2025-04-03@17:04:11 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2348

«wasu kasashe»:

    Wata gobara da ta tashi da yammacin ranar Alhamis ta lalata wani sashe na shahararren gidan Ado Bayero da ke ƙofar Nassarawa a Kano. Aminiya ta samu rahoton cewa lamarin ya faru ne a hawa na tara na ginin da cibiyar Jami’ar Northwest University take. Matafiya sun maƙale bayan ruftawar gada a Taraba Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Rahoton na cewa gobarar ta shafi wani sashe na sashen ilimin na’ura mai ƙwaƙwalwa na jami’ar. Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin jami’an kashe gobara amma abin ya ci tura domin an kasa samun jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kashe gobara, Saminu Yusif Abdullahi ta wayar salula zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.
    A kokarin magance matsalar karancin ruwan sha da garin Rano ke fuskanta na tsawon shekaru, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya umarci Ma’aikatar Albarkatun Ruwa da ta fara amfani  da  Madatsar Tiga don samar da ruwa mai a garin. Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya karɓi bakuncin Sarkin Rano, Ambasada Dr. Muhammad Isa Umar, wanda ya kai masa ziyarar gaisuwar Sallah a Fadar Gwamnati da ke Kano. Gwamna Yusuf ya yaba wa Sarkin Rano bisa jajircewarsa wajen kare muradun al’ummarsa, inda ya tabbatar masa da cewa gwamnati na daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar ruwa a garin. Ya bayyana cewa an riga an tsara shirin gina rijiyoyin burtsatse tare da hadin gwiwar ƙaramar...
    Masu ababen hawa da dama sun maƙale a gadar Namne da ta rufta daura da hanyar Jalingo zuwa Wukari a Ƙaramar hukumar Gassol ta Jihar Taraba sakamakon ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a da aka yi ranar Laraba. Ruwan sama ya kawar da gadar da aka gina ta wucin gadi a hanyar da aka yi ta taimakon kai don taimakawa matafiya a kan hanya. Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya kama da wuta a Legas Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato Gadar taimakon kai da aka gina a madadin babbar gadar da ta rufta watanni bakwai da suka gabata, ta kasance hanyar shiga ga masu ababen hawa da ke bin hanyar. Gwamnan Jihar Taraba, Agbu Kefas...
    Gwamna Umar Namadi ya amince da naɗin Dr. Jummai Ali Kazaure a matsayin sabuwar shugabar Kwalejin Ilimi, Shari’a da Nazarin Addinin Musulunci (JSCILS) da ke Ringim. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim, ya fitar. A cewarsa, kafin wannan naɗi, Dr. Jummai ta kasance malama a Kwalejin Ilimi ta Jihar Jigawa da ke Gumel. Tana da digiri na uku (Ph.D.) a fannin Gudanarwa da Tsare-tsare, tare da gogewa a harkar koyarwa daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. “Dr. Jummai ta rike mukamai da suka gada da Darakta a Makarantar Sakandaren gwamnati ta ‘yan mata da ke Kazaure da kuma Darakta a Makarantar Sakandare ta larabci da ke Babura. Mace ce...
    “A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka.   “Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkun kayan aiki da sabbin fasahohin haƙar ma’adinai don tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci. “Lokacin da ya je masana’antar, Gwamna Lawal ya zagaya wurare da dama, inda ya fara tun daga magudanar ruwa da zuwa duka sassan injina da kayan aiki.   “Gwamna Lawal ya kuma ziyarci wurare daban-daban a cikin masana’antar, ciki har da gidan wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga ɗaukacin kamfanin,...
    A jiya Laraba 2 ga wata, rundunar sojojin ‘yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar, ta kaddamar da wani atisayen soji mai taken “Strait Thunder-2025A”, a yankunan tsakiya da kudancin zirin Taiwan, wanda ya kasance matakin da aka dauka dangane da kalamai na shirme da jagoran yankin Taiwan, Lai Ching-te ya furta a kwanakin baya, da ma yunkurin jam’iyyar DPP da ke karkashin jagorancinsa na neman ‘yancin kan yankin Taiwan. Duk da haka, wasu ‘yan tsirarrun kasashen yamma da ma kungiyoyi sun sake fitowa suna kara wa miya gishiri a kan batun, inda suka ce wai suna kin amincewa da daukar matakin kashin kai na canza yanayin da ake ciki a zirin tekun Taiwan. To, bari...
    An shiga firgici da safiyar Alhamis  ɗin nan, bayan wani kwale-kwale na kamfanin Lagos Ferry Services (LAGFERRY) ya kama da wuta a tashar jirgin ruwa ta Ipakodo da ke Ikorodu, a Legas inda mutane da dama suka jikkata. Majiyoyi sun ce tashin wutar ta haifar da wata babbar gobara da ta tashi daga injin jirgin ruwan. Wutar ta bazu cikin masaukin fasinjoji da sauri ta kama wasu fasinjojin da ke ciki. Ruwan sama ya lalata aƙalla gidaje 70 a Filato INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye “Akwai wani babban abin fashewa daga ɓangaren injin jirgin wanda hakan ya haifar da gobara wadda ta laƙume jirgin. Majiyar ta ƙara da cewa, “har yanzu ba a san...
    Sama da gidaje 70 ne suka lalace da rumfuma a wata guguwa da ta yi ɓarna a unguwar Mabudi, Sabon Gida, da sauran unguwanni a ƙaramar hukumar Langtang ta Kudu a Jihar Filato. Wakilinmu ya ruwaito cewa, mamakon ruwan sama da aka yi a daren Laraba, wanda ya biyo bayan ruwan sama, ya yi ɓarna matuƙa. INEC ta yi watsi da buƙatar yi wa Sanata Natasha kiranye Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang Mazauna yankin sun shaida wa wakilinmu cewa kimanin gidaje 70 ne rufinsu ya ɗaga, yayin da wasu gine-gine suka ruguje. Nanbol Nanzing, wani mazaunin ɗaya daga cikin unguwar da lamarin ya shafa, ya koka da yadda lamarin ya faru tare da...
    Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa takardar neman tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta tsakiya a Majalisar Dattawa, ba ta cika sharuɗɗan doka da kundin tsarin mulki ya tanada ba. INEC ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa takaitacciya da ta wallafa a shafinta na Facebook yau Alhamis, tana cewa: “Takardar neman tsige Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya ba ta cika sharuɗɗan da ke cikin sashi na 69(a) na kundin tsarin mulkin Nijeriya na 1999 ba.” INEC Ta Karɓi Takardun Yi Wa Sanata Natasha Akpoti Kiranye  Kotu Ta Dakatar Da INEC Karɓar Buƙatar Yin Kiranye Ga Senata Natasha Sai dai hukumar ta yi alƙawarin fitar da cikakken bayani kan wannan ci gaba nan ba da...
    Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana cewa buƙatar da wasu suka shigar don yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Mazaɓar Kogi ta Tsakiya kiranye, bai cika sharuɗa ba. INEC ta ce yunƙurin bai cika sharuɗan Sashe na 69(a) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya tanadar ba. Bello Turji ya kashe manoma 11 a wani sabon hari a Sakkwato  NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wannan sanarwa ta fito ne daga shafukan sada zumunta na INEC a ranar Alhamis, 3 ga watan Afrilu, 2025. Wasu ƙungiyoyi sun yi ƙoƙarin yi wa Sanata Natasha kiranye, wanda suka ce Sanatan na neman jefa su cikin rikicin da ka iya hana su samun romon dimokuraɗiyya. Ƙungiyoyin sun...
    Ƙasurgumin ɗan bindiga, Bello Turji, da mayaƙansa sun kai mummunan hari garin Lugu da ke Ƙaramar Hukumar Isa a Jihar Sakkwato, inda suka kashe manoma 11. Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne yayin da Turji ke dawowa daga wata ziyarar sallah da ya kai yankin. Najeriya ta yi kuskuren barin Boko Haram ta yi ƙarfi — Muftwang NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Wani mazaunin Isa, Basharu Altine Giyawa, ya ce, “Tun a ranar Asabar muka samu bayanai cewa Turji zai ziyarci Gatawa, kuma mun sanar da hukumomi. “Duk da haka, shi da mutanensa sun bi ta ƙauyukanmu, sun yi bikin sallah, sannan suka kashe manoma 11 a hanyarsu ta komawa Fakai.” Ɗan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku. Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na 0.5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensu, daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS). A cikin wata sanarwa haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da kudaden ne don tafiyar da al-amuran ƙungiyar. Harajin, wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani...
    Gwamnatin HKI ta sha mamaki da ganin gwamnatin shugaba Trumo na kasar Amurka ta sanya mata harajin shigowar kayakin HK zuwa kasar Amurka, a yayinda, kafin haka ta bada sanarwan cire dukkan kudaden fito ko haraji ga kayakin Amurka da ke shigowa HK. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta majiyar kafafen yada labarum HKI na fadar haka daga bakin wani jami’an gwamnatin kasar. Labarin ya kara da cewa, Amurka ta dorawa HKI kudaden fito na kasha 17% kacal, sai dai ba abinda take tsammani zai faruba, tsammaninta shi ne irin wanda ta yi wato babu kudaden fito. Gwamnatin Amurka dai ta rikita harkokin kasuwanci da dama a duniya saboda kudaden fito da ta karawa kusan kasashen duniya gaba...
    Jami’ar Bayero Ta Kaddamar da shirin amfani da adaidaita Sahu wajen zirga zirga a Jami’arA wani gagarumin yunkuri na bunkasa zirga zirga da walwalar dalibai, Shugaban Jami’ar Bayero Kano Farfesa Sagir Adamu Abbas, ya kaddamar da shirin amfani da babura masu kafa uku ko adaidaita a harabar jami’ar a hukumance. Wannan yunƙurin na nufin samar wa ɗalibai da ma’aikata hanyar sufuri mafi aminci, mafi dacewa, da sauƙaƙe ƙalubalen da ke tattare da zirga zirga tsakanin sassan jami’ar. Shugaban jami’ar wanda ya samu rakiyar magatakarda Haruna Aliyu da mataimakin shugaban jami’ar Farfesa Haruna Musa da shugaban dakin karatu na jami’ar Dr. Kabiru Dahiru Abbas da shugaban hulda da jama’a na jami’ar Lamara Garba da Farfesa Yakubu Magaji Azare, Shugaban jami’ar ya...
    Gwamna Caleb Mutfwang na Jihar Filato, ya yi gargaɗin cewa Najeriya ta yi kuskure a baya wajen barin Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ’yan bindiga har suka yi ƙarfi. Ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da ya kamata ta mallaki makamai ko ta samu ƙarfin guiwar ƙalubalantar hukumomin tsaro. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Da yake jawabi a Abuja yayin ƙaddamar da jiragen yaƙi marasa matuki da bama-baman da aka ƙera a Najeriya, wanda kamfanin Briech UAS ya samar, Mutfwang ya buƙaci haɗin gwiwa da kamfanonin fasahar tsaro na cikin gida. “Dole ne mu tabbatar da cewa babu wata ƙungiya da...
        Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Wani matashi mai shekaru 27, Rabiu Suleiman, ya daɓa wa abokinsa Yunusa Muazu wuƙa, tare da yi masa mummunan rauni, a kan budurwa a yankin Gwagwalada da ke Abuja. Lamarin ya faru ne a daren Talata a wani gidan kallon fina-finai a Unguwar Dodo. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi Suleiman ya zargi Muazu da yin soyayya da budurwarsa wadda yake shirin Jamila Yakubu. Faɗan ya fara ne lokacin da Suleiman ya samu Jamila da Muazu suna tattaunawa a gidan kallon fina-finan. Suleiman, ya fusata lokacin da ya ga Jamila tare da abokinsa, sai ya tafi kai-tsaye ya hau abokinsa da duka. A lokacin da suke...
    Asusun Bada Lamuni na Duniya (IMF), ya buƙaci Gwamnatin Najeriya da ta tabbatar da cewa manufofin tattalin arziƙin ƙasar sun kare muradun mutane masu rauni. Daraktar Hulɗa da Jama’a na IMF, Julie Kozack, ta bayyana hakan a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Washington, D.C. NAJERIYA A YAU: Ƙalubalen Da Iyaye Ke Fuskanta Wajen Tarbiyyar ‘Ya’yansu Uromi: Barau ya ziyarci iyalan waɗanda aka kashe, ya ba su kyautar N16m Ta jaddada muhimmancin bai wa talakawan Najeriya masu fama da ƙuncin rayuwa tallafin kuɗi sakamakon sauye-sauyen tattalin arziƙi. Aminiya ta ruwaito cewa cire tallafin man fetur, wanda IMF ta ba da shawara a kai, ya haifar da tashin farashin man fetur daga kimanin Naira 200 kan kowace lita zuwa...
    Rahotanni daga kasar Lebanon sun ce jiragen yakin HKI sun kai hari a garin “Naqura” dake kudancin Lebanon da safiyar yau Alhamis. Jiragen yakin na ‘yan sahayoniya sun kai harin ne har sau uku ajere akan wata tsohuwar cibiyar kiwon lafiya dake cikin garin, haka nan kuma akan wasu gudajen mutane da suke a kusa. Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani akan asarar rayuka sanadiyyar wadannan hare-haren na’yan sahayoniya. A shekaran jiya Talata ma dai sojojin na mamaya sun kai wa unguwar Dhahiya dake birnin Beirut hari wanda ya yi sanadiyyar shahadar mutane da dama da kuma jikkata wasu. Hari na shekaran  jiya shi ne irinsa na biyu a cikin unguwar Dhahiya tun bayan tsagaita wutar yaki. Haka nan...
    Yanzu da ya rasu, Hauwa ta ce ba ta da tabbas kan yadda za ta yi rayuwa da ‘ya’yanta. Lamarin mai tayar da hankali ya faru ne a ranar 27 ga watan Maris, lokacin da wasu matafiya 16 ‘yan asalin Arewacin Nijeriya suka faɗa tarkon wasu ‘yan sa-kai a Uromi, a Jihar Edo, inda suka kashe su. Wani rahoto na musamman da gidan talabijin na News Central TV, ya bayyana halin da Hauwa ke ciki, wanda ya nuna irin tasirin da wannan lamari ya haifar. Yanzu tana fuskantar babban ƙalubale na kula da ‘ya’yanta bakwai, tare da neman mafita game da rayuwa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    Wani makusancin dangin Janar tsiga, ya shaida wa Daily trust cewa, bayan sun karbi kudin, masu garkuwa da mutanen sun ajiye Tsiga har tsawon mako guda kafin su tuntubi iyalan shi, inda daga bisani suka hada Janar din da ‘yan uwanshi a waya domin tattaunawa da su.   Ya kara da cewa, masu garkuwa da mutanen sun bukaci a kara musu kudin fansa, amma hakan ba ta yi wu ba.   Wata majiya mai tushe ta sojoji ta kuma tabbatar da sakin Tsiga. Majiyoyi na kusa da dangin sun ce yana cikin koshin lafiya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na...
    Birgediya-Janar Maharazu Tsiga (mai ritaya), ya kuɓuta bayan shafe kwana 56 a hannun ’yan bindiga. An sace Janar Tsiga, wanda Tsohon Shugaban Hukumar NYSC ne, a garinsu da ke Ƙaramar Hukumar Bakori a Jihar Katsina, a ranar 5 ga watan Fabrairu, 2025. Mutum ɗaya ya rasu, 3 sun jikkata a rikicin ’yan sara-suka a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Hakazalika, aharan sun sace mutum tara a tare da shi a lokacin da suka kai harin. Duk da cewa iyalansa sun biya kuɗin fansa, ’yan bindigar sun ci gaba da tsare shi na tsawon makonni. Rahotanni sun nuna cewa har yanzu ba a san adadin kuɗin da aka biya a matsayin kuɗin fansar ba. Wasu sun ce Naira...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Babban daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa Rafael Grossi ya sanar da shirin kai ziyara birnin Tehran nan da makwanni masu zuwa a yayin da ake ci gaba da tattaunawa don tsaida takamaimen lokacin. Ziyarar ta zo ne a wani bangare na ci gaba da huldar diflomasiyya tsakanin Iran da hukumar IAEA, da nufin tinkarar batutuwan da suka shafi Nukiliya, da samar da hadin gwiwar fasaha cikin tsarin alkawurran da Iran ta dauka a karkashin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT). Ziyarar ta kuma jaddada irin hadin gwiwar da Tehran ke ci gaba da yi da hukumar ta IAEA, duk da matsin lamba daga waje da kuma zargin siyasa daga kasashen yammacin Turai. Da yake amsa...
    Wani rikici tsakanin matasan ƙungiyoyin Sara-Suka ya yi sanadin mutuwar mutum ɗaya tare da jikkata wasu uku a unguwar Yantifa da ke Jos ta Arewa, a Jihar Filato. Shaidu sun ce matasan sun far wa juna da makamai irin su adduna, wanda ya sa mazauna yankin tserewa don tsira da rayukansu. Tinubu ya yi ta’aziyyar rasuwar Galadiman Kano, Abbas Sanusi HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Rikicin ya ɓarke ne a dare ranar Talata, lamarin da ya jefa jama’a cikin fargaba. Lawan Chizo, wani jigo a ƙungiyar tsaro ta sa-kai, ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya bayyana cewa sojoji da jami’an tsaro sun shiga tsakani don kwantar da tarzomar. Ya ce rikicin ya haɗa da mambobin Sara-Suka daga...
    Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa sojojin kasar na karbe iko da wasu yankunan zirin Gaza, a wani mataki na kara matsin lamba kan kungiyar Hamas domin tilasta ta sakin mutanen da ta ke garkuwa da su. “Muna karbe zirin Gaza tare da kara matsin lamba mataki-mataki domin tilasta su mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su,”inji  Netanyahu a wani faifan bidiyo da ofishinsa ya fitar. Ya kara da cewa, Sojoji na karbe yankuna, suna kai farmaki kan ‘yan wadanda ya danganta da ‘yan ta’adda in ji shi, yana mai sanar da samar da wata sabuwar hanya karkashin ikon Isra’ila don raba garuruwan Khan Younis da Rafah (kudu). Tunda farko dama ministan tsaron Isra’ila Israel Katz ya...
    Kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa (ICC) mai hedkwata a birnin Hague ta yi Allah-wadai da matakin da kasar Hungary ta dauka na kin mutunta sammacin kame firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da zai ziyarci kasar da ke tsakiyar Turai a ranar Alhamis. Mai magana da yawun kotun, Fadi El Abdallah, ya fada yayin wani taron manema labarai cewa, bai kamata mambobin kotun ICC su yi watsi da hukuncin kotun ba. Kakakin ya ci gaba da cewa dole ne mambobin kotun su aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke. Ana sa ran Netanyahu zai isa Budapest a yammacin yau Laraba don ziyarar kwanaki hudu, bisa gayyatar Firaministan Hungary Viktor Orbán. Shugaban na Hangari mai tsatsauran ra’ayi ya gayyaci takwaransa...
    Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya nanata shirin Tehran na shiga tattaunawar da Amurka kan shirinta na nukiliya na zaman lafiya, yana mai gargadin cewa barazanar soji daga Amurka na dagula halin da ake ciki a yanzu. “Jamhuriyar Musulunci, kamar yadda ta kasance a baya, a shirye take don yin shawarwari na hakika,” in ji Araghchi a wata wayar tarho da takwaransa na Holland, Caspar Veldkamp, yau Laraba. Ya jaddada cewa wannan “yana bukatar yanayi mai kyau da kuma nisantar hanyoyin da suka shafi barazana.” Ministan ya yi Allah wadai da barazanar da jami’an Amurka suka yi wa Iran da cewa “ba za a amince da su ba”, ya kara da cewa sun saba wa kundin tsarin mulkin MDD...
    Gwamnatin Nijar ta saki kusan mutane 50 da suka hada da ministocin da aka tsare tun bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023. Baya ga tsaffin ministocin da akwai wasu sojoji da ake zarginsu da yunkurin juyin mulki a shekarar 2010 da suma aka sake su.  “An sako wadannan mutane ne bisa ga shawarwarin da babban taro na kasar ya bayar,” kamar yadda sakataren gwamnatin kasar ya karanta a gidan talabijin din kasar a cikin daren jiya. Cikin tsaffin ministocin da aka saki har da tsohon ministan man fetur Mahamane Sani Issoufou, dan tsohon shugaban kasar Mahamadou Issoufou, da kuma tsohon ministan tsaro Kalla Moutari, da tsohon ministan kudi Ahmat Jidoud, da kuma tsohon...
    Tun daga ranar 1 ga watan Afrilu, dakarun rundunar sojojin ’yantar da al’umma ta kasar Sin ko PLA shiyyar gabashin kasar ta kaddamar da atisayen hadin gwiwar rukunoni masu kunshe da sojojin kasa, da na ruwa, da na sama da dai sauransu a kewayen tsibirin Taiwan. Atisayen da ya kasance wani salo na jan kunne mai karfi ga mahukuntan gwamnatin Lai Ching-te dake rajin “’yancin kan Taiwan”, kana mataki mai karfi da ya wajaba na kare ikon mulkin kai da cikakkun yankunan kasar Sin. Kamar yadda aka sani, Taiwan wani sashe ne na kasar Sin, wanda ba ta taba zama kasa ba, kuma ba zai taba zama ba a nan gaba. Sunan yankin Taiwa a MDD shi ne “Lardin Taiwan...
    A lokacin da yake wurin, Kefas ya shaida wa masu ababen hawa da matafiya cewa, gwamnatin jihar za ta samar musu da wata hanyar da za su amfani da ita kafin a kammala gyaran gadar, alkawarin da har yanzun bai cika ba, ga kuma wani mamakon ruwan sama da aka yi a daren ranar Talata, wanda ya wanke gadar wucin gadi da mutanen yankin suka gina a matsayin madadi.   Wakilin LEADERSHIP a wurin gadar da sanyin safiyar Larabar nan, ya gano cewa, hanyar wucin gadi da mazauna kauyen suka gina, ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a daren ranar Talata ya wanke ta, lamarin da ya sa masu ababen hawa da matafiya suka makale a gaɓar...
    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau I. Jibrin, ya ziyarci iyalan mafarauta 16 da aka kashe a yankin Uromi da ke Jihar Edo, tare da ba su tallafin Naira miliyan 16. Matan matatan sun fito ne daga ƙananan hukumomin Bunkure, Kibiya, Rano, da Garko a Jihar Kano. Mutum 2 sun rasu, 13 sun ɓace a hatsarin jirgin ruwa a Bayelsa HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Barau ya gana da iyalan mamatan a Masallacin At-Taqwa da ke Bunkure a ranar Laraba tare da Ministan Harkokin Gidaje, Yusuf Abdullahi Ata da sauran manyan jami’ai. Barau, ya yi ta’aziyya da kuma tabbatar da cewa waɗanda suka aikata laifin za su fuskanci hukunci. “Na zo nan ne domin na taya ku jaje kan...
    Karin harajin kwastam na iya haifar da yakin kasuwanci. Kasashen da wannan harajin ya shafa za su iya mayar da martani, lamarin da ka iya haifar da rudanin da zai cutar da kasuwancin duniya. Wannan na iya haifar da karin farashin kayayyaki, sallamar ma’aikata daga aikinsu, dakile hanyoyin samar da kayayyaki, da takaita ci gaban tattalin arziki a duniya. Don haka, ana kyautata tsammanin cewa, wannan sabon tsarin harajin zai sake fasalin yanayin kasuwanci a duniya, ganin cewa, wasu masana’antu za su fuskanci tsadar kayayyaki da kuma durkushewar hanyoyin samar da kayayyaki.       Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da ake ci gaba da neman wasu mutum 13 da suka ɓace yayin wani hatsarin jirgin ruwa a Jihar Bayelsa. Hatsarin ya faru ne da yammacin ranar Talata, lokacin da jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji ya yi karo da wani jirgin kamun kifi. HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar Galadiman Kano Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus Masu nutso a ruwa sun fara ƙoƙarin ceto waɗanda suka ɓace. Bayanai sun nuna cewar wani jirgi mai suna ‘Meeting Marine’ wanda ya taso daga Anyama Ijaw zuwa Lubia da Foropa ya yi karo da jirgin kamun kifi. Jirgin na da injin 115HP kuma wani mutum da ake kira Saturday ne yake tuƙa shi. Shugaban...
    Wani basakkwace, Musa Abubakar, wanda a bayan nan ya yi ridda saboda zullumin ’yan bindiga masu kai hare-hare da ta’adar garkuwa da mutane, ya sake karɓar addinin Musulunci. A ranar Asabar ce mutumin tare da matansa biyu suka sake karɓar addinin Islama bayan  ridda da suka yi a kwanan baya. Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa Kisan Mafarauta: Babu wanda aka kai wa harin ramuwar gayya a Kano — Ƙungiyoyin Matasa Bayanai sun ce Musa Abubakar ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni da ke Sakkwato ya yi ƙaura zuwa Jihar Taraba a sakamakon yanayin tsaro a mazauninsa. Bayan komawa Taraba ne kuma ya shawarci matansa uku da su  karɓi addini Kiristanci, kuma ya yi nasara biyu suka amince....
    Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bar Abuja a yau Laraba zuwa Paris, na ƙasar Faransa, domin ziyarar aiki ta makonni biyu. A cewar mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga, Shugaba Tinubu zai yi bitar mulkinsa na rabin wa’adi, inda zai tantance nasarorin da ya cimma da kuma irin sauye-sauyen da yake aiwatarwa. Haaland Zai Ziyarci Likita Saboda Raunin Da Ya Samu A Ƙafa Sanarwar ta ce wannan lokaci zai ba shi damar tsara hanyoyin da za su inganta ci gaban ƙasa yayin da yake shirin cika shekaru biyu a kan mulki. Duk da kasancewarsa a waje, Onanuga ya tabbatar da cewa Shugaba Tinubu zai ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati tare da tuntuɓar manyan jami’ansa har zuwa lokacin...
    Ƙungiyar matasan Arewa ta yi Allah-wadai da jita-jitar da ake yaɗawa cewa an kashe wani ɗan ƙabilar Ibo a Jihar Kano saboda kisan wasu Hausawa mafarauta da ɓatagari suka yi kwanan a Jihar Edo. A wani taron manema labarai da gamayyar ƙungiyoyin matasa na ƙabilu daban-daban, ta ce abin takaici ne kisan da aka yi wa Hausawa kuma tana miƙa ta’aziyya ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su. Isra’ila ta kashe yara 322 cikin kwanaki 10 a Gaza — UNICEF Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Kazalika, ƙungiyoyin sun yaba wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa koƙarinsa na tabbatar da zaman lafiya ya ci gaba da ɗorewa a jihar ta hanyar ɗaukar...
    Haka kuma, yana shirin gina masana’antar sarrafa itace da samar da sabbin hanyoyin ruwa domin rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwa na Apapa da Lekki. Wannan jari ya zo ne a daidai lokacin da Kamaru ke faɗaɗa tashar jiragen ruwa na Kribi domin ƙara inganta kasuwanci a yankin. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Gwamnatin Jamus ta ce tana ci gaba da samun galaba na daƙile kwararar baƙin haure masu shiga ƙasar tare da mayar da wadanda aka yi watsi da takardunsu na neman mafaka zuwa inda suka fito. Ministar harkokin cikin gida ta Jamus, Nancy Faeser, ta bayyana cewa gwamnatin ƙasar mai barin gado ta taka muhimmiyar rawa wajen daƙile shigar baƙin haure cikin ƙasar. Tinubu ya cire Mele Kyari daga shugabancin NNPC DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta Faeser ta ce gwamnatin na ci gaba da daukan matakin mayar da baƙin haure ƙasashen da suka fito, inda yanzu haka aka samu raguwar masu ajiye takardun neman mafaka a ƙasar, mafi ƙarfin tattalin arziki tsakanin ƙasashen Turai. Faeser ta...
    A wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban hukumar makamashin Nukliya ta duniya Rafael Grossy  Abbas Aragchi ministan harkokin wajen kasar Iran ya bukaci hukumar ta bayyana matsayinta dangane da shirin makamashin nukliyar kasar Iran. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto ministan yana fadawa Grossy bayyana matsayin hukumarsa dangane da shirin nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya, mai yuwa yayi tasiri a barazanar da kasar Iran take fuskanta na kai hare-hare kan cibiyoyin nukliyar kasar. Aragchi ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran na zaman lafiya ne, kuma har yanzun kasar Iran tana kan bakanta na aiki tare da hukumar makamashin nukliya ta duniya don kare hakkinta na mallakar fasahar makamashin nukliya wannan dokokin kasa da...
    Babban mai bawa jagoran juyin juya halin musulunci Dr Ali Larijani, ya ce duk tare da cewa jagoran juyi juya halin musulunci ya bada fatawar hana kera makaman nukliya, amma idan an kaiwa kasar Iran hari kan shirinta na makamashin nukliya, wannan yana iya tunzura kasar ta kai ga mallakar makaman Nukliya. Jaridar Tehran time ta nakalto Dr Larijani ya kara da cewa idan Amurka ko HKI ko duka biyu suka kaiwa cibiyoyin nukliyar kasar, to kuwa zata kera makaman nukliya. A ranar Lahadin da ta gabata ce, Dr Larijani ya bayyana haka. Sai dai a daren Litinin ne Dr Larijani ta kara jaddada wannan matakin. Sai dai kafin haka shugaban ma’aikatar leken asiri na Amurka ta tabbatarwa tashar talabijin...
    Sojojin kasar Yemen sun yi amfani da makamai masu linzami samfurin cruise a hare-haren da suka kai kan kataparen jirgin yaki mai daukarjiragen saman yaki na kasar Amurka da suke cikin tekun maliya a karo na ukku a cikin sa’o’ii 24 da suka gabata. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar sojojin kasar ta Yemen na fada a jiya Talata, kan cewa sun yi amfani da makamai masu linzami da kuma jiragen saman yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa a wadan nan hare-hare kan USS Harry S.Truman kuma saun sami bararsu kamar yadda aka tsara. Labarun ya kara da cewa yakin yana ci gaba tsakanin bangarorin biyu. Kuma wadan nan hare hare sun zo ne saboda...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Tun bayan kisan mafarauta 16 da ke hanyar su ta dawowa gida a garin Uromi da ke karamar hukumar Esan ta Jihar Edo ne dai al’umma da dama ke ta aikewa da sakon alhini ga ‘yan uwa da abokan arziki yayin da wasu kuma ke ta neman amsoshin tambayoyi game da lamarin da ya shige musu duhu. A yayin da wasu ke ganin a matsayin su na ‘yan kasa masu cikakken ‘yanci, suna da damar kutsawa lungu da saƙo na ko’ina a fadin kasar nan, wasu kuwa tambaya suke shin me ya kai ‘yan Arewa har kudancin kasar nan don yin farauta? NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A yau Talata, kasar Sin ta bayyana cewa, za ta dauki matakan ramuwar gayya domin mayar da martani game da sanarwar da Amurka ta fitar ta saka takunkumin biza a kan jami’an kasar Sin, bisa hujjar hana izinin shiga yankin Xizang mai cin gashin kansa, da ke kudu maso yammacin kasar Sin. A yayin taron manema labarai da aka saba yi a-kai-a-kai, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin, Guo Jiakun ya bayyana cewa, yankin Xizang a bude yake ga kowa da kowa, kuma ba a hana baki daga kasashen waje shiga ba, inda ya kara da cewa, yankin yana karbar dimbin matafiya da sauran al’ummomi da dama daga sassa daban-daban a kowace shekara, domin ko a shekarar...
    Tawagogin ma’aikatan ceto na kasar Sin na ci gaba da aiki a yankin da ya fi shan wuya na Mandalay da ke tsakiyar kasar Myanmar, sakamakon girgizar kasar da ta afku mai karfin maki 7.9 a makon da ya gabata, inda zuwa yanzu suka ceci mutum takwas da suka tsira daga ibtila’in, da misalin karfe 8 na safiyar ranar Talata, agogon kasar. A yayin bikin bayar da gudummawar kudi ga wadanda girgizar kasar ta shafa a birnin Nay Pyi Taw a yau Talata, shugaban majalisar gudanarwar kasar Myanmar, Min Aung Hlaing, ya ce, mutanen da suka mutu sakamakon mummunar girgizar kasar wacce ta afku a kasar a ranar Jumma’a, sun kai 2,719, yayin da wasu 4,521 suka jikkata, kana 441...
    Sanata mai wakiltar mazabar Kogi ta tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, da aka dakatar, ta bayyana cewa “ita ba mahaukaciya ba ce”, kuma “ba ta tsoron kowa” a yayin da take jawabi ga dimbin magoya bayanta a lokacin da ta dawo gida a Ihima, karamar hukumar Okehi ta jihar Kogi a ranar Talata da yamma. Dawowarta ta zo ne a daidai lokacin da ake cike da rikicin siyasa, domin tun da farko gwamnatin jihar Kogi da rundunar ‘yansandan jihar ta kafa dokar hana tarukan jama’a, saboda dalilan tsaro. Sannan kuma, shugaban karamar hukumar Okehi, Hon. Amoka Eneji, ya kuma sanya dokar hana fita a karamar hukumar a wani yunkuri na dakatar da shirin dawowar Natasha gida a yayin bukukuwan Sallah tare da...
    Alƙaluman Asusun Tallafawa Ƙananan Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya UNICEF ya ce Isra’ila ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 cikin kwanaki 10 da suka gabata a hare-haren da suke ci gaba da kai wa sassan Gaza. Alƙaluman da UNICEF ta fitar ta ce a jimilla ƙananan yara fiye da dubu 15 ne Isra’ilan ta kashe cikin kusan watanni 18 da ta shafe tana yiwa yankin na Gaza luguden wuta, kuma daga lokacin da ƙasar ta katse yarjejeniyar tsagaita wutar da ke tsakaninta da Hamas ta kashe ƙananan yaran da yawansu ya kai 322 tare da jikkata 609. Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi, ya bayyana a yau Talata cewa, al’ummar Sinawa da ’yan kasar Rasha sun ba da gudummawa gaya wajen samun nasarar yakin duniya na biyu. A wata hira da ya yi da rukunin gidajen rediyo da talabijin mallakin kasar Rasha wato Russia Today a yau a birnin Moscow, Wang ya bayyana cewa, bana shekara ce ta cika shekara 80 da samun nasarar yakin da Sinawa suka gwabza na tirjiya a kan zaluncin kasar Japan, da kazamin yakin kishin kasa na Tarayyar Soviet, da kuma yakin duniya na biyu. Atisayen Dakarun PLA Horo Ne Mai Tsanani Ga Masu Rajin Neman ’Yancin Kan Taiwan Sanata Yari Zai Tallafa Wa Marayu 20,000 A Zamfara Wang, ya yi...
    “Muna shirye-shiryen bayar da diyya ga duk wadanda lamarin ya shafa.   “Ina kuma yabawa mutanen jihar Kano da daukacin arewa saboda rashin daukar doka a hannunsu da kai harin ramuwar gayya,” inji shi.   Ya yi addu’ar Allah ya jikan mafarautan da suka mutu.   Gwamnan Edo ya kara, da cewa, tuni aka fara cafke wadande ake zargi da aikata wannan aika-aika.   “An riga an kama kimanin mutane 14 da ake zargi, za mu ci gaba da bin diddigin lamarin har sai an gurfanar da su a gaban kotu an yi wadanda aka kashe adalci”. In ji Okpebolo Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne. Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda dalilin da ta ce na tsaro ne. Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Miller Ɗantawaye, ya ce hana taron ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu cewa za a samu barzanar tsaro, wanda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar matakin. Sai dai Natasha wadda ta isa jihar a...
    Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar, ta ce taron barka da sallah da ta yi a mazaɓarta a yammacin Talata duk da haramta taruka da gwamnatin jihar ta yi ba karya doka ba ne. Ana iya tuna cewa Gwamnatin Kogin dai ta hana duk wani nau’in taro ko gangami a jihar, saboda dalilin da ta ce na tsaro ne. Haaland zai yi jinyar mako bakwai — Guardiola HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah Kwamishinan ‘Yan sandan jihar, Miller Ɗantawaye, ya ce hana taron ya biyo bayan bayanan sirri da suka samu cewa za a samu barzanar tsaro, wanda ya tilasta gwamnatin jihar ɗaukar matakin. Sai dai Natasha wadda ta isa jihar a...
    Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, a ranar Talata ya yaba wa Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano bisa bayar da fifiko akan ilimi, kiwon lafiya, noma, da tsaro a jihar. Sarki Sanusi II ya bayyana jin dadinsa ne a lokacin da ya kai gaisuwar Sallah ga gwamnan Kano, kamar yadda aka saba gudanarwa a al’adance duk shekara. Sin Da Zambiya Sun Daddale Yarjejeniyar Fitar Da Kwarurun Macadamia Nuts Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL “Mun zo ne domin mika gaisuwar mu ta barka da Sallah tare da gode muku bisa gagarumin aikin da kuke yi, musamman a fannin ilimi da noma, inda kuka samar da tallafin kayan aikin noma na zamani. “Muna godiya...
    Kociyan Manchester City, Pep Guardiola, ya ce ɗan wasan gaban ƙungiyar, Erling Haaland, zai yi jinyar mako bakwai a sakamakon raunin da ya samu a idon sahunsa a wasan kofin FA da ƙungiyar ta fafata da Bournemouth a ranar Lahadi. Ɗan wasan na ƙasar Norway bai ƙarasa wasan ba, inda aka cire shi a minti 61 da fara wasan bayan ya farke ƙwallo ɗaya, kafin daga bisani City ta doke Bournemouth da ci biyu da ɗaya domin zuwa wasan kusa da na ƙarshe. HOTUNA: Sarki Sanusi ya kai wa Abba ziyarar barka da Sallah Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha Tun a jiya Litinin ce City ta ce Haaland zai ga ƙwararren likita saboda raunin da...
    A jiya Litinin ne kasashen Sin da Zambiya suka rattaba hannu kan wata yarjejeniya kan fitar da kwarurun macadamia nuts zuwa kasar Sin. Bikin rattaba hannu kan yarjejeniyar ya samu halarcin mukaddashin jakada na ofishin jakadancin Sin da ke Zambiya Wang Sheng, da ministan noma na kasar Zambiya Mtolo Phiri. Kano Pillars Ta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Kocinta, Usman Abdallah Farashin Man Fetur Ya Ƙara Tashi Sakamakon Rikicin Dangote Da NNPCL A jawabinsa, Wang ya bayyana cewa, rattaba hannu kan yarjejeniyar ya kasance wani babban mataki na bude kasuwar kasar Sin ga kwayoyi dangin gyada na kasar Zambiya, wanda zai amfanar da manoman kasar nan gaba ba da jimawa ba. Ya kara da cewa, baya ga wannan yarjejeniyar...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Gangamin da zan yi a mazaɓata babu fashi — Natasha Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah. Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi baƙuncin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, a fadar gwamnatin jihar. Sarkin dai ya kai wa gwamnan ziyarar ce kamar yadda aka saba a Hawan Nassarawa da ake gudanarwa bisa al’ada duk shekara. Sai dai a sakamakon haramcin gudanar da haye-hayen sallah da rundunar ’yan sandan jihar ta yi, Sarkin bai cika duk tsare-tsaren da al’ada ta tanada ba na gudanar da Hawan Sallah. Aminiya ta ruwaito cewa, Sarkin wanda ya yi ƙoƙarin kawar da idon jama’a, ya bi ta wasu hanyoyin da ba su aka saba bi wajen kai wa gwamna ziyara a yayin gudanar da hawan cikakke. Haka kuma, Sarkin ya yi amfani da jerin gwanon motoci ƙalilan maimaiko hawa...
    Sanata Natasha Akpoti wadda a kwanan nan Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar na tsawon watanni shida, ta ce “babu gudu babu ja da baya dangane da gangamin gaisuwar Sallah” da ta shirya yi a mazaɓarta. Hakan na kunshe ne cikin wani sakon mayar da martani da Sanata Natasha ta wallafa a shafinta na Facebook. Muna kiran Natasha ta jingine gangamin da za ta yi a Kogi — ’Yan sanda HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta bayyana cewa “babu gudu babu ja da baya dangane da wannan gangamin na Sallah. Ta yi zargin cewa duk wani abu da ya faru za ta ɗora alhakinsa ne a kan Gwamna jihar, Ahmed Usman Ododo...
    Rundunar ’yan sanda ta nemi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta jingine shirinta na kai ziyara da zummar hada gangamin bikin Sallah a Jihar Kogi. Wata sanarwa da kakakin ’yan sandan Jihar Kogi, ASP William Aya ya fitar, ta ambato Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP William Ɗantawaye na cewa gangamin ya ci karo da haramcin gudanar da gangamin siyasa da gwamnatin jihar ta yi ranar Litinin. HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi “A sakamakon rahoton sirri kan barazanar tsaro a jihar Kogi da ya sanya hana duk wani gangami da jerin gwano da gwamnatin jihar Kogi ta yi, rundunar ‘yan sandan na...
    Cibiyar da take dakile yaduwar cutuka masu yaduwa ( NCDC) ta sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a kalla mutane 118 ne su ka rasa rayukansu sanadiyar yaduwar zazzabin Lassa tun daga farkon wannan shekara ta 2025. A wata sanarwar da cibiyar ta fitar ta bayyana cewa; An sami yaduwar wannan cuta a cikin jahoji 33 na fadin kasar, kuma bincike da aka yi akan wadanda ake tsammanin ta kama, ya tabbatar da cewa an sami mutane 645 da su ka kamu da ita. Ita dai wannan cutar mai yaduwa a Nigeria, ana kamuwa da ita ne ta hanyar cudanya a tsakanin mutane ko kuma taba kayan gida da su ka gurbana daga bahaya ko fitsari na mutane...
    Jami’an tsaro sun bazama akan titunan manyan garuruwan kasar Zimbabwe domin dakile zanga-zangar da ake shirin yi domin yin kira ga shugaban kasa Emmerson Mnangagwa ya yi murabus. Tsofaffon sojoji da mayakan da su ka samarwa kasar ‘yanci ne dai suka yi kiran a yi zanga-zangar, saboda kin amincewa da shirin shugaban kasar na tsawaita wa’adin mulkinsa. A cikin watan Janairu na wannan shekarar ne dai jam’iyyar ZANU-Party, mai mulki a kasar ta sanar  da cewa tana son Mnangagwa ya ci gaba da rike mukamin shugaban kasar har zuwa 2023. Mnangagwa dai ya hau karagar mulkin kasar ta Zimbabwe ne tun a 2017,bayan sauke Robert Mugabe daga kan karagar mulki cikin ruwan sanyi. Shugaban mayakan nemawa kasar ‘yanci Blessed Geza...
    Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Jihar Edo Monday Okpebholo, sun ziyarci garin Torankawa da ke Kano domin jajanta wa iyalai da yan uwan mafarautan nan guda 16 da aka kashe a Jihar Edo. Gwamnonin biyu sun ziyarci garin ne da manufar tabbatar wa da iyalan waɗanda lamarin ya shafa cewa lallai gwamnatin jihar Edo za ta hukunta waɗanda suka yi wannan aika-aika sannan kuma gwamnatin za ta biya su diyya. Ta zuba wa abokan aikinta guba bayan taƙaddama kan ƙarin matsayi Mene ne matsayin azumin Sitta Shawwal a Mazhabar Malikiyya “Wannan ziyara ba kawai ta jaje da ta’aziyya ba ce, a’a ta nuna tabbacin ƙoƙarin samar da adalci. “Iyalan waɗannan mamata na buƙatar abin da ya...
    Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib. Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba kuma za mu yi taraddudin daukar dukkanin matakan kare kai ba, akan jiragen ruwan abokan gaba a nan gaba. Kwanaki biyu da su ka gabata, sojojin Yemen sun kai wasu hare-hare akan jirgin dakon jiragen yaki na “Trauman’ da sauran jiragen yakin da suke ba shi kariya. Sojojin na Yemen suna kuma ci gaba da kai wa HKI hare-hare da jiragen sama marasa matuki da...
    Babban Darakta Muryar Najeriya VON, Malam Jibrin Baba Ndace ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su kara kaimi wajen addu’o’in samun nasara ga gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bisa tsarinta na sabunta fata.   Ya yi wannan kiran ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi da aka rabawa manema labarai a Minna jihar Neja.   Malam Jibrin Baba Ndace ya tunatar da ’yan Najeriya cewa ya zama wajibi saboda nasarar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta samu ya kasance nasarar mu baki daya, don haka akwai bukatar mu kasance cikin nasara.   Daga nan sai ya mika gaisuwar ban girma ga daukacin al’ummar Musulmin Nijeriya da ma na duniya baki daya na bikin sallah karama tare...
    Kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen jihar Kebbi, NUJ, ta taya gwamnatin jihar da al’ummar musulmin jihar murnar zagayowar ranar Sallah.   Majalisar a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar na jiha, Kwamared Bello Sarki Abubakar da Sakatare, Ismail Adebayo, ta yi murna da al’ummar musulmin jihar kan kammala azumin kwanaki 29 na watan Ramadan da kuma bikin Eid-Fitr.   Ta yi kira da a zauna lafiya da juna a tsakanin al’ummar jihar bisa koyarwar addinin Musulunci da manzon Allah mai tsira da amincin Allah tare da la’akari da muhimmancin watan Ramadan da Idi-El-Fitr.   Majalisar ta yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin gwamna Nasir Idris kan kayayyakin abinci da aka rabawa musulmi a...
    Haka kuma, an Ƙwato bindiga ƙirar gida da Naira miliyan 4.84 da ake zargin kuɗin fansa ne. An ceto Dokta Yushau ba tare da wata matsala ba. A wata arangama daban, jami’an ‘yansanda sun kama wani Kafinta Musa a Jihar Taraba bisa zargin fashi da makami, garkuwa da mutane, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba. An ƙwato bindiga ƙirar AK-49 a hannunsa, kuma ana ci gaba da bincike don kama sauran miyagun da ke tare da shi. Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya jinjina wa jami’an da suka gudanar da wannan aikin tare da kira ga al’umma da su ci gaba da ba da bayanan sirri da za su taimaka wajen yaƙi da laifuka. Daga kanmu, magana...
    Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Yamma, Dakta Abdul’aziz Yari, ya yi kira ga ‘yan siyasa da masu hannu da shuni da su kara kaimi wajen gudanar da ayyukansu na alheri fiye da watan Ramadan.   Da yake zantawa da manema labarai a mahaifarsa Talatan Mafara, a wani bangare na sakonsa na Sallah, Yari ya jaddada muhimmancin ci gaba da al’adun bayar da Zakka, Sadaka, da sauran nau’o’in tallafi ga marasa galihu a duk shekara.   Ya yabawa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa bullo da shirye-shiryen jin dadin jama’a da nufin inganta rayuwar ‘yan Najeriya.   Dokta Yari ya yi kira ga ‘yan kasar da su ba da cikakken goyon baya ga kokarin shugaban...
    Game da aka yi wa mafarauta 16 a Udune Efandion, karamar hukumar Uromi ta jihar Edo, gwamna Monday Okpebholo ya yi kakkausar suka ga wannan aika-aika na rashin hankali, yana mai bayyana hakan a matsayin “wani abu da kuma muguwar dabi’a.     Okpebholo, tare da Gwamna Abdullahi Yusuf na Jihar Kano, sun yi addu’a ga rayukan wadanda abin ya shafa a kauyen Bunkure na jihar Kano inda wadanda abin ya shafa suka fita tare da kuma da bada tabbacin ga iyalan wadanda abin ya shafa cewa za a gurfanar da masu laifin gaban kuliya.   Allah wadai da gwamnan ya biyo bayan harin da wasu gungun ’yan bindiga suka kai wa mafarautan, wadanda aka yi kuskuren cewa masu garkuwa...
    Jami’ar Bayero Kano (BUK) ta kaddamar da wani tsari na yanar gizo wanda zai baiwa dalibai damar shiga da duba sakamakon kammala karatunsu ta hanyar lambobi.   Wannan sabon yunkuri shine karo na farko da cibiyar ta samar da sakamako ta hanyar irin wannan dandali.   An sanar da shirin ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun mataimakin magatakarda kuma shugaban hukumar kula da harkokin jama’a Lamara Garba Azare.   A cewar sanarwar jami’ar, tsarin da myBUK Team ya kirkira kuma yana bawa ɗalibai damar dawo da sakamako kai tsaye ta hanyar amfani da sashen rajistar dalibai.   Takardun sakamakon za su nuna a sarari na kowane kwasa amma dole ne ɗaliban da suka kammala shekarar ƙarshe...
    Ana tuhumar wata ma’aikaciyar kamfanin masaka a Jihar Goias ta ƙasar Brazil da laifin saka wa abokan aikinta guba bayan ta yi jayayya da su a kan abin da matar ta kira da rashin adalci wajen ƙarin matsayi da kamfanin ya yi. Lamarin ya faru ne a wata masana’anta da ke Abadia de Goias, wani gari a yankin Goiânia Metropolitan. NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Za Su Kwaɗaita Muku Azumtar Sitta Shawwal Iran ta mayar wa Amurka martani kan barazanar kai mata hari ’Yan sanda sun yi iƙirarin cewa, kyamarar daukar hoto cikin sirri (CCTV) ta kama wadda ake zargin mai shekara 38 tana buɗe wasu gorunan abin sha, wanda daga bisani wata ma’aikaciya ta sha, inda ta ji wani...
    Haka kuma, ya yaba wa Gwamna Okpebholo bisa tattaunawarsa da shugabannin al’ummar Hausa a Edo domin hana rikici da kuma alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan. “Biyan diyya da aka alƙawarta abu ne mai kyau, amma dole ne a tabbatar da hakan cikin gaggawa domin taimaka wa iyalan da suka rasa masu ɗaukar nauyinsu,” ya ƙara da cewa. A nasa ɓangaren, Gwamna Okpebholo ya nuna matuƙar damuwarsa kan wannan kisa, inda ya tabbatar da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata laifin. “Ina samu labarin abin da ya faru, na garzaya zuwa Uromi. Na gana da al’ummar Hausa a wajen, kuma mun yi ƙoƙarin kwantar da tarzoma. “Ina tabbatar muku da cewa za a hukunta waɗanda suka aikata wannan ta’asa,”...
    Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasa da kasa “ Amnesty International” ta zargi fira ministan HKI da cewa, mai aikata laifin yaki ne, da kuma amfani da yunwa a matsayin makamin yaki akan fararen hula. Kungiyar ta kare hakkin bil’adama ta bayyana cewa a cikin ganganci Netanyahu yake kai wa fararen hula harer-hare da kuma aikata laifuka akan bil’adama. Haka nan kuma kungiyar ta yi gargadi akan ziyarar da Netanyahu zai kai wata kasa daga cikin wadanda su ka rattaba hannu a yarjejeniyar kafa kotun duniya ba tare da an kama shi ba. Kungiyar “Amnesty Interational” ta ce rashin kama Fira ministan na HKI zai kara ba shi karfin gwiwar ci gaba da aikata laifuka. Dangane da gayyatar da kasar...
    Mai bai wa jagoran juyin musulunci na Iran shawara Dr. Ali Larijani ya ce, idan har Amurka da Isra’ila su ka fake da batun shirin makamashin Nukiliyar Iran na zaman lafiya, su ka kawo mata hari, to ya zama wajibi a gare ta ta kera makaman Nukiliya. Dr. Ali Larijani wanda tashar talabijin din Iran ta yi jira da shi a jiya Litinin da dare, ya bayyana cewa; manyan kasashen duniya suna son yin alaka kai tsare da Iran cikin ‘yanci, sai dai suna da fuskantar matsin lamba daga Amurka. Tsohon shugaban Majalisar shawarar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa; Idan har Amruka da HKI su ka kawo wa Iran hari, to, za ta dau hanyar kera makaman...
    Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Arakci ya bayyana cewa, duk wata barazana da za a yi wa Iran za ta sa makiya su yi babbar nadama. A wata hira a tashar talabijin din almasirah ta kasar Yemen ta yi da shi, ministan harkokin wajen na Iran  ya ce, farfagandar da ake yi ta cewa, kai wa kasar Yemen hari  share fage ne na yaki da Iran ba sabon abu ba ne, an sha yin irin wannan barazanar a baya. Abbas Arakci ya kara da cewa; Iran ba za ta taba kyale duk wani mahaluki da zai rika yin Magana da ita da harshe na barazana ba, sannan ya kara da cewa makiya za su yi nadamar wannan barazanar. Da yake...
    Da safiyar Yau Talata jiragen yakin HKI sun kai hare-hare akan unguwar Dhahiya dake Beirut tare da bayyana cewa ta kai wa wani kusa ne a kungiyar Hizbullah hari. Harin na yau shi ne irinsa na biyu da HKI ya kai a unguwar Dhahiya tun daga tsagaita wutar yaki a cikin watan Nuwamba na shekarar da ta gabata. Jiragen yakin na HKI sun yi shawagi a kasa-kasan birnin Beirut kafin aji karar fashewar abubuwa masu karfi. Kafafen watsa labarai sun ambaci cewa jiragen sun kai harin ne akan wani dogon gini a cikin unguwar. Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon ta sanar da cewa ya zuwa yanzu mutane 3 ne su ka yi shahada,yayin da wasu 4 su ka jikkata. Masu...
    Gwamna Okpebholo ya bayyana takaicinsa kan lamarin, yana mai cewa tuni an kama mutum 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za su fuskanci hukunci. Bayan tattaunawa, Gwamna Abba ya jagoranci Gwamna Okpebholo zuwa ƙaramar hukumar Bunkure don jajanta wa iyalan mamatan. Gwamnan Edo ya sha alwashin ganin an yi adalci ga mamatan da iyalansu. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Al-Qur’ani mai girma a cikin suratul Baqarah, Allah Ya wajabta wa musulmi da suka cika wasu sharuɗan azumtar watan Ramadana. Kamar yadda malamai suka sha faɗi, wannan wata na ɗauke da wasu falala maras misaltuwa da bawa kan samu idan ya maida kai wajen ibada don samun rabauta daga ubangiji. Kazalika, hadisai sun ruwaito falalar azumtar kwanaki shida na watan Shawwal, watan da ke biye da Ramadan. NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana DAGA LARABA: Yadda Farashin Kayan Masarufi Suke Gabanin Sallah Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan falalar da ke akwai ga wanda ya azumci kwanaki shidda na watan...
    Jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya yi kakkausan gargaɗi kan barazanar Amurka da ƙawayenta na kai wa ƙasarsa hari. Khamenei ya sha alwashin maida mummunar martani idan har Amurka da ƙaddamar da hare-hare a ƙasar ta Iran. Gargaɗin nasa martani ne kan barazanar da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi wa ƙasar cewa za su kai mata hari. Muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka kan kashe ’yan Arewa a Edo — Sarkin Musulmi Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka “Suna yi min barazana, kuma idan suka sake suka kawo min hari tabbas zan rama,” in ji shi. Yayin wata tattaunawa a ranar Asabar ne Trump ya yi alƙawarin kai wa Iran...
    Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ta Jihar Edo na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Gwamnan Edo ya kai ziyarar jaje Kano Gwamnan Kano ya karɓi baƙuncin takwaransa na Edo, Monday Okpebholo wanda ya ziyarci jihar domin jajanta wa gwamnati da al’ummar dangane da kashe mafarautan...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    A Gaza fiye da mutane 1,000 ne Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga watan Maris, tun bayan sake dawo da yaki a Zirin. Hakan ya sanya adadin falasdinawan da Isra’ila ta kashe tun watan Oktoba ya kai 50,350 tare da raunata 114,400 a cewar ma’aikatar lafiya ta Gaza. Hare-haren da Isra’ila ta kai a zirin Gaza sun kashe akalla Falasdinawa 80 a ranar Lahadi. Sanarwar da ma’aikatar ta fitar ta ce, an kai mutane 53 da lamarin ya rutsa da su zuwa asibitoci a Gaza a ranar Lahadin, wato ranar farko ta bikin Eid al-Fitr.   Ma’aikatar ta kara da cewa, “har yanzu da yawan wadanda abin ya shafa na makale a karkashin baraguzan gine-gine, saboda masu ceto...
    A Faransa, an haramta wa Marie Le Pen yin takara har na tsawon shekaru biyar kuma hakan na nufin ba za ta yi takarar shugabancin kasar ba a shekarar 2027. An dai samu yar siyasar ne da laifin almubazzaranci da kudaden jama’a wajen daukar nauyin jam’iyyarta ta National Rally mai tsaurin ra’ayi.   An tuhumi Le Pen tare da wasu manyan yan jam’iyyar tata guda 20 da daukar masu taimaka musu aiki wadanda suka yi wa jam’iyyarta aiki maimakon Majalisar Turai wadda ita ce ke biyan ma’aikatan albashi.   Ms Le Pen, mai shekaru 56, ba za ta iya shiga zaben shugaban kasa mai zuwa da aka shirya gudanarwa a shekara ta 2027 ba, inda a yanzu ake ganin ita...
    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar, ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da kashe matafiya ’yan Arewa da aka yi a Jihar Edo. Saboda haka Sarkin ya ce suna dakon ganin hukuncin da za a ɗauka dangane da faruwar wannan mummunan lamari. Kisan Mafarauta: Matakan da gwamnatin Edo da ta Kano suke ɗauka Dalilin da muka soke Hawan Bariki — Masarautar Zazzau Da yake miƙa saƙon gaisuwar Sallah ga Gwamnan Sakkwato, Alhaji Ahmad Aliyu a ranar Litinin, Sarkin ya ce “mun ga an ɗauki mataki kan yanayin da ake ciki a Jihar Edo. “Saboda haka muna jiran ganin hukuncin da za a ɗauka bayan kammala bincike don ba wani dalili ka kashe mutum ba tare da wani haƙƙi ba....
    Mai martaba Sarkin Lere dake Kaduna Alhaji Sulaiman Umaru ya amince da nadin Sani Ahmed Lere Sardaunan Matasa zuwa Falakin Lere.   Hakan na kunshe ne a cikin takardar nadin da Sakataren Majalisar kuma Sadaukin Lere Alhaji Muhammad Lawal Ahmed ya sanya wa hannu. Alhaji Muhammad Lawal Ahmed yace sabon nadin ya fara aiki ne nan take. Ya bayyana cewa nadin Sani Ahmed Lere a matsayin Falakin Lere daga matsayinsa ne daga Sardaunan Matasan Lere wakilin Matasa a Masarautar zuwa Falakin Lere dan Majalisar Sarki kuma PPS ga Sarki.
    Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike. A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun...
    Yau Litinin, ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS ya kira wani taro na nazarin ayyukan kiyaye muhallin halittu, da rahoton ayyukan kewaye da kwamitin tsakiyar JKS karo na 20 ya gabatar, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jagoranci taron. Taron ya nuna cewa, sa ido kan aikin kiyaye muhallin halittu wani muhimmin mataki a kokarin da kwamitin ya yi na kiyaye muhalli. Dole ne a nace ga jagorancin da JKS ta bayar a wannan bangare, da ma sauke nauyin dake wuyan hukumomin wurare daban-daban karkashinta. Taron ya kuma jadadda cewa, ya kamata a kara karfin sa ido a siyasance, da mai da hankali kan yadda ake tabbatar da manufofi da tsare-tsaren kwamitin, ta yadda za a ba da tabbaci...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya. A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya. Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus. Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa —Gwamnatin Kano Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar...
    Jagunlabi ya ce za a gudanar da shirin ne tare da hadin gwiwar gwamnatocin jihohi domin mayar da wuraren tarihi zuwa wuraren shakatawa domin samar da kudin shiga wanda hakan zai haifar bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi a fannin fasaha da nishadi.   Ya bayyana cewa, aikin zai mayar da hankali ne wajen maidowa tare da kiyaye wuraren tarihi, kayayakin tarihi, da inganta ilimin al’adu da inganta sana’o’in cikin gida. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    “Da farko na ki amincewa saboda hakan ya saba wa tsarin kamfanina, amma bayan na yi tafiyar kusan kilomita biyu sai na ji hakan bai dace ba kuma ‘yan uwana ne daga Jihar Kano, sai na koma na dauke su,” inji direban.   A cewarsa, sun yi tafiya cikin lumana har suka iso Uromi, inda ’yan banga suka tare su. Daga nan ne, shugaban ‘yan bangar ya fara yi wa direban tambayoyi game da kayan da ya dauko da kuma fasinjojin sa. Duk da gabatar da takardar sahalewar hanya amma shugaban ‘yan bangar ya nuna zargi kan mafarautan, musamman saboda makamansu da karnukan da su ke tare da su a cikin motar.   Saboda haka, “Shugaban ‘yan bangar bai amince...
      Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Masarautar Zazzau ta sanar da soke Hawa Bariki a wannan sallar ta bana — daya daga cikin haye-hayen shagulgulan Sallah na al’ada da masarautar ke gudanarwa a washegarin idin karamar Sallah. A bisa al’adar Hawan Bariki, Sarkin Zazzau ya kan kai wa Gwamna gaisuwar sallah tare da duk hakimansa yayin da mazauna za su yi dakon wadanda ke haye-hayen dawakan a gefen titi su ma suna yi wa Sarki gaisuwar ban girma. Nijar ta fice daga rundunar MNJTF mai yaƙi da masu iƙirarin jihadi NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Komawa Cin Abinci Yadda Ya Kamata Bayan Watan Ramadana Sarki yakan jagoranci tawagar masarautar ta Zazzau inda zai ratsa ta cikin garin Zazzau sannan ya shiga unguwar Sabon Gari inda zai ziyarci...
    A safiyar yau litinin ce a nan Iran da kuma wasu kasashen duniya da dama suka gudanar da sallar Idi wanda ya kawo karshen watan Ramadan mai al-farma wanda musulmi suka yi azuminsa daga safe zuwa faduwar rana na tsawon kwanaki 29-ko 30. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya bayyana cewa a nan Tehran dubban daruruwan mutanen suka fito zuwa babbar masallacin Imam Khumaini dake tsakiyar birnin Tehran inda suka gudanar da sallah mai raka’o’I biyu tare da jagorancin Jagoran juyin juya halin musulunci a kasar Imam Sayyid Aliyul Khamina’e. Duk da cewa ana samun babbanci tsakanin musulmi kan ranar ajiye azumun amma akalla ba wanda zai yi azami kasa da kwanaki 29. A cikin watan dai, musulmi...
    Jam’iyyun siyasa a kasar Gabon sun fara yakin neman zabe wanda za’a gudanar a ranar 12 ga watan Afrilu na wannan shekara ta 2025 a jiya Asabar. Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya nakalto shugaban kasar Riko Brice Clotaire Oligui Nguema wanda ya jagoranci juyin mulki wa tsohon shugaban kasar Ali Bongo, sannan daga baya ya sauka don ya sake dawowa da hanyar zabensa ya fara yakin neman zabe a jiya, inda yake kira ga mutanen kasar su zabe shi saboda kyautatuwar kasar Gabon. A cikin watan Augustan shekara ta 2023 ne sojoji suka kifar da gwamnatin Ali Bongo wanda ya gaji babansa Umar Bongo bayan rasuwarsa ba tare da zabe ba. A halin yanzu dai yan takara...
    Kungiyar bada agaji ta RED CROSS ta yi allawadai da HKI saboda kissan likitoci 8 a garin Rafah na kudancin gaza a ranar 23 ga watan Maris da muke ciki. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a jiya lahadi bayanda aka basu daman dauko gawakin likitocin wadanda suka rasa rayukansu a cikin watan Motar amblance ta daular marasa lafiya. Labarin ya bayyana cewa lokitocin suna kan hanyarsu ta zuwa unguwar Hashasha inda HKI ta kai hare-hare kan Falasdinawa don basu taimakon gaggawa. Banda haka sai da aka dauki mako guda cur da kashe likitocin kafin sojojin yahudawan su bada damar a dauki gawakin nasu. Ya zuwa yanzu dai tun bayan fara yakin Tufanul...
    Bayanai da ma’aikatar sufuri ta kasar Sin ta fitar a jiya Asabar sun nuna cewa, a shekara ta 2024, yawan kayayyakin da aka yi hada-hadarsu a tashoshin jiragen ruwa na kasar ya kai tan biliyan 17.6, kuma yawan kwantenan da aka yi hada-hadarsu ya kai miliyan 330, hakan ya sa kasar ta ci gaba da kasancewa a matsayi na farko ta fannin a duniya. Har wa yau, daga cikin tashoshin jiragen ruwa 10 da suka fi hada-hadar kayayyaki a duniya, akwai tashoshin jiragen ruwan kasar Sin guda 8, ta fannin hada-hadar kwantenoni kuma, guda 6 na kasar Sin ne. (Mai fassara: Bilkisu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Watan azumin Ramadana kan zo da sauye sauye da dama da suka haɗa da ƙara ƙaimi wajen bauta wa ubangiji, samun lada ta hanyar ciyar da al’umma da kuma falala masu yawa da ba su misaltuwa. Wani sauyi da watan azumin watan Ramadana ke zuwa da shi shi ne canjin yanayin cimar al’umma, inda mutane ke canzawa daga cin abinci sau uku ko sama da haka a rana zuwa sahur da kuma buɗe-baki. Bayan kwanaki 29 zuwa talatin na samun waɗannan canji, ta waɗanne hanyoyi ne al’umma za su koma cimaka kamar yadda suka saba gabanin watan Ramadana NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Musulmi Su Yi Kafin Da Kuma Ranar Sallah...
    Watan Ramadan mai alfarma na wannan shekara ya zo ni’imomi masu Yawa wanda matasa da sauran mutanen kasa sun amfani da ayyukan ibada wadanda suka hada da karatun Alkur’ani mai girma, mun yi addu’o’I mun kuma yi magana da All..mun roke shi a cikin watan. Da fatan All..ya karbi ayyukammu. Amma a wani bangare a cikin wannan Ramadan, duk tare da jin dadin da muka samu, amma watan yana tattare da dacinsa, kissan mutanen Falasdinu, tare da goyon bayan Amurka. Kasashen yamma suna tuhumar Iran tana amfani da sojojin wadanda suke wakiltantan a abinda yake faruwa a yankin. Amma gaskiyar al-amarin sune suke da wakili a wannan yakin, kuma itace HKI, wacce taek wakiltansu a ayyukan ta’addanci da take yi...
    Yan wasan kwallon kafa na kasar Iran sun zama zakara karo na 4 a kwallon kafa na yashin bakin teku a karo na 4 a cikin kasashen Asiya. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ba bayyana a gasa ta karshe wanda kungiyar kwallon kafa ta yashin bakin take wanda aka gudanar tsakanin JMI da kuma Omman an tashi da ci 8-1. Wannan nasarar dai ta tabbatar wa kasar Iran fifiko a wannan wasar har saw hudu a jere. Kuma ba’a taba samun nasara a kan ta gaba daya a dukkan wasannin da ta yi a duk tsawon gasar ba. Mai horar da yan wasan Iran a wannan gasar Ali Nadiri ya bayyanawa IP kan cewa nasarar da JMI ta...