2025-04-29@19:37:00 GMT
إجمالي نتائج البحث: 3277

«Ababen fashewa»:

    Aƙalla wasu mutum 10 mafarauta sun rasa rayukansu yayin aikin ceto a ƙauyen Kopire da ke Ƙaramar Hukumar Hong ta Jihar Adamawa. Shugaban ƙungiyar mafarautan Nijeriya reshen Arewa maso Gabas, Shawulu Yohanna ne ya tabbatar wa Aminiya hakan a ranar Talata. Wani abin fashewa ya kashe mutum 26 a Borno An dawo da wutar lantarki...
    Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ya bayyana kalaman gwamnatin ‘yan sahayoniyya a matsayin wani rudu da ba shi da amfani da har zai yi tasiri a zaman tattaunawan Iran da Amurka Wanda ba na kai tsaye ba, yana mai cewa duk wani hari ko da karami ne za a kai kan Iran zai zama tamkar tartsatsin...
    Gwamnan lardin Hormozgan (mai hedikwata a Bandar Abbas), Mohammad Ashouri, ya ce wani bangare na lamarin tashar jiragen ruwa na Shahid Raja’i ya faru ne sakamakon keta sanarwar adana kayayyaki ne, wani bangaren kuma na da alaka da sakaci da rashin kulawa (a wajen ajiya). AShouri, wanda ya bayyana ta hanyar faifan bidiyo a wata...
    Jaridar The Guardian ta Buga Labarin Cewa: Gidajen yarin Girka sun cika makil da ‘yan gudun hijirar Sudan Jaridar The Guardian ta kasar Britaniya ta ruwaito cewa: Mahukuntan kasar Girka na tsare da daruruwan bakin haure ba bisa ka’ida ba a karkashin wata doka mai tsauri da ta fara aiki a shekara ta 2014 kuma...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Aisha Shehu Mujaddadi a matsayin shugabar Hukumar Kula da Zuba Jari ta Jihar Jigawa (InvestJigawa). Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce “Aisha Mujaddadi ta samu digirinta na...
    Shi ma dayan, bayan ya bayyana cewa, sun kasance barayin mota ne a jihar Katsina amma wani abokinsu ya gayyace su zuwa jihar Filato domin ci gaba da sana’ar.    Yayin da ya amince zai jagoranci Tawagar Soji zuwa maboyarsu, jami’an sun gano bindiga kirar fistul daya da mukullai da suke amfani da su wajen...
    kauyuka a China, ana nufin yankunan da suka bunkasa, wadanda suka kasance, sun yi kamance-ceniya da sun anguwanin GRA a Nijeriya da kuma a nahiyar Afirka.   A yankin na Hero Bay, an tanadar da tituna inganciyyar wutar lantarki, tsaftatattacen ruwan sha da kuma kafar Inernet   Akwai manyan bene masu tsawo a yankin, wadanda...
    Wani abin fashewa da ake zargin bam ne ya kashe aƙalla mutum 26, ciki har da mata da yara a kan hanyar Rann zuwa Gamboru Ngala da ke Jihar Borno. Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Litinin a lokacin da motoci suka tayar da bama-baman da aka ɗana a gefen hanyar, da ya rutsa...
    Wani saurayi ya wallafa wani labarinsa a kafar sada zumunta ta Reddit tare da yin nadama, inda ya ce matar da suke soyayya ta faɗa masa cewa, an haife ta ne a shekarar 1998, har sai da ya duba bayanan fasfo dinta. A wani lamari mai ban al’ajabi da ban tsoro, matashin ɗan shekara 26...
    Sauran mambobin kwamitin sun hada da wakilan kungiyar ma’aikatan sufurin mota ta kasa (NURTW), kungiyar makarantar tuki ta Nijeriya (DSAN), kungiyar direbobi mata (FDA), kungiyar masu motocin dakon kayayyakin da ake shigo da su ta ruwa (AMATO) da kuma mambobin kungiyar masu binciken tuki ta Nijeriya (IDIN).   Da yake jawabi a wajen kaddamar da...
    Wannan ya sa wasan yau zai zama mai ɗaukar hankali, domin kowanne daga cikinsu na burin ɗaukar kofin a karo na farko, domin a dakatar da yawan dariyar da ‘yan adawa ke musu. A zagayen rukuni da suka haɗu a farkon wannan kakar, Arsenal ta lallasa PSG da ci 2-0. Kocin Arsenal yanzu, Mikel Arteta,...
    Wata koutun soja ta yanke wa wani jami’inta hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samun sa da laifn kashe buduwarsa. Kotun da ta zauna a Hedikwatar Runduna ta 82 da ke Enugu, ta yanke wa Private Adamu Mohammed hukuncin kisa kan laifin budurwar taas mai suna Hauwa Ali. Da yake sanar da hukuncin, Shugaban kotun,...
    A nasa ɓangaren, mai bai wa Gwamnan Shawara Kan Al’ammuran Tsaro, Janar Dahiru Abdusalam (Mai Ritaya), ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar tana ɗaukar matakai tare da jami’an tsaro don samar da tsaro mai inganci. Ya kuma bayyana cewa duk da matsalolin tsaro da ake fuskanta a hanyar Damaturu zuwa Gujba, jami’an tsaro na ƙoƙarin...
    “Lokacin da abubuwa suka fara lalacewa a lokacin shugaba Buhari, na fito na faɗi gaskiya. Lokacin da tsarin sauya fasalin Naira ya jefa jama’a cikin wahala, na ƙalubalanci gwamnati duk da cewa jam’iyyar APC ce ke kan mulki. Na fi biyayya ga Nijeriya fiye da kowane mutum,” in ji shi. El-Rufai ya ƙaryata jita-jitar cewa...
    Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun kashe masu zaman makoki bakwai tare da jikkata wasu a ƙauyen Kopl da ke Ƙaramar Hukumar Chibok ta Jihar Borno. Shugaban Karamar Hukumar, Honorabul Modu Mustapha, ya ce mayaƙan sun buɗe wa mutanen wuta ne a yammacin ranar Litinin, a yayin da suke shirin gudanar da addu’o’i ga ’yan uwansu...
    Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda. An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su. ‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike. Kwamishinan...
    Haka kuma ya nemi kotu da ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsoffin takardun kuɗi na Naira 200, 500 da  kuma 1000. Baya ga haka, ya buƙaci a umarci su da su nemi gafara ta hanyar wallafa bayani a manyan jaridu biyu na ƙasa. Amma a zaman kotu na ranar Litinin, wanda...
    An fara kasuwar baje koli na kayakin kasuwancin da ake samarwa a cikin Iran ko IRAN EXPO 2025, karo na 3 a nan Tehran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kasuwar baje koli na Iran EXPO 2025 zai jawa masu zuna jari daga kasashen Afirka. Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas...
    Wakilin falasdinawa a kutun kasa da kasa ta ICJ da ke birnin Haque na kasar Nerthelands yace HKI tana amfani da hana kayakin agaji daga ciki har da abinci shiga gaza a matsayin makami kan Falasdinawa don kashesu. Tashar talabijib ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Ammar Hijazi jakadan kasar Faladinu a cibiyoyin MDD...
    Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata. Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an...
    Shugaban  kungiyar hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Na’imKasim ya bayyana cewa, kungiyarsa tare da Sojojin kasar da kuma mutanen kasar ne zasu tabbatar da ci gaban kasar Lebanon a wannan halin da ake ciki. Tashar talabijin ta Al-Mayadeen ta nakalto sheikh Na’im kasim yana fadar haka a wani jawabin da ya gabatar a jiya Litinin,...
    Wasu abubuwan fashewa da ake zargin ’yan ta’addan Boko Haram ne suka dasa, sun kashe kimanin mutane 26, ciki har da mata da ƙananan yara a kusa da garin Rann da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge ta Jihar Borno. Majiyoyin tsaro da na cikin gari sun bayyana cewa mutane da dama sun jikkata bayan da...
    Shugaban Putin Na Rasha Ya Bada Sanarwan Tsagaita Wuta Da Ukraine Na Bangaren Guda kuma na sa’o’ii 72 ko kwanaki 3, daga 8-10 na watan Mayu mai zuwa. Jaridar Daily Trust ta Najeriya nakalto jakadan kasar Rasha a Abuja yana fadar haka a wani taro baje kolin hotinan yaki Rasah da Nazi a dai dai...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rahotanni suna nuna cewa farashin shinkafa, ɗaya daga cikin nau’ukan abincin da ’yan Najeriya suka fi ci, ya karye a wasu sassan ƙasar. Sauyin farashin ya sa ana tambayoyi — shin me ya haifar da wannan sauyi? Kuma me hakan ke iya haifarwa a rayuwar talaka? NAJERIYA A...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai a Jihar Kebbi ta bayyana cewa ta kammala dukkan shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a Ƙasa Mai Tsarki. Amirul Hajji na jihar na shekarar 2025 kuma Sarkin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad Mera, ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a lokacin taron farko da aka gudanar a hedkwatar...
    Bari mu dauki dala a matsayin misali, tattalin arzikin Amurka na dogara ne kacokan da girman dalar Amurka. Yayin da kasafin kudinta ke gazawa wajen biyan bukatunta na cikin gida, kuma tana da al’adar dogaro da kasashen waje kan kudaden da take kashewa da ke da alaka da jingina gazawar mulkinta ga sauran kasashen duniya,...
    Bankin Duniya ya yi hasashen cewa adadin waɗanda talauci ya yi wa katutu a Nijeriya zai ƙaru zuwa kaso 3.6 cikin ɗari a 2027. Wannan dai na ƙunshe ne cikin wani rahoto da Bankin Duniya ya fitar game da tattalin arziki da kuma yanayin tsadar rayuwa a Nijeriya. Ɗaukewar wutar lantarki ta tsayar da al’amura...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau Litinin cewa, babu wata tattaunawa da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin kasashen Sin da Amurka a baya-baya nan, haka kuma bangarorin biyu ba su cimma wata yarjejeniya ko su tuntubi juna game da batun haraji ba. (Fa’iza Mustapha)   Daga...
    Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kwara ta fara yi wa maniyyata rigakafin cututtuka kafin gudanar da aikin Hajji na shekarar 2025. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin rigakafin da aka gudanar a harabar hukumar da ke Ilori, shugaban hukumar, Alhaji Abdulsalam Abdulkadir, ya bayyana rigakafin a matsayin wani sharadi da ya zamto...
      Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, ya amince da nadin Mai Martaba Sarkin Kazaure, Alhaji Dr Najib Hussaini Adamu, a matsayin Amirul Hajj na Jihar Jigawa, kuma shugaban tawagar Gwamnatin jihar domin gudanar da aikin Hajjin 2025. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya sanya...
    Shugaban kasar Iran ya nuna murnarsa da yin maraba lalai da masu zuba hannun jari daga kasashen waje a Iran Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana Iran a matsayin dandalin da ta dace wajen zuba hannun jari da gudanar da harkar kasuwanci, yana maraba da masu zuba hannun jari na kasashen waje da ‘yan...
    Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Duk wani harin wuce gona da iri kan Iran zai fuskanci mayar da martani daidai da shi cikin gaggawa Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya tabbatar da cewa Iran na da kwarin gwiwa kan iya dakile duk wani yunkuri da wasu bangarorin ke yi na kawo cikas...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Ci gaba da killace Gaza da kuma kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, laifi ne da ba a taba yin irinsa ba a tarihin dan Adam A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Masar Badar Abdel Ati a yammacin jiya Lahadin...
    Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada wajabcin komawa kan Shirin tsagaita bude wuta a Gaza Wakiliyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na musamman ta jaddada a yau Litinin cewa: Akwai tsananin bukatar komawa ga Shirin tsagaita bude wuta a Gaza. A lokacin da take ba da shaida a zaman kotun kasa da kasa kan wajabcin da...
    Tawagar jami’ai da ‘yan kasuwan kasar Tunisiya ta gana da mataimakin shugaban kasar Iran A yayin ganawarsa da ministan kasuwanci da fitar da kayayyaki na kasar Tunisiya Samir Ben Salem Obeid, mataimakin shugaban kasar Iran na farko na Jamhuriyar Musulunci ta Iran Mohammad Reza Aref ya jaddada cewa: Lokaci ya yi da za a dauki...
    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, ya bayyana cewa sauyin jam’iyyar da manyan ‘yan suke yi zuwa jam’iyyar APC ana kamba ma shi fiye da yadda ya kamata, yana cewa wannan sauyin ba zai shafi kokarinsa na neman mafita ga matsalolin Nijeriya ba. Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai a Kano yau...
      Bikin baje kolin na wannan karo da ake gudanarwa a birnin Guangzhou dake kudancin kasar Sin daga ranar 15 ga watan Afrilu zuwa ranar 5 ga watan Mayu, an shirya shi ne cikin matakai uku. Matakin farko ya mayar da hankali ne kan masana’antu masu ci gaba, na biyu a kan ingantattun kayayyakin gida,...
    Kazalika, domin daidaita ci gaban cinikayyar waje, manufofin da za a aiwatar sun hada da na tallafawa kamfanonin dake fitar da hajoji, ta yadda za su rage hadurra daka iya aukuwa, da fadada fitar da hidimomin da ake samarwa ga karin sassan duniya, da karfafa gwiwar kamfanonin waje, ta yadda za su kara zuba jarinsu...
    Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Muhammad Sa’ad, ya bayyana cewa gobe Talata, 30 ga watan Afrilun 2025, ita ce za ta kasance 1 ga watan Zhul Qi’ida na shekarar 1446 ta Hijiriyya. Wata sanarwa da shugaban kwamatin ganin wata na fadar, Farfesa Sambo Wali ya fitar ta ce an ɗauki matakin ne saboda ba a ga...
    A wannan yanayi na matsin tattalin arziki a Nijeriya, mata na gasar neman haihuwar ’yan uku domin cin gajiyar tallafin tsabar kuɗi da abinci da tufafi da ragunan suna a Jihar Sakkwato. Burin wadannan mata ta karu ne sakamakon yadda farin ciki nau’i uku ya lullube Malama Bela’u Sabo da iyalanta, bayan da ta haifi...
    Gwamnatin tarayya ta umarci hukumar shirya jarrabawar WAEC da NECO da su fara amfani da cikakken tsarin amfani da Komfuta (CBT) ga dukkan jarabawar su nan da shekarar 2026. Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ne ya bayar da wannan umarnin a ranar Litinin yayin ziyara da kuma duba yadda ake gudanar da gwaje-gwaje na CBT...
    Fadar Kremlin ta kasar Rasha ta ayyana tsagaita wuta na kwana biyu ita kaɗai a yakinta da kasar Ukraine. Shugaba Vladimir Putin ya sanar a ranar Litinin cewa Rasha za ta aiwatar da tsagaita wutar ne daga tsakar dare na 8 ga Mayu zuwa tsakar dare na 10 ga Mayu. A ranakun da za a...
    Wani wanda ake zargi da safarar sassan jikin ɗan Adam ya shaida wa jami’an tsaro cewa ya shafe sama da shekara 10 yana sayar da sassan jikin mutum don samun kuɗi. Dubun mutumin sun cika ne a ranar Asabar din da ta gabata inda sojoji suka kama shi a yankin Kulanla Odomoola da ke Jihar...
    A cewarsa, tuni aka shirya wuraren kwana da abinci ga maniyyatan a kasar Saudiyya.   Abdulkadir ya tabbatar da cewa, ana shirye-shirye, inda za a yi alluran rigakafi a ranar 28 ga Afrilu, za a raba tufafi a 30 ga Afrilu, sannan kuma za a raba jakunkuna a ranar 1 ga Mayu.   Ya kara...
    Jagoran juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae, a karon farko da yayi magana dangane da fashewar tashar jiragen ruwa na Shahida Rajae ya gabatar da Ta’ziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu ko suka jikata a wannan hatsarin. Ya kuma bukaci a gudanar da bincike mai mai zurfi don gano musabbabin fashewar. Kamfanin...
    Mutane da dama daga nahiyar Afirka ne suke cikin mutane kimani 50 wadanda suka rasa rayukansu sanadiyyar hare-haren da jiragen yakin Amurka suka kai kan wani gidan kaso a lardin Sa’ada na kasar Yemen. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kamfanin dillancin labaran Al-Masirah yana cewa makaman Amurka sun fada kan wani...
    Shugaban Palasdinu da kuma kungiyar kwatar yencin falasdinawa PLO Mahmud Abbas ya nada magajinsa da kuma wasu mataimaka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran, ta bayyana cewa Abbas dan shekara 89 ya nada mataimakinsa ne bayan taron majalisar gudanarwa ta gwamnatinsa  a makon da ya gabata. Labarin ya kara da cewa kasashen yamma da...
    Shugaban kasar Siriya ya ki amincewa da bukatar kurdawan kasar daga dakarun Democradiyyan  kurdawa wato (SDF), na samar da tsarin tarayya a kasar bayan kifar da gwanatin Basshar Al-Asab. Jaridar The Nation ta nakalto shuga Al-Ahmad Sharaa yana fadar haka a jiya Lahadi ya kuma kara da cewa tsarin tarayyar barazana ce ga hadin kan...
    Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a...
    A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.   “Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa....