2025-02-20@09:12:32 GMT
إجمالي نتائج البحث: 112

«Bwari»:

    Kafofin yada labarai da manazarta na kasa da kasa, sun jinjinawa babban taron ‘yan kasuwan kamfanonin kasar Sin masu zaman kansu da aka gudanar ranar Litinin, inda suka ce gwamnatin Sin na marawa wadannan kamfanonin baya wajen taka rawar gani a bangaren kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire, kuma Sin ta gabatar da sako mai yakini...
    Ofishin Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF da ke Kano, ya ce zai ci gaba da hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa a bangarori da dama da suka hada da kiwon lafiya, da ilimi, da samar da abinci mai gina jiki, da kare yara, da al’umma. Shugaban ofishin , Mista Rahama...
    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe...
    Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.”   Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif...
    Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
      Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai.   Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja.   Ya ce,...
    An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yada labarai da yada labarai na gidan gwamnatin Kano, Sanusi Tofa, ya fitar ranar Talata.   A nasa jawabin, gwamnan ya jaddada aniyar gwamnatinsa na samar da romon dimokuradiyya da habaka ci gaban zamantakewa da tattalin arziki a jihar.   Ya kuma nuna jin...
    Abin ban takaicin shi ne duk wannan hauhawar farashi da karin harajin zai haifar a kan talakawa zai kare, domin kuwa farashin kayayyakin da ake kerawa daga irin wadannan ma’adanai na Karafa da Sanholo zai yi tashin gwauron zabo. A bayyane take cewa kasashen da wannan karin haraji ya shafa ba za su rungume hannuwansu...
    ’Yan kasuwa da abokan hulɗa da dama sun jikkata yayin da gubar harsashi ta tarwatse wannan Talatar a Jihar Zamfara. Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a babbar kasuwar garin Talatan Mafara wadda ke ci duk ranar Talata. Galibi waɗanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwar ne da kuma wasu abokan hulɗarsu...
    Ministan tsaron HKI Israel Katz ya bayyana cewa gwamnatin HKIba zata bar a kafa kasar Falasdinu ba, saboda hakan barazana ce ga samuwar HKI. Israek Kazt ya bayyana haka ne a lokacin ganawar jami’an gwamnatin HKI da tawagar kasar Amurka. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto ministan yana fadar haka a taron...
    An kammala aikin gina wani jirgin ruwa sabon kira mai bambaro saman ruwa, da samarwa, da adanawa, da saukewa wato FPSO a takaice, wanda ke da na’urar rike iskar carbon da wurin adanawa, a Shanghai, a cewar Jaridar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Jirgin dai shi ne irinsa na farko a duniya kuma ana...
    Kazalika, Rabi da ta zo daga kauyen Mai Rage cikin Nijar ta bayyana irin yadda jami’an kiwon lafiya ke haba-haba da su idan sun zo neman lafiya. Ta kara da cewa babban abin da ya sa suke zuwa Nijeriya maimakon su tsaya Nijar shi ne, yadda ba a nuna masu bambanci kuma ana wayar masu...
    “Mutanen nan sun matsa mana iya matsi, suna kafa sabbin sansanoni, duk wanda ke yankin nan babu wanda bai san shi ba, kuma jami’an tsaronmu na iya bakin kokarinsu.” BBC ta tuntuɓi kakakin rundunar Fansar Yamma, Laftanar-Kanal Abubakar Abdullahi ta waya domin jin ko sun san da wannan sabon sansani, sai dai ba mu same...
    Shi kuwa tsohon Janar Manaja na Hukumar ta NPA Joshua Asanga, ya jaddda mahimmancin amincewa da karin biyan harajin wanda ya sanar da cewa, sahalewar za ta taimaka wajen samar da kayan aiki a Tashar Jiragen Ruwan, inda kuma shi ma wani mai ruwa da tsaki a fannin ya yi kira da a zuba hannun...
    Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini. Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka...
    Peters ya tsunduma cikin harkar mai da iskar gas a matsayin dan kasuwa a shekarar 1999 kuma ya fara gudanar da kasuwancinsa a fannin da ke samar da mai na karkashin ruwa, wato ‘Downstream Sector’. Duk da haka, Aiteo ya zama kamfani mafi girma da ke hako mai a Nijeriya cikin kankanin lokaci. A cikin...
    ‘Yan gwagwarmayar Falasdinawa suna ci gaba da mayar da martini kan hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila suke kai wa kan gabar yammacin kogin Jordan Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmakin soji a cikin dare da safiyar kan garuruwan da suke gabar yammacin kogin Jordan, inda sojojin mamayar suka...
    Yau Jumma’a, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin, Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai na yau da kullum. Yayin taron, ya ce, a ko da yaushe Sin tana kiyaye karfinta na nukiliya a matsayin mafi karancin mataki da ake bukata don tsaron kasa, kuma ba ta shiga gasar makamai da sauran kasashen duniya. Ya...
    Hakan dai ya faru ne dalilin baiko da fitaccen mawaƙin ya yi da ’yar majalisar jiha mai wakiltar Egor a jihar Edo, Natasha Osawuru, a wani bidiyo da ya karaɗe soshiyal midiya. Ɓullar bidiyon ke da wuya mahaifiyar 2Face, Rose Idibia, ta fito a wani bidiyo tana roƙon duk wata uwa ta taya ta roƙon...
    Jami’ai a yankin kudu masu yammacin Pakistan sun ce aƙalla mutum 11 sun mutu sakamakon fashewar wata motar da ke ɗauke da masu haƙar ma’adinai a yankin Harnai da ke lardin Balochistan. Jami’an yankin sun ce suna ci gaba da bincike kan abin da ya haifar da fashewar, to amma ana kyautata zaton abubuwan fashewa...
    Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu. Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana...
    An yi nasarar watsa liyafar bikin fitilu na gargajiya na Sin na 2025 ta CMG jiya Laraba a mabambantan dandamali, lamarin da ya samu yabo sosai. Alkaluman masu kallo ta talabiji da sauran kafofi na zamani sun karu sosai fiye da bara. Kididdiga ta nuna cewa, an kalli liyafar da aka watsa kai tsaye ta...
    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta jaddada cewa: Al’ummar Iran ba zata taba amincewa da gudanar da duk wani zaman tattaunawa karkashin matsin lamba ba Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta mayar da martani ga yarjejeniyar tsaron kasa ta shugaban kasar Amurka, tana mai jaddada cewa: Iran ta yi watsi da duk wata tattaunawa karkashin matsin lamba,...
    Babban layin wutar lantarkin Najeriya, ya faɗi a karon farko a shekarar 2025, lamarin da ya haddasa ɗaukewar wuta a wasu sassa. Wannan matsala ta haifar da katsewar wuta a wasu sassan ƙasar, wanda ya jefa masu amfani da lantarki cikin damuwa. Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda...
    A lokacinda yake ganawa da masana masu fasaha a masana’antun makamai na kasar da kuma manya-manyan Jami’an sojojin Kasar Iran, Jagoran Juyin Juya Halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminae ya bayyana cewa fitowar mutane a zanga-zangar cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar, a ranar litinin da ta gabata, wata alama...
    Kungiyar Hamas ta sha alwashin dakile shirin shugaban Amurka Trump na neman tilastawa Falasdina gudun hijira daga Zirin Gaza Kungiyar Hamas ta lashi takobin dakile shirin shugaban Amurka Donald Trump na neman tilastawa Falasdinawa gudun hijira zuwa kasashe makwabta, tare da yin watsi da barazanar da ya yi na bude kofofin jahannama a yankin Falasdinu...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba...
    Yau Talata, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jiakun ya gudanar da taron manema labarai da aka saba yi yau da kullum, inda ya yi tsokaci game da rahoton dake da alaka da rarrabuwar iko tsakanin kasashen duniya na taron tsaro na Munich, yana cewa, bisa binciken da taron ya yi, kasa da kasa sun...
    An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar. Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban...
    Honorbaul Isika Ibrahim ya zama sabon Mataimakin Mai Tsawatarwa na Majalisar Wakilai. Majalisar Tarayya ta nada shi ne bayan rasuwar Honorabul Oriyomi Onanuga, mai rike da mukamin. Shugaban Majalisar, Honorabul Tajuddeen Abbas ne ya sanar da haka a yayin zaman majaliasr a safiyar Talata.
    Bikin zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a Iran ya jaddada kare tushen tsarin kasar da gwagwarmaya Dukkanin sassan kasar Iran sun gudanar da zanga-zanga da dukkanin bangarori na al’umma suka halartar domin tunawa da zagayowar cikan shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar. Tun daga...
    Shugaban kasar Amurka ya bayyana cewa: Akwai yiwuwar nan gaba kasar Ukraine ta iya zama wani bangare na tsarin tsaron kasar Rasha Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a ranar Litinin cewa: Dole ne kasar Ukraine ta tabbatar da tsaron kudaden Amurka da aka zuba a cikinta, saboda zata iya zama karkashin kasar Rasha wata...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Iran tana gudanar da bukukuwan zagayowar nasarar juyin juya halin Musulunci yau tsawon shekaru 46 tare da samun nasarori da kalubale A yau Litinin ne, al’ummar Iran suke gudanar da bukukuwan tunawa da cika shekaru 46 da samun nasarar juyin juya halin Musulunci a kasar, wanda marigayi Imam Ruhollah Khomeini (Yardan Allah ta tabbata a...
    Yanzu haka, an kara tura manyan injuna domin gudanar da aikin ceto a wurin da zaftarewar kasa ta auku a lardin Sichaun na kasar Sin. Da farko za su kwashe duwatsu da kasa da suka lullube wurin, kuma da zarar an ga alamun gini, za a sanar da ma’aikatan dake wurin domin kara bincike. Zuwa...
    Wani matashi ɗan kasar Argentina mai shekara 23 ya rasa ransa a sakamakon daɓa masa wuƙa da budurwarsa ta yi saboda kawai ya gaisa da wata mata a kan titi. Kishi madaidaici zai iya zama abu mai masu alaka da juna, amma mafi yawanci na iya wuce kima! Abba ya naɗa sabon Sakataren Gwamnatin Kano...
      Mata a Karamar Hukumar Danja suna kira ga Gwamnatin Jihar Katsina da ta gyara hanyar Tsangamawa a Babban Rafi saboda yawan rasuwar mata masu juna biyu da jariransu.   Sun yi wannan kira ne a yayin wani taron gaggawa da manyan jiga-jigan al’umma suka shirya domin tattauna matsalar da ta dade tana addabar jama’a...
    Hukuma mai kula da samar da magungunan HIV/AIDS ko (UNAISD) ta MDD ta bada sanarwan cewa mai yuwa mutane kimani miliyon 6 ne zasu mutu a duk fadin duniya a cikin shekaru 4 masu zuwa saboda rashin samun tallafin Amurka a cikin shirin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayyana cewa, a...
    Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya  raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya. Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Yayi...
    Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu ’yan mata shida masu shekaru tsakanin 15 zuwa 17 a yankin unguwar Pandogari da ke Ƙaramar hukumar Rafi ta Jihar Neja. Mazauna garin sun shaida wa Aminiya cewa, da tsakar daren Laraba ne ’yan bindigar suka kaiwa unguwarsu hari inda suka kashe wani ɗan banga mai suna...
    Kasar Sin ta yi watsi tare da nuna kin amincewarta da tsegumin da aka yi mata daga bangaren Amurka, inda sakataren harkokin wajen Amurkar, Marco Rubio ya yi wasu zarge-zarge marasa tushe balle makama a kan kasar ta Sin, yayin da yake ziyara a yankin Latin Amurka da Caribbean. Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin...
    Kazalika, a Arewacin Nijeriya, Robar Tumatir mai nauyin kilo 25  yanzu, ana sanar da ita kan Naira 6,500. Shugabar kungiyar masu noman Tumatair da sarrafa shi ta kasa, Rabiu Zuntu ta sanar da cewa, an samu girbin Tumatir mai yawan gaske, duba da cewa; yanzu ana cikin watan Fabrairu, lokacin da ake samun yawaitarsa. A...
    Wasu da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu masallata a wani masallaci a unguwar Bushe da ke Ƙaramar hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato. Waɗanda da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai farmaki masallacin ne da asubahin ranar Alhamis a yayin da masu ibada ke yin Sallar Subhi da...
    Kasashen Italiya da Spain sun ki amincewa da tilastawa Falasdinawa yin gudun hijira daga Zirin Gaza Ministan harkokin wajen kasar Italiya Antonio Tajani, a yayin wani taron manema labarai da takwaransa na haramtacciyar kasar Isra’ila Gideon Sa’ar a tashar jiragen ruwa ta Ashdod, ya jaddada kin amincewa da kakkausar murya da kasarsa ta yi na...
    Ɗanbayan Manchester United Lisandro Martinez ba zai sake taka leda ba a sauran wasannin kakar nan saboda raunin da ya ji a guiwarsa, a ranar Lahadi. An fitar da ɗanwasan ne mai shekara 27, a karawar da United ta yi rashin nasara a gida a hannun baƙinta Crystal Palace, raunin da tun a lokacin kociyan...
    Kwamishiniyar Mata, Yara da Nakasassu ta Jihar Kano, Hajiya Amina Abdullahi, ta gargadi ma’aikatan Cibiyar Reformatory Institute ta Kiru da su guji karkatar da kayayyakin da aka ware domin gina cibiyar.   A yayin ziyarar duba aikin gyare-gyaren, kwamishina Amina ta jaddada muhimmancin yin amfani da kudaden da aka ware wajen abubuwa masu inganci a...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Shin mene ne dalilin faɗuwar farashin tumatir warwas a kasuwa? Idan ba a manta ba, a watannin baya farashin tumatir ya yi tashin gwauron zabo wanda aka daɗe ba’a ga irinsa ba. A wancan lokacin, sai da farashin ya kai ga iyalai da dama sun haƙura da shi...
    Gwamnan ya bayyana haka a yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai yankin na Rimin Zakara a yammacin ranar Alhamis 06, ga watan Febarairun 2025.   A yayin ziyarar l, gwamnan ya yi alkawarin gina wa jama’ar yankin na Rimin Zakara katafaren Masallacin Juma’a a matsayin sadaka jariya ga wadanda suka rasu a dambarwar filayan...