2025-03-04@13:59:05 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1062
«Biya»:
Masarautar Katsina ta ba wa dagattai da masu unguwaninta horo a kan sasanta jama’a a matsayin ginshikin samun dauwamammen zaman lafiya. An gudanar da taron ilmantarwar na tsawon kwanaki uku ne a kan yadda za a assasa zaman lafiya a tsakanin al’umma ta hanyar sasanci don samun aminci mai dorewa. Shugaban kamfanin tuntuba na Green...
Yayin da al’ummar Musulmai a Najeriya da duniya ke fara azumin watan Ramadan, Gidauniyar Tunawa da Sir Ahmadu Bello ta aike da sakon fatan alheri, tana kira da a yi amfani da wannan lokaci mai daraja wajen sabunta zukata da nuna tausayi da karfafa hadin kai a kasa. A cikin wata sanarwa da...
Kwamitin ya kunshi Bola Oyebamiji a matsayin shugaba, wanda kuma shi ne babban darakta na hukumar dake kula da sufuri akan doron ruwa ( NIWA), sai kuma wakilai daga gwamnatocin jihohi, da hukumar matuka kwale-kwale ta cikin gida, hukumar kwararru ta kula da lafiyar zirga-zirga akan doron ruwa. An kuma zabi Adams Offie a mastayin...
Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadadna a halin yanzu sun isa kasar Poland. Jaridar “Bloomberg” ta bayyana...
A karon farko manazarta a Iran sun yi nasarar samar da maganin farfadiya da kuma ciwon rabin kai Gabanin wannan lokacin ana amfani da maganin “Topiramate” wanda ake shigo da sanadari mafi muhimmanci na hada shi daga waje, domin yinsa a matsayin kwayoyi da kuma kafso. Wannan maganin ya sami karbuwa a matsayin na uku...
Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, ta bayyana cewa saɓani ne ya shiga tsakanin matashin da mahaifiyarsa, wanda ya haifar da tashin hankalin. Majiyoyi daga unguwar sun ce matashin yana shaye-shaye, kuma mahaifiyarsa ta faɗa masa ya daina, wanda hakan ne ya fusata shi. Kwamishinan ‘yansandan Jihar Bauchi, CP Auwal...
Ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa da Toto daga Jihar Nasarawa, Honorabul Abdulmumin Ari ya ba da cekin Naira miliyan 45 don biyan kuɗin jarabawar WAEC ga daliban sakandare a mazaɓarsa. Da yake jawabi a wajen taron a garin Keffi, Abdulmumin Ari ya bayyana cewa kimanin shekara biyar ke nan yake aikin agaza wa...
Kotu ta tsare wani magidanci a gidan yari kan zargin barazana ga rayuwar matarsa da yake zargin ta da maita. Babbar Kotun Musulunci da ke Gazawa a Jihar Kano ta tsare mutumin ne bayan ya yi barazana tare da yunƙurin kai wa matar tasa farmaki da adda. Mai gabatar da ƙara, Sadiq Yusuf ya shaida...

Hamas Ta Ce Yarjeniyar Tsagaita Wuta Ne Kadai Za Ta Kubutar Da Fursinonin Yahudawa Daga Hannun Kungiyar
Wani babban Jami’in kungiyar Hamas Osama Hamdan ya bayyana cewa hanya daya tilo ta kubutar da ragowar Fursinonin yahudawan HKI daga hannun kungiyar, kuma ita ce dabbaka bangare na 2 na yarjeniya tsagaita wuta tsakanin kungiyar da kuma HKI. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Osama Hamdan yana fadar haka a jiya...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Esmail Baghaei ya yi kira ga gwamnatin kasar Turkiya ta sake tunani kan kalamanta dangane da JMI. Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Baghaei ya na fadar haka a jiya Litinin, a taron mako mako da ya saba gabatarwa a ko wace litinin. Ya yi...
Kasar Angola ta bada sanarwan cewa, zata shiga shirin kungiyar kasashen kudancin Afirka SADC na yankunan kasuwanci, wanda hakan zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin kasashen yankin . Kamfanin dillancin labaran Sputnik na kasar Rasha ya bayyana cewa shigar Angola cikin tsarin yankunan kasuwanci, SADC kuma a matsayin mamba na 14 a wannan tsarin zai dauke...
Bidiyon batsa ya ja wa wasu ’yan Tiktok biyu hukuncin ɗaurin shekara guda kowannensu a gidan yari bayan an gurfanar da su gaban kotu a Jihar Kano. Kotun Majiatare da ke Norman’s Land a Ƙaramar Hukumar Fagge ta yanke wasu ’yan Tiktok din hukunci ne bayan samun su da laifin saɓa wa dokokin Musulunci da...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai...
A ranar 28 ga watan Fabarairun da ya shude ne aka saki wani fim din kasar Sin mai lakabin “Creation of the Gods II: Demon Force”, a gidajen kallon sinima 39 dake sassan tarayyar Najeriya, da kuma wasu 2 dake kasar Ghana, da sinima 1 a Laberiya. Wannan ne dai karon farko da aka saki...
Hukumar kula da gandun daji da filayen ciyayi ta kasar Sin ta bayyana cewa, a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, namun dajin kasar ta Sin sun karu yadda ya kamata ba tare da cikas ba. Adadin manyan dabbobin Panda ya karu daga kimanin 1,100 a shekarun 1980 zuwa kusan 1,900 a yau, yayin da...
Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) ta bayyana cewa ta kama wani mutum da take zargin madugun fataucin ƙwayoyi ne, Ogbonnaya Kevin Jeff, a maɓoyarsa da ke Jihar Legas. Sanarwar da mai magana da yawun NDLEA, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce kamen mutumin mai shekaru 59 na zuwa...
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...
Majalisar Dokokin Jihar Legas ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus. Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda. Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da rabon abincin buɗa-baki HOTUNA: Tinubu ya...
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce Paris da London na aiki kan shirin tsagaita wuta na wata guda a Ukraine. A wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa, Emmanuel Macron ya ce London da Paris suna ba da shawarar tsagaita wuta na wata guda da kuma samar da makamashi.” Daga baya a cikin jawabin...
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gana da takwaransa na Saliyo Julius Maada Bio a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Ganawar tsakanin shugabannin ƙasashen Afirka biyu ta gudana ne a bayan labule, inda jami’an gwamnati kalilan ne suka halarta. NLC ta yi fatali da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu...
Karamar hukumar Malam Madori da ke jihar Jigawa, ta yi barazanar daukar matakin hukunta malaman makaranta da ba sa zuwa aiki. Shugaban karamar hukumar, Alhaji Salisu Sani Garun-Gabas ya bayyana haka a wata hira da manema labarai bayan raba kudi dubu hamsin a matsayin tallafin karatu ga dalibai ashirin da biyar a yankin. A cewarsa,...
Rashin kishin wani mutum ya zama abin mamaki bayan ya bayyana cewa, yana zaune lafiya tare da matarsa da suka yi shekara uku da wani saurayinta har ma sun shigo da shi cikin gidansu. Prince Soy, matashi mai dafa abinci a kasar Japan kuma mai amfani da intanet, wanda ke tallatawa da siyar da abincin...
Cocin Christ Evangelical & Life Intercessory Ministry da ke yankin Sabon Tasha a Ƙaramar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna, ya raba wa makarantun Islamiyya Musulmi masu ƙaramin ƙarfi akalla 1,000 hatsi albarkacin watan Ramadan. Shugaban Cocin, Fasto Yohanna Buru, ya ce sun yi haka ne domin yauƙaƙa dangantaka da kuma wanzar da zaman lafiya a...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta ɗora laifin ɓacewar bindigo 3,907 a hannun jami’anta a kan sakaci da kuma ƙarancin iliminsu game da kula da makamai. Da take ƙarin bayani kan yawaitar ɓacewar bindigon, rundunar ta ɗora laifin ci gaban matsalar a kan abin da ta kira “sakacin” manyan jami’ai wajen tura ’yan sandan da ba...
Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya (MDD), Antonio Guterres, ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar watan Ramadan, yana mai bayyana wannan lokaci a matsayin mai cike da falala, tausayi, da zaman lafiya. A sakon da MDD ta fitar ta hannunsa, Guterres ya ce, “Ramadan lokaci ne da ke karantar da kyawawan ɗabi’u na tausayawa, taimakekeniya, karamci,...
’Yan bindiga sun yi garkuwa da ɗalibai huɗu a Jami’ar Tarayya da ke Dutsinma a Jihar Katsina. ’Yan bindigar sun sace daliban ne a ɗakunan kwanansu da ke yankin Paris Quarters a garin na Dutsinma. Maharan ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47 sun kutsa yankin ne da misalin ƙarfe 4 an asubahin ranar Lahadi, suka yi...
Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya yi watsi da batun aike wa da dakarun zaman lafiya zuwa kasar Ukiraniya kamar yadda kasashen turai suke tattaunawa akai. Ministan harkokin wajen kasar ta Rasha ya bayyana cewa, gwamnatin Amurka tana son a kawo karshen yaki, da shimfida zaman lafiya,amma kuma kasashen turai suna son a...
Fitaccen dan siyasar kasar Lebanon Walid Junbilat ya bayyana cewa, ‘yan sahayoniya suna son yin amfani da kungiyoyin da ake da su a Syria domin tarwatsa hadin kan kasar. Walid Junbilat wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyyar “ al-takaddumil-Ishtiraki” ya ce zai ziyarci kasar Syria domin ganawa da mahukuntanta akan hatsarin dake tattare da tsoma...
Jagoran juyin juya halin musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya bayyana cewa; al’ummar Iran tana fuskantar makiya kafirai da munafikai, amma kasar ba ta da matsala da sauran al’ummun duniya. Har ila yau jagoran ya ce, alkur’ani mai girma yana kunshe da hanyoyin da ya kamata a yi mu’amala da dukkanin wadannan makiyan,...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Yanayin tsadar rayuwa da ake ciki ya sa dole a yi tattalin kuɗin da ake kashewa. An saba a watan Ramadana ana yawan yin girke-girke da kayan buɗa-baki iri-iri, amma kuma wannan azumin ya zo cikin yanayi na matsin tattalin arziki. NAJERIYA A YAU: Yadda Azumi Ke Inganta...
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio...
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars wacce ake wa laƙabi da Masu Gida ta doke abokiyar karawarta Enugu Rangers da ci 2-1 a filin wasa na Sani Abacha dake Kano. Wasan wanda aka fara da karfe 4 na yammacin ranar Lahadi, ya na daga cikin manyan wasanni masu zafi da ke ɗaukar hankalin masu sha’awar...
’Yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Bagiza da Rausa Kade a Ƙaramar Hukumar Arewa, Jihar Kebbi, inda suka kashe mutum shida a makon da ya gabata. Maharan sun kashe mutum biyar a Rausa Kade, sannan suka hallaka ɗaya a Bagiza yayin harin da suka kai domin satar shanu. Matata ta taɓa kawo min ƙarar Akpabio...
Jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya bayyana a cikin wani jawabi ta bidiyo da ya gabatar ga taron kolin jagorancin Sin na Duke-UNC a ranar 28 ga watan Fabrairu cewa, kasancewar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Sin da Amurka a duniya, abu ne da ya zama wajibi kuma nauyi ne dake kan wuyansu....
Mijin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Emmanuel Oritsejolomi Uduaghan, ya bayyana cewa matarsa ta taɓa kawo masa ƙorafi game da cin zarafin da ta ce Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi mata. A cewarsa, rikicin ya fara tun lokacin da Natasha ta tsaya takarar kujerar Sanata a 2019 a ƙarƙashin jam’iyyar SDP, inda ta nemi...
An kaddamar da cibiyar likitancin gargajiya na Sin ta farko, ranar Juma’a a Freetown, babban birnin kasar Saliyo, wadda ta zama muhimmin mataki a yunkurin kasar na amfani da likitancin gargajiya na Sin domin amfanawa al’umma. Kadammar da cibiyar ta biyo bayan kammala wani aikin binciken kiwon lafiyar al’umma a kasar wanda likitocin kasar Sin...
Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), ta ce ita ce ta kai samame otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Minna, Babban Birnin Jihar Neja. A yayin farmakin, an kama aƙalla baƙi 10 da ake zargi da aikata damfara a Intanet, wanda aka tafi da su Kaduna. Girke-girken...
Yau a filin namu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake yin Tsiren Dankali. Za a iya amfani da girkin namu na yau a matsayin abin buɗa-baki, da zarar an sha ruwa. Mahara sun yi basaja da kayan EFCC wajen sace mutum 10 a otal Sojoji sun ƙwato makamai a dajin Sambisa Ga...
‘Yan majalisar dokokin kasar Iran sun kada kuri’ar tsige ministan harkokin tattalin arziki da kudi Abdonnasser Hemmati daga mukaminsa saboda matsalolin tattalin arziki da kuma faduwar darajar kudin kasar. Hemmati ya rasa kuri’ar amincewa a zaman majalisar na wannan Lahadi inda ‘yan majalisa 182 daga cikin 273 suka kada kuri’ar tsige shi. ‘Yan majalisa tamanin...
Bisa labarin da shafin intanet na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin NPC ya fitar, za a gudanar da taron manema labarai na taro na uku na NPC karo na 14, a zauren taron manema labarai na babban dakin taron jama’a, da karfe 12 na safiyar ranar 4 ga watan Maris, inda mai magana da yawun...
Hamas ta tabbatar cewa “Shawarar da Netanyahu ya yanke na dakatar da shigar da kayan agajin da jin kai na kasashen duniya zuwa zirin Gaza, hakan na a matsayin laifin yaki da kuma keta yarjejeniyar tsagaita bude wuta da musayar fursunoni.” Kungiyar ta yi kira ga masu shiga tsakani da kasashen duniya da su matsa...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba...
Masar ta jaddada matsayinta kan duk wani yunkuri na kawo barazana ga hadin kan Sudan da ‘yancin kanta da kuma yankinta, tare da yin gargadin cewa kafa gwamnatin rikon kwarya na iya kawo rudani a kasar. A cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Lahadi, Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar da cewa “Jamhuriyar...
Wasu ’yan bindiga sun yi basaja a matsayin jami’an Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), tare da sace mutum 10 a Otal ɗin White Hill da ke kan titin Shiroro a Ƙaramar Hukumar Chanchaga a Jihar Neja. Wani masani kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 4:58...
Dakarun Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar JTF na Operation Hadin Kai, sun kai farmaki dajin Sambisa, inda suka ƙwato makamai da alburusai masu yawa. Wata majiya ta bayyana cewa sojojin, sun kai samame yankin Ukuba tare da bataliya ta musamman ta 199 da kuma ‘yan sandan JTF domin bincike da ƙwato makaman da ‘yan...
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
Wadannan ayyuka suna tunatar da duniya hakikanin fuskar Musulunci. Kuma ko da yaushe na kan zama mafi samun kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci. A cikin wannan wata mai alfarma, dukkkanmu muna samun daukaka ta hanyar dabbaka wadannan dabi’u kuma muna rungumar ‘yan uwantaka don gina duniya mai adalci da zaman lafiya ga...
’Yan sanda sun cafke wani magidanci mai shekaru 50, Alhaji Nuru Isah kan zargin lakaɗa wa matarsa dukan da ya yi ajalinta a dalilin abincin buɗa-baki. Bayanai sun ce taƙaddamar wadda aka soma gudanar da bincike a kanta ta auku ne a ranar Asabar a yankin Fadaman Mada da ke Jihar Bauchi. Burina in yi...
Maryam Abubakar sabuwar jaruma ce a Masana’antar Kannywood ’yar Hajiya Hauwa Garba da aka fi sani da ’Yar Auta ko Sabirar Gidan Badamasi. A zantawarta da Aminiya ta ce babban burinta shi ne ta yi fice da suna kamar yadda mahaifiyarta Hajiya Hauwa Garba ta yi: Mene ne takaitaccen tarihinki? Sunana Maryam Abubakar wadda aka...