Hujjar mu a nan ita ce, kundin tsarin mulkin Nijeriya, sama yake da kowanne dan kasar da kuma sauran dokokin kasar, duba da cewa, kundin ya bayar da damar a yi Shari’ar a bisa adalci kuma a bayyane, ga wadanda ake tuhumar da aikata laifi.

Bugu da kari, dole ne mu tuhumi matakan da mahukuntan kasar suka dauka na yiwa wadanda ake tuhumar Shari’ar a, asirce.

Akwai dimbin tambayoyi a zukatan ‘yan Nijeriya wanda kuma suke bukatar amsa, misali, a ina ne aka cafke su? ta yaya ne, aka kama su? yaushe ne, aka gurfanar da su, a gaban Kotu? Shin an barsu sun dauki Lauyoyin da za su tsaya masu gaban Kotu? har tsawon wanne lokaci ne, suke ci gaba da fuskantar Shari’a kuma kan wanne laifi ne, Kotu ke tuhumarsu?, me ya sanya ake yi masu Sharia’a a, asirce?

Tabbas, ‘yan Nijeriya na bukatar amsar wadannan tambayoyin, duba da cewa, kamata ya yi, a ce, ana yin masu Shari’ar bisa bin ka’ida, ko dai mutum dan kasa ne ko kuma bakin haure ne, ya kamata a ce, ana yi masu Shari’ar a bayya ne.

Yi wa mutanen, Shari’ar a, asirce ya savawa ka’ida duba da cewa, kundin tsarin mulkin Nijeriya, ya tanadi a bai wa, duk wanda ake zargi, ‘yancin da yi masa adalaci, kan tuhumar da ake yi masa.

Wannan Shari’ar da ake yiwa mutanen a asirce, hakan ya jefa ‘yan Nijeriya a cikin  bakin duhun, sanin  hakikanin yadda Shari’ar ke tafiya, hujojin da aka gabatar a kansu a gaban Kotu tare da kuma cewar, wadanda Kotun ke tuhuma, a kan wanne takamaiman laifi ne, aka gurnar da su kuma wanne irin hukuncin da aka yanke masu.

Hakan ya nuna cewa, rashin bin ka’ida a yi masu Shari’ar, tare da taka dokar kasa da kuma take ‘yancin ‘yan Adam.

Kazalika, hakan ya sanya nuna rashin aminta da Gwamnatin Tarayya, na cewa, ko za yi hukuncin bisa gaskiya.

Abin tambaya a nan shi ne, ta yaya irin wadannan gungun tantiran ‘yan ta’addar, musamman ‘yan ta’addar Boko Haram da suka fara aikita ta’addancin su tun a 2009, a kuma ce wai za yi masu Shari’a asirce?

‘Yan Nijeriya na bukatar sanin shi wadanne mutane ne, ke taimakawa ‘yan ta’addar wajen aikata ta’asarsu.

A gafe daya kuma, ‘yan ta’addar na ci gaba da kai farmaki ga sansanonin dakarun soji tare da kuma hallaka su da kuma kashe sauran fararne Hula, ciki har da dattijai, mata da kuma yara, inda ta’asar ta su, ta mayar da yaran marayu, matan kuma suka zama zawarawa ba tare da sun aikatawa ‘yan ta’addar wani laifi ba.

‘Yan ta’addar, sun zama tamkar, wasu mala’ikun mutuwa sanadiyyar kisan da suke yi, hakan ya janyo tarwatsa mafarkin wadanda lamarin ya rutsa da su da kuma tarwatsa su, daga matsugunan su, da suka gada tun daga kaka da kakanni.

Har zuwa yau, ‘yan makarantar Boko, musamman ‘ya’ya mata ana ci gaba da yin garkuwa da su, a wasu sassan kasar nan, tare da kuma yadda ‘yan ta’addar ke tilasta su, su aure su da kuma sanya su a aikin bauta.

‘Yan Nijeriya na ci gaba da hadiye fishinsu duba da cewa, wadanda suka dauki nau’yin ‘yan ta’addar da suka aikata masu ta’asar, amma Gwamnatin Tarayya ta yi uwa ta kuma yi makarviya, wajen kin yiwa ‘yan ta’addar da masu daukar nauyinsu Shari’a a asirce.

A namu ra’ayin domin ‘yan Nijeriya su yi ammana da Shari’ar da ake yiwa wadnda ake tuhumar a, asirce, ya zama wajbi Gwamnatin Tarayaya ta bayyana su, ta hanyar wallafa sunayensu, hotunansu, kanannan hukumomin da suka fito da kuma jihohin su na haihuwa, irin laifin da suka aikata aka kaisu gidan kaso da kuma irin hukuncin da aka yanke masu, a cikin a Jaridun kasar.

Yin hakan zai bai wa kamfanoni masu zaman kansu yanke duk  wata nau’in hada-hadar kasuwanci da su da kuma hana hukumomin gwamnati daukar su, aiki.

Muna shawartar Gwamnatin Tarayya cewa, da ta sake yin tunani, kan dabarun da ta dauka, na yiwa wadnada ake tuhumar, Shari’ar asirce.

Daukar wannan shawarar na da matukar mahimmanci, musamman domin a tabbatar da yin gaskiya da adalci tare da kuma kare kimar ‘yancin Adam da kuma girmama  dokar kasa.

Hakazalika, Gwamnatin Tarayya, ta tabbatar da yi masu Sharia’r bisa gaskiya, a bar su, su dauki Lauyoyi da za su tsaya masu, kuma hujjojin da aka gabatar kan zarginsu, su kasance na gaskiya ne, wadanda kuma za a iya gabatarwa, a gaban Kotu.

Abu ne, mai kyau a yaki da ta’addanci, amma ya kamata a yi hakan, ta hanyar mutunta ‘yancin daidaikun mutane, tabbatar da yin gaskiya da adalci da kuma mutunta, ‘yancin ‘yan Adam.

Batun yi wa masu aikata ta’addanci Shari’a ko kuma masu daukar nauyin aikata ta’addanci a kasar nan a, asirce, abu ne da ya savawa turbar mulkin Dimokiradayyar Nijeriya.

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Shari a Gwamnatin Tarayya a yi masu Shari yan Nijeriya yan ta addar masu Shari a tare da kuma duba da cewa ake tuhumar

এছাড়াও পড়ুন:

 Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza

A daidai lokacin da ake ci gaba da takaddama a HKI dangane da wasikar da wasu sojojin sama su ka rubuta na sukar yakin Gaza, wasu tsoffin ma’aikatar hukumar leken asiri ta “Mosad” sun bi sawunhu.

Kafafen watsa labarum HKI sun ambaci cewa, fiye da tsoffin jami’an leken asirin kungiyar MOSAD 200 ne su ka rattaba hannu akan wata takarda suna nuna goyon bayansu da sojan sama da su ka yi kira a kawo karshen yakin Gaza.

Kwanaki kadan da su ka gabata, tashar talabijin din Channel 13; ta watsa labarin da yake cewa; Wasu ma’aikatar rundunar leken asiri ta soja sun shiga cikin masu kira da a kawo karshen yakin na Gaza da kuma dawo da fursunoni daga can.

An kuma samu irin wannan halayyar ta yin kira a kawo karshen yakin a tsakanin likitocin soja su 100 sai kuma malaman jami’a su ma daruruwa.

Kiraye-kirayen da sojojii suke yi a HKI da na kwo karshen yakin Gaza da mayar da fursunonin yaki, ya bude wata sabuwar takaddama a tsakanin ‘yan  siyasa.

Wasikar ta bude jayayya a tsakanin ‘yan sahayoniya akan cewa, Netanyahu yana ci gaba da yin yaki ne saboda maslahar kashin kansa.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Kaduna ta Amince da Kudirin Kula da Lafiyar Kwakwalwa na Jihar
  • Rundunar “Gulani” Ta Shiga Sahun Masu Kin Amincewa Da Yaki
  • An yi garkuwa da masu ibada a Kogi
  • Sin Na Maraba Da Masu Zuba Jari Domin Su More Damammakin Bunkasarta
  • Gwamnatin Kebbi Za Ta Dauki Nauyin Karatun Dalibai A Saudiyya
  •  Tsoffin Ma’aikatan Hukumar Leken Asiri HKI  Mosad Sun Shiga Cikin Masu Kiran A Kawo Karshen Yaki Da Gaza
  • Brice Ologui Ya Lashe Zaben Shugaban Kasar Gaban Da Kashi 90.35% A Jiya Lahadi
  • An kama kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano
  • A daina cutar ’yan Najeriya ta hanyar rabon kayan tallafi