Aminiya:
2025-02-20@08:57:12 GMT

Majalisun Tarayya sun amince da kasafin kuɗin N54.9trn na 2025

Published: 13th, February 2025 GMT

Majalisar Dattawa da ta Wakilai, sun amince da kasafin kuɗin shekarar 2025 wanda ya kai Naira Tiriliyan 54.9.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya gabatar da kasafin kuɗin, inda aka duba shi dalla-dalla kafin a amincewa da shi.

Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas An yanke hukuncin sare hannun matashi kan sare hannun yaro a Gombe

A majalisar wakilai, ’yan majalisa sun yi nazari kan kasafin kuɗin mataki-mataki kafin su amince da shi a ranar Alhamis.

Shugaban kwamitin kasafin kuɗi na majalisar, Hon. Abubakar Kabir Abubakar Bichi ne, ya gabatar da shi a zaman majalisar.

Bayan tattaunawa da kwamitocin majalisar, an kaɗa ƙuri’ar amincewa da kasafin kuɗin ƙarƙashin jagorancin Kakakin Majalisar, Abbas Tajuddeen.

Sabon kasafin kuɗin ya ƙunshi kuɗaɗen da aka ware wajen doka, biyan bashi, ayyukan gwamnati, da kuma manyan ayyukan raya ƙasa.

A ɓangaren majalisar dattawa, an amince da kasafin kuɗin bayan rahoton da kwamitin kasafin kuɗi ya gabatar, wanda Sanata Solomon Olamilekan Adeola ke jagoranta.

Bayan kammala karanta takardar kasafin kuɗin, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya karanta cikakkun bayanai kafin a kaɗa ƙuri’a.

Sanata Opeyemi Bamidele ne, ya gabatar da ƙudirin amincewa da kasafin kuɗin karo na uku, inda Sanata Abba Moro ya mara masa baya.

Bayan amincewa da kasafin kuɗin, gwamnati ta bayyana yadda za a kashe kuɗaɗe a shekarar 2025, inda za a mayar da hankali kan ci gaban tattalin arziƙi, manyan ayyuka, da walwalar al’umma.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan majalisa Amincewa Majalisar Dattawa Majalisar Wakilai amincewa da

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5

Gwamnatin tarayya ta ce ta bai wa gwamnatin jihar Jigawa tallafin kayayyakin noma na sama da naira biliyan 5 domin bunkasa noman abinci a fadin jihar.

 

 

Ministan noma da samar da abinci Sanata Abubakar Kyari ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi a garin Dabi da ke karamar hukumar Ringim a bikin ranar manoman alkama ta bana.

 

Ya bayyana cewa, matakin na daga cikin kudirin gwamnatin tarayya na tallafawa jihar wajen bunkasa noma domin kasuwanci.

 

Sanata Kyari ya yi nuni da cewa, gwamnatin tarayya ta gamsu sosai da yadda gwamnatin jihar Jigawa da manoma suka yi, na rungumar ayyukan noman rani.

Ministan ya yaba da kokarin gwamnatin jihar Jigawa da manoma, bisa goyon bayan shirin gwamnatin tarayya na bunkasa noman alkama,  ta hanyar samar da kayan amfanin gona da dabarun zamani.

A nasa jawabin, Gwamna Umar Namadi ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na bullo da wasu tsare-tsare da za su samar da guraben ayyukan yi da wadata kasa da abinci.

A cewarsa, tuni ya sayo taraktoci 300, ingantattun irin shuka, da sauran kayayyakin aikin gona domin noman amfanin gona daban-daban a fadin kananan hukumomin jihar 27.

Tun da farko a jawabinsa na maraba kwamishinan noma da albarkatun kasa na jihar Alhaji Muttaqa Namadi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bayar da tan 3,500 na ingantaccen irin alkama, da injinan ban ruwa 10,000 domin tallafawa noman alkama a jihar.

Ministan da mukarrabansa da Gwamna Umar Namadi sun ziyarci gonakin alkama da dama a Yakasawa da Dabi a karamar hukumar Ringim.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, kayayyakin da gwamnatin tarayya ta bayar sun hada da injinan ban ruwa 10,000, da lita 10,000 ta maganin kwari, taki na ruwa da injinan feshi.

Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayya FRCN, Dr Mohammed Bulama,  da sarakuna da malaman addini, da wakilan kungiyar sarrafa fulawa ta kasa, da manoman alkama da wasu manyan jami’an gwamnati.

Usman Muhammad Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Palasdinawa Ne Zasu Fayyanace Makomarsu Ba Wasu Dan Mulkin Mallaka Ba: Qalibof
  • Zargin Daukar Nauyin Boko Haram: Tinubu Na Ganawar Sirri Da Akpabio A Villa
  • Majalisar Edo ta tanadi hukuncin kisa kan masu garkuwa da mutane
  • Gwamnatin Tarayya Ta Bai Wa Jihar Jigawa Kayayyakin Noma Na Sama Da Naira Biliyan 5
  • Majalisa ta tsayar da ranar sauraron ra’ayin jama’a kan ƙudirin Dokar Haraji
  • Za a binciki INEC kan jinkirin gudanar da zaɓen cike giɓi
  • Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya
  • Yadda Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa Ta Gudanar Da Tantance Sabbin Kwamishinoni
  • Kotu ta hana Gwamnatin Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano
  • Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Tarayya Daga Riƙe Wa Ƙananun Hukumomin Kano 44 Kuɗaɗensu