2025-03-14@13:12:51 GMT
إجمالي نتائج البحث: 1365
«yan majalisa»:
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayyana cewa mutane bakwai sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da suka afku a jihar cikin watan Fabrairu 2025. Rahoton ya kuma nuna cewa an samu tashin gobara 77, an gudanar da ceto 11, yayin da aka samu ƙarar bogar bogi guda uku a cikin wannan lokaci. Sanarwar...
Jihohin Sakkwato da Kebbi na fuskantar ƙalubale sakamakon cutar sanƙarau da ta ɓulla a jihohin, inda rahotanni suka tabbatar da cewa cutar ta kashe aƙalla mutum 50, yayin da sama da mutum 200 suka kamu da cutar. A Jihar Kebbi, ƙananan hukumomin Aliero, Jega, da Gwandu ne suka fi fuskantar matsalar, inda cutar ta fara...
Alhaji Dangote, hamshakin attajirin nahiyar Afirka, ya ce sun hada kai da gwamnatin jihar ne wajen tabbatar da ganin an raba abincin ga mabukata a kowace jiha dake fadin Nijeriya. Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya jagoranci kaddamar da rabon tallafin abincin a matakin kasa na wannan shekara, ya ce aiwatar da wannan...
Gwamnatin mulkin sojin Sudan ta ayyana haramta duka kayayyakin da aka shigar da su ƙasar daga Kenya, a wani mataki na martani karɓar baƙuncin RSF da ƙawayenta da Nairobin ta yi. Ministan kasuwancin Sudan, ya ce an ɗauki matakin ne bisa shawarar, majalisar ikon ƙasar, wadda ta zargi Kenya da rura tashin hankali a Sudan....
“Muna kokarin kawar da bangaren dala. Abin da muke so mu yi shi ne mu biya a cikin kudin gida na duk kamfanonin jiragen sama. Kuma za a biya kudin ne daidai da farashin dala a halin yanzu a lokacin da ake biya. “Kason da ya dace ya ba ku damar gudanar da ayyukanku dukkan...
A jiya Alhamis sojojin HKI sun cigaba da keta aiki da kuduri mai lamba 1701 ta hanyar yin shawagi a samaniyar Lebanon da kuma kai hare-hare a yankunan Jenta da Biqa. Tashar talabijin din ‘almanar ta watsa labarin da yake cewa; Jiragen yakin abokan gaba ‘yan sahayoniya sun kai hare-hare har sau uku a yankin...
Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke yi, tana yi ne da nufin gyara makomar yara masu tasowa. Yayin da yake jawabi ga kungiyar ‘Yan majalisa ta uku – wadda ya kasance cikin a Jamhuriya ta uku – da suka kai masa ziyara a fadarsa, Shugaba Tinubu ya ce...
Ya ce: “Bari in ce mun tsallake tudu, kuma wahalhalun da aka sha a baya suna raguwa yayin da tasirin waɗannan sauye-sauye suke fara bayyana. “A halin yanzu, muna gani muraran yadda farashin kayan abinci yake saukowa, farashin musayar kuɗaɗe yake daidaituwa, kuma farashin man fetur yana raguwa. Waɗannan duk alamu ne cewa ayyukan...
‘Yan mata 74,452 ne suka ci gajiyar tallafin kudi a karkashin shirin samar da ilimi da karfafawa ‘yan mata matasa AGILE a fadin kananan hukumomi 19 da ke Kano, wanda ya kunshi rukuni daya da na biyu. AGILE wani shiri ne na taimakon Bankin Duniya na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya wanda aka tsara don...
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Alkawarin Samar da Dokar Shirye-Shiryen Matasa Da Ayyukan Ministan ci gaban matasa, Ayodele Olawande, ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na karfafa matasa domin samar da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasar nan. Ministan ya ce ziyarar da ya kai jihar Sokoto na da nufin kara cudanya da...
Hukumar raya yankin arewa maso yamma NWDC ta bukaci gwamnatocin jihar Kano da su taimaka tare da hadin gwiwa da nufin cimma manufofinta. Shugaban Hukumar Alhaji Isma’il Lawal Abdullahi Yakawada ya nemi hadin kan a lokacin da ya jagoranci mambobin hukumar a ziyarar ban girma da suka kai wa gwamnan a gidan gwamnatin...
Ministan kasa a ma’aitar tsaro, Mohammed Bello Matawalle, ya ba magoya bayan jam’iyyar (APC) a jihar Zamfara gudumuwar kudi naira miliyan 500 domin a taimaka musu wajen gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki. Mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa Mattawalle, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga ne ya bayyana hakan a...
’Yan bindiga sun kai hari tare da tarwatsa mazauna ƙauyuka biyar da ke Karamar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Ƙauyukan da abin ya shafa sun haɗa da Unguwan Tauka, Unguwan Lalle, Sonudazuwa, Tsauni Dodo, da Dandauka. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Galibin ’yan Najeriya na neman muƙaman gwamnati don...
Jami’an tsaro a Jihar Filato, sun ceto mutum bakwai da ’yan bindiga suka sace. An gano mutanen a yankin Ganawuri, da ke Ƙaramar Hukumar Riyom, bayan da sojojin Operation SAFE HAVEN (OPSH) suka kai farmaki maɓoyar ’yan bindigar. Muƙarraban Uba Sani ne suka sace tsohon Kwamishina na – El-Rufai Da amincewar Buhari na fice daga...
A Nijeriya sha’anin siyasar mata wani babi ne mai zaman kan sa da mata ke kuka da kokawa kan yadda ake nuna masu kyama da kabilanci a dukkanin jam’iyyu tamkar wani jinsi ne ba na mutane ba. A bayyane yake cewar gagarumar gudunmuwar da mata ke bayarwa a farfajiyar siyasar Nijeriya ta fi gaban a...
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ce da tuni Najeriya ta faɗa cikin mummunan yanayin matsin tattalin arziƙi ban da gwamnatinsa ta ɗauki matakan da suka dace a kan lokaci. Da yake jawabi a fadar gwamnati da ke Abuja, Tinubu ya bayyana wa wata tawagar tsofaffin ’yan majalisa cewa dole ne gwamnatinsa ta ɗauki matakai...
Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayar da rahoton cewa, a wani taron sirri da kwamitin sulhu na MDD ya yi a wannan mako kasar Rasha ta yi Allah-wadai da sabuwar gwamnatin kasar ta Syria dangane da kisan kiyashin da jami’anta suke yi a kan tsiraru a kasar. Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar...
Ministar Harkokin Wajen Senegal, Yacine Fall, ta ce hukumomin kasarta sun bayyana rashin jin dadi game da tsare ‘yan Senegal da kuma tilasta musu barin kasar bisa zarginsu da zama cikin Mauritania ba bisa ka’ida ba. Hukumomin kasar Mauritaniya sun kaddamar da wani gangamin korar bakin haure daga kasashen Afirka daban-daban. A wani jawabi da...
Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin da kungiyar al-Shabaab ta kai a wani otel da ke garin Baledweyne, inda shugabannin kabilu ke ganawa ya kai mutane 10, kamar dai yadda majiyoyin ‘yan sanda na kasar ta Somalia suka tabbatar. Sannan kuma bayanin hukumar ‘yan sandan ta kasar Somalia ya tabbatar da cewa, akasarin wadanda suka...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Rashin aikin yi na ɗaya daga cikin manyan matsalolin da Najeriya ke fuskanta a wannan lokaci, musamman idan aka yi la’akari da yadda ake ci gaba da samun matasa masu lafiya da kuzari amma ba su da aikin yi. Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), ta fitar da rahoto...
Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin...
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fasa baragurbin ƙwai kan zargin sace Jafaru Sani, tsohon Kwamishina a gwamnatinsa. El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kafin ya miƙa mulki ga Sanata Uba Sani, wanda shi ne ɗan takarar da ya fi so ya gaje shi, ya bayyana wannan batu ne...
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Mao Ning, ta ce alkaluma sun nuna cewa, har yanzu kasar Sin ce ke kan gaba a duniya a matsayin wacce ta fi samun jari daga kasashen waje, kuma tana maraba da kamfanonin kasashen wajen su zo su kara zuba jari. Mao Ning ta kara da cewa, ba tare da...
Shugaban Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Mista Peter Tanko Dogara, ya tabbatar da aniyarsa na yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sarakunan gargajiya domin samar da tsaro da samar da ayyukan ci gaban ƙaramar hukumar. Mista Dogara ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu da ya kai zuwa ga masarautu...
Wasu ’yan bindiga da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne sun yi garkuwa da wasu ’yan ƙauye su goma daga wasu unguwanni uku da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna. Lamarin ya faru ne a daren ranar Larabar, da misalin ƙarfe 2 na tsakar dare inda wasu gungun ’yan bindiga suka kai farmaki...
Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, ya yi ganawar sirri da Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed. Taron ya gudana ne a Ramat House da ke Bauchi, sai dai ba a bayyana manufar taron ba. Da amincewar Buhari na fice daga jam’iyyar APC — El-Rufai ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan...
Ministan man fetur da ma’adanai na gwamnatin tarayyar kasar Somaliya Taha Shari Muhammad ya sanar da cewa, ya zuwa yanzu aikin da kamfanin kasar Turkiya yake yi na hako man fetur a kasar ya yi nisa, kuma da akwai yiyuwar nan da shekara ta 2026 kasar za ta fara fitar da man Fetur. Taha Shari...
Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Hamas ta yi gargadi akan cewa; Wata sabuwar yunwa za ta bulla a Gaza saboda yadda HKI take ci gaba da killace yankin da hana shigar da kayan agaji hatta a cikin watan Ramadan. Kakakin kungiyar ta Hamas Abdullatif al-Qa’uni wanda ya fitar da wani bayani ya ce; Falasdinawa a yankin...
Ya ce, muddin ‘yan siyasan Nijeriya ba su haɗa kansu waje guda ba, ƙalubalen da suke cikin ƙasar nan za su yi wuyar kawuwa. Ya ce, akwai kuma buƙatar tunƙarar matsalolin taɓarɓarewar tattalin arziki a Nijeriya. Ya ce, tuntuɓar da suka fara da gwamnan Bauchi a matsayinsa na fitaccen ɗan siyasa a Arewa kuma...

Tabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A SinTabbaci Kan Bunkasuwar Tattalin Arziki Mai Dorewa A Sin
Babban abin da ya bai wa Sin nasarar bunkasuwar tattalin arziki cikin sauri shi ne yadda gwamnati ta maida hankali wajen gina manyan ginshikai da tattalin arziki ke dogara da su domin samun ci gaba mai dorewa. Misali, irin layukan dogon da aka shimfida da suka sada ko wane lungu da sako a duk fadin...
Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce galibin ’yan Najeriya suna sha’awar yin amfani da muƙaman gwamnati ne kawai don arzuta kansu da abokan hulɗarsu su durƙusar da ƙasar fiye da yadda suka same ta. Tsohon Shugaban ƙasar ya ce waɗannan mutane suna karɓar rancen biliyoyin Nairori, suna ganin cewa biyan kuɗaɗen gwamnati bayan an...
Gwamnatin Tarayya ta ce ‘yan Najeriya sun fara samun sauki yayin da farashin kayan abinci ke raguwa da farashin fetur ke daidaita, kuma naira ke karɓar ƙarfi. Da yake magana a taron manema labarai na ministoci karo na huɗu a Abuja, Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Mohamed Idris, ya ce...
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour (LP) a 2023 kuma tsohon gwamnan Jihar Anambra, Peter Obi, ya kai ziyara Jihar Bauchi a ranar Alhamis don wata ganawa ta musamman. Da isarsa filin jirgin sama na Sir Abubakar Tafawa Balewa, Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi, Rt. Hon. Mohammed Auwal Jatau, ne ya tarɓe shi. Obi ya...
Magaji ya yaba wa ‘yan jarida bisa irin goyon bayan da suke bai wa gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule. Ya ce gwamnatin jihar na ci gaba da ayyukan ci gaba da kuma inganta abubuwan da gwamnatoci na baya suka aiwatar. Haka kuma, ya shawarci ‘yan jarida da su tabbatar da tantance labarai kafin su watsa su,...
Ta ce tallafin zai taimaka wajen bai wa mata damar zama masu dogaro da kansu a fannin tattalin arziƙi. An raba kuɗin ne ga kungiyoyin mata manoma daga ƙananan hukumomi 13 a faɗin jihar, inda kowacce ƙungiya ta samu Naira miliyan biyu. Haka kuma, ƙungiyoyin matasa manoma su ma sun amfana da tallafin don bunƙasa...
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufa’i, ya tabbatar da cewa ya bar jam’iyyar APC ne da sanin Tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari. El-Rufa’i ya bayyana komawarsa jam’iyyar SDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook. ’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani a Katsina ’Yan sanda sun hallaka hatsabibin ɗan...
Gidauniyar Attahiru Bafarawa ta fara rabon tallafin kudi naira miliyan goma sha uku da dubu dari takwas ga iyaye mata marayu dari biyu da saba’in da bakwai da masu bukata ta musamman a jihar Sokoto domin tallafawa kananan sana’o’i. Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin, Shugaban shirin, Malam Lawal Maidoki ya bayyana...
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗi a baya-bayan nan dangane da ƙaruwar yanayin zafi a sassan ƙasar, yayin da jihohi da dama suke fuskantar ƙarin matsanancin zafi. Gargaɗin ya kuma nuna cewa, tsananin zafin da za a yi fama da shi cikin kwanaki uku ko huɗu masu zuwa wanda zai haddasa damuwar...
Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi. A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da...
Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya, ta kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga, Salisu Mohammed, wanda aka fi sani da Dogo Saleh, a wani artabu da suka yi da shi a dajin Gidan-Abe da ke kan iyakar Bwari da Kaduna. Sun samu nasarar ne bayan samun bayanan sirri kan shigowar ‘yan bindiga yankin daga Kaduna. NAJERIYA...
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi, ya ba da umarnin cewa, wadanda harin da ‘yan bindiga suka kai a sansanin ‘yan gudun hijira da ke karamar hukumar Arewa ta jihar, su koma gidajensu nan da makonni biyu masu zuwa bayan an dauki matakai a yankunan da lamarin ya shafa. Gwamnan, ya ba da umarnin...
Mai Bai Wa Shugaba Bola Tinubu Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai, Daniel Bwala, ya ce akwai yiwuwar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya koma jam’iyyar APC mai mulki. Bwala ya bayyana haka ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na TVC, inda ya...
Jami’an tsaro da ke rakiyar tawagar Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, sun daƙile wani harin Boko Haram a kusa da garin Gujba a Jihar Yobe. Gwamnan da tawagarsa na kan hanyarsu ta komawa Maiduguri daga Biu lokacin da suka haɗu da ’yan ta’addan, wanda hakan ya tilasta musu tserewa bayan musayar wuta. Majalisar wakilai...
Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran, Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya ce kiran da shugaban Amurka Donald Trump ya yi na tattauanwa da Iran ba komai ba ne illa wani yunkuri na yaudarar al’ummar duniya. “Mun zauna tsawon shekaru muna tattaunawa, mun zamna da su teburin tattaunawa, bayan hakan shi wannan mutumin ya yayyaga...
Kungiyar Raya Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka ECOWAS ta kaddamar da wata rundinarta mai manufar yaki da ayyukan ta’addanci da miyagun laifuffuka a yankin. Ministan tsaron Nijeriya, Mohammed Badaru Abubakar ne ya sanar da hakan a yayin taron Kolin ECOWAS na hafsoshin tsaro karo na 43 a babban birnin tarayyar Nijeriya Abuja a ranar Talata....
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na ci gaba da tsananta, lamarin da ya sa wasu al’umma ke neman hanyoyin kare kansu. Ɗaya daga cikin hanyoyin da wasu yankuna suka ɗauka shi ne yin yarjejeniya da ’yan bindiga da ke addabar su, domin samun zaman lafiya. NAJERIYA A YAU:...
Wannan magana tana nuni da cewa idan mutum ya nemi kariya a wurin Allah da zuciya ɗaya, to Allah zai amsa roƙonsa kuma zai kare shi daga duk wani abu mai cutarwa. Wannan yana da asali a cikin koyarwar Musulunci, inda ake koyar da Musulumi su nemi tsari wurin Allah kaɗai daga sharrin Shaiɗanun aljanu...
Cikin kasa da wata guda, an yi asarar hannayen jari da darajarsu ta kai dala triliyan 4, inda damuwar da duniya ke da shi kan manufofin haraji na Amurka ke haifar da fargaba a kasuwar hannayen jari ta kasar. Wani nazari da kafar CGTN ta gudanar tsakanin jama’ar duniya masu amfani da intanet ya nuna...
Idan ka dauki bangaren tsofaffi da kananan yara, za ka iya cewa su ne mafi rauni a cikin al’umma. Tsofaffi sun gajiya don haka suna bukatar taimako, yara kanana kuma ba su kawo karfi ba, bisa haka dole suna bukatar madafa. A nan, sai mu ce gwamnatin Sin ta yi tunani mai kyau. Kundin rahoton...