An kama gungun masu yi wa Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura
Published: 28th, January 2025 GMT
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna.
Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare.
Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja.
Igweh ya bayyana sunayen ababen zargin da ke hannu da suka haɗa da Shamsudden Yunusa mai shekara 30 da Zahraddeen Saidu mai shekara 25 sai kuma Mustapha Haruna mai shekara 22.
Ya bayyana cewa sun samu jimillar babura 22 a hannun ababen zargin da kuma tarin mukullai da wayoyin hannu.
Ya yi ƙarin haske da cewa ababen zargin sun ƙware wajen sauya fasalin babura da aka sato suna bayar da haya ko sayar wa miyagu ciki har da mayaƙan Boko Haram da suka yi sansani a jihohin Neja da Kaduna.
Ya ƙara da cewa, jagora a cikin ababen zargin—Shamsudden—ya bayyana cewa ya kan sayar da duk babur ɗaya kan farashin Naira dubu 200 zuwa 250.
“Ya faɗa mana cewa a kwanan nan ya karɓi kafin alƙalami har Naira dubu 250 a hannun wani mai suna Ibrahim Kabiru da ke zaune a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari domin kawo masa babura ƙirar Bajaj.
“Shi kuma Zahraddeen shi ne mai jigilar kai babu ga masu saye, inda ya shaida mana cewa ko a kwanan nan ya kai wasu babura da ya karɓo a hannun wani mai suna Mustapha a garin Suleja.
“Shi kuma Mustapha ya ƙware wajen sauya fasalin babura da yi musu gyare-gyare gabanin a sayar wa abokan hulɗarsu,” in ji Igweh.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Babura Boko Haram Jihar Kaduna Jihar Neja ababen zargin
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kaduna za ta ɗauki ma’aikatan lafiya 1,800 aiki
Gwamnatin Jihar Kaduna, ta sanar da shirin ɗaukar ma’aikatan lafiya 1,800 aiki don inganta tsarin Kiwon Lafiya a Matakin Farko (PHC) a faɗin jihar.
Wannan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin ma’aikata da kuma inganta ayyukan kiwon lafiya a jihar.
Ƙungiyar JNI ta raba wa marayu 50 kayan Sallah a Borno An sake harbe wani ƙasurgumin ɗan bindiga a ZamfaraKamar yadda Kwamishiniyar Lafiya, Hajiya Umma Ahmad, ta bayyana, wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da yara.
“Wannan mataki zai cike giɓin da ake da shi a cibiyoyin lafiya, domin tabbatar da samun ingantaccen kiwon lafiya ga al’ummar Kaduna,” in ji ta.
Gwamnatin jihar ta fara gyara cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko guda 255 tare da samar da kayan aiki na zamani da magunguna.
Wannan zai bayar da damar kula da cututtuka kamar su ciwon suga, hawan jini, da kuma bayar da agajin gaggawa ga mata masu naƙuda.
“Ingantaccen kiwon lafiya ba gata ba ne, haƙƙi ne,” in ji Hajiya Umma, yayin da ta ke jadadda ƙudirin gwamnatin jihar kan kiwon lafiya.