An dakatar da Max Air na tsawon wata 3 bayan hatsari a Kano
Published: 29th, January 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya, ta dakatar da zirga-zirgar jiragen Max Air na tsawon wata uku, bayan ɗaya daga cikin jiragen kamfanin, tayarsa ta yi bindiga yayin sauka a filin jirgin saman Malam Aminu Kano a daren ranar Talata.
Jirgin Max Air ƙirar Boeing 734 mai lamba 5N-MBD ne ya samu matsalar kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Dukkanin fasinjoji 53 da ke cikin jirgin sun kuɓuta cikin ƙoshin lafiya.
Wannan shi ne karo na uku da jirgin Max Air ke fuskantar matsala cikin watanni uku da suka gabata.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasa (NCAA), ta sanar da dakatarwar domin bai wa kamfanin damar sake duba yanayin aikinsa, yayin da Hukumar Binciken Haɗuran Jiragen Sama (NSIB), ta fara bincike kan lamarin.
Daraktan Harkokin Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na NCAA, Michael Achimugu, ya yi ƙarin haske kan lamarin.
Ya ce, “Za mu iya gano musababbin wannan hatsari ne kawai bayan binciken NSIB, amma dole ne mu ɗauki matakan kariya don tabbatar da tsaro.”
Ya ƙara da cewa, “A lokacin dakatarwar watanni uku, NCAA za ta gudanar da cikakken bincike kan tsaro da kuma ƙarfin tattalin arziƙin Max Air.
“Kamfanin jirgin zai iya ci gaba da zirga-zirga ne kawai idan ya cika dukkanin sharuɗan da ake buƙata.”
NCAA ta nemi afuwar fasinjojin da wannan mataki zai shafa, amma ta jaddada cewa lafiyar fasinjoji ita ce abin da yafi muhimmanci a wajenta.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ababen fashewa dakatarwa fashewa Hatsari Jiragen sama Taya
এছাড়াও পড়ুন:
Kano Pillars Ta Koma Ta 4 A Teburin Firimiyar Nijeriya
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar ƙwallon ƙafa a Nijeriya.
Kano Pillars Ta Dakatar Da Kocinta Na Tsawon Makonni Uku Me Dakatarwar Da Pillars Ta Yi Wa Usman Abdalla Ke Nufi?Rabiu Ali da Jerry Alex ne su ka jefa wa Pillars ƙwallayensu biyu a wasan, da wannan sakamakon Sai Masu Gida su ka koma matsayi na 4 akan teburin gasar Firimiyar Nijeriya.
Ƙungiyar ta Kano ta dakatar da kocinta Usman Abdallah, inda mataimakinsa Ahmed Garba Yaro Yaro ya jagorance ta a wasanni uku na baya bayan nan.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp