2025-03-03@16:53:30 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9

«Rwanda»:

    Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar...
    Manyan jami’an MDD dake aiki a nahiyar Afirka sun yi gargadi a yayin taron gaggawa na kwamitin tsaro akan cewa hare-haren da ‘yan tawaye masu samun goyon bayan Rwanda suke kai wa a gabashin DRC, zai iya haddasa yakin da zai  hada kasashe da dama na yankin. ‘Yar sakon musamman ta MDD a DRC, Bintu...
    Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango ta yanke shawarar rufe sararin samaniyarta ga “dukkan jiragen sama na farar hula ko na gwamnati masu rijista dake zaune a Rwanda”. A cewar Kamfanin Dillancin Labarai na Kwango, matakin ya “hana shawagi da sauka a cikin kasar ta Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, saboda dalilai na rashin tsaro da ke da nasaba da...
    Shugabannin kungiyoyin raya kasashen gabashi da kuma kusanci na Afrika (EAC da SADC), sun yi kira da a gaggauta tsagaita wuta a gabashin Jamhuriyar DR Congo. Bangarorin sun bayyana hakan a wani taron hadin guiwa da suka gudanar a birnin Dar es Salaam, na kasar Tanzania a jiya Asabar. A cikin wata sanarwar hadin gwiwa...
    Yau Asabar shugabannin kasashen raya tattalin arzikin kasashen Gabashi da Kudancin Afrika EAC da SADC za su gana a birnin Dar es Salaam na kasar Tanzaniya domin tattauna rikicin gabashin DRC. Shugaban kasar Kenya, William Ruto, dake jagorantar kungiyar EAC, ya sanar da halartar takwarorinsa na Congo da Rwanda. Tun da farko a ranar Juma’a,...
    A yau ne ake sa ran kwamitin kare haƙƙin dan adam na MDD zai yi zaman gaggawa kan yaƙin da ya rincabe a jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo. Ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya dai sun karɓe iko da birnin GOMA. MDD ta yi ƙiyasin cewa sama da farar hula 2,900 ne aka kashe,...
    Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo...
    Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da...
    Shugaban kasar Kenya William Ruto a wata sanarwa da ya fitar ya sanar da cewa, zai gudanar da wani babban taro na musamman na kungiyar kasashen gabashin Afirka EAC a cikin sa’o’i 48 masu zuwa tare da halartar shugaban kasar Congo Félix Tshisekedi da shugaban Rwanda Paul Kagame. Taron dai na zuwa ne a daidai...
۱