2025-04-27@18:08:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 2317
«Siyasar addinni»:
Ban da karuwar yawan wutar lantarki da aka samar ta aiki da makamashin nukiliya, karfin kasar Sin na yin kirkire-kirkire da kanta a wannan bangare ya kyautata matuka. A shekarar bara, Sin ta samar da dukkan muhimman sassan na’urorin samar da wutar lantarki masu aiki da makamashin nukiliya ta hanyar dogaro da kanta.(Amina Xu) ...
An kashe sojoji 12 a yankin Tillaberi na yammacin ƙasar mai iyaka da Mali da Burkina Faso, yankin da ke zama tungar masu iƙirarin jihadi da ’yan ina da kisa masu nasaba da ’yan ƙungiyoyin al Qaeda da IS. Ma’aikatar tsaron Nijar ta sanar da cewa an yi wa dakarunta na bataliyar ko-ta-kwana mai suna...
Sun ƙara da cewa, “Samun shugabannin matasa masu jajircewa a wannan yankin babbar albarka ce ga al’ummarmu. “Hakan na nuna mana cewa akwai kyakkyawar makoma ta ci gaba a Arewa gaba ɗaya.” Sannan sun bayyana cewa sun aike wa ƙungiyoyinsu a dukkanin jihohi 19 na Arewa goron gayyata domin naɗin sabbin muƙamai a Masarautar Daura....
Bugu da kari, an fi samun kyautatuwa a bangaren samar da kayayyaki, inda yawan ribar da aka samu a farkon watanni 3 na bana ya karu da 7.6%, saurin karuwar ya kai 2.8%. (Amina Xu) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Hakimin Kafin Hausa, Dan Amar na Hadejia, Alhaji Aliyu Usman Ginsau, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, bisa aiwatar da jerin manyan ayyuka a fadin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata. Hakimin ya yi yabon ne yayin bikin kaddamar da wani littafi a garin Kafin Hausa. A jawabinsa yayin taron, Gwamna...
Gamayyar Ƙungiyoyin Matasan Arewa, sun yaba wa Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk, bisa bai wa Nasir Bala Ja’o’ji muƙami a Majalisar Zartaswa ta Babbar Kwalejin Ilimi da Fasaha ta Tarayya, Potiskum, da ke Jihar Yobe. A wata wasiƙar taya murna da shugaban shiyyar ƙungiyar, Makama Dan Kaduna, ya sanya wa hannu bayan wani...
Rundunar ’yan sanda a Jihar Taraba ta cafke mutane tara kan zargin satar mutane. Haka kuma, rundunar ta gano bindigogi ƙirar AK-47 guda huɗu da kuma bindigogi ƙirar AK-49 guda uku da alburusai guda arba’in da biyar a hannun waɗanda aka cafke. Dalilin faɗuwar farashin kayan abinci a kasuwannin Arewa Ƙungiyoyin da suka yi shuhura...

Saboda In Nuna Wa Duniya Asalin Al’adar Bahaushe Ya Sa Na Fara Fina-finan Turanci A Arewacin Nijeriya – Jammaje
A wata hira da Jammaje ya yi da rfI Hausa an jiyo shi ya na cewa sunana Kabiru Musa Jammaje haifaffen Jihar Kano, nayi karatu a Bayero Unibersity da ke birnin Kano inda na karanci English kafin in tafi kasar Amurka domin zurfafa karatu, bayan na dawo gida Nijeriya kuma na shiga Jami’ar koyo daga...
“Muna kira ga sauran kungiyoyi, ‘yan siyasa, masu hannu da shuni tare da gwamnatoci, cewa kofarmu a bude take wajen neman taimakon kayan abinci, tufafi da makamantan su.” In ji Goni Alhaji Goni ya kara da cewa, gungiyar su ta direbobi, ta na da mambobin sama da 30,000 a fadin jihar Yobe. Ya ce,...
A wani hari da jirgin sama maras matuki da dakarun kai daukin gaggawa su ka kai akan sansanin ‘yan hijira a Jahar ” Nahrun-Nil” a Arewacin Sudan sun kashe mutane da dama da kuma jikkata wasu, haka nan kuma sun yi sanadiyyar yanke wutar lantarki a yankin. Kafar watsa labaru ta “al-muhakkak” ta ce; Dakarun...
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Musulmai ta Jihar Kaduna ta sanar da cewa dukkan mahajjatan da suka yi rijista domin aikin Hajjin 2025 dole ne su gudanar da binciken lafiya cikin wannan mako. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Yunusa Muhammad Abdullahi, ya fitar, inda...
Wannan wata mahawara ce da aka daɗe ana yi kan wace kungiya ce ta fi gawurta a Birtaniya? Shin wace kungiya ce ta fi lashe kofuna? Wacce ce ta fi tara kudin shiga ko kuma ta fi yawan mabiya a shafukan sada zumunta? Wace kungiya ce ta fi filin wasa mai girma? Wacce ce ta...
Sunana Fatimah Zahra Mazadu Daga Jihar Gomben Nigeria: Ba abun da ke janyo haka sai sakaci da rashin wayo, ta wani fannin kuma aljihu da halin maza dan suma suna nan a gari, za ka ga wata ta birgeka amma taka ta gida ka gagara kashe mata dan tayi kyau, sannan ba yadda za a...
Mai magana da yawun Gwamnan, Mamman Mohammed ya bayyana sakon a matsayin kirkirarre kuma marar tushe da makama, wanda yayi hannun riga da gaskiya, ta wane bangare a cikin wannan shaci-fadi. Ya ce ba a taba yin makamancin wannan sakon ba, kuma mai wannan maganar bai taba zama makusancin Gwamna ba, ballantana ya iya...
Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya bayyana cewa, ya zuwa yanzu ya yaba da yadda tattaunawa da Amurka kan shirin Nukliyar kasar yana tafiya kamar yadda ta dace. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ya nakalto Aragchi yana fadar haka bayan, bayan ya fito daga taron tattaunawa ta ukku wanda aka gudanar...
Ana kara samun karin ta’aziyya da kuma tallafa daga kasashen waje bayan fashewar da ta auku a tasahr jiragen ruwa na Dr Rajai a Bandar Abbasa. Tashar talabijin ta Press Tv ta nakalto ministan harkokin cikin gida Eskandar mumunina yana fadar haka, yana kuma cewa ya zuwa yanzu, mutane 14 aka tabbatar da mutuwarsu a...
Kungiyar Hamas a Gaza, ta yi allawadai da ma’aikatar sharia ta kasar Amurka wacce ta cire rigar kariya ga ma’aikatan hukumar bada agaji ta falasdinwa wanda MDD take kula da ita. Kungiyar UNRWA ta na bada agaji ga falasdinawa ne tun bayan kafa HKI da kuma korar Falasdinawa a karon farko daga kasarsu a shekara...
Shugaban kasar Iran Masoud Pezeskiyan ya bayyanawa firai ministocin kasashen Indiya da Pakistan a maganar da yayi da su ta wayar tarho a jiya Asabar, kan cewa mu hada kai gaba daya don yaki da ayyukan ta’addanci a yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Pezeshkiya yana fadawa shuwagabannin kasashen biyu, kan...
Sama da kwanaki hamsin da suka shuɗe ne aka aiwatar da sasanci a tsakanin wasu ’yan bindigar daji da al’ummomin da suka addaba don ganin an samu zaman lafiya a tsakanin yankunan. Sasancin, rahotannin da muka samu sun ce, jami’an tsaron Gwamnatin Tarayya ne suka shirya tare da tsara yadda za a yi shi karkashin...
Kwanan nan, wakiliyar CMG ta zanta da shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliyev wanda ya kawo ziyarar aiki a kasar Sin. A yayin zantawar, shugaba Aliyev ya waiwayi dadadden tarihin cudanyar kasashen biyu da ma zumuncin da ke tsakaninsu, kuma ya yi imanin da cewa, kasancewar dukkansu kasashe masu tasowa ne, kasashen biyu za su hada...
Kazalika, a cikin daukacin gwamnatin tarayya da kuma na jihohin kasar, an tsara yadda za su dakile kalubalen da fannin aikin noma da kuma yadda za a sama wa manoman kasar sauki, bunkasa rayuwar mazauna karkara da kuma habaka tattalin arzikin kasar. Akasarin manufar aikin na SAPZ shi ne, domin inganta aikin noma a...
“Abin takaici ne ganin yadda jami’an CJTF biyu da aka kashe a ranar Juma’a, sannan kuma wasu mutane 10 da suka je daji neman itace aka kashe su yau. “Mun riga mun birne mamatan kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, kuma an kwashe waɗanda suka ji rauni zuwa Maiduguri domin nema musu kulawar likitoci,” in...
Alkaluman zuba jari na kasashen waje sun hau kan mizani mai kyau a rubu’i na farko, a kan hakan kuwa, kasar Sin za ta kara bude kofarta domin maraba da jarin waje na duniya. Har ila yau ana sa ran karin kamfanonin waje za su zuba jari da gudanar da kasuwanci a wannan kasa mai...

Iran ta Bayyana cewa: TattaunawarMuscat Wata Dama Ce Ta Samun Zaman Lafiya Kan Batutuwan Masu Sarkakiya
Mai ba da shawara ga Jagoran juya juya halin Musulunci kan harkokin siyasa ya bayyana cewa: Tattaunawar Muscat wata dama ce ta samun zaman lafiya kan batutuwa masu sarkakiya Ali Shamkhani mai ba Jagoran juyin juya halin Musulunci shawara kan harkokin siyasa ya yi tsokaci kan tattaunawar ba na kai tsaye ba da ake yi...

Sojojin Mamaya Sun Yi Kasan Kiyashi A Zirin Gaza Da Kuma Ci Gaba Da Killace Falasdina Cikin Masifar Yunwa
Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kashe-kashen kisan kiyashi, kuma ana ci gaba da fama da yunwa a Gaza a daidai lokacin da kasashen duniya suka yi shiru An shiga rana ta arba’in da fara sabon farmakin da haramtacciyar kasar Isra’ila ke kai wa Zirin Gaza, a daidai lokacin da ake ci gaba da...
Kwamishina CP Ibrahim Maikaba ya yaba da ƙoƙarin jami’ansa, yana kuma ƙara jaddada niyyar rundunar na yin aiki tare da al’umma domin samar da tsaro. Ya buƙaci mutane su riƙa bai wa rundunar sahihan bayanai a kan lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka. Rundunar ta kuma fitar da lambobin da za a iya kira...
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da magance cin zarafin da Amurka ke yi ita kadai, ba wai kawai don kare hakki da moriyarta ba, har ma da kiyaye moriyar kasashen duniya. Ya bayyana hakan ne a jiya Jumma’a yayin ganawarsa da takwaransa na kasar...
Kazalika, ya ce, kasar Sin tana son kara zurfafa hadin gwiwa tare da IMF wato asusun ba da lamuni na duniya, da kuma ba shi goyon baya wajen taka muhimmiyar rawa a kan kiyaye tafiyar da tattalin arziki da hada-hadar kudin duniya cikin kwanciyar hankali. Bugu da kari, Pan ya jaddada bukatar gaggauta...

An Gudanar Da Dandalin Kirkire-kirkire Na Kafofin Watsa Labarai Na Duniya Karo Na 4 A Birnin Qufu Na Kasar Sin
A jiya Juma’a, an gudanar da taron dandalin tattaunawar kirkire-kirkire na kafofin watsa labaru na duniya karo na 4, wanda babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice da gwamnatin lardin Shandong dake gabashin kasar Sin suka dauki nauyin shiryawa a birnin Qufu na lardin. Taron dandalin mai taken...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar Sojin Najeriya ta samar da cewa dakarunta sun kashe ’yan ta’adda 1,770, sun kama wasu 3,070 a yankin Arewa maso Yamma a shekaru uku da suka gabata. Rundunar ta kuma yi nasarar ceto mutane fiye da 2,515 da harin ya rutsa da su ta hanyar gudanar da ayyukan haɗin gwiwa a jihohin da lamarin...
Manomin da zai shuka Irin noman Kanumfari, ana bukatar ya sa hakuri, idan har kana bai wa Bishiyarsa kulawar da ta dace, za ta iya shafe tsawon shekara 100 ko sama da haka. Ana bukatar wanda zai shuka shi, ya tabbatar ya shuka Irin noman a kasar noma mai inganci, sannan kuma yana daukar dogon...
Wani matashi mai shekaru 30 ya kashe kansa bisa rahotanni bayan rasuwar ƙaramar matarsa a ƙauyen Ikumi da ke Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja. Majiyoyi sun bayyana cewa magidancin mai mata biyu ya sha fama da matsalolin tunani da na zuciya tun bayan rasuwar matarsa ta biyu a watan Maris na wannan shekara. Sun...
Kungiyar kwallon kafa ta PSG – wadda tuni ta lashe gasar League 1 ta Faransa na daya daga cikin kungiyoyin da ake ganin za su lashe gasar Zakarun Turai ta bana saboda karfin da tawagar take da shi sannan kuma kungiyar a gine take hadi da kwararren mai koyarwa, Luis Enrikue, tsohon kociyan Barcelona da...
A dai-dai lokacinda kasashen Indiya da Pakisatn suke tada jijiyoyin wuta kan wani harin ta’addanci da ya kai ga mutuwar mutane 27 masu yawon shakatawa a yankin Kashmir na kasar Indiya, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi ya gabatar da tayin shiga tsakani don dai-daita tsakanin kasashen biy. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar...
Shugaban rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed Al-sharaa ya bayyana cewa gwamnatinsa a shirye take ta samar da hulda da HKI a dai-dai lokacinda ya dace. Jaridar Middle East Eye ta kasar Burtaniya ta nakalto Ahmed Sharaa yana fadar haka a wata wasikar da ya rubutawa shugaba Donal Trump Har’ila yau shugaba Al-sharaa ya fadawa...
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya nuna damuwarsa game da sake haduwa da ƙara ƙarfin mayakan Boko Haram a yankunan Tumbus na Tafkin Chadi da kuma tsaunukan Mandara a cikin dajin Sambisa. Yayin da yake jawabi ga Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, da manyan hafsoshin soji a Maiduguri, Gwamna Zulum ya yaba da ƙoƙarin...
Kasar Rasha ta fara tura iskar gasa zuwa kasar Iran ta kasar Azarbaijan, wanda daga karshe zai shiga kasuwan ga kasar ta rasah. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto gwamnatin kasar ta na fadar haka a yau Asabar. Labarin ya kara da cewa tun taron kwamin hadin guiwa na kasuwanci da tattalin...
Bayan ya sake daga sabowar tutar kasar Siriya a cibiyar MDD da ke birnin NewYork ministan harkokin wajen kasar Siriya Asaad Al-shaibani, ya gabatar da jawabi a gaban kwamitin tsaro na MDD a jiya jumma’a inda ya roki kwamitin ya dagewa kasarsa takunkuman tattalin arziki wadanda aka dorawa gwamnatin da ta shude. Jaridar Middle eart...

Dalilin Da Ya Sa Nijeriya Ke Ci Gaba Da Rike Kambun Kasa Na Mafi Yawan Samar Da Danyen Mai A Afirka — OPEC
A cewar kungiyar ta OPEC, wannan ya ya faru ne duk da raguwar yawan man da Nijeriya ta samar a watan da ya gabata, musamman idan aka kwatanta da ganga miliyan 1.46 a kowace rana a watan Fabrairun da ya gabata. Rahoton ya ci gaba da cewa, duk da raguwar, yawan Man da kasar...
Wannan dai, wani bangare ne na shirin kara habaka hada-hadar kawance tsakanin kasar da China. Kazalika, hakan na daga cikin yunkurin Gwamnatin Shugaban Kasa Bola Tinubu, na jawo masu zuba jari da yawansa ya kai kimanin dala biliyan daya a fannin habaka samar da Sikari a kasar. Bisa tsarin wannan yarjejeniya, kamfanin zai...
Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umaru Radda, ya gargaɗi sabbin masu yin hidimar ƙasa (NYSC) da aka tura zuwa jihar da su guji shiga ƙungiyoyin sirri, da ayyukan siyasa, da kuma nuna kiyayyar addini a duk tsawon lokacin hidimarsu. A cikin jawabin gwamnan, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan jihar Abdulkadir Mamman Nasir, ya gabatar a...
A wannan makon Aminiya ta samu tattaunawa da shahararren jarumi a masana’antar fina-finan Hausa ta Kannyood, Malam Inuwa Ilyasu, wanda ya shafe sama da shekara 40 yana harkar wasan kwaikwayo. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Gabatar da kanka? To da farko dai sunana Inuwa Ilyasu. Yaushe ka fara harkar fim? Gaskiya dai kusan da...
Mai Magana da yawun dakarun ‘Kassam” Abu Ubaidah ya sanar da cewa; sun harbo sojojin mamaya 4 ta hanyar wani kwanton bauna da su ka yi musu a Beit-Hanun. Kakakin dakarun na ” Kassam” ya kuma ce; Har yanzu suna ci gaba da kwamawa da ‘yan mamaya da kuma yi musu kwanton bauna a wurare...
Jiragen yakin HKi sun kai hare-hare da safiyar yau Asabar a birnin Gaza da hakan ya yi sanadiyyar samun shahidai da dama. Mutane 4 sun yi shahada a harin na jiragen ‘yan sahayoniyar akan wani gida dake unguwar “al-Sabrah’ a kudancin birnin Gaza. Haka nan kuma jiragen yakin na HKI sun kai wani harin da...
Ya koka kan halin da kasar ke ciki, kuma ya bukaci ‘yan arewa da su yi taka-tsantsan da ‘yan siyasa masu rarraba kawunan mutane da yaudara, gabanin babban zabe mai zuwa. “Muna son gwamnati da za ta fahimci matsalolinmu kuma ta magance su. Bayan shekaru takwas na mulkin Muhammadu Buhari, mun dauki darasi. ...
Ya kara da cewa kungiyar dattawan Arewa ba za ta lamunci cin zarafin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba. Sai dai da take magana da LEADERSHIP, ACF ta bayyana cewa kungiyar ba za ta goyi bayan duk wani dan takarar shugaban kasa a bainar jama’a a zaben 2027 ba. Da yake magana ta wayar...
A watan Janairu kawai, marigayi shugaban ‘yan fashin daji, Isuhu Yellow, ya sanya harajin naira miliyan 172.7 a kauyuka 25, ciki har da bukatar amfanin gona. A misali, an kakaba wa kauyen Gijinzama harajin naira miliyan 8.5, Dakolo naira miliyan 5 da buhunan wake 20, da Kibari, Kunchin Kalgo naira miliyan 20, Sungawa naira...

A Karon Farko A Tarihi Adadin Lantarki Da Sin Ke Iya Samarwa Ta Karfin Iska Da Hasken Rana Ya Zarce Wanda Ake Iya Samarwa Ta Amfani Da Dumi
Sashen masana’antun samar da sabbin makamashi na kasar Sin ya samu ci gaba cikin sauri a shekarun baya bayan nan, a gabar da ake ta aiwatar da managartan matakai na bunkasa tattalin arziki ba tare da fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi ba. Tun daga shekarar 2013, adadin kayayyakin samar da lantarki daga...
Gwamnan ya bayyana cewa ba za a yi amfani da kudin al’umma ba ga mutanen da ba za su iya kula da mahajjata yadda ya kamata ba. Gwamna Radda ya kara da cewa ya yi taro da shugabannin kananan hukumomi guda 34 domin tabbatar da cewa malaman da suka cancanta ne kadai aka zaba...