Aminiya:
2025-03-25@17:55:35 GMT

Gwamnatin Najeriya za ta sake ƙara kuɗin lantarki

Published: 3rd, February 2025 GMT

Gwamnatin Tarayya ta sanar das shirye-shiryenta na sake kara kudin wutar lantarki nan da watanni masu zuwa.

Ta bayyana cewa ana tsara karin ta yadda zai zo da tallafi ga masu karamin karfi cikin masu amfani da wutar.

Mashawarciyar Shugaban Kasa kan Makamashi, Olu Verheijen, ce ta sanar da hakan a Babban Taron Shugabannin Lantarki na Kasashen Afirka da ke gudana a Dar es Salaam, hedikwatar kasar Tanzania.

A yayin taron ta gabatar wa mahalarta da shirin na Najeriya na kashe Dala biliyan 32 domin inganta wutar lantarki zuwa shekarar 2030.

Batun karin na zuwa ne bayan a bara gwamnatin ta yi ninka kudin wuta sau uku ga kwastomomi da ke amfani da Band A.

A yanzu kuma kamfanonin rarraba wutar lantarki, wadanda basuka suka riga suka yi musu katutu, sun matsa wa gwamnatin lamba ta bari su kara kudi domin samar da wutar yadda za su share hawayen kwastomominsu.

A watan Afrilun 2024 Hukumar Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta yi karin kudin wuta da kashi 300%, daga N68 zuwa N225 a kan kowane kilowat ga masu amfani da Band A.

Da yake sanar karin, Mataimakin Shugaban NERC, Musliu Oseni, ya ce kashi 15% na masu amfani da wutar ne ya shafa, kuma zai inganta samuwar wutar.

Hakazalika Ministan Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa idan aka ci gaba da biyan tallafi ga masu amfani da Band A, yawan kudin da gwamnati ke biya na tallafin a shekara zai karu zuwa Naira tiriliyan biyu.

Amma dai daga bisani an rage kudin zuaw N209.5.

Sabon kafin farashi

Game da sabon karin kudin, hadimar shugaban kasan ta bayyana cewa Najeriya na kokarin samar da tsarin samun wutar lantarki gwargwadon yadda aka biya kudin, domin jawo masu zuwa jari a bangaren.

Ta shaida wa taron cewa, “Daya daga cikin kalubalen da muke  kokari magancewa nan da ’yan watanni masu zuwa shi ne komawa tsarin shan wutar lantarki gwargwadon yadda aika biya.

“Da haka ne bangaren zai tara kudaden da ake bukata domin jawo ’yan kasuwa masu zuwa jari tare da kare talakawa da masu rauni daga cuta.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: gwamnati Karin kudin wuta Lantarki wutar lantarki

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin

Hukumar birnin istambul ta bada sanarwan dakatar da Akram Imamoglu daga matsayinsa na magajin garin birnin Istambul na wucin gadi, har zuwa lokacinda za’a tabbatar da kubutarsa daga abubuwan da aka zarginsa da su.

Tashar talabijin ta Almayaddeen ta kasar Labanon ta nakalto mahukunta a birnin Istambul na bada labarin cewa za’a zabi wanda zai maye gurbinsa na wucin gadi a ranar Laraba mai zuwa.

Labarin ya kara da cewa ana zirgin Imamoglu da karban rashawa da cin hanci da kuma kafa kungiyar yan ta’adda.

Kama Imamoglu magajin garin na birnin Istambul dai a makon da ya gabata, ya sa dubban daruruwan masu goyon bayansa a birnin  Istambul da wasu birane a kasar suka fito kan tituna tare da bukatar a sake shi.

Ana ganin Imamoglu zai iya zaman dan takarar shugaban kasa wanda zai iya kada shugaba Ordugan a zaben shugaban kasa mai zuwa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Kafa Rundunar Daukin Gaggawa Don Magance Matsalolin Tsaro
  • Hamas : Isra’ila ta yi amfani da sulhu wajen tattara bayanai kan shugabannin Hamas domin kashe su
  • Za mu ɗauko hayar sojojin ƙetare domin horas da dakarun Nijeriya — Badaru
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Ake Yi Wa ‘Yan Majalisar Ƙasa Kiranye
  •  Shugaban Majalisar Dokokin Lebanon Ya Yi Gargadi Akan Masu Tunanin Kulla Alakar Kasar Da HKI
  • Wajibcin Gina Al’ummar Duniya Mai Kyakkyawar Makomar Bai Daya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda watan Ramadana ke tasiri a harkokin kasuwanci
  • Hukumar Birnin Istambul Ta Dakatar Da Akram Imamoglu Daga Matsayinsa Na Magajin Garin Birnin
  • Gwamnatin Jigawa Ta Nanata Dokar Haramta Kiwon Dare
  • Gwamnatin Jigawa ta ƙaddamar da shirin noman rani na Lallashi