APC ta kori tsohon Gwamnan Osun, Aregbesola daga jam’iyyar
Published: 1st, February 2025 GMT
Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar.
Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar.
Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lauSun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun.
A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai suna “Omoluabi Caucus” ba tare da amincewar jam’iyyar ba.
Sannan ya yi furuci na ɓatanci ga shugabannin jam’iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, tsohon gwamna Bisi Akande, da kuma tsohon gwamna Gboyega Oyetola.
Kwamitin ladabtarwa na jam’iyyar ya rubuta wa Aregbesola wasiƙa, inda suka ba shi sa’o’i 48 ya mayar da martani kan zarge-zargen da ake masa.
Sai dai Aregbesola bai yi wani jawabi ba kan hakan ba, wanda ya sa jam’iyyar ta ɗauki matakin korarsa.
Wannan rikici ya ƙara nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara tsamari a jam’iyyar APC a Jihar Osun, musamman dangane da bambance-bambancen da ke tsakanin Aregbesola da wasu shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da na ƙasa.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Aregbesola Jihar Osun Kora Siyasa tsohon gwamna a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Hisbah Ta Kama Wasu Ma’aurata Da Suka Yi Aure A Asirce
Hukumar Hisbah ta damke wasu matasa a jihar Kano bisa laifin yin aure a asirce ba tare da sanin iyayensu ko amincewar iyayensu ba.
A cewar Sheikh Mujahid Aminudeen Abubakar mataimakin kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, ma’auratan sun yi aure ne a wani wurin shakatawa bayan wani ya dauki nauyin biyan sadaki.
Abubakar ya yi Allah-wadai da wannan auren, inda ya bayyana shi a matsayin wanda bai dace da addinin Musulunci ba, kuma ba a yarda da shi ba.
“Hukumar ta kama ma’auratan kuma za ta ci gaba da bincike tare da kame abokansu da kuma wadanda suka taimaka wajen auren sirri.”
Abubakar ya yabawa wadanda suka sanar da hukumar auren sirri, sannan ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani abu da ba a yarda da shi ba+ ga hukumomin da abin ya shafa.
Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, hukumar Hisbah ta jihar Kano na ci gaba da tabbatar da bin doka da oda a jihar.
Daga Khadija Aliyu