Sarkin Jiwa a Abuja ya yi rashin mahaifiya
Published: 5th, February 2025 GMT
Mai martaba sarkin Jiwa a yankin birnin tarayya Abuja, Alhaji Idris Musa ya yi rashin mahaifiyarsa mai suna Hajiya Ramatu Ibrahim.
Ta rasu ne a safiyar Lahadi kamar yadda sarkin malamai na masarautar malam Jibrin Yakubu Adam ya tabbatarwa Aminiya.
Hajiya Mai Babbar Ɗaki, kamar yadda ake yi mata laƙabi, ta rasu ta bar ‘ya’ya huɗu da kuma jikoko sama da 30.
Cikin waɗanda suka halarci jana’izar akwai Sarkin Bwari Alhaji Muhammad Auwal Ijakoro, da Gomo na Kuje Alhaji Haruna Tanko Ibrahim, da Sarkin Pai Alhaji Abubakar Sani Pai, sai kuma shugabannin ƙananan hukumomin Birnin Abuja da kewaye (AMAC) da kuma takwaransa na Abaji, wato Mista Christopher Zakka Mai Kalangu da malam Abubakar Umar Abdullahi.
A yayin ziyarar ta’aziyya da ya kai ga sarkin Jiwa a ranar Litinin, Sarkin Rubochi da ke yankin Kuje a Abuja, Alhaji Muhammad Ibrahim Pada, ya bayyana marigayiyar a matsayin uwa ta gari da ta samar da kyawawan tarbiyya abin koyi ga ‘ya’yanta, inda ya yi addu’ar Allah Ya gafarta mata da kuma yi mata rahama da Aljannah.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ban bai wa majalisa haƙuri ba — Natasha
Sanata mai wakilatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta musanta batun da ake yaɗawa cewa ta bai wa Majalisar Dattawa haƙuri.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, Natasha ta ce tana na kan batunta, kuma ba za ta taɓa bai wa majalisar haƙuri a kan gaskiyarta ba.
Fursunoni 12 sun tsere bayan fasa gidan yari a Kogi Za mu farfaɗo da Madatsar Ruwa ta Biu — ZulumIdan za a tuna dai majalisar ta dakatar da Natasha tsawon watanni shida tare da dakatar da albashi da alawus-alawus ɗinta ne bisa saɓa wa dokokin majalisar da kwamitin ƙorafi da ladabtarwa ya tabbatar.
Lamarin dai na zuwa ne a daidai lokacin da kuma Sanata Natasha take ci gaba da zargin shugaban majalisar, Godswil Akpabio, da cin zarafinta.
Daga bisani kuma Natasha ta shigar da koken nata a Majalisar Ɗinkin Duniya.
“Zan ci gaba da yaƙi domin ƙwato ‘yancin matan Najeriya har sai ranar da aka fara sauraronmu. Yunƙurin da ake yi domin rufe bakina ba na wasa ba ne, amma ko a jikina.
“Gaskiyar wasan kwaikwayon da ake yi akan idon ‘yan Najeriya za ta bayyana watarana, sannan duk ‘yan rashawar da suka mamaye gwamnatin za su yi bayani dalla-dalla,” in ji Natasha.
“Don haka ina kira gare ku, da ku yi watsi da da duk wani rahoto da kuka ci karo da shi cewa na bai wa majalisa haƙuri, domin ba gaskiya ba ne.
“Ina na kan batuna, kuma zan ci gaba da yaƙi a kan gaskiyata duk rintsi duk wuya.
To sai dai Natasha na wannan maganar ne a daidai lokacin da hukumar zaɓe ta kasa ke bayyana cewa ta samu takardar neman yi wa ‘yar majalisar kiranye daga mazabarta.
Sakatariyar hukumar Rose Oriarana-Anthony ce ta bayyana hakan inda ta ce takardar ta iske ta ne a ranar Litinin.