali. Jaridar Premium times ta Najeriya ta bayyana cewa agendar taron nasu na kwanaki biyu, sun hada da huldar kungiyar da kasashen uku, musamman cibiyoyin ECOWAS da suke cikin kasashen, sannan da batun kudaden fito na kashi 0.5% wanda kungiyarsu ta (AES) ta dorawa kayakin da suke shigowa  kasashensu da sunan gudanar da kungiyarsu. Labarin yace kungiyar ECOWAS bata karban kudaden fito da Visa  daga kasashen kungiyar gaba daya tun kafin kasashen uku su fita amma a halin yanzu su suna karba. Kasashen uku sun bayyana ficewarsu daga ECOWAS ne daga farkon wannan...
    Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st. Peter dake birnin Vatican amma za’a ajiye gawarsa don yi mata kallo na karshe a daga gobe Laraba a St. Peter’s Basilica har zuwa ranar Jana’izar. Shafin yanar gizo na labarai “Africa News” ya bayyana cewa paparoma Francis ya mutane a ranar 20 ga watan Afrilu yana dan shekara 88 a duniya, kuma fatansa a cikin jama’a da kuma jawabinda na karshe kwana guda ne kafin rasuwarsa. Labarin ya kara da cewa paparoman ya shahara da son talaka, da kuma wadanda aka zalunta, musamman al-ummar Falasdinu, wadanda yahudawan HKI suke yiwa kissan Gila tun sdhekara...