2025-02-24@18:02:17 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1258

«majalisar da»:

    Kungiyar Hamas ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa da HKI har zuwa lokacin da ta saki fursinoni Falasdinawa wadanda yakamata ta sakesu bayan da Hamas ta saki yahudawa 6 a karo na 7 na musayar fursinoni. Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto daya daga cikin shuwagabannin kungiyar Mahmoud Mardawi yana fadar haka a yau Litinin ya kuma kara da cewa, a ranar Asabar da ta gabata ce kungiyar ta saki fursinoni yahudawa  6, kuma take fatan HKI za ta saki falasdinawa 620 kamar yadda yake cikin yarjeniyar tsagaita wuta, amma ta ki yin hakan, da dalilin cewa wai kungiyar Hamas ta wulakanta daya daga cikin fursinoni 6 da ta saka. Jami’in na Hamas ya ce tawagar tattaunawar...
      Kungiyar Tarayyar Makiyaya ta CORET ta ce zata tallafawa yara makiyaya 1,600 a makarantun makiyaya guda shida a Jihohin Kaduna da Jigawa a wani yunƙuri na rage ƙarancin abinci da rashin ingantaccen abinci.   Sakataren Janar na CORET, Mohammed Bello Tukur ne ya bayyana hakan a lokacin ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai na haɗin gwiwa a Laddauga, wurin kiwon dabbobi na Kachia a Jihar Kaduna.   Ya bayyana cewa, manufar wannan shiri ita ce tallafa wa shirin ciyar da ɗalibai na makarantun makiyaya.   Sakatare Janar ya ƙara da cewa kashi 60 na waɗanda za su amfana ‘yan mata ne, kuma shirin zai ƙarfafa ilimin kyawawan ɗabi’u a fannin abinci mai gina jiki, tsafta, tsabtace muhalli, da kuma...
    Sojojin Iran sun gwada amfani da sabbin jiragen yakin na zamani da suka kera a cikin gida, a cikin atisayen Zulfikar 1403 da ke gudana a kudancin kasar, wanda kuma ya hada rundunonin sojojin kasar daban-daban. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar atisayin na cewa sojojin sun gwada amfani da jirgin saman yaki samfurin Yak-130 a cikin atisayen. Inda suka tabbatar da ingancinsa. Ana gudanar da atisayen Zulfikar 1403 ne a yankin Tekun Omman da kuma wani bangare na yankin Tekun farasa daga kudancin kasar Iran. Bugediya Janar Alireza Sheikh kakakin atisayen ya fadawa tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran kan cewa wannan bangare kadan ne daga atisayen, amma a yau sun...
    Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
    Ministan ya yi zargin cewa, furucin Shugaban na daya daga cikin dalilan da suka sa Allah ya karbe mulki daga jam’iyyar duk da nasarar da ta samu a zaben gwamna na 2023.   Amma da yake mayar da martani, Abbas ya yi zargin cewa Ata ya yi wa jam’iyyar zagon kasa a zaben 2023, kuma sun bayyana haka ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.   Abdullahi Abbas ya ce, “A gare mu ‘yan APC Yusuf Ata ba dan jam’iyyar APC ba ne. Ba mu ma san dalilin da ya sa aka nada shi minista ba. Duk fadin jihar Kano a karamar hukumarsa ne muka zo na uku a zaben 2023.   “Ba mu san cewa an nada shi minista ba. Mun...
    Shugaban hukumar Leken asiri na kasar Iraki Hamid al-Shatri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iraki ta isar da sako ga sabuwar gwamnatin kasar Siriya dangane da samuwar ragowar mayakan kungiyar yan ta’adda ta Daesh a wasu yankunan kasar. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta Nakalto Hamid al-Shatri ya na fadar haka ga kafafen yada labarai a birnin Bagdaza, sannan ya kara da cewa al-amuran tsaro a kasashen biyu suna hade juna ne, don haka dole ne gwamnatocin kasashen biyu su yi aiki tare don ganin bayan wadannan yan ta’adda, masu kafirta musulmi. Kamfanin dillancin labaran INA na kasar Iraki ya nakalto al-Shatri yana fadar haka a taro na 7TH na tattaunawar Bagadaza  a jiya Lahadi. Ya kara da...
    A yau Litinin ce aka sanya Sayyid Safiyyuddeen shugaban kungiyar Hizbullah wanda yayi shahada a hannun sojojin HKI a yakin Tufanul Aksa a makwanccinsa ta karshe a garinsu Deir-Qannoon Al-nahr dake kudancin kasar Lebanon. Tashar talabijan ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bayyana cewa dubban duruwan mutane ne suka halarci Jana’izar sa, sannan mutanen kauyuka a yankin da dama sun halarci jana’izar. Mutane daga kasashen duniya da dama wadanda suka halarci jana’izar a jiya Lahadi a Beirt sun  halarci jana’izar Sayyid shahid Hashim safiyyudeen a yau a kudancin kasar ta Lebanon.
    Hukumar tsaro ta farin kaya  (NSCDC) reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin sojan gona ga aikin hukumar. Jami’in hulda da jama’a na hukumar NSCDC reshen jihar Kano SC Ibrahim Idris Abdullahi ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce mutanen biyu, Muhammad Sarari da Madaki Zaharaddeen,   masu shekaru 43 da 32, mazauna Goron Dutse ne, a karamar hukumar Dala, da Hotoro kwatas a karamar hukumar Nassarawa. A cewar jami’in hulda da jama’an, wadanda ake zargin suna zuwa hukumomin da ma’aikatun gwamnati ne, inda suke yaudarar manyan ma’aikata tare karbar kudade daga hannunsu. “Dubunsu ta cika ne a lokacin da suka yi yunkurin tsoratar da...
    A wannan Litinin ɗin ɗaliban Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma FUDMA suka shiga rana ta biyu ta zanga-zangar kisan wani ɗalibi da ake zargin jami’an bijilanti na JTF sun yi a ranar Lahadi. Aminiya ta samu rahoton cewa ’yan bijilantin sun buɗe wa wasu ɗalibai da ke tafe kan babur wuta ba tare da sun tsayar da su domin tuhuma bisa zargin cewa masu yi wa ’yan bindigar daji leƙen asiri ne. NNPP ta dakatar da Kawu Sumaila da Ali Madakin Gini Mun gano inda Bello Turji ya ɓoye —Sojoji Wannan harbin da suka yi ya yi sanadiyar mutuwar wannan ɗalibi mai suna Saidu Abdulkadir. Ana iya tuna cewa, a kwanakin baya an kama wani ɗalibin jami’ar yana safarar makamai....
    To, ma iya cewa kasar Amurka ta riga ta fusata dukkan kasashen duniya. Idan an sa wata kasar dake nahiyar Afirka fuskantar matakin da kasar Amurka ta dauka ita kadai, to, za ta ji akwai matsin lamba. Sai dai yanzu za a saki jiki, saboda ko da yake kasar Amurka ta kan ci zarafin sauran kasashe, amma ba ta da karfin cin zarafin dukkan kasashe a sa’i daya. Wannan shi ne dalilin da ya sa ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya bayyana a wajen taron aikin tsaro na Munich da ya gudana a kwanan nan, cewa bai kamata a ji tsoron aikace-aikacen kasar da ta ke ta nuna fin karfi a duniya ba, saboda galibin kasashen duniya dake...
    Babbar kotun tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara ta dakatar da majalisar dokokin jihar daga tsige Honarabul Aliyu Ango Kagara, dan majalisar APC mai wakiltar mazabar Talata Mafara ta Kudu. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya bayyana cewa hukuncin ya biyo bayan wata kara mai lamba FHC/GSCS/10/2025 da Kagara ya shigar kan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara,  da Kakakinta, da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC). Ta ce shari’ar da mai shari’a Salim Olasupo Ibrahim ya jagoranta ta kalubalanci tsige Kagara da shugabannin majalisar suka yi. A cewar sanarwar, kotun ta bayar da umarnin wucin gadi na hana INEC gudanar da zaben cike gurbi na mazabar...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta sanar da tsawaita lokacin yin rajistar maniyyata zuwa Hajjin 2025 a Ƙasar Saudiyya har bayan Azumin Ramadan. Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Sale Usman, ya bayyana hakan a wata hira da aka yi da shi a Abuja. Farfesa Usman ya kuma bayyana cewa an rage naira biliyan 54 daga kudaden da masu ruwa da tsaki ke caji domin saukaka wa maniyyata wajen biyan kuɗin tafiya. Ya tabbatar da cewa ana duba sabbin hanyoyin inganta muhimman ayyuka kamar abinci, masauki, da kula da lafiyar alhazai yayin da suke ƙasa mai tsarki. A cewarsa, hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin tafiyar ƙwararrun masu dafa abinci 60 da za su sa ido kan shirye-shiryen abinci a wuraren...
    Jam’iyyar NNPP a jihar Kano ta dakatar da wasu mambobinta da suka hada da Sanata da wasu ‘yan majalisar tarayya uku bisa zargin zagon kasa ga jam’iyyar.  Shugaban jam’iyyar NNPP na jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Kano ranar Litinin, inda ya bayyana rashin jin dadin jam’iyyar da halayyar ‘yan majalisar da aka dakatar. NNPP Ta Dakatar da ‘Yan Majalisa Huɗu Bisa Zargin Yi Wa Jam’iyya Zagon Ƙasa Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  ‘Yan majalisar da aka dakatar sun hada da Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu a majalisar dattawa, da kuma ‘yan majalisar wakilai uku, wato Alhaji Abdullahi Sani Rogo (Mazabar Tarayya ta Rogo),...
    Jam’iyyar NNPP reshen jihar Kano ta dakatar da ‘yan majalisar tarayya huɗu bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa manufofin jam’iyya. Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Hashimu Dungurawa, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano a ranar Litinin. Waɗanda aka dakatar sun hada da Kawu Sumaila (Sanatan Kano ta Kudu), Ali Madakin Gini (Dala), Sani Rogo (Rogo/Karaye), da Kabiru Rurum (Rano/Kibiya). Dungurawa ya ce waɗannan ‘yan majalisa sun samu tikitin NNPP ne, amma daga baya suka fara aikata abubuwan da suka sabawa jam’iyyar. Nan Kusa Ƴan Majalisun NNPP Za Su Koma APC – Ganduje  Jam’iyyar NNPP Daya INEC Ta Amince Da Ita – Shugaban Jam’iyyar  Ya ce misali, Sanata Sumaila ya ƙaddamar da...
    Jam’iyyar NNPP a Kano ta dakatar da Sanata Kawu Sumaila da wasu ƙusoshin jam’iyyar uku kan zargin cin amanarta. Sauran waɗanda jam’iyyar kan zargin cin amana sun haɗa da Ali Madakin Gini, Sani Abdullahi Rogo da kuma Kabiru Alhassan Rurum.  
    Sojojin Sudan sun ce sun kawo ƙarshen iko da birnin el-Obeid na yankin kudancin ƙasar na kusan shekaru biyu da dakarun RSF suka yi. Wannan nasara na zuwa ne ‘ƴan sa’o’i bayan da RSF ta rattaɓa hannu kan yarjejeniyar siyasa a Nairobi da ke ƙasar Kenya na kafa gwamnatin aware a yankunan da ke ƙarƙshin ikonta. Tun dai shekarar 2023 ne rundunar RSF da sojojin Sudan ke fafatawa, inda dubban fararen hula ke mutuwa sannan da dama na barin gidajensu. Rikicin dai ya raba ƙasar ɓangarori biyu, inda sojoji ke iko da arewa da gabashi, yayin da su kuma RSF ke iko da mafi yawancin yankin Darfur da ke yammaci da wasu sassan kudanci. Birnin El-Obaid dai wanda shi ne...
      Barazanar Ata Kan Ficewa Daga APC A cikin bidiyon da ke yawo a shafukan sada zumunta, Minista Yusuf Ata ya yi magana da magoya bayansa, yana mai cewa idan ba a sauya shugabancin APC a Kano ba, to zai fice daga jam’iyyar. “Muna faɗa wa kowa, idan aka mayar da irinsu, duk irinmu fita za mu yi,” in ji Ata. Ya ƙara da cewa, “Idan suka dawo da shi, za mu fice, kuma na rantse da Allah jam’iyyar za ta sake faɗuwa a zabe.” Wannan rikici na ƙara nuna rabuwar kai a cikin APC a Kano, wanda ka iya shafar ƙarfi da tasirin jam’iyyar a jihar nan gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da...
    Babban Jami’in Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ya bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji. Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba. “Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka. Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa. Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin...
    Babban Jami’in Ayyuka na Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya, Manjo-Janar Emeka Onumajuru, ya bayyana cewa saura kiris su gama da jagoran ’yan ta’adda, Bello Turji. Manjo-Janar Emeka Onumajuru ya bayyana cewa sojojin suna kan bibiyar motsin Bello Turji, kuma sun gano inda yake, amma bai yi ƙarin bayani ba. “Babu wani kwan-gaba-kwan-baya a wurin sojoji kan maganar Bello Turji, mun gano inda maɓoyarsa take,” in ji Janar Emeka. Ya ci gaba da cewa a halin yanzu sojoji sun riga sun rutsa Turji a maɓoyarsa, babu inda zai iya motsawa ya je, saboda tsoro Ya bayyana haka ne a safiyar Litinin yana mai cewa kwanakon Turji sun kusa karewa. Janar din ya bayyana haka ne a yayin hirar da gidan talabijin...
    Galadima Muri, na Masarautar Muri, kuma Hakimin Jalingo, Alhaji Lamido Abba Tukur, ya yi kira ga manoma da ‘yan kasuwa a Taraba da su yi la’akari da halin da talakawa ke ciki, su rage farashin kayan abinci. Ya yi wannan kiran ne a yayin cikarsa shekaru 40 akan karagar mulki a matsayin Galadima a Jalingo. Basaraken  ya nuna damuwarsa kan yadda hauhawar farashin kayayyakin abinci a kullum ke kara ta’azzara, da kuma kalubalen tattalin arziki da talakawa ke fuskanta. Galadiman ya yabawa gwamna Agbu Kefas kan yaki da matsalar tsaro a Taraba, inda ya bayyana ci gaban da aka samu a shekarun baya-bayan nan a matsayin abin a yaba. “Amincewa da gudanar da wannan biki na cika shekara 40 akan...
    Gwamnatin jihar Jigawa ta bayyana jin dadinta bisa gagarumin nasarorin da aka samu wajen aiwatar da manufofinta guda 12 don inganta rayuwar al’umma da ma ci gaban jihar baki daya. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a yayin taron wayar da kan jama’a da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. Ya bayyana cewa shirin da ke da nufin kusantar da jama’a ga gwamnati, zai kuma tabbatar da cewa manufofi da shirye-shiryen da aka aiwatar sun dace da  muradin al’umma. Don haka Namadi ya yabawa al’ummar yankin bisa yadda suka rungumi ayyukan da gwamnatin jihar ke  aiwatarwa hannu bibbiyu, tare da yin alwashin ci gaba da samar da ingantattun ayyuka. Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa, zai yi nazarin...
    An gurfanar da wata matar aure a kotu kan zargin ta da cinna wa mijinta wuta a Jihar Kano. Ana zargin matar ta watsa wa mijin nata fetur sannan ta cinna masa wuta ne saboda ya shiga dakin sabuwar amaryarsa, suna tattaunawa da ita. Shaidu sun bayyana cewa wadda ake zargin ta yi aika-aikan ne bayan ta nemi mijin nata ya fito daga dakin amaryar tasa amma ya ƙi amincewa. Magidancin ya samu munanan kuna a sakamakon wutar da matar tasa ta yi masa. Lauyar Gwamantin Jihar Kano, Saima Garba, ta karanta wa matar takardar tuhumar aikata kisa da ake mata, amma ta musa. Daga nan alƙalin kotun Majistare mai Lamba  25, Halima Wali, ta ba da umarnin tsare matar...
    Iran ta yi kakkausar suka kan ta’addancin Isra’ila game da keta hurumin kasar Lebanon, bayan da jiragen yakinta suka yi shawagi a yankin da ake gudanar da jana’izar tsoffin shugabannin kungiyar Hizbullah. A wani sako da ya wallafa a shafin sada zumunta a daren Lahadi, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Esmaeil Baghaei, ya ce gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta shiga wani sabon yanayi na kara tabbatar wa duniya da cewa ita bata bin dokokin kasa da kasa. Baghaei ya ce jiragen yakin haramtacciyar kasar Isra’ila sun yi kokarin tarwatsa dubban daruruwan ‘yan kasar Lebanon da wasu da suka taru domin nuna girmamawa ga jarumtansu, shugaban kungiyar Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah da mataimakinsa da suka nada Sayyed Hashem Safieddine. Baghaei ya...
    Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta. Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa. “Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar...
    Pars Today – Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran ya sanar da cewa za a gudanar da taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar 2025 a farkon shekara mai zuwa wato (Kalandar Iran). Mataimakin shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Muhammad Reza Aref, a wata ganawa da ya yi da shugabannin jami’an diflomasiyyar Afirka a birnin Tehran ya bayyana cewa, raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya da nahiyar Afirka, na daya daga cikin muhimman batutuwan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanya a gaba. Aref ya kara da cewa, shirya taron hadin gwiwar tattalin arziki tsakanin Iran da Afirka karo na uku da kuma bikin baje kolin na shekarar...
    Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina ta hana wani yunƙurin ‘hari da ‘yan bindiga suka kai kan jami’an NSCDC a kan hanyar Dutsinma-Kurfi a ƙaramar hukumar Dutsinma. Kakakin rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu, ya bayyana cewa lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, 23 ga Fabrairu, 2025. Bayan samun kiran gaggawa da misalin ƙarfe 12:57 na dare, ‘yansanda daga ofishin Dutsinma suka gaggauta kai ɗauki, wanda ya haifar da musayar wuta da ‘yan bindigar. ‘Yan Bindiga Sun Kashe Wani Mutum Tare Da Sace Mutum Biyu A Kaduna Gwamnatin Katsina Ta Kashe Naira Biliyan 5.7 Wajen Sayen Awaki 40,000 Domin Raba Wa Mata A sakamakon haka, ‘yan bindigar sun tsere da raunukan harbin bindiga, yayin da aka samu gawar ɗaya daga cikinsu...
    Tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (murabus) ya bayyana dalilin da ya hambarar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari a 1985. Janar Babangida ya bayyana dalilin da gwamnatinsa ta karya darajar Naira da sauran sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta yi bayan kifar da Buhari. Babangida, wanda shi ne babban hafsan sojin kasa a lokacin Buhari, ya taka rawar gani a juyin mulkin da aka yi wa Shugaba Shehu Usman Shagari a 1983 da kuma na 1985 da ya kawo shi kan karagar mulki. Ya ba da cikakken bayani game da abubuwan da suka faru a cikin littafin tarihin rayuwarsa da ya ƙaddamar a makon jiya. Har yanzu Najeriya na buƙatar shugabanni nagari – Sheikh Gumi NAJERIYA...
    A yayin taron ministocin harkokin wajen kasashen G20 da aka yi a birnin Johannesburg, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na Afirka ta Kudu Ronald Lamola sun yi wata ganawa ta musamman, inda suka tattauna dangantakar kasashensu da manufofinsu. Sun amince da manufa guda don habaka tasirin Duniya, da nufin tabbatar da ingantacciyar murya guda ta kasashe masu tasowa. Wang ya bayyana a yayin taronsu cewa, kasar Sin a shirye take ta kara karfafa hadin gwiwar cin moriyar juna tsakaninta da kasar Afirka ta kudu, da kara gaggauta bunkasuwar kasashen biyu, da kuma kara yin hadin gwiwa don kara daukaka murya da wakilci na kasashe masu tasowa, musamman kasashen Afirka a cikin ajandar kasa da kasa. Wannan...
    Al’ummar gari sun wani ɗan shekara 65 dauke da bindiga sun damƙa shi a hannun hukumar ’yan sanda. Rundunar ’yan sandan Jihar Akwai Ibom ta kama mutumin ne tare da wani abokinsa da bindiga kirar ‘Double Barrell’ da harsasai da cocila da sauran kayayyaki a cikin wata kakar matafiya. Kakakin rundunar, DSP Timfon John, ya ce dubun dan shekara 65 din mai suna Nehemiah Sunday Udo ne a ranar Asabar baya al’ummar kauyen Ekpene Obo da ke Ƙaramar Hukumar Esit Eket sun ritsa shi. John ya ce bayan samun kira daga al’ummar yankin ne ’yan sanda suka kai samame inda suka samu mutanen sun kai wanda ake zargin fadar basaraken yankin. Ana zargin malami da azabtar da ɗalibi kan shan...
    Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa matukar aka samu mamaya to za a samu manyan mutane irin shahid Sayyeed Hasan Nasrallah da za su tsaya tsayin daka kan yaki da hakan, kuma ba za su bari ‘yan mamaya su cimma manufarsu ba. Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya tabbatar da cewa, Hizbullah tana nan a raye kuma tana ci gaba da bin tafarkinta mai daraja fiye da kowane lokaci a baya. A yayin zaman majalisar ministocin kasar Iran, Pezeshkian ya bayyana cewa, matukar dai abin ake yi na zalunci da danniya a kan masu rauni zai ci gaba, to kuwa tabbas ba za a rasa mutane irin Nasrallah ba, masu tsayin daka da jajircewa wajen tunkarar zalunci da...
    Kungiyar Hamas ta jinjina da irin babbar gudunmawa da tsayin dakan da Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine suka yi wajen goyon bayan Palastinu, da kuma shahadar da suka yi a kan wannan tafarki. A cikin wata sanarwa da ta fitar dangane da jana’izar shahidan biyu, kungiyar Hamas ta ce, muna addu’ar Allah ya jikan su da rahama, tare da mika ta’aziyyarmu ga al’ummar kasar Labanon da dukkanin al’ummar mu Larabawa da musulmi. Kungiyar ta tabbatar da cewa, laifuffukan Haramtacciyyar Kasar Isra’ila da kuma kisan gillar da ta yi wa shugabannin gwagwarmaya a Falasdinu, Labanon da sauran su, ba za su dakatar da tafarkinmu ba. Har ila yau sanarwar ta bayyana matsayin shahid Sayyid Hassan Nasrallah da jajircewarsa da...
    Tawagar gwamnatin Iran da ke ziyara a birnin Beirut domin halartar jana’izar shugabannin gwagwarmaya Sayyed Hassan Nasrallah da Sayyed Hashem Safieddine karkashin jagorancin shugaban majalisar dokokin kasar Mohammad Bagher Ghalibaf da ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi sun gana da shugaban kasar Labanon Joseph Aoun. Bayan nan kuma tawagar ta gana da shugaban majalisar dokokin kasar Nabih Berri, sannan ta ci gaba da tattaunawa da sauran jami’ai da suka hada da firaministan kasar Labanon Nawaf Salam. Ghalibaf da sauran jami’ai sun tafi kasar Lebanon a safiyar Lahadi don halartar jana’izar Sayyid Hassan Nasrallah, tsohon babban sakataren kungiyar Hizbullah, da kuma magajinsa  Sayyed Hashem Safieddine, wadanda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kashe su a karshen shekarar da ta gabata. Da yake...
    Ana zargin malamin makarantar Aliyu Mustapha Academy da ke Jimeta a Jihar Adamawa kan wuce gona da iri da kuma azabtar da wani ɗalibinsa a dalilin shan mangwaro a lokacin ‘break’ a harabar makarantar. Aminiya ta ruwaito cewa a lokacin da ake tsaka da hutun tara ne malamin yan kama ɗalibin yana shan mangwaro, inda ya lakaɗa wa ɗalibin dukan tsiya. Shaidu sun ce har da naushi malamin ya riƙa yi wa ɗalibin, lamarin da ya sa taron ya ƙuƙƙuje tare da barin sa da tabbai a jikinsa. Malamin yana tsaka da dukan ɗalibin ne mahaifin yaron ya je makarantar domin tabbatar da biyan kudin makarantar ɗan nasa. NAJERIYA A YAU: Matakan Kariya Daga Cutar Ƙyandar Biri Har yanzu Najeriya...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    Kungiyar Rapid Support Forces na Sudan (RSF) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da kawayenta na kafa gwamnati ta bai daya, a cewar majiyoyin AFP, ba tare da yin la’akari da gargadin da aka yi cewa irin wannan matakin zai raba kasar da yaki ya daidaita ba. Yarjejeniyar, wacce aka rattaba hannu a kanta a bayan fage a Nairobi babban birnin kasar Kenya, za ta kai ga samar da gwamnatin adawa a kasar Sudan, wadda za ta hada kungiyoyin  Rapid Support Forces, United Civil Forces, da kungiyoyin kwararru, da kuma SPLM-N. Kamfanin dillancin labaran AFP ya ce, wannan yarjejeniya ta yi kira ga kafa gwamnati mai zaman kanta, da dimokuradiyya, daidaito, da adalci, ba tare da nuna bambanci ga...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Cutar ƙyandar biri da aka fi sani da Mpox ta ƙara ɓulla a Najeriya. Na baya-bayan nan shi ne ɓullarta a Jihar Filato inda aka samu mutum 11 da suka kamu da ita, sai wanda ya rasa ransa mutum ɗaya. Cutar ta ɓulla ne a ƙananan hukumomi biyar da suka haɗa da Jos ta Arewa da Bokkos da Shendam da Mangu da kuma Kenke. Ko waɗanne irin matakai ya kamata al’umma su ɗauka don kauce wa kamuwa da wannan cuta? NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Ba Za Mu Sauke Farashin Burodi Ba —’Yan kasuwa DAGA LARABA: Dalilan Da ’Yan Najeriya Ke Haɗa Buga-Buga Da Aikin Albashi Shirin Najeriya A Yau na wannan rana...
    Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rika ba da muhimman bayanai ga hukumomin tsaron  kasar nan. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ne ya yi wannan kiran a lokacin da yake jawabi a wani taron jama’a na gwamnatin jihar Jigawa da aka gudanar a karamar hukumar Birnin Kudu. A cewar sa, kiran ya zama wajibi domin karfafa tsaro a fadin Najeriya. Alhaji Badaru Abubakar, ya yi nuni da cewa an samu ingantuwar harkokin tsaro a fadin kasar cikin ‘yan watannin nan. Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi iya bakin kokarinta wajen yaki da rashin tsaro, kuma za ta ci gaba da jajircewa wajen cimma manufofin da ake so. Ministan ya...
    Adadin balaguron fasinjoji a tsakanin manyan yankuna na fadin kasar Sin yayin ruguntsumin bikin Bazara na all’ummar Sinawa na tsawon kwanaki 40, wanda aka fi sani da Chunyun, ya kai biliyan 9.02, kamar yadda bayanan hukuma suka nunar a yau Lahadi. A cewar tawagar da aka nada ta musamman domin tabbatar da nasarar balaguron al’umma ba tare da wata matsala ba lokacin Chunyu da aka kammala jiya Asabar, alkaluman bana sun nuna an samu karuwar kashi 7.1 cikin dari a kan adadin da aka samu na daidai irin wannan lokacin a shekarar 2024. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
    Matakin Amurka Na Takaita Zuba Jari Zai Cutar Da Wasu Da Ita Karan Kanta
    Fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan, Sheikh Ahmad Gumi, ya ce har yanzu Najeriya na neman shugabanni nagari da za su fifita jin daɗin al’umma maimakon mayar da hankali kan wajen tara wa kansu dukiya. Ya bayyana hakan ne yayin bikin karramawa da ƙungiyar tsofaffin ɗaliban Makarantar Firamare ta Sultan Bello (SUBOPA), ta shirya domin girmama wasu mambobinta biyu – Manjo Janar Abdulmalik Jibrin (mai ritaya) da Birgediya Janar Abdulkadir Gumi (mai ritaya), bisa sababbin muƙaman da suka samu a gwamnati. Arewa na buƙatar haɗa kai da Kudu Maso Kudu don ceto Najeriya — El-Rufai Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP An naɗa Manjo Janar Jibrin a matsayin Sakatare na Hukumar...
    Kasar Sin Ta Zayyana Muhimman Ayyukanta Na Zurfafa Gyare-gyare A Yankunan Karkara Da Inganta Raya Su
    Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Dass ta jihar Bauchi, Yunusa Umar, ya jagoranci mambobi fiye da 7,500 zuwa jam’iyyar PDP. Cikin waɗanda suka sauya sheka har da Shugaban Matasa na APC a yankin, Yusuf Inuwa Bora, da Sakatare mai kula da jin daɗin mambobi, Isah Zakaria. An karɓi waɗannan sabbin ‘yan jam’iyyar ne a hukumance a ranar Lahadi, inda Shugaban PDP na ƙaramar hukumar Dass, Hon. Yusuf Sabo, da Shugaban ƙaramar hukumar, Hon. Mohammed Abubakar Jibo, suka tarɓe su. Umar ya bayyana cewa kyakkyawan shugabancin Gwamna Bala Mohammed ne ya sa suka bar APC. Wata Ɗalibar Kwalejin Fasaha Ta Tarayya Da Ke Bauchi Ta Rasa Ranta A Haɗarin Mota Gwamnan Bauchi Ya Rantsar Da Mashawarta 11, Ya Horesu...
    Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin ya yi Allah wadai da kasar Australia bisa yadda ta zargi kasar Sin da yin atisayen soja bisa doka a tekun dake kusa da kasar ta Australia. Kakakin, Wu Qian ya bayyana hakan yayin da yake amsa tambayoyin kafofin watsa labaru game da zargin na Australia cewa jiragen ruwan yaki uku na kasar Sin sun yi atisayen soja a tekun dake kusa da kasar Australia. Wu Qian ya bayyana cewa, zargin da kasar Australia ta yi ba shi da tushe balle makama, domin yankin tekun da jiragen ruwan yakin na kasar Sin suka yi atisayen soja yana can nesa da layin teku na kasar Australia, kuma yanki ne da ba ya cikin mallakar wata kasa....
    Jaridar Wall Satreet Journal ta ambaci cewa kasashen Faransa da Birtaniya suna shirya yiyuwar aikewa da sojojin tabbatar da zaman lafiya a cikin kasar Ukiraniya idan an tsagaita wutar yaki. Jaridar ta Amurka ta kuma kara da cewa; Idan an kai ga cimma tsagaita wutar yaki to da akwai yiyuwar turawan za su aike da sojojin zaman lafiya da za su kai 30,000 daga cikin har da na kasar Switzerland. Sai dai kuma aiwatar da shirin na turai yana da alaka ne da yadda Donald Trump zai amince da kasarsa ta taka rawa, idan har Rasha ta kai wa turawan hari, ko ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta, kamar yadda jaridar ta ambato wani jami’in turai din yana fada. Jaridar ta...
    Lokacin kadan da ya gabata ne dai aka rufe shahid Sayyid Hassan Nasrallah a makwancinsa na kare dake kusa da filin saukar jiragen sama na Beirut,bayan da aka dauki tsawon yau ana gudanar da jana’izarsa. Dubun dubatar mutanen Lebanon da kuma wasu daga wajen kasar ne su ka halarci taron jana’izar Sayyid Shahid Hassan Nasrallah da kuma ta Sayyid Hashim Safiyuddin da  aka gudanar a cikin birnin Beirtu. Tashar talabijin din al’mayadin ta bayyana cewa bisa kirdado adadin mutanen da su ka halarci jana’izar sun kai mutane miliyan daya da 400,000. Mahalarta jana’izar sun cika filin wasa na birnin Beirut da kuma manyan tituna ta yadda babu masaka cinke, da hakan ya sa motar da take dauke da makararsa da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka, sharhin bayan labarammu zai yi magana dangane da ‘Sayyid Haassan Nasarallah’ shahidin Al-umma’ wanda aka yi jana’izar sa a ranar lahadin da ta gabata. Wanda ni tahir amin zan karanta. A ranar lahadi 23  ga watan Fabrayrun shekara ta 2025 ne aka gudanar da Jana’izar babbsan sakataren kungiyar Hibullah, sayyid Hassan nasaralla, da kuma magajinsa na tsawon kwanaki 6 Sayyid Hashim safiyyuda deen, kafin haka shi ne shugaban majalisar zartarwa na kungiyar Hizbullah.   An haifi sayyid Hassan nasaralla (r ) a ranar 31 ga watan Augustan shekara ta 1960  a wani kauye a kudancin kasar Lebanon, Sayyid ya tashi a cikin gida mai saukin rayuwa, ya fara karatu kamar yadda ko wani...
    Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya buƙaci manyan ‘yan siyasa daga yankin Arewa da Kudu Maso Kudu su haɗa kai gabanin zaɓen 2027. El-Rufai, ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi dattijo kuma jagoran yankin Neja Delta, Edwin Clark. Babu ɗan Arewa mai hankali da zai yi tallan APC a 2027 – Jigo a PDP Fasinjoji 4 sun rasu yayin da bas ta kama da wuta a Jigawa A cewarsa, Najeriya tana cikin matsala mai tsanani kuma tana buƙatar ɗauki cikin gaggawa. “A shekarun baya, Arewa da Kudu Maso Kudu sun kasance abokan siyasa,” in ji El-Rufai. “Kada mu manta da hakan. Mu koma kam wannan haɗin kai. Mu ceci wannan ƙasa...
    A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah Sheikh Na’im Kassim ya bayyana Shahidin al’umma Sayyid Hassan Nasrallah da cewa, jagora ne na musamman na al’ummun larabawa da musulmi kuma shugaban gwgawarmaya. A cikin jawabin da ya gabatar a lokacin jana’izar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah, da Shahid Hashim Safiyuddin, inda ya bayyan cewa: A wannan rana muna yin ban kwana da jagora na tarihi na musamman wanda kuma yake a matsayin alkiblar ‘yantattun na duniya. Sheik Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah ya kasance wanda ‘yan gwgawarmaya suke kauna, wanda Falasdinu da birnin Kudus ne manufarsa, ya kuma taka rawa wajen farfado da batun kare hakkokin Falasdinawa. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya kuma ce; Sayyid...
    Wanda ya wakilci jagoran juyin juya halin musulunci na Iran a wajen jana’izar Babban magatakardar kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrallah da kuma Shahid Safiyuddin Hashim, ya gabatar da jawabi da a ciki ya bayyana cewa: Jagoran jihadi mai girma, kuma shugaban gwgawarmaya a cikin wannan yankin, Sayyid Hassan Nasrallah ( Allah ya daukaka matsayinsa)  ya kai matsayi na koli na daukaka da izza. Sayyid Mujtaba al-Husainy ya kuma ce; A wannan lokacin za a binne gangar jikin Sayyid a cikin kasar da ya yi jihadi saboda Allah akanta, amma ruhinsa da kuma tafarkinsa na gwgararmaya zai kara daukaka fiye da kowane lokaci a baya. Sayyid Mujtaba al-Husaini ya kuma ce:Makiya su kwana da sanin cewa, gwgawarmaya za ta cigaba da...
    Jagoran harkar musulunci ta Najeriya wanda ya halarci jana’izar shugaban kungiyar Hizbullah Sayyid Shahid Hassan Nasrallah a birnin Beirtu ya bayyana cewa; Yadda miliyoyin mutane su ka halarci jana’izar yana nuni da cewa, gwgawarmayar musuluncin ta sake jaddada kanta. Sheikh Ibrahim Yakub Ibrahim El_Zakzaky ya kuma ce; Sayyid Hassan Nasrallah yana a matsayin takaitaccen hoton al’ummar musulmi ne, kuma  gudanar da jana’izar da na gani yana nuni da cewa; Ruhinsa yana nan a raye cikin fagen daga. Har ila yau jagoran ja harkar musulunci a Nigeria ya ce, abokan gaba ‘yan sahayoniya sun zaci cewa ta hanyar kisan gilla za su kawo karshen gwgawarmaya,amma abinda yake faruwa a yau, yana nuni da cewa gwgawarmaya ta kara sabunta kanta, kuma da...
    Sin: Manufar Zuba Jarin Amurka Na Matukar Kassara Hadin Gwiwar Kasuwancin Kamfanonin Sin Da Amurka
      dimbin Asarar Da Manoman Cittta Suka Tabka: Shugabar kungiyar manoman Citta da sarrafata ta kasa (GGPMAN) Florence Edwards, ta alakanta samun raguwar Cittar da ake fitarwa daga kasar nan zuwa kasashen ketare da barkewar cutar da ta lalata gonakin wasu manomanta. Florence ta kara da cewa, akasarin irin samfurin Cittar da manoman ke shukawa a fadin kasar nan, sun shafe sama da shekaru 20 suna amfani da shi. Ita ma wata manomiyar Cittar a Jihar Kaduna, Joy Bolus ta bayyana cewa, ta kashe sama da Naira miliyan daya a shekarar da ta gabata wajen aikin noman Cittar a tata gonar, ta hanyar yin hadaka da miinta, amma saboda barkewar cutar a bara, hakan ya jawo gonar ta lalace baki-daya....
    Thomas Bach: Kasar Sin Ta Ba Da Gagarumar Gudummawa Ga Bunkasa Wasannin Olympics
    Matuƙar Abdullahi Abbas Ya Cigaba Da Zama Shugaban APC A Kano, Zan Fita – Ata
    Amurka Ta Zama Jagorar Bata Ka’idoji Da Dokar Duniya Bisa Amfani Da Makamin Harajin Kwastam
    Mutane huɗu sun rasa rayukansu, wasu 10 kuma sun samu raunuka bayan wata motar bas ƙirar Hummer ta kama da wuta a garin Gwaram da ke Jihar Jigawa. Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar Asabar, a kusa da makarantar sakandaren gwamnati ta Government Girls Unity Secondary School da ke Gwaram. Gobara ta ƙone gidaje, amfanin gona da dabbobi a Borno  Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Kakakin ’yan sandan Jihar Jigawa, SP Lawan Adam, ya tabbatar da faruwar hatsarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi. Ya ce motar ta taso daga Ƙaramar Hukumar Zaki daga Jihar Bauchi zuwa ƙauyen Ribadi da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram. Sanarwar ta bayyana cewa...
    Gwamnan ya gargadi jami’an gwamnati da su kauce wa dabi’ar nuna san kai da rashin gaskiya wajen zabo matan da za su amfana da wannan tallafi. A cewar Gwamna Radda, an zabo mata 10 daga kowace guduma, kuma za a bai wa kowace mace awaki guda hudu da suka hada awaki uku da bunsuru daya, sannan za a bai wa kwararren manomi guda hamsin wanda zai koyar da su dubarun kiwo. Tun da farko da take jawabi, kwaminisiyar harkokin mata ta Jihar Katsina, Hajiya Hadiza Yar’adua ta bayyana wannan tallafi a matsayin wata gagarumar gudummawa da gwamnati za ta bunkasa harkokin mata ta hanyar dogoro da kai. A cewarta, taimakon da Gwamna Radda ya bayar ko shakka babu zai amfani...
    Wata gobara ta tashi a ƙauyen Bukar da ke Ƙaramar Hukumar Konduga a Jihar Borno, ta yi ɓarna mai tarin yawa. Gobarar ta lalata gidaje, amfanin gona, da dabbobi na miliyoyin Naira, amma babu wanda ya rasa ransa. ’Yan bindiga sun harbe fasto, sun sace wasu a coci Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Wani mazaunin ƙauyen ya ce gobarar ta fara ne daga wutar girki a wani gida, sai iska mai ƙarfi ta bazata zuwa wasu gidaje, lamarin da ya sa mutane suka kasa shawo kanta. Bayan kamawar wutar, sojojin Najeriya da ke yankin sun garzaya domin kai ɗauki. Sun taimaka wajen kashe wutar tare da ceton tsofaffi da yara. Kazalika, gobarar ta cinye...
    Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025. Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta...
    ’Yan bindiga sun kai hari wata coci da ke yankin Ogwashi-Uku a Jihar Delta, inda suka yi awon gaba da masu ibada a daren ranar Juma’a. Sun harbi fasto sannan suka sace masu i ada shida a cocin, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici. Gawuna ne ya lashe zaɓen Gwamnan Kano a 2023 — Ata Jami’ar Sojoji ta BIU ta ƙaddamar da taron magance zamba Sun kai harin ne da misalin ƙarfe 10 na dare kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Delta. Maharan sun harbi fasto, Apostle Divine Omodia, wanda yanzu haka yake kwance a asibiti. Mutanen yankin suna cikin fargaba kan rashin tsaro a wuraren ibada, inda suke roƙon gwamnati ta ceto mutanen da aka sace...
    Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)  
    Wasu rahotannin na cewar Ratcliffe ya zuba kudin da ya kai fam miliyan (£300m) a United, domin bunkasa filin atisaye na Carringhton da tsara yadda za a fuskanci gina sabon filin wasa sannan ana jiran Ratcliffe ya bayar da izinin fara shirin gina sabon filin da za a kashe sama da fam biliyan biyu (£2bn), ko kuma a yi wa tsohon filin wasa na Old Trafford kwaskwarima da zai ci Fam biliyan 1.5. Manchester United ta sanar da yin hasarar kasuwanci da ya kai Fam miliyan 113.2 daga ranar 30 ga watan Yunin 2024 kuma kawo yanzu kungiyar tana mataki na 15 a teburin Premier League, bayan wasan mako na 24. Amma kuma har yanzu kungiyar tana buga gasar cin...
    Daga karshe, jarumin wanda ya shafe shekaru fiye da 10 a Masana’antar Kannywood, ya shawarci matasa masu sha’awar shiga harkar fim, su tabbatar sun zama masu hakuri da biyayya ga na gaba da su, muddin suna son samun nasara a rayuwarsu ta jarumai. “Dole ne ka kasance mai hakuri a rayuwa, domin kuwa babu wanda ya zama wani abu ba tare da ya sanya hakuri a cikin al’amuransa na yau da kullum ba, duk wanda ka gani ya zama wani abu, ko ya samu wata daukaka ko shahara a rayuwa, to dole akwai kalubalen da ya fuskanta, domin kuwa ko a makaranta sai an ware wani lokaci da za a yi jarrabawa; domin gane masu fahimta da wadanda ba sa...
      Masu kira ta waya a shirin Zamani Abokin Tafiya na FRCN Kaduna sun bayyana damuwa kan jinkirin biyan basussukan fansho ga tsofaffin ma’aikata duk da umarnin shugaban ƙasa da aka bayar kwanan nan. Sun jaddada bukatar jami’an da ke kula da lamarin su hanzarta aiwatar da biyan kuɗaɗen domin girmama sadaukarwar da dattawan ƙasa suka yi da kuma rage cin hanci da rashawa a hidimar jama’a. Masu kiran sun yi kira ga jami’ai da su nuna kishin ƙasa da tsoron Allah a yayin gudanar da aikinsu domin cika burin al’umma da kuma ci gaban ƙasa. Alhaji Ibrahim Muhammad Katsina, Isya Soba, Ibrahim Allarama, Umar Aliyu Soba, Shafi’u Nalantawa, da Maza Jiya Soba, waɗanda su ma suka yi kira, sun...
    “Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.”   Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa.   Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba.   “Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.”   Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya...
    Jami’ar Sojojin Nijeriya da ke Biu (NAUB) ta ƙaddamar da taron magance zamba ta hanyar binciken fasaha karo na farko, wanda ya nuna ƙaruwar tasirin wannan jami’a a fagen ilimi a Nijeriya. Taron ya gudana ne bisa taken “Kididdigar Forensic: Zuwa Ga Sabon Tsarin Magance da Gano Zamba,” wanda Farfesa Ahmad Imam, ƙwararre a fannin ƙididdigar kuɗi da magance zamba ya gabatar. Za a kafa ƙarin makarantu a Zariya — Abbas Tajudeen Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe Tattaunawar ta jaddada dabarun zamani domin tunkarar zamba mai salo da kuma tsare-tsaren da za su taimaka wajen gano da magance laifukan kuɗi da ke ƙara ƙamari. Shugaban Jami’ar NAUB, Farfesa Kyari Mohammed, ya bayyana wannan taro a matsayin...
    DPS Abubakar ya ce kwamishinan ‘yansandar jihar, CP Aliyu Abubakar Musa, ya gode wa babban sufeton ‘yansanda, Kayode Egbetokun da Gwamna Dikko Radda saboda goyon bayan da suke bayarwa wajen karfafa tsaro.
    Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya jaddada kudirinsa na karfafawa matasa sana’o’i da ayyukan yi a jihar. Ya bayyana haka ne a yayin bikin bude wani katafaren shago da wani bawan Allah ya gina a kan titin Malam-Madori a karamar hukumar Hadejia. Ya bayyana cewa, bai wa matasa damar yin sana’o’i shi ne jigon tsare-tsaren gwamnati mai dauke da manufofi 12,  da ke da nufin daukaka jihar zuwa matsayi mafi girma. A cewarsa, daya daga cikin ginshikan tsare-tsaren gwamnatinsa shi ne samar da damammaki da ke bai wa matasa sana’o’in dogaro da kai, domin samun ci gaba a kasuwar hada-hadar kudi. Gwamna Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta kaddamar da kafa shaguna da za a rika sayar da kayayyaki...
      Ya kuma bayyana kalubalen samar da ruwan sha da al’umma ke fuskanta, inda ya bayyana cewa suna da rijiyoyin burtsatse, amma ba sa aiki.
    Shugaban Majalisar Wakilai, Dokta Abbas Tajudeen ya ce Kasafin Kuɗin Nijeriya na baɗi zai ba da damar kafa ƙarin makarantu na matakin Tarayya a mazaɓarsa ta Zariya. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara-shekara karo na 31 da 32 na ƙungiyar bunkasa ilimi ta Zariya, watau ZEDA da aka gudanar a Zariya. Mai Pataskum ya buɗe masallacin garin Danga a Yobe An kama mutum biyu kan kisan wata mata saboda maita Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun haɗa da makarantar firamare da sakandare na yara masu buƙata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo. Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafin na musamman ga ɗaliɓin da ya fi...
    Mai martaba Mai Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wuriwa Bauya, ya jagoranci bikin buɗe sabon masallacin Juma’a da aka gina a Garin Danga a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke Jihar Yobe. Bikin kaddamar da sabon masallacin Juma’ar, wanda ya jawo shugabannin al’umma, malaman addini, da mazauna yankin ya nuna irin gagarumin ci gaba da aka samu a harkokin addinin musulunci a yankin. Mai Pataskum, wanda ya yi fice wajen bayar da gudunmawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba a yankin, ya yaba da kokarin da masu bayar da tallafi na kasar Malaysia suka yi na gina masallacin, tare da jaddada rawar da yake takawa wajen samar da haɗin kai da ci gaban yankinbmasarautar. Mai martaba Sarkin ya yi...
    Rundunar ‘yan sandan yankin Biu ta tsare wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wata mata ‘yar shekara 50 da ake zargi da bokanci da maita. Kwamishinan ‘yan sandan jihar Borno, Yusuf Lawan ya tabbatar da hakan ga manema labarai a Maiduguri. Ɗan shekara 43 ya auri mai shekara 88 Yadda ƙananan yara ke zaman kurkuku ba tare an da kai su kotu ba Kwamishinan ya ce an kashe matar mai suna Hajara Saleh ne a ranar 21 ga watan Fabrairu a unguwar Bantine da ke Ƙaramar Hukumar Biu ta Jihar Borno. Kwamishinan ya bayyana cewar, waɗanda ake zargin — Ja’o Muhammad da Idris Muhammad — sun yi tarayya wajen kashe matar a dalilin zargin maita da suke mata....
    Hukumomin da ke kula da wasannin kwallon kafa a kasar Ingila sun fara shirin fara amfani da fasahar tantance satar gida a karon farko a gasar cin kofin FA ta Ingila. A ranar Alhamis hukumar kwallon kafa ta Ingila ta sanar da cewa za a yi amfani da fasahar a wasanni bakwai da za a fafata a filayen kungiyoyin gasar Premier kuma hukumar FA ta ce nan gaba za a yi amfani da fasahar a wasannin gasar Premier. Tun da farko kungiyoyin Premier sun amince da a soma amfani da fasahar a kakar wasa ta 2024 zuwa 25 amma aka jinkirta domin kammala gwaji kuma a kakar wasa ta 2022 zuwa 2023 ne hukumar kwallon Turai ta UEFA ta soma...
    Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi kira da a gaggauta bibiyar bayanan manyan laifuka na shugabannin gwamnatin mamayar Isra’ila A wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na kasar Holland, ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya yi Allah wadai da ci gaba da mamaya da kuma laifukan da yahudawan sahayoniyya suke yi a Falasdinu, tare da yin kira ga kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa wajen hanzarta bibiyar bayanan shari’a da laifuka a kotunan duniya dangane da kisan kiyashi da laifukan yaki da shugabannin mamayar Isra’ila suka aikata. Kamfanin dillancin labaran Fars ya habarta cewa: Ministan harkokin wajen kasar Holand Caspar Veldkamp da takwaransa na Iran Abbas Araqchi sun tattauna kan batutuwan da suka shafi kasashen...
    Tawagar Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa: Ba a hana sayar da jirgin mara matuki ciki na ‘Shahed’ ba Tawagar Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ta mayar da martani kan baje kolin jirgin saman Iran a babban taron jam’iyyar Republican inda ta ce: Babu wata doka da ta haramta sayar da jirgin sama maras matuki ciki na Shahed. Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa: Jirgin sama mara matuki ciki na Shahed yana daya daga cikin mafi kyawun nau’ikan jiragen sama marasa matuka ciki a duniya, kasancewar yana da kwarewa sosai wajen ganowa, sa ido da kuma aiwatar da aiki inda ya dace, sannan kuma yana da araha da...
    ‘Yan daban sabuwar gwamnatin Siriya sun kai samame wani Masallaci da ke cikin karkarar birnin Damascus tare da korar masu ibada Kungiyar kare hakkin bil’adama ta kasar Siriya ta sanar da cewa: Jami’an tsaron kasar da ke da alaka da gwamnatin rikon kwarya a kasar Siriya sun kai farmaki kan Masallata da ‘yan kasar ke gudanar da ibadu a cikin masallacin Al-Mustafa da ke unguwar Andalusia a garin Babila a cikin karkarar birnin Damascus, bayan da suka ki mika musu makullan masallacin da kuma rufe Masallacin saboda sabanin Mazhaba. Hakazalika ‘yan daban Al-Jolani sun lalata ofisoshi da hotuna da ke cikin masallacin, lamarin da ya fusata mazauna birnin. Masu lura da al’amura sun bayyana cewa: An gina masallacin ne da...
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Shirinsa kan Zirin Gaza yana da kyau, amma ba zai tilasta aiwatar da shi ba, sai dai zai ci gaba da ba da shawara kawai An gudanar da wani zaman taron koli na kasashen Larabawa a kasar Saudiyya, inda aka tattauna Shirin kalubalantar kudirin shugaban Amurka Donald Trump dangane da Gaza. Taron tuntuba da aka gudanar bisa gayyatar yarima mai jiran gado na Saudiyya; Zaman ya tattauna ra’ayoyi kan kokarin hadin gwiwa na goyon bayan al’ummar Falasdinu. Kamfanin dillancin labaran Saudiyya ya watsa rahoton cewa: An gudanar da taron na yau da kullun tare da halartar sarkin kasar Jordan, shugaban kasar Masar, da kuma kasashen Larabawan yankin Tekun Fasha, in ban da masarautar Oman,...
    Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki. Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai...
    Rayuwar Nura Muhammad dan shekara 13 a duniya ta gamu da cikas bayan da ya tsere tsallake rijiya da baya a lokacin da gungun wasu ’yan ta’adda suka kai hari a kauyensu da ke Karamar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato, inda suka raba shi da iyaye kuma babu matsuguni. Don haka ba shi da wani zabi, dole ya koma garin Sakkwato, domin fara sabuwar rayuwa. Ko da aka tambaye shi inda iyayen nasa suka, sai ya kada baki ya ce, “Ban san inda iyayena suke ba,” ko sun rayu a lokacin da aka kai wa kauyen hari a farkon shekara ta 2023. PDP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomin Osun Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna...
    Dauda ya kara da cewa, babu wata waka da zai yi ba tare da an bukaci ya yi ta don isar da wani sako ba. Haka zalika, Shugaba Tinubu, ba shi da wani buri na tara dukiya a halin yanzu; illa kawai dai fatan barin tarihi mai kyau a matsayinsa na Shugaban kasa, kamar yadda sauran mazan jiya; irin su Sir Ahmadu Bello da Abubakar Tafawa Balewa suka bari. Dangane da abin da wasu ke dauka cewa, ana biyana makudan kudade; don yin wakokin da za su kawar da hankalin mutane, su sani cewa; na fi mayar da hankali a kan noma fiye da yadda nake yi wa harkar waka, dalili kuwa; ni manomi ne wanda a yanzu haka duk...
    Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya bayyana aniyar kafa karin makarantu a Zaria. Shugaban majalisar wakilai, Dr Abbas Tajuddeen ya ce za a kafa karin makarantu a mazabar tarayya ta zaria a kasafin kudin shekarar 2026. Shugaban majalisar ya bayyana haka ne lokacin babban taron shekara karo na 31 da 32 na kungiyar bunkasa ilimi ta zaria, watau ZEDA da aka gudanar a Zaria. Ya bayyana cewa makarantun da ake shirin kafa wa sun hada da makarantar firamare da sakandare na yara masu bukata ta musamman da kwalejin tarayya na koyon aikin noma da kiwo. Shugaban majalisar ya kuma bayyana fara bada tallafi na musamman ga dalibin da ya fi kowa kwazo a fannin koyon ilimin kwamfuta da kuma...
    “Duk da cewa an dan samu raguwar kai hare-hare amma har yanzu ana samun wasu su shiga su kashe mutane sannan su tafi da wasu domin kuɗin fansa” in ji ɗan majalisar. Sannan ya kuma kalubalanci rashin hanya mai kyau a yankunan wanda a cewarsa hakan ma yana kawo tsaiko wajen fatattakar yan ta’adda. Danlami Stingos ya kuma yabi gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da take yi na yaƙi da yan ta’adda sannan ya kuma riko gwamnatin da ta dage wajen samar da hanyoyi a yankunan da suke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
    Sannan dadin abin aka fada amma mene ne illar da ka iya biyo bayansa? Shin hakan ma batun yake a ilmance ko kuwa? Wannan ta sa da zarar haihuwa ta gabatowa mace kowa sai ka ga shawara yake ba ta akan komai ma, musamman ma atsakaninsu mata, Eh munsan kuna yi ne bisa kyakkyawar manufa da son ku ga ta haihu lafiya, amma fa ba duk ‘yan’adam bane zubin halittarsu tare da komai yai daidai da na juna ba. Ba mamaki wata kuka ji ta yi irin haka ta wanye lafiya, amma mu tuna fa idan wani ya yi abu ya kwana lafiya to fa wani in ya yi wahala zai sha. Babu wani abu da sunan zaki jikin mai...
    Wannan bayanin da Babangida ya yi a kan zaɓen ya haifar da maganganu a kan irin rawar da Abacha ya taka wajen soke zaɓen da yadda ya hana Nijeriya komawa mulkin dimokuraɗiyya a wancan lokacin. Marigayi Sani Abacha dai ya yi mulkin soja a Nijeriya daga shekara ta 1993 zuwa 1998 da ya rasu.
    Jam’iyyar PDP mai ci a Jihar Osun ta lashe zaɓen dukkan kujerun ƙananan hukumomi jihar guda 30 da na kansiloli 332 da aka gudanar yau Asabar. Shugaban hukumar zaɓen jihar OSSIEC, Hashim Abioye ne ya sanar da sakamakon a wani taron ganawa da manema labarai da ya yi a jihar. Wani mutum ya yi wa agolarsa fyaɗe ta samu juna biyu An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Da yake jawabi a yammacin wannan Asabar ɗin a birnin Osogbo, Hashim Abioye ya ce an samu nasarar gudanar da zaɓen bisa duk wasu tsare-tsare da dokoki suka tanadar. Ya bayyana cewa jam’iyyu 18 ne suka shiga zaɓen domin cike giɓin da ake da shi a madafan iko na ƙananan hukumomin...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta cafke wani mutum mai shekaru 28, Samuel Alfred bisa zargin yi wa wata agolarsa fyaɗe har ta samu juna biyu. An cafke mutumin ne tare da wani abokinsa, Ikechukwu Obi mai shekaru 30 kan zargin wannan aika-aikar. An haifi alade mai fuskar mutum a Philippines Ko Real Madrid za ta iya lashe Gasar Zakarun Turai bana? Bayanai sun ce ababen zargin sun kai budurwar mai shekaru 14 wani ɗaki da ke yankin Ojo na jihar ta Legas inda suka raba ta da budurcinta. Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da faruwar lamarin wanda ya ce mahaifiyar yarinyar mai suna Deborah ce ta kai ƙorafi ofishinsu da ke Okokomaiko. Hundeyin ya ce...
    Ministan harkokin wajen kasar Sin, Wang Yi ya bayyana a jiya Jumma’a cewa, kasar Sin tana goyon bayan tsarin ciniki cikin ‘yanci tare da zaman kungiyar ciniki ta duniya, watau WTO a matsayin wadda za ta yi uwa-ta-yi-makarbiya a kan tsarin, kuma za ta ci gaba da mara baya ga yin garambawul a kungiyar ta kasa da kasa. Wang, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da babbar darektar WTO, Ngozi Okonjo-Iweala, a gefen taron ministocin harkokin wajen kasashen G20, a birnin Johannesburg, birni mafi girma kuma cibiyar hada-hadar tattalin arzikin Afirka ta Kudu. A nata bangaren, Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, a tsakiyar rudanin da duniya ke fama da shi, kasar Sin ta hau kan turba mai kyau,...
    Mansa Mūsā, ko dai shi jikan ko kuma abokin wasan Sundiata wanda shi ne ya kirkiro Daular Mali yah au kan karagar mulkin ne a shekarar. A karni na 17 (1324),lokacin ne ya tafi aikin Hajjin wanda ya zama abinmagana saboda dalilai masu dama. Aikin Hajjin da ya tafi ne ya sa idon duniya ya bude saboda irin arzikin da Allah ya yi wa kasar ta Mali.
    Mamallakin aladiyar da ta haihu mai suna Alfredo Cardinas Junior, ya firgita bayan da ɗaya daga cikin aladun nasa ta haihu yana kallo, inda ya ji sautin kukan ɗan aladen kamar na dan-adam kuma yake kama da na jaririn ɗan-adam. Jaririn aladen mai siffar mutum yana daga cikin jarirai takwas da aladiyar Mista Cardinas ta haifa kuma babu wani daga cikinsu da aka rawaito cewa ya samu naƙasu. Haɗarin mota ya laƙume rayuka 12 a Neja Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Kano ta raba kayan tallafi Mai aladen, Alfredo Cardinas Jr, ya bayyana cewa ya firgita sosai a lokacin da aka haifar masa jaririn aladen mai fuskar mutum. Ya bayyana cewa: “Na ji tsoro sa’ad da na fara ganin jaririn. Na kara...
    Jagoran kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka a bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, ya zanta da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ta kafar bidiyo jiya Jumma’a 21 ga wata, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasashen biyu, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma. Bangarorin biyu duk sun amince da muhimmancin alakokin tattalin arziki da kasuwanci a tsakaninsu, inda suka yarda su ci gaba da tuntubar juna kan batutuwan da suka fi daukar hankulansu. Har wa yau, kasar Sin ta nuna matukar damuwa kan matakin da Amurka ta dauka kwanan nan, na kara sanya wa hajojin kasar Sin...
    Kungiyar Hamas ta saki yahudawa 6 a marhala ta 7 na musayar fursinoni tsakaninta da HKI karo na 6 a yau Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar Falasdiawan na fadar cewa, bayan wannan musaya ta 7, suna dakon a fara marhala ta biyu na yarjeniyar da ke tsakaninta da HKI. Labarin ya kara da cewa a wannan karon dakarun Hamas sun mika fursinonin yahudawan ne a garin Rafah na kan iyaka da kasar Masar. Kuma kamar yadda aka saba hamas ta mika yahudawan ne ga kungiyar red Cross wanda suke mikasu ga HKI. Hamas ta bada sanarwan cewa firsononi Falasdinawa 50 wadanda aka yankewa hukuncin kisa, sannan 60 wadanda aka yankewa hukuncin mai tsawo, da...
    Mutane 12 Sun Rasu A Hatsarin Mota A Neja
    A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
    Sojojin kasa na jumhuriyar Musulunci ta Iran sun hada guiwa da sojojin ruwa don atisayen hadin guiwa wanda suka sanyawa suna Zulfikar 1403. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kakain atisayen Brigadier General Alireza Sheikh yqana cewa a cikin wannan atisayen suna son gwada aiki tare da sojojin masu aiki a sama da na ruwa don samar da yanayi irin na yanayi yaki da gaske don fahintar da harkokin yaki suke tafiya. General Alireza Sheikh yace a bangare na farko na wannan atisayen mun gwada yadda jiragen yakin masu saukar ungulu zasu sauka su tashi a dai dai lokacinda ake cikin budewa juna wuta da makiya. Sannan manufar atisayen gaba daya itace samar da yanayi ta yadda...
    A jiya Jumma’a ce aka kammala taron kungiyar kasashen G20 a birnin johanasboug na kasar Afrika ta Kudu, kuma inda batun yake-yake a yankunan daban-daban na duniya ne suka mamaye taron. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa yakin Ukraine da Rasha Hamas da HKI, Congo da sauransu ne suka mamaye taron inda ministocin harkokin wajen kasashen na G20 suka tattauna a kansu. Ministan harkokin wajen na kasar Afrika ta Kudu Ronal Ramola ya bayyana cewa duk tare da cewa babu wani babban jami’an gwamnatin kasar Amurka a taron amma taron ya gudana kamar yadda ake saba. Kungiyar G20 Taron kasashe masu arziki a duniya, wadanda suke da kasha 85% na  tattalin arziki a duniya sannan suna...
    Jakadan Kasar Sin Ya Bukaci Dakatar Da Duk Wani Tashin Hankali A Gabashin Kongo
    An shawarci shugabanni da aka zaba da su girmama hukuncin kotu domin tabbatar da dimokuradiyya a ƙasar. Wani malami a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Kamilu Fagge, ya bayar da wannan shawara a Kaduna, yana nuna damuwarsa kan zargin karya dokokin kotu a harkokin siyasa. Ya bayyana damuwarsa kan matakin da Gwamna Ademola Adeleke na Jihar Osun ya dauka na gudanar da zaɓen kananan hukumomi duk da umarnin kotu da ke hana hakan. Farfesa Fagge ya gargaɗi shugabanni da aka zaɓa cewa rashin mutunta hukuncin kotu, duk da rantsuwar da suka yi na kare kundin tsarin mulkin ƙasa da bin doka, na iya zama barazana ga dimokuradiyya. SULEIMAN KAURA