Aminiya:
2025-03-13@12:00:32 GMT

Peter Obi ya kusa dawowa APC — Hadimin Tinubu

Published: 13th, March 2025 GMT

Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki.

Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya ce babban aminin Obi, Valentine Ozigbo, ya koma jam’iyyar APC domin yin takarar gwamna.

NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa? ’Yan sanda sun ceto mutum 30 daga hannun ’yan bindiga a Katsina

“Kun san muna rage ƙarfin jam’iyyar LP kuwa?” in ji Bwala.

“Valentine Ozigbo ya shigo jam’iyyarmu, Balami ma haka, Peter Obi ma zai zo. Idan har Ozigbo ya shigo jam’iyyar – wanda ke da kusanci da Obi – to na tabbata Obi ma zai biyo bayansa.”

Sai dai Obi bai mayar da martani kan wannan iƙirari ba.

A baya, ya sha musanta jita-jitar cewa zai bar jam’iyyar Labour Party.

Kakakin jam’iyyar, Obiora Ifoh, ya yi watsi da wannan magana, inda ya bayyana cewar wasu ’yan siyasa ne ke ƙoƙarin lalata jam’iyyar.

“Abin mamaki ne ganin yadda wasu ke ƙoƙarin haddasa matsala tsakanin jam’iyyar da shugabanninta,” in ji Ifoh.

“Peter Obi ya sha nanata cewa zai yi Labour Party cikakkiyar biyayya saboda manufofinta a kan al’umma sun dace da burinsa. Ba zai taɓa komawa wata jam’iyyar da ke kare muradun attajirai ba.”

Wasu masana siyasa na ganin cewa Obi ba zai bar Labour Party ba, domin ya samu karɓuwa sosai tun bayan zaɓen 2023.

Wasu kuwa na ganin rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyar na iya tilasta masa neman wata mafaka.

Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, makomar Obi a siyasa na ci gaba da zama abin tattaunawa.

Ko zai ci gaba da kasancewa a Labour Party ko kuma zai yanke shawarar komawa wata jam’iyya, wannan mataki nasa zai taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Daniel Bwala jam iyya Siyasa Labour Party a jam iyyar

এছাড়াও পড়ুন:

Ukraine Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Wata Guda Da Rasha

Majiyoyi sun bayyana cewa Donald Trump na shirin tattaunawa da Vladimir Putin a cikin makon nan domin ƙara fahimtar juna dangane da wannan shiri.

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, na kira ga ƙasashen Turai da su haɗa kai domin tallafa wa Ukraine wajen tabbatar da tsaron ƙasar bayan wannan tsagaita wuta.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai
  • Ukraine Ta Amince Da Tsagaita Wuta Na Wata Guda Da Rasha
  • Tambuwal Ya Raba Shinkafa Ga Gidaje Dubu 30 A Sokoto
  • Wata Miyar Sai A Makwabta…
  • Rikicin ƙabilanci ya yi ajalin mai juna biyu da wasu mutum 10 a Nasarawa
  • Ana fargabar ɓarkewar Sanƙarau a Sakkwato
  • Ficewar El-Rufai Daga APC Babban Rashi Ne – Tsohon Hadimin Buhari
  • Tambuwal Ya Tallafawa Magidanta Dubu 30 Da Kayan Abinci
  • Abin da ya sa na sauya sheƙa daga APC zuwa SDP — El-Rufai