Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, ya bayyana cewa sojojin ƙasar na tunkarar ’yan tawayen M23 da suka kaɗɗammar da munanan hare-hare tare da ƙwace ikon muhimman wurare a Birnin Goma da ke gabashin ƙasar.

Hare-haren mayaƙan M23 da ke samun goyon bayan ƙasar Rwanda sun kashe Gwamnan Birnin Goma, a makon jiya a yayin da dubban mutane ke gudun hijira domin tsira da rayukansu.

A ranar Laraba mayaƙan M23 suka ƙwace wasu yankuna biyu a Lardin Kivu da ke gabashin ƙasar, daga hannun sojoji.

A jawabinsa na ranar Laraba ta talabijin, Shugaba Tshisekedi ya zargi ƙasashen duniya kan rashin ɗaukar mataki kan lamarin, musamman hannun Rwanda a cikin lamarin, wanda ya ce katsalandan ne ga dimokuraɗiyya kuma yana iya ƙara munin al’amarin.

NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu Za a dawo da ’yan Najeriya sama da 5,000 da ke zaune a Amurka

Ƙazancewar halin da ke ciki a Gabashin kasar ta DR Congo ya haifar da fargabar ƙara taɓarɓarewar yanayin rayuwar ’yan gudun da matsalar abubuwan more rayuwa a ƙasar.

Amma a ranar Laraba Shugaba Tshisekedi ya bayyana cewa ’yan tawayen suna ɗanɗana kuɗarsu a hannun sojojin ƙasar mai arziƙin zinare da lu’ulu da sauran ma’adinai.

Shugaba Felix Tshisekedi, a jawabinsa na farko tun bayan faruwar hare-haren na M23 a tsawon makonni, ya bayyana cewa sojojin sun samu gagarumar nasara.

Gabashin ƙasar Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ya shafe shekaru sama da 30 yana fama rikici inda ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai ke addabar al’umma, baya ga tawaye ga gwamnati.

Ana alaƙanta wanna rikici da kisan kiyashi da aya auku a shekarar 1994 lokacin yaƙin basasa ƙasar Rwanda, maƙwabciyar DR Congo.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Mayaƙan M23 Rwanda

এছাড়াও পড়ুন:

BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa

Duk da haka, ɗalibai masu kammala makaranta sai sun jira amincewar Majalisar Jami’ar kafin su samu damar duba sakamakonsu.

Ana sa ran wannan ci gaba zai inganta ayyuka a Jami’ar da kuma sauƙaƙa wa ɗalibai gudanar da harkokin karatunsu cikin sauƙi.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu zai tafi ziyarar makonni biyu a Faransa
  • Muna samun galabar daƙile kwararowar baƙin haure — Jamus
  • Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
  • Iran: Larijani Ya Ce Iran Zata Fara Kera Makaman Nukliya Idan An Kai Mata Hari Kan Shirin Ta Na Makamashin Nuliya
  • DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Arewa Ke Tafiya Kudu Farauta
  • BUK Ta Ƙaddamar Da Shafin Intanet Da Ɗalibai Za Su Ke Duba Sakamakon Jarrabawa
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  •  Larijani:  Dole Iran Ta Kera Makaman Nukiliya Idan Amurka Da Isra’ila Su Ka Kawo Ma Ta Hari
  • HKI Ta Sake Kai Wa Unguwar Dhajiya Dake Beirut Hari
  • Gaza : Fiye da mutane 1,000 Isra’ila ta kashe tun daga ranar 18 ga Maris