Yadda Tinubu Ya Shirya Wa Kansa Mafitar Siyasa Kafin Zaben 2027
Published: 23rd, March 2025 GMT
Ita maganar bada damar tsayawa takara ba tare da zaben fidda gwani ba an dauki matakin ne saboda yadda aka ga ‘yan adawa ko jam’iyyun adawa suke kokarin tayar da babbar kura mai hayaki,wa ita jam’iyyar mai rike da kambun mulki a 2027 domin “Ba a san maci Tuwo ba sai Miya ta kare”.
Ana dai ganin tarurrukan da aka yi na mambobin APC,wadanda suke ganin ba,a kyauta masu ba da kuma Shugabannin adawa suna yin wani shiri wanda zai iya sa wasu daga cikinsu su yi jerin Tururuwa na komawa jam’iyyar SDP,kamar dai yadda tsohon Gwamnan Jihar Kaduna,Malam Nasiru El Rufa’i ya fara kasancewa na farko wanda ake ganin akwai wadanda za su iya goyo masa baya.
Idan dai ba a manta ba mako biyu da ya wuce kwamitin zartarwar jami’iyyar ya nuna amincewa da ayyukan da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi,hakan yana nuna ko dai su amince da bashi tikitin takara k kuma akashin hakan.
Akwai majiya mai tushe da ta bayyana a cikin taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar da aka yi a Abuja ya nuna cewa kamar yadda abin yake an tattauna ne kan yadda tsarin Shugabancin jam’iyyar yake tun daga sama zuwa kasa,ko kuma daga na kasa, Jiha, Karamar Hukuma har zuwa na mazabar Kansila (Ward) an tattauna komai kan hakan.
Akwai majiyar da bata son a ambacin sunanta, da yi bayanin akwai wasu daga cikin Gwamnonin da basu amince da lamarin ba gaba daya ba,su ma da akwai wani tsarin da ake yi wanda zai basu damar su zabi wadanda suke son tsayawa takarar majalisar Jiha a Jihohinsu.
Idan har shi tsarin da aka yi an samu yin amfani da shi kwatin zartarwar jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin Dakta Umar Abdullahi Ganduje da takwarorinsu na Jihohi za a barsu su ci gaba da tafiyar da jam’iyyar,saboda su taimakawa shirin da ake yi na kasancewar Bola Ahmed Tinubu shi ne dan takarar jam’iyyar.
Dankararar jam’iayyr daya tilo,suma ‘yan majalisun Dattawa da Wakilai wadanda suka ba jam’iayyar goyon baya tun daga lokacin da,Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya fara mulki.
“Shugabannin jam’iyyar sun san kura- kuren da aka yi a baya wanda matsala ce ta cikin gida wadda ta so sa wa jam’iyyar wani babban Tarnaki abinda daga karshe ya sa lakar jam’iyya ta kasance tamkar “Kazar da Kwai ya fashe ma ta a Ciki”. Wannan lokacin, ana bukatar ne kada a samu wata matsalar da zata iya kawo koma-baya. Hanya mafi dacewa ta yin hakan ita ce a ci gaba da tafiya irin yadda TSARIN Shugabancin jam’iyyar APC ya tsara ayi, domin a kaucewa aukuwar lamarin da zai sa ayi ta yin kumfar Baki saboda zaben fidda gwani.
“Idan za a tuna a zaben shekarar 2019, a babban zaben a Jihar Zamfara, mun rasa Jihar Zamfarar ne “inda jam’iyyar PDP ta samu dame a kala”,saboda rikicin cikin gida wanda ya fara ne sanadiyar zaben fidda gwani wanda aka ci gaba har zuwa 2023.
“Hakanan ma jam’iyyar APC, bata da ‘yan takara a Jihar Ribas saboda zaben fidda gwanin da mambobin jam’iyyar suka yi sau biyu kuma mabambanci.Hakanan ma akwai matsala wadda zaben Shugabannin jam’iyyar ya kusan gamawa da Jihar Imo. Idan ba lamarin kotu ba mun kusa rasa kujerar mu jam’iyyar PDP ta samu.”
Shugaban kasa ya samu rahoton sirri wanda ya nuna wadansu ‘yan jam’iyyar ba a kyautata masu ba, suna shirin barin jam’iyyar su koma wasu jam’iyyun adawa.
“Salon farko na su shi ne su samar da matsala cikin jam’iyyar APC idan an yi sabon zaben Shugabannin jam’iyyar.Domin maganin hakan, hanya mafita ita ce kada ayi zaben Shugabannin jam’iyyar,da kuma zaben kasa na jam’iyyar kafin babban zaben 2027.
“Hankalin sa kwance yake wajen tabbatar da babu wata matsala cikin jam’iyya,da kuma hana yiyuwar rigingimun bayan zabe wadanda suna iya kawo koma- baya. Ci gaba da wadannan Shugabannin ita ce mafita kuma zai taimaka wajen samun kwanciyar hankali kamar yadda majiyar ta ce”.
An samu labarin cewa jam’iyyar tana son ta amince da wata doka tunda har yanzu ba a bada sanarwa game da zaben kasa wanda za a ci gaba da tafiya da Shugabannin da ake da su a ci gaba da tafiya da su,tun daga na kasa har zuwa ta karshe ta matakin mazabar Kansila wato ward ke nan.
Matakin zai kara karfin Tinubu kan yadda taswirar jam’iyyar ta ke da kuma zabubbukan fidda gwani.
“Jam’iyyar ta shirya yadda zata zabi Shugabannin ta wanda a ranar ce, wani zai bada shawarar cewa a ci gaba da tafiya da Shugabnnin da ake fara tafiyar da su,tun daga na kasa har zuwa Ward har sai bayan babban zabe na shekarar 2027 kamar yadda bayanin ya nuna”.
Wadanda ake damawa da su a jam’iyya sun ce matakin shi ne abinda aka fi amincewa da shi, watao kwamitin zartarwar kasa na jam’iyyar ya amince da yadda Ganduje ya tafiyar da aikinsa tare da kwamitin gudanarwar sa.Matakin ya amince ne da yadda suka iya tafiyar da jam’iyyar duk kuwa da ta fuskanci matsaloli ma su yawa.Duk da hantarar da suka rika fama da ita sai da suka yi duk yadda suka iya suka samu aka amince da shi ne dantakarar ta na Shugaban kasa a shekarar 2027 ba tare da bata wani lokaci ba.
Hakanan ma ‘yan majalisun Dattawa dana Wakilai na jam’iyyar suma za su amfana da tsarin jam’iyyar su sake tsayawa ba tare da wata hamayya ba.
“Akwai maganar amincewa a jam’iyya kan lamarin amincewa da sa ita jam’iyyar ta sa kanta yin wani abinda zai iya kawo masu ko mata matsala. Yawancin ‘yan jam’iyyar da suke majalisun Dattawa da na Wakilai wadanda suka nunawa jam’iyyar ladabi da shi Shugaban kasa,ba sai sun tsaya sun fuskanci zabubbukan tantance gwani ba.Maimakon haka ma dama ce kawai za a basu su, su sake tsayawa takara ba tare da wata matsala ba sais u sake komawa kujerar tasu,”cewar wani babban kusa a jam’iyyar da baya son a ambaci sunansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Shugabannin jam iyyar a ci gaba da tafiya zaben fidda gwani jam iyyar da na jam iyyar jam iyyar su jam iyyar ta a jam iyyar
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Rashin Ilimi Ke Cutar Da Rayuwar Al’umma
Ilimi Gishirin Rayuwa
Babu shakka ba tun yanzu ba, dan’adam ya dade da fahimtar muhimmancin ilimi ga cigaban rayuwarsa. Walau ilimin addini ko na cigaban rayuwa. Addinin Musulunci ya koyar da mu muhimmancin bai wa ilimi fifiko, kamar yadda aka rawaito a cikin Hadisi. Ma’aikin Allah (SAWA) yana cewa ‘mu nemi ilimi ko da a Birnin Sin ne’. Kuma ya gaya mana cewa, “haddar yaro karami kamar rubutu ne akan dutse…” Kenan, wannan yana karfafa mana gwiwa mu koyawa yaranmu Ilimi tun suna kanana, don za su fi rikewa ya zauna a kwakwalensu. Ilimi tamkar fitila take, yana haskakawa mutum abubuwa na rayuwa, yadda zai koyi zaman duniya da gina wa kansa rayuwa mai inganci. Wannan ilimin kuwa ko da wanda ake koya a wajen aiki ne ko wajen sana’a, ba lallai sai a cikin aji ba. Ana koyon ilimi na aiki da hannu, ko da baki ko a rubuce. Sannan yanzu da zamani ya canza, akwai kafofin sadarwa daban-daban da mutum zai iya samun ilimi ba tare da ya shiga aji ba. Akwai manhajoji irin su YouTube, LinkedIn, Facebook da sauransu da mutum zai iya shiga ya koyi abubuwa da dama na ilimi. Lallai yana da kyau iyaye su rika zaunar da yaran su suna koya musu karatu da ilimin rayuwa, tun daga matakin gida, ko a dauki nauyin mai koya musu, ko kuma a saka su a makaranta. Rashin sa yaro a makaranta na sa ya girma babu wayo, kuma zai rika rayuwar jahilci, da rashin sanin inda yake masa ciwo. Sannan gwamnati ta saukaka hanyoyin samun ilimi, a rika koyarwa da harshen uwa a matakin farko, a samar da ilimi kyau, a rika ba da tallafin karatu ga manya.
Sunana Aminu Adamu Malam Maduri A Jihar Jigawa:
To magana ta gaskiya hanyoyin da rashin ilimi ke cutar da al’umma suna da yawa domin shi ilimi jigo ne na rayuwar dan’adam muddun kuwa aka ce babu shi to dole abubuwa da dama ba za su tafi daidai ba, domin shi ilimi dan jagora ne ga duk kanin dan’adam shi ke haskawa mutum hanyar daya kamata ya bi da wacce ya kamata ya kaucewa don matsalolin da rashin ilimi ke haifarwa sun fi gaban kidayawa ko kirdado. To magana ta gaskiya a wannan fannin gwamnati ya kamata ta tashi tsaye wajen inganta fannin ilimin dama samar da shi kyauta ga duk kanin al’ummar kasa, sai kuma iyaye suma su tashi tsaye wajen kulawa da sa ‘ya’yansu a makaranta da kuma kula da zuwan yaran akan lokaci. To magana ta gaskiya kimiyya da fasaha tana bada gagarumar gudunmawa wajen saukaka samun ilimi a wannan zamani da muke ciki shi ya sa za ka ga dukkanin kasashen da suka cigaba ta fannin ilimin kimiyya da fasaha to sun fi samun cigaba a fannin ilimi. To amfanin ilimi ko muhimmancin ilimi ga rayuwar dan’adam ya fi gaban kidayawa ko kirdado domin sai da ilimi ne rayuwar take yin kyau kuma sai da ilimi ne ake samun cigaba a rayuwa. To hakika ya kamata irin wannan iyaye su sake tunani domin fa ilimi shi ne hasken rayuwa wanda duk ya rasa ilimi to ya rasa komai a rayuwarsa don haka ya kamata iyaye su tashi tsaye wajen kulawa da ilimin ‘ya’yansu.
Sunana Fatima Nura Kila A Jihar Jigawa:
Rashin ilimi na haifar da matsaloli musamman a cikin al’umma kamar su sata, fyade, rashin girmama manya duk wadannan rashin ilimi na kawo su. Hanyar daya kamata abi shi ne; Gwamnati ta zage damtse wajen tura yara makarantu da kuma saukaka karatu tun daga matakin firamare, har gaba da sakandare. Ilimin kimiyyya nada matukar amfani ga al’umma ta fuskar tabbatar da sauye-sauye tare da samar da cigaban rayuwa, musamman abin da ya shafi bunkasa tunanin dan’adam wannnan ba karamar taka muhimmiyar rawa yake ba. Ilimi jigo ne sannnan mahadin rayuwa ne, ilimi na da amfani musamman wajen zamantakewa da kuma kasuwancinmu na yau da kullum. Shawarar da zan basu shi ne su bar ‘ya’yansu su je makaranta domin Ilimi shi ne ginshikin rayuwa, mutum mai ilimi ma ya fita daban a cikin al’umma.
Sunana Lawan Isma’il (Lisary), Jihar Kano Rano LGA:
Hanyoyin suna da yawa amma daya daga ciki ita ce; aikata ibada ba daidai ba da sabawa Allah kai tsaye. Samar da ilmi ta internet duk da mafiya yawan wasu mutanen tuni sun yi nisa ta wannan fannin. Wajen kirkirar wasu abubuwan da bamu saba ganinsu ba a yankunanmu. Daya daga cikin amfani Ilmi shi ne; aiki da shi a dukkan al’amuranka. Shawarata a garesu ita ce gaskiya su canja tunani kada iyaye su ga wai yanzu idan ka yi karatu ba a samun aikin yi a’a shi ilmi koda irin ‘yan iskan gari ne za ka ga sun bambanta da wadanda ba su yi ba, a saka yara su yi Ilmi ko wanne iri ne domin a can gaba za a ga amfaninsa. Allah ya sa mudace.
Sunana Aisha T Bello Jihar Kaduna:
Rashin ilimi cuta ce gaskiya, saboda ilimi shi ne kishin zaman duniya, yanzu misali; gida babu miji ya rasu in mata na da ilimi za ta nemi aiki dan ta kula da yaranta. Saboda yanzu duniya da zaran ba maigida ba masu kulawa da marayu Allah ne gatansu. Kimiya da fasaha na taka rawa sosai wajen kawo, cigaba ga al’umma bakidaya. Ga iyayen da basu tura yara makaranta gaskiya babbar cutarwa ce, domin kuwa yanzu duniya ta ci gaba, yanzu idan baka da ilimi kana ji kana gani ka zama dan kallo, don haka iyaye su daure su tura yara makaranta don cigaban al’umma bakidaya. Allah ya amfanar damu baki daya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp