2025-02-20@09:11:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 24
«Gwamnatin Tarayya»:
Ta ce: “Fafutukar sa, hikimar sa mai zurfi, da jajircewar sa wajen cigaban ƙasa sun sa shi ya zama murya mai matuƙar tasiri a siyasar Nijeriya. Za a yi kewar shawarwarin sa masu amfani da kuma gudunmawar sa ba tare da son rai ba wajen gina ƙasa.” Idris ya miƙa ta’aziyya ga iyalan Cif Clark, da gwamnatin Jihar Delta, da ɗaukacin ’yan Nijeriya da suka amfana da irin rayuwar sa ta hidimar jama’a. “Muna addu’ar Allah ya jiƙan sa, ya uma ba iyalan sa da duk masu jimami haƙuri da juriya,” inji shi.
Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar. Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana. Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci. Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani. Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma,...
Gwamnatin Tarayya tayi matukar alhinin rasuwar Dattijo kuma Tsohon Kwamishinan Yada Labarai na Tarayya, Cif Edwin Clark, wanda ya rasu yana da shekaru casa’in da bakwai. Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohammed Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Abuja. Ya ce, Marigayi Cif Clark gwarzo ne mai kishin kasa, mai fafutukar tabbatar da adalci da gaskiya, kuma ginshiki ne a ci gaban dimokuradiyyar Najeriya. Mohammed Idris, ya kara da cewa, Marigayi ya sadaukar da kansa wajen bautawa kasa a fannoni da dama, musamman a matsayin shi na ɗan siyasa da mai kishin kasa, wanda ya bar gagarumar alama a harkokin mulki, hadin kai, da ci...
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta haramta wa Gwamnatin Tarayya riƙewa ko kuma yi wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar katsalandan. Mai Shari’a Musa Ibrahim Muhammad ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kai dangane da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayyar ke ware musu. Mutum biyu sun shiga hannu kan yi wa ’yar shekara 12 fyaɗe a Yobe Gwamnati ta raba wa mata tallafin awakai na N5bn a Katsina Wannan shari’ar dai ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da bai wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗe, bisa zargin tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin da...
LEADERSHIP ta ruwaito cewa, Hon. Abdullahi Abbas, Hon. Aminu Aliyu Tiga, da Jam’iyyar APC ne suka shigar da karar inda suke kalubalantar wasu hukumomin gwamnatin tarayya da na jihohi da suka hada da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun raba kudi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan kananan hukumomi 44 da ke Kano a gaban kotu. Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da hakkin kananan hukumomi na samun kudadensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta rike kason su. Da yake jawabi bayan yanke hukuncin, lauyan kananan hukumomi 44, Barista Bashir Wuzirchi, ya bayyana matakin a matsayin nasara ga jihar Kano.
“Hakkinmu ne mu tabbatar da cewa kuɗin jama’a ba su faɗa hannun jagorori marasa cancanta ba. Saboda haka, za mu ɗaukaka ƙara kuma mu ci gaba da fafutuka har sai an yi mana adalci,” in ji shi.
Sai dai ya ce, dole ne a fayyace gaskiya don hana wannan yaudarar samun gindin zama. Ya ce: “Karo na farko da Mista Gambaryan da tawagar sa suka zo Nijeriya, sun zo ne karan kansu ba tare da wata gayyata daga gwamnati ba. Sai dai da aka sanar da gwamnati wani batu na neman cin hanci a lokacin, sai aka buɗe bincike nan take, ko da yake babu wanda ya shigar da ƙorafi kai-tsaye.” Ya bayyana cewa, ziyarar Gambaryan ta biyu ta kasance wani ɓangare na bincike kan yadda ake amfani da kamfanin hada-hadar kuɗi na Binance don sarrafa darajar naira. Ya ce, amma binciken ya gamu da cikas sakamakon dabarun da Gambaryan da tawagar sa suka yi amfani da...
Ya ce kungiyar ta lura da yadda ake samun karuwar wasu cututtukan daji da aka yi watsi da su a Nijeriya kamar cutar Kansar colo-rectal, yara, obarian, da kuma ciwon daji na jini. Ya yi kira ga ma’aikatar lafiya da walwalar jama’a ta tarayya, da ta mai da hankali sosai kan cutar daji da aka yi watsi da su a Nijeriya. Shugaban NCS ya kuma bukaci majalisar dokoki ta kasa da ta ware naira biliyan 25 don sauya tsarin kiwon lafiyar cutar Kansa zuwa asusun inshorar lafiya. Ya kara da cewa, NCS ta bukaci majalisar dokoki ta kasa da gwamnatin tarayya da su dace da karin kudade don rufe ba da tallafin naira biliyan 97.2 a cikin shirin nan na...
Jami’ar Tarayya ta Lafia ta yi bikin rantsar dalibai 8,000 da suka sami gurbin karatu a sassan 76 a tsakanin tsangayoyin jami’ar 12. Da yake jawabi a wajen bikin, Shugaban jami’ar Farfesa Shehu Abdul-Rahman, ya sake jaddada matsayar hukumar a kan duk wani nau’i na rashin da’a da kuma shiga kungiyoyin asiri. Shugaban jami’ar wanda mataimakin shugaban jami’ar na sashen koyarwa, Farfesa Alemchi Chuku ya wakilta ya ci gaba da cewa basu da hakuri ga duk wani nau’i na rashin da’a kuma za su yi kakkausar suka ga munanan dabi’u. Ya kuma bukaci sabbin daliban da su mutunta juna da kuma ma’aikatan jami’ar da malamai na jami’ar domin ganin zamansu ya kasance mai amfani. “Ba...
Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 wanda ya kai Naira Tiriliyan 54.9. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya gabatar da kasafin kuɗin, inda aka duba shi dalla-dalla kafin a amincewa da shi. Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe A majalisar wakilai, ’yan majalisa sun yi nazari kan kasafin kuɗin mataki-mataki kafin su amince da shi a ranar Alhamis. Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ne, ya gabatar da shi a zaman majalisar. Bayan tattaunawa da kwamitocin majalisar, an kaɗa ƙuri’ar amincewa da kasafin kuɗin ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen. Sabon kasafin kuɗin ya ƙunshi...
Shugaban kungiyar dalibai ta makarantar (SUG), Comrade Haruna Umar, ya bayyana cewa marigayiya tana cikin shirye-shiryen kammala rajistar ta a makaranta ne ma kafin rasuwarta, kana ya roƙi ɗalibai da su kasance cikin hakuri da lumana, yana mai tabbatar da cewa hukumar makaranta da ta tsaro suna iya ƙoƙarinsu na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da an yi adalci a kan lamarin. Har ila yau, ya yi kira ga hukumar makarantar da ma Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC), da su girke tudu-tudu na rage gudu a kusa da makarantar domin kaucewa irin hatsarin nan gaba.
’Yan sanda sun kama gungun wasu makiyaya 47 ɗauke da makamai kan zargin kutse da yunƙurin aikata kisa a Kwalejin Kimiyya da Ƙere-kere ta Tarayya ta Umaru Waziri da ke Shinkafi a Jihar Kebbi. Kakakin ’yan sandan Jihar Kebbi, CSP Nafi’u Abubakar ya ce makiyayan sun haɗa baki ne da wani mutum wajen rusa katangar makarantar suka kutsa cikinta da garken shanu sama da 300. Ya ce da shigarsu ke da wuya. sai suka zarce zuwa ɓangaren gidajen ma’aikata suka lalata musu haki. Ya ƙara da cewa makiyayan sun kuma sari wani jami’in tsaron makarantar da adda a ƙafarsa ta dama a hannunsa na dama. Dalibai 179 sun kammala Dirigi da Daraja ta Ɗaya a Jami’ar Bayero Gwamnan Zamfara ya...
Gwamnatin tarayya ta yabawa gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa kammala aikin kaso 97 na ayyukan tituna da ya gada daga gwamnatin da ta gabata a jihar. Ministan tsaro, Alhaji Badaru Abubakar ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Auyo yayin kaddamar da shirin wayar da kan jama’a da gwamnati da al’umma a jihar Jigawa. Badaru wanda ya nuna gamsuwarsa matuka, ya ce gwamnatin jihar ta kammala ayyukan tituna guda 23 cikin 26 da ta gada. Ya kara da cewa sauran ayyukan tituna guda uku sun kusa kammaluwa domin amfanin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar. Ya kuma bayyana cewa gwamnati mai ci za ta kawo karin ayyukan raya kasa, don haka akwai...
’Yan sanda a Babban Birnin Tarayya Abuja sun buƙaci al’umma su kawo musu rahoton duk wanda aka ga yana sana’ar bola-jari a cikin gari. Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, Disu Olatunji, ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Tsaro ta Babban Birnin Tarayya wanda Minista Ezenwo Nyesom Wike ya jagoranta. Idan ba a manta ba, a ranar 13 ga watan Janairu, 2025 ne Hukumar Babban Birnin Tarayya ta haramta ayyukan ’yan bola-jari a cikin faɗin birnin. Umarnin ya taƙaita ayyukansu ga kan juji da ke ya yankunan da suke wajen birnin. A lokacin zaman ne aka dakatar da ayyukan ’yan gwangwan na tsawon makonni biyu, saboda zargin alaƙarsu da ’yan bola-jari. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu...
Shirin Inganta rayuwar al’umma na jihar Jigawa ya raba katinan cire kudi na ATM a kananan hukumomi 10 daga cikin 27 domin al’umma su sami tallafin naira dubu saba’in da biyar biyar na gwamnatin Tarayya. Shugaban shirin na jihar, Malam Mustapha Umar Babura ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar. Yayi bayanin cewar, ana rabon katinan karbar kudin ne ga wadanda za su sami tallafin inganta rayuwa na naira dubu sabain da biyar. A cewarsa, duk da korafe korafen da ake samu wajen rabon katinan, aikin na cigaba da gudana yadda ya kamata. Mustapha Umar Babura ya ce ana ta kokarin warware duk matsalolin da ma’aikatan suke cin karo da su wajen rabon katinan ga al’umma....
Wannan ya hada da kilomita 65 daga Legas zuwa Ogun da wani karin da zai tashi daga Kalabar ta Akwa Ibom, wanda titin zai ginu a karkashin ‘Engineering, Procurement, and Construction’ (EPC) da tsarin za su kula da shi na tsawon shekaru goma bayan ginawa. Majalisar zartarwar ta amince da kashe naira biliyan 470.9 domin gina hanyar da ta nausa Jihar Delta da kuma wani naira biliyan 148 don gina hanya a Jihar Anambra zuwa gada ta biyu a Neja. Shi kuma babban hanyar Lagos zuwa Ibadan ya samu amincewar naira biliyan 195 domin a gina shi a karkashin asusun shirin inganta hanyoyi na shugaban kasa (PIDF), da ke da manufar rage cunkoso da inganta sufuri a manyan hanyoyin da...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu varna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
Obuah ya ce, makasudin yin bayanin shi ne don tabbatar da cewa masu aiki da doka ne kawai ke aiki a Babban Birnin Tarayya Abuja da kuma yaki da matsalar masu barna a yankin. Ya ci gaba da cewa, wani samame da ‘yansanda suka kai a wasu kasuwannin Pantaker a baya-bayan nan ya yi nasarar kwato dukiyar al’umma da aka sace da suka kai sama da Naira biliyan daya. “Saboda haka, Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja, tare da jami’an tsaro, ta bayar da umarnin cewa duk wani ma’aikacin pantaker dole ne a yi rajista da kuma bayyana sunansa. Wannan zai ba mu damar gano masu aiki na gaske kuma mu fahimci ayyukan kasuwancinsu. “Haka zalika za a bukaci masu gudanar...
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirin ƙara farashin wutar lantarki a watanni masu zuwa, tana mai cewa hakan ya zama dole domin samar da tsarin farashin da ya dace da kuɗin aiki, wanda zai jawo zuba hannun jari daga fannoni masu zaman kansu a ɓangaren makamashi. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin makamashi, Olu Verheijen, ne ya bayyana hakan a taron shugabannin ƙasashen Afrika kan makamashi da aka gudanar a Dar es Salaam, Tanzaniya, inda Nijeriya ta gabatar da shirin dala biliyan 32 na faɗaɗa samar da wuta zuwa shekarar 2030. An Sace Kayayyakin Turakun Wutar Lantarki 18 A Cikin Kwanaki 6 – TCN Jami’in Kenya: Fasahar Sin Na Ingiza Samar Da Wutar Lantarkin Kenya Ta ce duk da...
Gwamnatin tarayya ta ce za ta hada gwiwa da gwamnatin jihar Jigawa wajen bunkasa kiwon dabbobi domin dorewar samar da abinci da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan kula da ci gaban harkokin dabbobi Alhaji Idi Mukhtar Maiha ya bayyana haka, a lokacin da ya karbi bakuncin gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi a ma’aikatarsa da ke Abuja. Ya yi nuni da cewa, wani bangare na shirin shi ne kafa jami’an hadin gwiwa don gano wuraren da za a ba da fifiko da kuma samar da manufofin da za a iya aiwatarwa cikin gaggawa. Da yake yabawa jihar Jigawa bisa manufofinta na kiwo, ministan ya ce tsarin da gwamnatin jihar ta bullo da shi na bunkasa kiwon dabbobi...
A na sa jawabin Ministan Bunkasa Hakar Ma’adanai Dakta Dele Alake, ya godewa Gallezot, kan yin aikin da ya yi dashi, wajen tabbatar da rattaba hannun wannan yarjejeniyar, duk da karancin lokacin da ake dashi na lokacin da yake da shi, a lokacin da Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ziyarci Shugaban kasa Bola Tinubu. Adeleke ya yi nuni da cewa, sake sabunta wannan yarjejeniyar ta kawo karshen yunkurin ‘yan adawar siyasa na kasar nan, kan yunkurinsu na gayawa ‘yan Nijeriya bayanan karya kan manufar wannan yarjejeniyar. Ministan ya ci gaba da cewa, Kungiyar ta Makomar Ma’adanan Kasa, za ta bai wa kasashen biyu damar fahimtar yadda za a samar da tsare-tsare da dabaru da kuma ayyukan da ya kamata...

Gwamnatin Tarayya Ta Gargaɗi Jama’a Kan Ajiye Abubuwa Masu Fashewa Don Haƙar Ma’adanai Ba Bisa ƙa’ida Ba
Idris ya ce: “Waɗannan bala’o’i ne da yawancin su ɗan’adam ke haddasawa, kuma ba za mu bari su ci gaba da faruwa ba. “Shugaban Ƙasa ya umarci Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA) da ta ƙara ƙaimi wajen faɗakar da jama’a da wayar da kan ‘yan Nijeriya, musamman masu wannan haramtacciyar sana’a. Wannan yanki yana da albarkatun ma’adinai da dama. “Kwanan nan, Ma’aikatar Raya Ma’adinai ta Tarayya ta fara gyaran tsarin haƙar ma’adinai a faɗin ƙasar nan, kuma muna fatan za su ɗauki wannan darasi da muhimmanci.” Ministan ya bayyana cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Raya Ma’adanai ta Tarayya da ta ƙara ƙaimi wajen tsaftace harkar haƙar ma’adanai don...
Kungiyar Manyan Ma’aikatan Jami’a (SSANU) ta bayyana cewa jami’o’in gwamnati da dama a Najeriya sun shafe sama da watanni uku ba tare da wutar lantarki ba da za su gudanar bincike ko darussa ba. Kungiyar ta kuma yi barazanar ɗaukar tsattsauran mataki kan gwamnatocin jihohi da kamfanoni da suka ki fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ba na Naira dubu 70 da sauran sauye-sauye da ke tattare da shi zuwa ƙarshen watan Maris na shekarar nan ta 2025. Shugaban Ƙungiyar SSANU ta Kasa, Kwamred ohammed Ibrahim, ne ya sanar da haka a yayin taron Majalisar Tuntuba ta Ƙasa (NAC) da ƙungiyar ta gudanar a Abuja. Kwamred Ibrahim ya bayyana cewa har yanzu Gwamantin Tarayya da na wasu jihohi ba...
Sai dai, an kwashe fasinjoji 53 da ke cikin jirgin ba tare da jin wani rauni ba cikin aminci. Ita ma Hukumar kula da Tsaro ta Nijeriya (NSIB) ta fara gudanar da bincike kan lamarin. Amma hukumar da ke kula da harkokin tsaro, NCAA, a wata sanarwa da ta tabbatar da faruwar lamarin, ta ce za ta bayar da duk wani tallafin da ake bukata ga NSIB domin gudanar da cikakken bincike kan wannan lamarin. Daraktan Hulda da Jama’a, Michael Achimugu a cikin wata sanarwa ya ce, “NSIB ce kadai za ta iya bayyana musabbabin wannan hatsarin idan ta kammala bincikenta.”