Eid-el-Fitr: Sarkin Kauru Ya Gargadi Masu Bai Wa ‘Yan Ta’adda Bayanai
Published: 31st, March 2025 GMT
Masarautar Kauru da ke jihar Kaduna ta jaddada kudirinta na tabbatar da tsaro, inda ta bukaci mazauna yankin da su kasance masu taka-tsan-tsan duk da ci gaban da gwamnati ta samu a baya-bayan nan wajen magance matsalar ‘yan fashi da garkuwa da mutane da kuma munanan hare-hare.
Mai martaba Sarkin Kauru, Alhaji Zakari Ya’u Usman na biyu, ya jaddada muhimmancin hadin kai wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro a lokacin da ya gabatar da sakon Sallar a fadarsa da ke Kauru.
Alhaji Zakari Ya’u Usman ya kuma yi gargadi game da masu ba da labari da ke taimaka wa masu laifi tare da karfafa gwiwar mazauna yankin da su kai rahoton duk wani abu da ake zargi.
Dangane da harkokin kiwon lafiya, Sarkin ya bukaci iyaye da su ba da fifiko ga allurar rigakafin yara don kare su daga cututtukan da za a iya rigakafin su.
Ya kuma shawarci mata masu juna biyu da su rika zuwa duba lafiyarsu akai-akai, sannan ya shawarci jama’a da su nemi kulawar lafiya a kan lokaci domin rage kamuwa da cututtuka kamar hawan jini da ciwon suga.
A cewarsa, Masarautar ta nuna godiya ga gwamnatin jihar kan aikin hanyar Pambeguwa zuwa Kauru da kuma tallafawa manoma ta hanyar rabon taki. Sai dai Sarkin ya roki a kara ayyukan hanyoyin da suka hada da Kauru zuwa Mariri a karamar hukumar Lere, Unguwan Ganye zuwa Dokan Karji mai hade da Kasuwan Magani a karamar hukumar Kauru, da kuma titin mai tsawon kilomita 10 a cikin garin Kauru.
Ya kuma bukaci a kammala kashi na biyu na gyaran fadar Kauru, musamman a wuraren da ke bukatar kulawar gaggawa, musamman a lokacin damina.
Sarkin ya yi addu’a don ci gaba da zaman lafiya da wadata a shekaru masu zuwa.
Hakazalika, Sakataren Masarautar, Malam Muhammad Sani Suleiman (Danburan Kauru) ya nuna jin dadinsa ga wadanda suka halarci bukukuwan Sallah tare da jajantawa iyalan wadanda rashin tsaro ya shafa.
COV/Yusuf Zubairu Kauru
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Yan Ta adda Bayanai Gargadi Sarkin Kauru
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban Majalisar Neja Ya Mika Sakon Easter Ga Al’ummar Kirista.
Kakakin majalisar dokokin jihar Neja, Barr. Abdulmalik Sarkin-Daji, ya mika sakon taya murna ga al’ummar kiristoci a jihar da ma sauran sassan jihar bisa nasarar kammala azumin Easter na kwanaki 40.
A madadin shugabanni da membobin majalisar ta 10, shugaban majalisar ya yaba wa mabiya addinin kirista saboda sadaukarwar da suka yi da kuma ci gaban ruhaniya a wannan lokaci mai tsarki.
Duk da haka ya yaba musu bisa sadaukarwar da suka yi a wannan lokacin kuma fatan sabunta ruhi da aka samu a lokacin Azumi ya kawo zaman lafiya, farin ciki, da wadata ga kowa.
Barr AbdulMalik Sarkin Daji, ya amince da muhimmiyar rawar da shugabannin addinin Kirista ke takawa wajen jagorantar al’ummar Nijar cewa majalisar ta 10 za ta ci gaba da samar da dokokin da za su kawo wa al’ummar jihar tasiri kai tsaye kuma mai kyau.
.
Hakazalika ya ce majalisar dokokin jihar Neja ta ci gaba da jajircewa wajen ganin an samar da zaman lafiya a tsakanin dukkan mazauna yankin, ba tare da la’akari da addini ko al’ada ba.
Bikin Ista, ginshiƙin bangaskiyar Kirista, tashin Yesu Almasihu daga matattu, alamar nasara akan mutuwa da zunubi, taron tunatarwa ne na ikon canza bangaskiya da saƙon bege mai ɗorewa wanda ke bayyana a tsawon shekaru.
PR ALIYU LAWAL.