Kotu ta hana Gwamnatin Tarayya riƙe kuɗin ƙananan hukumomin Kano
Published: 17th, February 2025 GMT
Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta haramta wa Gwamnatin Tarayya riƙewa ko kuma yi wa kuɗaɗen ƙananan hukumomi 44 na jihar katsalandan.
Mai Shari’a Musa Ibrahim Muhammad ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin, biyo bayan ƙarar da wakilan ƙananan hukumomin jihar suka kai na kare ‘yancinsu na cin gashin kai dangane da kuɗaɗen da Gwamnatin Tarayyar ke ware musu.
Wannan shari’ar dai ta samo asali ne bayan da jam’iyyar adawa ta APC ta nemi kotu da ta dakatar da bai wa ƙananan hukumomin jihar kuɗaɗe, bisa zargin tafka maguɗi a zaɓen ƙananan hukumomin da aka gudanar a watan Oktoban 2024.
Aminiya ta ruwaito cewa, Shugaban Jam’iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas ne ya jagoranci shigar da ƙarar wadda take ƙalubalantar wasu hukumomin Gwamnatin Tarayya da suka haɗa da Babban Bankin Nijeriya (CBN), Asusun Raba Kuɗi na Tarayya (FAAC), da kuma dukkan ƙananan hukumomi 44 na Kanon.
Sai dai kuma hukuncin da babbar kotun Kano ta yanke ya tabbatar da haƙƙin ƙananan hukumomi na karɓar kudadtensu, tare da hana gwamnatin tarayya ko wasu hukumominta riƙe kuɗaɗen .
A watan Nuwambar bara ce dai Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi, Ibrahim Muhammad ya jagoranci tawagar masu shigar da ƙara ta hannun lauyansu, Bashir Yusuf Muhammad, suna neman kotun ta hana riƙewa ko jinkirin sakin kuɗin ƙananan hukumomin jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamnatin tarayya Jihar Kano Kuɗin Ƙananan Hukumomi Gwamnatin Tarayya
এছাড়াও পড়ুন:
Kantoman Ribas Ya Naɗa Farfesa Lucky Worika A Matsayin Sakataren Gwamnati
A cewarsa ya zaɓe shi ne bisa la’akari da kwarjininsa da kuma gwanintarsa.
Farfesa Worika yana da digiri na uku a fannin Dokar Muhalli ta Ƙasa da Ƙasa da Man Fetur daga Jami’ar Dundee da ke Birtaniya.
Ya yi aiki a fannoni daban-daban da suka haɗa da harkokin ilimi da kuma ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Naɗinsa yana cikin ƙoƙarin gwamnatin Jihar Ribas na amfani da ƙwararru ‘yan jihar domin samar da zaman lafiya, kwanciyar hankali, da tsaro.
Farfesa Worika ya fito ne daga Ƙaramar Hukumar Okrika a Jihar Ribas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp