2025-04-04@00:37:14 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2835
«gargadi»:
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da hada karfi da karfe wajen gina kyakkyawar kasar Sin, da kuma sa kasar ta kara zama kore shar ta hanyar dasa itatuwa. Xi wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na sojan kasar, ya bayyana hakan...
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da nadin Dr. Mohammed Hassan a matsayin Darakta Janar na farko na Hukumar Fasahar Sadarwa da inganta Tattalin Arzikin ta fasahar zamani ta Jihar Jigawa. Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar a Dutse. Kafin nadin...
Gwamnatin jihar Kwara ta kaddamar da wani shiri na sauya fasalin noma domin habbaka kiwon dabbobi da bunƙasa yankunan karkara a fadin jihar. Jami’in shiri na musamman kan harkar noma wato Special Agro Industrial Processing Zone (SAPZ) a turance, Dr. Busari Isiaka ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya ce wannan shiri ne da...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Cibiyar yaƙi da ta’addanci ta ƙasa (NCTC) ta miƙa tsohon Darakta-Janar na masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Birgediya Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya) ga mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (NSA), Nuhu Ribadu. Tsiga, wanda aka kuɓutar bayan ya kwashe kwanaki 56 a tsare, a ranar Laraba an miƙa shi ne tare...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana yau Alhamis cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta gyara kuskuren da ta yi na kakaba “harajin ramuwar gayya,” kana ta magance sabanin dake tsakaninta da kasar Sin da sauran kasashen duniya dangane da tattalin arziki da cinikayya, ta hanyar yin shawarwari bisa daidaito,...
Mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha ya gargadi Amurka da cewa. duk wani harin soji a kan cibiyoyin nukiliyar Iran zai haifar da “mummunan sakamako” ga daukacin yankin. Sergei Ryabkov ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da wata mujallar harkokin kasa da kasa, bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi...
Shugaban kasar Burundi ya yi gargadin cewa Rwanda na da shirin kai wa kasarsa hari, bayan da sojojin Burundi suka taimakawa Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC) a yakin da take yi da ‘yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda. Shugaban kasar ta Burundi Evariste Ndayishimiye ya bayyana cewa, ya samu “sahihan bayanan sirri” da...
Dakarun Yaman sun sanar da mayar da martani kan harin baya-bayan nan da Amurka ta kai kan kasarsu, wanda ya hada da hare-hare ta sama har sau 36 a yankuna da dama a cikin gundumomin Sanaa, Sa’ada, da wasu jahohin kasar, wanda ya yi sanadin mutuwa da jikkatar mutane da dama. Kakakin Rundunar sojin Yaman...
Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawa a Gaza sun ketare dukkanin iyakokin kasa da kasa, tare da yin kira da a kawo karshen kashe-kashen mata da kananan yara da makamai masu guba, da yunwa, kishirwa, da cututtuka. A cewar jaridar Arabi 21, kungiyar malaman...
Aljeriya ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya domin tattauna halin da Falasdinu ke ciki. Bayan karuwar laifuffukan da yahudawan sahyoniyawa da suke aikatawa a kisan gillar da suke yiwa Palastinawa a yankin zirin Gaza da kuma ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri da sojojin yahudawan sahyoniya suka...
Ya ce, “Akwai rahoton cewa Turji ya shirya zai ziyarci yankin Gabashin Gatawa domin gudanar da bukukuwan Sallah, amma matakin da jama’a suka dauka na sanar da jami’an tsaro ya dakatar da shi ga hakan. “Wannan na iya zama dalilin da ya sa Bello Turji ya huce fushinsa a kan manoman da ba su...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama...
A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani da Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr....
Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka...
Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a...
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka. “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin...
A jiya Laraba 2 ga wata, rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan, wanda ya kasance matakin da aka dauka dangane da kalamai na shirme da jagoran yankin Taiwan, Lai Ching-te ya...
Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna...
Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba. INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar...
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a...
Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta...
Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na...

HKI Ta Sha Mamaki Da Ganin Sunanta A Cikin Jerin Kasashen Da Amurka Ta Karawa Kudaden Fito Na Kayakin Da Ke Shiga Amurka
Gwamnatin HKI ta sha mamaki da ganin gwamnatin shugaba Trumo na kasar Amurka ta sanya mata harajin shigowar kayakin HK zuwa kasar Amurka, a yayinda, kafin haka ta bada sanarwan cire dukkan kudaden fito ko haraji ga kayakin Amurka da ke shigowa HK. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta majiyar kafafen yada labarum...
Akalla mutane 2 ne suka rasa rayukansu a sabbin hare-haren da jiragen Amurka suka kai kan kasar Yemen a jiya Laraba da yamma, saboda hanata tallafin da take bawa falasdinawa a Gaza wadanda sojojin HKI sukewa kissan kare dangi a gaza. Tare da hana abinci shigowa yankin kimani watanni 2 da suka gabata. Tashar talabijin...
Sojojin HKI sun kashe akalla mutane 80 a asbitin Jabaliya a safiyar yau Alhamis, sannan sji ne hari mafi muni da ta kai kan gaza tun bayan da ta sake komawa yakin tufanul Aksa, makonni biyu da suka gabata. Asbitin hukumar UNRWA ta MDD na daga cikin wuraren da yahudawan suka kai hare-hare a garin...
Harajin kan motocin da ake shigo da su Amurka daga ƙasashen waje zai kai 25, wanda zai fara aiki daga ƙarfe 12 na daren ranar Laraba. Shugaba Trump ya ce matakin na nufin kare tattalin arziƙin Amurka da muradun ‘yan ƙasarta. Ana sa ran ƙasashe kamar Tarayyar Turai, China, Japan, da Koriya ta Kudu za...
Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar...
Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja. Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu...
Wakilan kungiyar tarayyar Afirka sun isa birnin Juba na kasar Sudan ta Kudu, a kokarin da suke yi na shiga tsakanin hana komawa yakin basasa. Tarayyar Afirkan ta fara kokarin shiga tsakani ne, bayan daurin talala da aka yi wa mataimakin shugaban kasa Riek Machar a gidansa,lamarin da ya sake jefa kasar cikin zaman dar-dar....
Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta sake jaddada azamarta ta bibiyar HKI a kotun duniya ta manyan laifuka akan laifukan kisan kiyashi da ta aikata a Gaza. Gwamnatin ta Afirka ta kudu, ta kuma yi watsi da duk wani matsin lamba da Amurka yake yi ma ta domin tilasta ma ta, ta ja da baya. Ministan...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa....
Da marecen jiya Laraba jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-hare akan biranen Damascus, Hums, Dar’ada Humah. Tashar Talabijin din ‘almayadin’ wai watsa shirye-shiryenta daga kasar Lebanon ta bayyana cewa; An kai harin ne akan wata cibiyar bincike a yankin Barzah dake arewacin birnin Damascus. Wata majiyar asibiti ta shaida wa tashar talabijin din...
Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk wanda ya kai shekara 40 ko sama da haka, zai iya tuna irin tarbiyyar da ya samu daga iyayensa a baya, da kuma yadda alaƙar da ke tsakanin yara da iyaye ta ke cike da girmamawa, kulawa, da soyayya. A yau, abubuwa sun canza sosai. NAJERIYA A...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanin kowa ne, ciniki mai inganci na bukatar kasuwa mai ‘yanci, da takarar da ake yi cikin daidaito, gami da manufa mai dorewa. Idan kasar Amurka ta ki samar da wadannan abubuwa, to, babu wani abun da za a yi, in ban da mai da kasar saniyar ware, da kara tabbatar da hadin kai tare...
Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su. Ya kara da cewa, masu garkuwa da...
Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato...
A ranar Talata ne, Allah ya yi wa Alhaji Abbas Sanusi, Galadiman Kano kuma babban mai nada sarki a masarautar Kano rasuwa. A safiyar Laraba, 2 ga watan Afrilun 2025 aka yi jana’izar sarkin wanda ya shafe fiye da shekaru 60 yana hidimtawa masarauta, ya rasu yana da shekara 92 bayan doguwar jinya. Ya bar...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar...
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya fitar, ya bayyana marigayin a matsayin babban ginshikin masarauta kuma mai neman ci gabanta. Shugaba Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Kano da majalisar masarautar Kano da kuma iyalan marigayin bisa wannan rashi mara misaltuwa. Shugaban ya yi...
Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da...
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin...
Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in...