An Tabbatar Da Ganin Watan Shawwal A Nijeriya
Published: 29th, March 2025 GMT
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya sanar da ganin jinjirin watan Shawwal a Nijeriya, kamar yadda kwamitin duban wata ya tabbatar.
Baya ga Nijeriya, ƙasashen Saudiyya, Bangladesh, da Indiya suma sun ga watan a yau, Asabar 29 ga watan Ramadan, 1446.
An Ga Watan Sallah A Ƙasar Saudiyya Abubuwan da Za ki Runguma domin Burge MijinkiSai dai wasu ƙasashe kamar Malaysia sun sanar da cewa za su yi Sallah ranar Litinin.
Hakan na nufin cewa azumin watan Ramadan ya ƙare, kuma al’ummar Musulmi a Nijeriya za su gudanar da bikin ƙaramar sallah gobe.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Kwamiti Sarkin Musulmi Wata
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa.
Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki.
Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin SallahShirin Najeriya A Yau zai yi nazari ne kan hanyoyin da mutum ya kamata ya bi don komawa cin abinci yadda ya kamata bayan azumtar watan Ramadana.
Domin sauke shirin, latsa nan