Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Biya Fiye da Mahajjata 3,000 Kudadensu.
Published: 1st, February 2025 GMT
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta biya fiye da Mahajjata dubu uku da suka kammala aikin Hajjin shekarar 2023 kudaden da Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta mayar masu.
Mai Magana da Manema Labarai na hukumar, Yunusa Mohammed Abdullahi, shine ya bayyana hakan sannan ya kara da cewa an turawa kowane mahajjati ya karɓi sama da naira dubu sittin da ɗaya a asusunsa bakinsa.
Hukumar Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa an mayar da kudaden ne saboda katsewar wutar lantarki a lokacin da maniyyata ke Muna, wanda ya shafi tsarin sanyaya iska kuma hakan ya janyo musu matsala.
Hukumar Alhazai na Jihar Kaduna ta ta yaba da hakurin wadanda har yanzun basu same kudadensu ba, inda ya bayyana cewa jinkirin ya faru ne sakamakon wasu maniyyata ba su bayar da cikakken bayanan asusun ajiyarsu na banki ba.
Mallam Yunusa Abdullahi ya tabbatar da cewa an shirya sake fitar da wani zagaye na biyan kudaden a mako mai zuwa, kuma hukumar tana aiki tukuru don tabbatar da cewa dukkan alhazan 2023 da suka cancanta sun karɓi kuɗinsu.
Jami’in Hulɗa da Jama’a ya jaddada muhimmancin gabatar da bayanan asusun banki cikin lokaci, yana kira ga duk maniyyatan 2023 da har yanzu ba su karɓi kuɗinsu ba su tuntubi jami’in rijista na ofishin ƙaramar hukumarsu.
“Waɗannan bayanai suna da matuƙar muhimmanci don hanzarta mayar da kuɗi ga sauran Mahajjatan,” yana mai jaddada cewa KSPWA na da ƙudirin tabbatar da an biya dukkan kudaden Mahajjatan mudin sun banyarda bayanan asusun bankinsu akan lokaci.
Idan baza a manta ba, Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya ce, “Mun fahimci muhimmancin mayarda waɗannan kudaden, kuma mun dukufa wajen tabbatar da cewa an kammala rabonsu cikin sauri da gaskiya.”
Sanarwar ta bayyana cewa, baya ga kammala biyan kudaden mayarwa na shekarar 2023, hukumar ta riga ta fara mai da hankali kan shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Rel/Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Biya Gwamnatin Jihar
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗan majalisa ya biya wa ɗaliban mazaɓarsa N45m na jarabawar WAEC
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa.
Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa daliban mazaɓar a duka matakai don cika alkawura da ya yi a baya.
Ya ce ya yanke shawarar yin haka ne don tallafa wa iyayen ɗalibai marasa galihu don ba su damar cimma burinsu na samar wa ’ya’yansu ilimin zamani dana addini.
Ya ce kawo yanzu ya kashe sama da Naira miliyan 500 a cikin shekara biyar da duka gabata a kan irin wannan aiki.
Ya kuma yi alƙawarin ci gaba da agazawa a fannin ilimi inda ya bukaci daliban da suka amfana da su tabbatar sun yi amfani da damar yadda ya dace, kana su mayar da hankalinsu ga karatunsu da sauran harkokin rayuwarsu na yau da kullum.
A jawabinsa Shugaban Kwamitin Jarabawar ta WAEC, Malam Awaje Nasarawa da Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Keffi, Honorabul Damagani da sauran manyan baki, sun yaba wa dan majalisar, sannan suka bukaci daliban da su yi kyakkyawar amfani da damar don kyautata rayuwarsu a nan gaba.
Wasu daga cikin daliban da suka amfana sun yaba wa dan majalisar inda suka yi addu’ar Allah Ya saka masa da alheri.