Sharhin Bayan Labarai: Masar Ta Ki Amincewa Da Komarwa Falasdinawan Gaza Zuwa Kasarsa
Published: 29th, January 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da rashin amincewar kasashen masar da Jordan kan maida Falasdnawa cikin kasashensu wanda ni tahir amin zan karanta.
A makon da ya gabata ne shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kafafen yada labarai a lokacinda yake cikin jirgin fadar shugaban kasa ko ‘Air Force 1, kan cewa yana duba yiyuwar kwasar Falasnidawa a Gaza zuwa kasar Masar sannan sauran falasdinawa a yankin yamma da kogin Jordan da kuma sauran wurare a kasar Falasdinu da aka mamaye zuwa kasar Jordan.
Wannan zancen dai ba sabuwa bace, a rikicin gabas ta tsakiya, shuwagabanin Amurka a baya, sun yi wannan maganar amma bata yuba.
A halin yanzun babu wata kasa, ya zuwa yanzu a duniya, wacce take goyon bayan ra’ayin shugaba Trump a kan wannan tunanin.
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi a wani jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa kasarsa ba zata taba amincewa da kaurar Falasdinawa zuwa kasarsa ba, don yin haka zalunci ne a fili, banda haka hatsari ne ga kasar masar kanta.
Gwamnatin kasar Jordan ma ta ki amincewa da hakan, banda haka rikicin gabas ta tsakiya ta zama rikici ne wanda yake girgiza dangantaka tsakanin kasashen yankin da ma, tsakanin sauran kasashen duniya. Har iyala yau rikicin zai tama dokokin kasa da kasa kan al-amura da dama. Daga cikin har da dokokin kasa da kasa, wadanda suka yi magana dangane da yencin zama dan wata kasa, da kuma yadda kasashen duniya suke daukar mutane a tsakaninsu.
A halin yanzu miliyoyin Falasdinawa suna rayuwa a kasashen Jordan, Siriya da Lebanon da Masar, da ma wasu kasashe a duniya. Wadannan a saryar da hakkinsu na komawa kasarsu ta asali, a inda ba’a dauke su yan kasa ba. Suna rayuwa a sansanonin yan gudun hijira fiye da shekaru 76. Akwai wata al-umma wacce aka zalunta a doron kasa kamar Falasdinawa?.
Banda haka maida Falasdinawa zuwa kasashen Masar da Jordan, don tabbatarwa yahudawan sahyoniyya kasar Falasdinu, zai tabbatar da rashin adalcin gwamnatin Amurlka a fili. Duk da cewa tana ci gaba da zaluntar Falasniya tun da dadewa ta bayan fage sannan a zahri wasu lokuta. Sai dai a wannan fagen kowa a duniya sai ya fahinci hakan.
Banda haka wannan zai jawa matsalar yan gudun hijira a kasashe daban daban na duniya, misali yan gudun hijira na Rohinga, sai a ce dole su koma kasar Bagladesh don su musulmi ne, alhali su yan kasar Myanmar ne, al’adarsyu ta mutanen myan marne kuma harshensu harshen myan mar ne.
Daon haka wannan ra’ayin idan ya tabbata zai rikita al-amuran zamantakewa a kasashen duniya da dama, musamman inda ake da yan gudun hijira.
Shugaban Assisi a jawabinsa ya bayyana cewa, gwamnatin kasarsa tana ganin hanyar warware wannan matsalar itace samar da kasashe biyu a kasar Falasdinu, kuma zata taimaka don tabbatar da hakan.
Kasashen larabawa gaba daya, tun da dadewa sun fitar da batun zaman Falasdnbiawa a wasu kasashen larabawa ko kuma wani wuri daban, suna ganin dole ne a maidasu kasaru ko ba dade ko ba jima.
Sai dai dangane da samar da kasashe biyu wanda wasu kasashen larabawa suke ganin cewa itace hanya tilo wajen warware wannan matsalan. Da farko su yahudawan da suka mamaye kasar Falasdinu shekaru fiye da 70 da suka gabata basu amince da haka ba, banda haka suna ma neman kara kwace wasu kasashen larabawa makobta da su don kara yawan kasar da suka mamaye. Sannan Falasdinawa masu asalin kasa basu amince da haka. Sun ganin kasar Falasdinu ta Falasdinawa ne daga tekun medeteranin har zuwa gogin Jordan.
Don haka idan har wadanda ake magana a kansu gaba daya basu amince da haka ba, to ra’ayin samar da kasashen biyu a kan kasar Falasdinu da aka mamaye ma, tilastawa mutanen biyu abinda ba ra’ayinsu bane.
Yanzu dai sai mu jira mu gani abinda Trump zai yi don tabbatar da ra’ayinsa.
Masu sauraro karshen sharhin bayan labaran Kenan.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasashen larabawa yan gudun hijira kasar Falasdinu wasu kasashe
এছাড়াও পড়ুন:
Hajjin 2025: Sahun Farko Zai Tashi Zuwa Kasa Mai Tsarki 9 Ga Watan Mayu
Sahun farko na Alhazan Najeriya zai tashi zuwa kasa mai tsarki a ranar 9 ga watan Mayun 2025.
Hakan na kunshe ne a cikin bayanin bayan taro da Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON, ta yi da Shugabannin Hukomomin Kula da Jin Daɗin Alhazai na Jihohi a ranar 22 ga watan Afrilun 2025.
Manufar taron ita ce tantance matakin shirin da kowace Hukumar Alhazai ta Jiha ta kai.
Wata sanarwa da mataimakiyar daraktar watsa labarai ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, ta ce shugaban hukumar, Farfesa Abdullah Saleh Usman, ya tunatar da mahalarta taron cewa harkar Hajji na cikin matakin karshe na shirye-shirye kafin fara aikin Hajjin shekarar 2025.
Ya bukaci jihohi da su sanar da NAHCON matsayin da suka kai wajen samar da biza, rigakafi, sayen jakunkuna da sauran batutuwa da suka jibancu aikin hajji.
A yayin taron, Kwamishinan Ayyuka na NAHCON, Prince Anofiu Elegushi, ya bayyana cewa kamfanin Air Peace zai yi jigilar alhazai 5,128 daga jihohin Abia, Akwa Ibom, Anambra, Rundunar Sojoji, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Ekiti, Enugu, Imo, Kogi, Ondo, Rivers, da Taraba.
Yayin da kamfanin FlyNas zai dauki alhazai 12,506 daga Birnin Tarayya Abuja, Kebbi, Legas, Ogun, Osun, Sokoto da Zamfara. Kamfanin na FlyNas ya ware jirage tara domin gudanar da wannan aikin.
Sai kamfanin Max Air da zai dauki alhazai daga jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Kwara, Oyo da Filato.
Kamfanin na Max Air ya yi alkawarin kammala jigilar alhazai 15,203 zuwa ranar 24 ga Mayu, inda zai yi amfani da jirage biyu, jirgin B747 mai daukar mutum 400, da wani mai daukar mutum 560.
Haka zalika, kamfanin Umza zai yi jigilar alhazai 10,163 daga jihohin Kaduna, Adamawa, Nasarawa, Neja da Yobe. Shi kuma zai yi amfani da jiragin B747 mai daukar mutum 477 da B777 mai daukar mutum 310.
Wadanda kamfanonin jiragen sama 4 za su yi jigilar alhazan Hajjin 2025 su 43,000.
Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Labarai da Ayyukan Laburare (PRSILS), Farfesa Abubakar Yagawal, ya bayyana wa mahalarta taron irin shirin da hukumar ta yi dangane da samar da asibitoci a Makka da Madina, rabon kati na Yellow Card ga jihohi, tare da tunatar da su da su guji yi wa mata masu ciki rijistar aikin hajji.
Sanarwar ta kara da cewa yayin da aka cimma matsaya cewa ranar 9 ga Mayu za a fara tashi, ana kuma sa ran kammala jigilar a ranar 24 ga watan Mayu.
Har ila yau, sanarwar ta ce za a fara dawowa daga kasar mai tsarki a ranar 13 ga watan Yuni zuwa 2 ga watan Yuli, idan Allah ya yarda.
Safiyah Abdulkadir