2025-02-01@19:05:54 GMT
إجمالي نتائج البحث: 9

«a jam iyyar»:

    Jam’iyyar APC a Jihar Osun, ta kori Tsohon Gwamnan Jihar kuma Tsohon Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola, bisa zargin cin amanar jam’iyyar. Wannan ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da shugabannin jam’iyyar na Ƙaramar Hukumar Ilesa ta Gabas suka gabatar. Yadda Kano ta koma matattarar ’yan TikTok bayan Hisbah ta daina kamensu Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Sun nemi a ɗauki mataki a kan Aregbesola saboda zargin kafa ƙungiyoyin da ke raba kan jam’iyyar da yin haɗin gwiwa da jam’iyyun adawa don raunana APC a Osun. A cikin wata wasiƙa da kwamitin zartarwa na APC na Osun ya aike wa shugaban jam’iyyar na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, sun bayyana cewa Aregbesola ya kafa wata ƙungiya mai...
    Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin  kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
    Jam’iyyar PDP ta yi irin wannan martani. Mataimakin shugaban matasan jam’iyyar PDP na kasa, Timothy Osadolor, ya ce furucin na Buhari ya nuna gazawar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu. Haka zalika, shugaban matasan jam’iyyar LP na kasa, Prince Kennedy Ahanotu, ya ce bai yi mamakin jawabin tsohon shugaban kasar ba, domin yana daya daga cikin ‘yan Nijeriyar da suka kasa daukaka kasar. Ahanotu ya kara da cewa, lokaci ya yi da ‘yan Nijeriya za su bai wa matasa damar gyara matsalolin da suka faru a baya. Ya ce, “Gaskiya ni ba masoyin Buhari ba ne kuma ban taba tsammanin zai yi abin kirki ba. Don haka ban yi mamakin cewa bai yi komai tsawon shekaru takwas ba. Amma abin da nake...
    An yi kokarin cire Damagum ta hanyoyin siyasa, ciki har da yiwuwar nada sabon shugaba daga yankin arewa ta tsakiya, amma hakan ya ci tura. Gwagwarmayar bangaranci dai ta kara dagula al’amuran cikin gida na jam’iyyar, inda aka samu bangaren masu biyayya ga fitattun mutane irin su tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar da ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Nyesom Wike. Wadannan rarrabuwar kawuna sun gaza samar da fahimtar juna, wadanda suka zama kalubalen da ya haifar da dakatarwar wasu daga cikin jami’an jam’iyyar. Yayin da watan Fabrairun 2025 ke gabatowa, masu ruwa da tsaki sun nuna damuwarsu na cewa PDP na fuskantar babban kalubale a gabanta.
    A kwanakin baya, jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyun adawa sun zargi APC da ruruta wutar rikicin da ke tsakaninsu, inda suka yi zargin cewa jam’iyya mai mulki na neman murkushe ‘yan adawa domin tabbatar da ci gaba da mulkin Shugaba Tinubu a 2027. APC ta musanta wadannan ikirari. Tun da aka hambarar da jam’iyyar PDP, jam’iyyun adawa sun yi yunkuri da dama amma ba su samu nasara ba. Na baya-bayan nan shi ne samar da wata sabon jam’iyyar siyasa mai suna ‘The Alternatibe’, domin tabbatar da madafun iko a babban zabe na 2027. Wani tsohon dan takarar shugabancin jam’iyyar PDP na kasa, Segun Sowunmi, wanda ke tallata wannan sabuwar jam’iyyar, ya ce an kafa jam’iyyar ne saboda ‘yan Nijeriya sun...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin shure-shure Jam’iyyar PDP take yi da ba ya hana mutuwa, ko kuwa motsi ne na alamun samun lafiya? Wannan ce tambayar da wasu ’yan Najeriya suke yi game da fito-na-fito da shugabannin jam’iyyar suka jima suna yi da juna. Tuni wasu ma suka fara ɗigaayar tambaya a kan makomar jam’iyyar bisa la’akari da tarin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta. NAJERIYA A YAU: Ainihin Dalilan Taƙaddama Kan Kafa Kotunan Musulunci A Kudu DAGA LARABA: Dalilan Da Mutane Suke Son Haihuwar Maza Fiye Da Mata Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai nazari don bankado abin da yake faruwa da jam’iyyar yayin da 2027 take kara matsowa. Domin sauke shirin, latsa nan
    Jami’an tsaro sun mamaye Sakatariyar Jam’iyyar PDP, bayan rikici ya ɓarke kan shugabancin jam’iyyar. Rikicin ya kunno kai ne tsakanin Samuel Anyanwu da Sunday Ude-Okoye kan wanda ke da haƙƙin zama Sakataren jam’iyyar na ƙasa. Matashiyar da ta watsa wa mai naƙuda tafasasshen ruwa ta shiga hannu Me kuka sani game da ficewar Mali, Nijar, da Burkina Faso daga ECOWAS? Rikicin ya fara ne lokacin da duka mutane biyun suka iso taron kwamitin amintattun. A lokacin taron, wani hadimin Anyanwu ya tilasta wa Ude-Okoye fita daga zauren taron, wanda hakan ya janyo gardama tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Jami’an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzoma. Matsalar ta samo asali ne bayan Anyanwu ya yi murabus daga kujerarsa don...
    Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin. Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati. Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping da sauran jagorori na kasar Sin sun ziyarci ko kuma sun gayyaci wasu su ziyarci tsoffin jami’ai da suka yi ritaya, sun mika gaisuwa gabanin bikin Bazara na al’ummar Sinawa na ranar 29 ga watan Janairun nan. Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma shugaban kwamitin koli na sojan kasar, da sauran jagororin kasar, sun taya tsoffin jami’an da suka yi ritaya murnar bikin Bazara, tare da musu fatan karin lafiya da kuma tsawon rai. A nasu bangaren kuwa, tsoffin jami’an da suka yi ritaya sun yaba da ayyukan kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin a shekarar da ta gabata, tare da bayyana goyon bayansu...
۱