Leadership News Hausa:
2025-04-03@02:11:11 GMT

Cece-kuce Ya Barke Kan Shirin “Kur’anic Convention”

Published: 31st, January 2025 GMT

Cece-kuce Ya Barke Kan Shirin “Kur’anic Convention”

“Kazalika, wasu kuma da suke da haddar Alkur’anin; ciki har da wadanda suka rubuta shi da hannunsu, ba a samun wata mahada da ake haduwa. Wannan dalili ne ya sa in sha Allahu, muka sanya kafin watan Azumi; dukkanin kungiyoyin addinin musulunci, babu abin da zai iya hada mu kamar Alkur’ani. Alkur’ani ya hada mu, ba mu da banbanci da kowa, domin kowa ya yarda da shi, in ji shi.

“Don haka, muna sa ran mahaddata Alkur’ani sama da 30,000, za su shigo garin Abuja, daf da sati guda kafin Ramadan a yi ‘Festival’ na Alkur’ani, mu ji sautuka daban-daban; domin kuwa akwai sautuka irin na Yarbawa, wanda idan suna yi suna jin dadi tare da motsawa, akwai kuma sauti irin na Larabawa, wanda shi ma idan an ji; ana motsawa da kuma sauti irin na su Alaramma, wato na gargajiya”, in ji Bala Balau.

Wadannan jawabai na Shugaban Kungiyar Izala, sun yi matukar tayar da kura tare da haifar da cece-kuce, domin kuwa da dama daga cikin mabiya kungiyar, sun yi wa shugaban nasu tawaye tare da bidi’antar da shirin.

Haka nan ma, a tsagin Darikar Tijjaniyya; Halifan Sheik Dahiru Usman Bauchi, Sheik Ibrahim; shi ma ya yi karin bayani a kan wannan biki da aka shirya na ‘Kur’an Festibal’, inda ya bayyana shirin da cewa, an kawo shawarar shirya shi ne; domin yin godiya ga Allah SWT, da ya azurta Nijeriya da mahaddata Al’kur’ani fiye da sauran dukkanin kasashen duniya.

“Wannan dalili ne yasa, wasu ‘yan’uwa suka kawo shawarar aiwatar da wannan biki, domin yi wa Allah godiya da wannan baiwa da ya yi wa Nijeriya. Shi yasa muke so in sha Allahu, za a tara mahaddata Alkur’ani a Abuja, ranar 22 ga watan Fabrairu, 2025, wanda ya yi daidai da 23 ga watan Sha’aban na shekara ta 1446, a Sitadiyom ; domin aiwatar da wannan biki”, in ji Sheik Ibrahim.

Har ila yau, Sheik Sani Yahya Jingir, guda cikin manyan jagororin Izala a Nijeriya, shi ma ya soki wannan shiri na ‘Kur’anic Festival’, da ake kokarin shiryawa, inda ya yi kira ga wadanda ragamar ke hannunsu, da sunan ‘yan damfara.

Jingir ya bayyana cewa, da dama daga cikin wadanda ake so a gayyata daga cikin mahaddata kur’anin, bai yadda da musuluncinsu ba, domin kuwa ya kira su da sunan Bokaye da Matsafa.

“Masu zagin Alkur’ani, suna auna shi da turare; su ne masana kur’ani, wadanda a gidansu aka fito aka zagi kur’anin a Kano; aka kuma yanke hukuncin kisa ta ridda a kansu, su ne masu haduwa su karanta Alkur’anin? Ko kuwa masu karanta kur’anin suna kada ganga suna watayawa tare da rausayawa, su ne masu karanta kur’anin?” tambayar da Sheik Jingir ya yi.

Shi ma, wani mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum a Nijeriya, Sani Ahmad Zangina, ya yi nuni da cewa; babu wani abu a cikin wannan shiri na ‘Kur’anic Festival’, illa zallar siyasa; wanda kawai malamai suka karbo kwangilarta, domin cika aljihunansu.

“Babban abin lura a nan shi ne, tunda an ce shiri ne da ya hada dukkanin alarammomin Nijeriya, idan ka kawo ‘yan Izalar Jos da na Kaduna, ‘yan Shi’a, ‘Yan Kala-kato da kuma sauran ‘yan Dariku, idan aka tashi yin sallar azahar a wajen taron, wane ne zai yi limanci?, tunda dai babu yadda za a yi a ce an yi taron har an tashi ba a yi sallah ba.

“Don haka, wannan taro na siyasa ne; babu komai a cikinsa idan ba siyasa ba. Saboda haka, mu abin da muke kallo shi ne, a tsaya a yi abin da ya kamata, domin kuwa a dan sanin da muke da shi; muna ganin ba daidai ba ne a yi wasa da wannan littafi na Allah, musamman wajen sayar da ayoyinsa, saboda wani abu na duniya”.

“Don haka, batun wannan ‘Kur’anic Festival’; akwai ayar tambaya a ciki, ya kuma kamata malamai su rike girmansu da mutuncin da suke da shi, musamman a irin wannan lokaci da zarge-zarge suka yawaita a kansu”, in ji Zangina.

Ya ci gaba da cewa, Alarammomin da ake so a dauko a kawo Abuja daga jihohinsu, musamman daga Arewacin Nijeriya, yankunan da suke fama da yunwa da matsalolin tsaro, kyautuwa ya yi a taimako, ba wannan yaudarar ba.

“Maimakon a ce kowane Alaramma da za a dauko daga jiharsa a kawo shi Abuja, idan misali Naira miliyan daya za a ba shi; mai zai hana ba za a ba shi kudin, amma ya yi zamansa a garinsu ya yi addu’ar a can ba, maimakon sai ya zo Abuja ya kashe akalla dubu dari ko dari biyu? Don Allah, kada mu yaudari kanmu ko mu yaudari Allah, tunda shi ne mafi sanin abin da yake ranmu”, in ji shi.

Har ila yau, ya kara da cewa, wannan taro na ‘Kur’anic Festibal’, ba shi da wata fa’ida; illa ma cutarwa, domin kuwa an samu zubewar mutunci, musamman daga wurin malaman da ke kan gaba-gaba wajen ganin an yi taron.

Ya sake bayyana cewa, ko da ba a zargin akwai siyasa a cikin wannan taro, a irin wannan lokaci na siyasa da ake bukatar jama’a, ku san kowa zai iya kallon taron da ido daya. Saboda haka, magana ta gaskiya ita ce, tunda an ce hadin kai ake nema; kada a ce saboda Al’kur’ani za a zo a yi taro, sannan kuma gobe a zo ana barranta tare da tsinewa juna, a cewar Zangina.

Dakta Ahmad Gumi, shi ma ya tofa albarkacin bakinsa a wannan dambarwa da ke ci gaba da daukar hankulan al’umma ta hanyar sukar shirin na ‘Kur’anic Festival’, inda ya bayyana shi a matsayin wata sabuwar bidi’a da aka bullo da ita.

“Kur’ani, ba ya bukatar biki; domin kuwa, zuciyarmu kullum cikin bikin kur’ani take, tun daga safe da za ka tashi ka yi ‘yan nafilfilolinka; idan mai yin nafilar ne, ko ka yi raka’atanil fijir, ka yi sallar asubahi, ka yi azakar, ka yi azahar, ka yi la’asar, ka yi magariba har zuwa sallar isha’i, wannan na nuna cewa; dukkanin rayuwarka Alkur’ani ce.”

“Saboda haka, ya kamata malamai su rika yin shawara; su kuma daina yin gaggawa, duk da cewa; da yawansu ba su san yadda aka kafa Sunnah ba. Sannan, wadannan malamai suna da rauni guda biyu, na farko; idan suna gaban shugaba da zarar sun fahimci ya karkata a kan wani abu da yake so, nan take sai su fara karanto ayoyi da hadisan da suka karkata a kan abin da shugaban yake so”, in ji Gumi.

Haka zalika, rauni na biyu kuma da malaman ke da shi a cewar Sheik Gumin shi ne, ga masu kudi, nan ma da zarar sun fahimci hankalin mai kudi ya karkata kan wani abu da yake so, nan take za su fara jawo ayoyi da hadisai, domin su kara karfafa shi ta yadda zai karfafi wannan abu da yake so.

“Babban abin lura a nan shi ne, ana so a kashe biliyoyin kudi a wajen wannan taro ta hanyar tara wadannan Mahaddata, domin su zo kowa ya baje kolinsa ko gwanintarsa. Don haka, ya kamata a san cewa, ka fito ka nuna kai Mahaddaci ne ma kadai, wannan raina Alkur’ani ne.

“Sannan kudaden da za a kashe, mai zai hana a je a gyara tsangayoyin da muke da su, ko kuma shi kansa malamin tsangayar a saya masa gida, domin ya ji dadin ci gaba da koyar da Alkur’anin? Saboda haka, wannan kirkirarriyar bidi’a ce. Sannan kuma, muna fata kungiyar Izala za ta rika yin shawara kafin aiwatar da duk wani abu da ya taso.

Kazalika kuma, ina kyautata zaton cewa; wannan taro ba siyasa ba ce, illa kawai dai wani mai kudi ne da yake ganin kamar yin wannan wani abu ne mai kyau, amma kuma babu wanda ya ankarar da shi tare da fada masa gaskiyar cewa, yin hakan ba daidai ba ne, in ji Gumi.

A gefe guda kuma, kamar yadda ‘yan Izala ke ci gaba da yi wa ‘yan’uwansu raddi kan wannan shiri na ‘Kur’anic Festival’, shi ma Imam Ali Abulfatahi, ya yi wa Sheik Ibrahim Dahiru Bauchi nasa raddin, a matsayin kira da kuma nasiha ga shugabannin Darikar Tijjaniya, wanda ya bayyana cewa; su ne alkiblarsu a nan gaba.

”Idan wannan ta kasance ita ce tafiyar Darika, to kuwa ko shakka babu; a nan gaba hoton Darika ba zai yi kyau ba, domin kuwa; iyayenmu da sauran Shehunanmu, ko kadan ba wannan ce matafiyarsu ba. Saboda haka, Ya Ibrahim; a irin wannan matafi da ake ciki a Darika, ana bukatar shawara ko tuntuba, domin a Nijeriya akalla akwai ‘yan Darikar Tijjaniyya sama da miliyan sittin zuwa saba’in, Almajiran Shehu Tijjani da Shehu Ibrahim.”

“Akwai maganarka da na ji kana cewa, a Darika kowa ya san na gaba da shi; babu shakka wannan gaskiya ka fada, shi yasa yau babu wanda zai fito a Darika ya ce shi ne shugaba, illa kawai dai kowa ya san na gaba da shi, sannan Allah ya sanya wa ‘yan Darikar tsananin biyayya ga na gaba da su; shi yasa farkon Darika ya zama ladabi, tsakiyarta ladabi, haka nan ma karshenta ladabi; wannan ne yasa abubuwa da dama suke faruwa da mu sakamakon wannan ladabi da muke da shi.

“Saboda haka, babu yadda za a yi ka zauna a Kasar Ingila, duk kuwa da irin yawan wadannan al’ummar da muke da su a Darika, kai kadai ka wakilce su; su sama da kimanin miliyan 60 zuwa 70, ba tare da ka shawarci kowa ba; ka yi garkuwa da Maulana Sheik Dahiru Usman Bauchi, ka ce shi ne ya fadi haka, saboda ka san cewa dole ne mu ce mun bi, tunda a dukkanin fadin wannan kasa ba mu da tamkarsa.

“In dai kuwa za a ci gaba da tafiya a haka, babu yadda za a yi Darika ta dunkule wuri daya, sau da dama idan aka kawo sukar Alhaji Ibrahim, dan maulana Sheik Dahiru Usman Bauchi, na kan ce; a yi masa uzuri, domin dama ya samu. Sannan, kashi 85 cikin 100 na ‘ya’yan Shehunanmu, duk wanda ya samu irin wannan dama, ko shakka babu; zai yi amfani da ita, duk da cewa ba a taru an zama daya ba, amma dai ya kamata mu sani duk abin da yake da farko, yana da karshe.”

Abulfatahi ya ci gaba da cewa, yanzu Sufanci da Darika sun yi gabas, su kuma sun yi yamma; saboda irin abubuwan da suke faruwa marasa dadi na son kai ko son zuciya. Babu tsoron Allah yanzu, babu zuhudu da kyawawan dabi’un da aka kafa a Darika ko Sufanci, wannan shi ne martanin na Abulfatahi ga Sheik Ibrahim Dahiru Usman Bauchi.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Siyasar addinni Tsangaya Sheik Ibrahim irin wannan wannan taro

এছাড়াও পড়ুন:

Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano

Har yanzu dai kisan wasu matafiya ’yan Arewa da aka yi a garin Uromi da ke Ƙaramar Hukumar Arewa maso Gabashin Esan ta Jihar Edo na ci gaba da tayar da ƙura a faɗin Nijeriya.

A bayan nan ne wasu hotunan bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta suka nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna far wa matafiyan da suka taso daga Kudanci zuwa Arewacin Nijeriya.

Hotunan bidiyon sun nuna yadda aka yi wa waɗanda abin ya shafa jina-jina sannan aka cinna musu wuta suka ƙone ƙurmus.

Gwamnan Edo ya kai ziyarar jaje Kano

Gwamnan Kano ya karɓi baƙuncin takwaransa na Edo, Monday Okpebholo wanda ya ziyarci jihar domin jajanta wa gwamnati da al’ummar dangane da kashe mafarautan da wasu ’yan sa-kai suka jagoranta a jiharsa.

Da yake sake bayyana takaicinsa, Abba ya buƙaci gwamnan na Edo ya gaggauta gurfanar da waɗanda aka kama kan kisan matafiyan a bainar jama’a.

Abba ya kuma yaba wa yadda Mista Okpebholo ya gaggauta tashi-tsaye kan lamarin da a yanzu har an cafke wasu mutum 14 da ake zargi da aika-aikar.

‘Muna so a nuna wa duniya fuskokin mutanen da aka kama’

Sai dai gwamnan na Kano ya ce “bayan kama su muna kuma so a yi holensu a bainar jama’a domin duniya ta ga fuskokin waɗanda suka yi wa ɗanyen aiki.” Ya nanata cewa Jihar Kano tamkar wata cibiya ce ta zaman lafiya “saboda haka muna gargaɗin duk ’yan Nijeriya cewa ƙasar nan ta kowa ce.”

Ya buƙaci shugabanni da su haɗa kai wajen ganin ba a sake maimaita irin wannan mummunan lamari ba a ko’ina a faɗin ƙasar, “saboda haka muna kira mahukunta sun ɗauki mataki mai tsauri a kan irin wannan.”

Da yake nasa jawabin, Gwamna Okpebholo ya ce za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin an bi kadin rayukan da aka kashe, yana mai cewa a halin yanzu tuni an kama wasu mutum 14 da ake zargi kuma za a miƙa su Abuja domin ci gaba da bincike.

Kazalika, ya ce ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin Hausawa da duk wasu ƙabilu da ke zaune a jihar ta Edo.

Za mu tura tawaga ƙauyen Torankawa — Gwamnatin Kano

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa zai tura tawaga ta musamman zuwa ƙauyen Torankawa domin jajanta wa iyalan mafarautan da aka kashe a Jihar Edo.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin saƙonsa na barka da sallah kamar yadda mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a jiya Lahadi.

Tun a jiya ne daman wasu majiyoyi daga fadar Gwamnatin Kano ta ce ana kuma sa ran karɓar baƙuncin Gwamnan Edo domin jajanta wa gwamnatin da kuma iyalan waɗanda lamarin ya shafa.

Al’ummar Edo a Kano sun yi Allah wadai da lamarin

Ƙungiyar al’ummar Edo mazauna Jihar Kano ta yi tir da faruwar lamarin, tana mai neman da a bi wa waɗanda lamarin ya shafa haƙƙinsu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun ƙungiyar, Mista Philip Tomon ya fitar, ya jajanta wa iyalan mafarautan da aka yi wa kisan gillar yana mai kiran mahukunta da su tabbatar an yi adalci a lamarin.

Ƙungiyar Mafarauta ta jingine zanga-zanga

A wata sanarwa da Sakataren Ƙungiyar Mafarautan Kano, Usman Mu’azu Abdullahi Yakasai ya fitar, ya ce sun jingine zanga-zangar da suka shirya gudanarwa.

Sai dai sakataren wanda aka fi sani da Alaska duk da tana cikin alhini ta jingine zanga-zangar ce bayan tuntuɓe-tuntuɓen da ta yi, inda ta miƙa wa Gwamnatin Kano ƙorafi a hukumance na neman yi wa waɗanda aka kashe adalci.

Alaska ya ce ƙungiyar ta gamsu da irin matakan da ake ɗauka wajen tunkarar lamarin, kuma tana fatan doka za ta yi aiki yadda ya kamata.

Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya dakatar da Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro a jihar Friday Ibadin, biyo bayan kisan da aka yi wa mafarauta 16 ƴan asalin yankin arewacin kasar a alhamis da ta gabata.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Umar Musa Ikhilor ya fitar mai cewa an ɗauki matakin ne la’akari da bayanan da ke ƙunshe a rahoton binciken farko da aka gudanar dangane da wannan lamari, wanda ya yi matuƙar girgiza jama’a a Najeriya.

“Lura da abubuwan da suka faru a ranar ta 27 ga watan Maris na 2025 a garin Uromi na ƙaramar hukumar Esan, inda aka samu asarar rayukan wasu matafiya, Mai Girma gwamna Monday Okpebholo, ya bayar da umurnin dakatar CP mai ritaye Friday Ibadin, Kwamandan Rundunar Samar da Tsaro ta jihar daga matsayinsa,’’ a cewar sanawar.

An rusa duk ƙungiyoyin ’yan bangar da ba su da rajista

Har ila yau, sanarwar da Sakataren Gwamnatin jihar ta Edo ya fitar ta ƙara da cewa an rusa ilahirin ƙungiyoyin ’yan banga da ba su da rajista a jihar, biyo bayan wannan kisa.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ’yan bangar da suka aikata wannan ta’asa, suna aiki ne ƙarƙashin inuwar wata ƙungiya da ba ta da rajista, saboda haka ya zaman wajibi a ɗauki wannan mataki don tabbatar da samar da yanayi na tsaro a jihar.

Mahukuntan Edo na tattaunawa da takwarorinsu na Kano kan lamarin

Yanzu haka ana ci gaba da bincike dangane da wannan lamari, kuma tuni aka kama mutane 14 da ake zargi, yayin da ake farautar wasu mutane da dama da suka arce kamar dai yadda Babban Sufeton ’yan sandan Nijeriya ya bayar da umarni.

Gwamnatin Edo ta ce tana ci gaba da tattaunawa da dangin marigayan, da kuma mahukuntan jihar Kano, lura da cewa mafi yawan ’yan asalin jihar ne, tare da ɗaukar alƙawarin cewa za a tabbatar da adalci ta hanyar hukunta waɗanda aka sama da laifi.

Bayanan da suka fito fili bayan faruwar wannan lamari, sun tabbatar da cewa mafarautan sun fito ne daga Fatakwal da ke Jihar Ribas a hanyarsu ta zuwa Kano domin yin bukukuwan sallah a cikin iyalansu.

‘Za mu tura ababen zargin 14 zuwa Abuja’

Gwamna Okpebholo a wata ziyara wannan Litinin ɗin da ya kai wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau a gidansa da ke unguwar Maitaima a Abuja, ya ce ababen zargin 14 da aka kan alaƙa da kisan matafiyan za a garzaya da su Abuja domin ci gaba da bincike.

Da yake nasa jawabin, Sanatan Barau mai wakiltar Kano ta Arewa a Majalisar Dattawan, ya yaba wa ƙwazon gwamnan kan matakan da yake ci gaba da ɗauka tun bayan faruwar wannan mummunan lamari domin ganin waɗanda ke da hannu a cikinsa sun fuskanci hukuncin shari’a.

Ya zama dole a hukunta masu laifi a lamarin — CAN

Ƙungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) ta yi tir da Allah wadai dangane da kisan da aka yi wa mafarauta 16 a lokacin da suke ratsa jihar Edo a hanyarsu ta komawa a arewacin ƙasar.

A sanarwar da ta fitar ɗauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Archbishop Daniel Okoh a ranar Lahadi, da farko CAN ta isar da saƙon nuna alhini zuwa ga ƴan uwa da aminan waɗanda suka rasa rayukansu, daga nan kuma ta yi kira ga mahukunta da su ɗauki matakan da suka wajaba domin tabbatar da cewa ana aiki da doka da kuma cusa wa jama’a ra’ayin yarda da tsarin shari’a na ƙasar.

Daga nan sai sanarwar ta ce ‘’alhaki ya rataya a wuyan gwamnati domin tabbatar da cewa an gudanar da bincike da nufin hukunta waɗanda ke da hannu a wannan lamari da za a iya bayyana shi a matsayin mummunan cin zarafin bil Adama’’.

Har ila Ƙungiyar ta Kiristocin Najeriya ta isar da saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi dangane da bukukuwan sallar da suke yi bayan sun kammala azumin watan Ramadan.

Ƙungiyar Amnesty International mai fafatikar kare haƙƙin ɗan Adam ta ce dole binciken da za a yi, ya zama sanadiyar hukunta waɗanda suke da hannu a kisa tare da ƙona matafiya ’yan arewa da aka yi a garin Uromi da ke Jihar Edo.

Shugaban ƙungiyar a Nijeriya, Isa Sanusi ne ya bayyana haka, inda, “dole hukumomin Najeriya su tabbatar an gudanar da bincike a bayyane, sannan kuma binciken ya zama silar adalci ga waɗanda aka kashe da iyalansu.

“Ya kamata a riƙa bayyana yadda binciken ke gudana tun daga farko har zuwa lokacin yanke hukunci.”

Amnesty ta ce abin da ya faru Uromi na nuna yadda ake ƙara samun ƙungiyar ’yan sa-kai na garuruwan da suke kusa da manyan hanyoyi suke tare hanyoyin suna aikata ba daidai ba.

“Yadda aka daɗe ana irin waɗannan kashe-kashen na nuna akwai gazawar gwamnati wajen kare rayukan al’ummarta.”

Isa Sanusi ya ƙara da cewa Amnesty ta yi Allah wadai da kisan, sannan ya sake nanata kiransu ga gwamnatin Najeriya da ta ɗauki matakin da ya dace.

Dole a kawo ƙarshen kisan gillar da ake yi wa ’yan Arewa

Ƙungiyar dattawan arewa ta magantu kan kisan matafiya ƴan yankin arewa da aka yi a garin Uromi da ke jihar Edo, inda ta ce yankin arewa ya daɗe yana haƙuri da cin kashin da ake yi masa, amma kuma an kusa ƙure su.

Ƙungiyar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinta, Farfesa Abubakar Jika Jiddere ya fitar.

Sanarwar ta ce, “dattawan arewa sun damu matuƙa da kisan dabbanci da rashin tausayi da aka yi wasu mafarauta ƴan arewa da suke hanyarsu ta komawa gida arewa domin bikin sallah. Muna Allah wadai da wannan aika-aikar.

“Mun daɗe muna haƙuri da irin wannan cin kashin da ake mana a kudancin Nijeriya. Dole a kawo ƙarshensa haka,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa dole a kama waɗanda suka aikata laifin, sannan a musu hukunci a bayyane.

“Sannan dole a biya diyyar waɗanda aka kashe kamar yadda yake a addinance, sannan dole gwamnatin Edo ta fito ta bayar da haƙuri.”

Dattawan sun kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta Edo ta cika waɗannan buƙatun nan da kwana da 14, “idan kuma ba a ga wani mataki ba zuwa lokacin, dattawan arewa za su yi amfani da duk matakan da suka dace wajen bin haƙƙin ƴaƴanta da aka kashe.”

A bi mana haƙƙi — ’Yan uwa

Wakilan Aminiya sun ziyarci ƙauyen Torankawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, inda suka zanta da wasu daga cikin iyalan mafarautan da aka kashe.

Wasu daga cikin iyalan mafarautan kuma mazauna ne a ƙauyukan ƙananan hukumomin Garko, Kibiya da Rano da ke Jihar Kanon.

Tun dai bayan samun labarin faruwar lamarin ne mazauna ƙauyen Torankawa da aka sansu da sana’ar farauta suka shiga cikin alhinin da suka ce ba su taɓa faɗawa makamancinsa ba.

Shida daga cikin mafarautan da aka kashe da wani ɗaya da ya tsallake rijiya da baya sun fito ne daga ƙauyen.

Daga cikin mamatan akwai Abdulkadir Umar, wanda ya rasu ya bar mata biyu da mahaifiyarsa.

Sai kuma Zahraddeen Tanko wanda ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu da kuma Haruna Hamidan wanda shi ma ya rasu ya bar mata ɗaya da ’ya’ya huɗu.

Akwai kuma Usaini Musa wanda ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya biyu da Abdullahi Harisu wanda ya yi aure watanni huɗu da suka gabata da kuma Ya’u Umaru da Abubakar Ado da ba su kai ga yin auren ba ma.

Duk ’yan uwan mamatan da Aminiya ta zanta da su sun bayyana alhini — wasunsu cikin hawaye suna roƙon mahukunta da su bi musu haƙƙinsu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Sabon Tsarin Harajin Kwastam Na Amurka Ke Shirin Gurgunta Tsarin Kasuwanci Na Duniya
  • Iran Ta Bukaci Hukumar IAEA Ta Bayyana Matsayinta A Shirin Makamashin Nukliya Na Kasar
  • Babu dokar da na karya saboda yin taro a mazaɓata — Natasha
  • Babu dokar da na karya saboda yin taron a mazaɓata — Natasha
  • Nigeria: Zazzabin “Lassa” Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 118 Tun Farkon Wannan Shekara
  • HOTUNA: Abba da Gwamnan Edo sun ziyarci iyalan mafarautan da aka kashe a Edo
  • Tsohon Gwamnan Zamfara Ya Bukaci A Ci Gaba Da Tallafawa Mabukata Bayan Ramadan.
  • Gwamna Abba Ya Nemi A Bayyana Fuskokin Waɗanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Edo
  • Muna so a nuna wa duniya mutanen da suka kashe ’yan Arewa a Edo — Gwamnan Kano
  • Gwamnan Edo Ya Ziyarci Sanata Barau Kan Kisan Yan Arewa 16