Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar.

NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo), Alhaji Abdullahi Rurum (Mazabar Tarayya ta Rano/Kibiya), da Ali Madakin Gini (Mazabar Tarayya ta Dala). LEADERSHIP na zargin cewa, daya daga cikin al’amarin da ya jawo dakatarwar shi ne gayyatar da fitattun shugabannin jam’iyyar APC na kasa, da suka hada da shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje, da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, suka yi a kwanakin baya, tare da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau, zuwa wani taro da Sanata Sumaila ya shirya. Tarukan sun hada da daurin auren diyarsa da bikin yaye dalibai na farko a jami’ar sa mai zaman kanta dake karamar hukumar Sumaila. Kasancewar shugabannin jam’iyyar APC a wajen taron, kuma an ki gayyatar ‘ya’yan jam’iyyar NNPP, ya janyo ce-ce-ku-ce a kan yiwuwar komawar Sumaila zuwa APC. Shugaban NNPP, ya kuma bayyana cewa jam’iyyar za ta kafa wani kwamiti da zai binciki lamarin tare da daukar matakin da ya dace da su a nan gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: yan majalisar majalisar da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki

Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da amfani da Hijabi ga jami’an tsaro mata a fadin jihar.

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana haka jim kadan bayan kammala taron majalisar zartarwa da aka gudanar a fadar gwamnatin  jihar da ke Dutse.

A cewarsa, majalisar ta bayar da umarni ga kamfanonin tsaro guda uku da ke aiki a jihar, su bai wa jami’an tsaro mata daga cikin matasa 9,969 da aka dauka aiki, damar sanya Hijabi yayin aiki, a matsayin girmamawa ga addini da al’adu.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce, wannan matsaya ta biyo bayan rahoton da kwamitin majalisar kan tsaron makarantu, asibitoci da kotuna ya gabatar, kuma aka sake jaddada kudurin gwamnatin na tabbatar da tsarin aiki mai cike da mutuntaka, da daidaito.

Ya ce, majalisar zartarwar ta kuma amince da kaddamar da makon kirkira da kere-kere na jihar (JISCIW) daga shekarar 2025.

Ya jaddada cewa, wannan tsari na nuna jajircewar gwamnatin wajen bunkasa basira da hazakar matasa, da kuma inganta kirkire-kirkire da tunani mai zurfi a fadin jihar.

Sagir ya bayyana cewa, JISCIW zai kara zaburar da matasa a fannoni daban-daban kamar fasaha, zane, kasuwanci da kuma harkokin fasaha.

Ya kara da cewa, majalisar ta amince da fitar da sama da Naira miliyan 516 domin sayen tikitin jirgi ga daliban jihar Jigawa 185 da ke karatu a fannin likitanci da kimiyyar kiwon lafiya a Jami’ar Near East dake kasar Cyprus, domin shirye-shiryen zangon karatu na shekarar 2024/2025.

Kwamishinan ya kara da cewa, wannan tallafi ya nuna yadda gwamnatin ke ci gaba da daukar nauyin ilimi da jin dadin daliban da ke karatu a kasashen waje, musamman a muhimman fannoni kamar likitanci da kiwon lafiya.

 

Usman Muhammad Zaria 

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisa ta gayyaci Kantoman Ribas, Ibok-Ete Ibas
  • Mizanin Hada-hadar Tattalin Arzikin Kasar Sin Ya Karu Da Kashi 5.4% A Rubu’in Farko Na Bana
  •  ‘Yan Hamayyar Tanzaniya Sun Ki Amincewa Da Hana Su Shiga Zabe
  • Dalilin da Kwankwaso zai dawo APC — Ganduje
  • NNPP Ta Mutu, Kwankwaso Zai Sake Dawowa APC – Ganduje
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bukaci Jami’an Tsaro Mata Su Rika Sanya Hijabi Yayin Aiki
  • Majalisar Kaduna ta Amince da Kudirin Kula da Lafiyar Kwakwalwa na Jihar
  • HOTUNA: Zulum ya karɓi baƙuncin Majalisar Sarakunan Arewa a Borno
  • ‘Yansanda Sun Kama Wasu Da Ake Zargin Ɓarayin Wayar Wutar Lantarki Ne A Yobe
  • ‘Yansanda Sun Gano Haramtaccen Wurin Hada Makamai A Kano