Saudiyya Ta Jaddada Rashin Amincewa Da Tilastawa Falasdinawan Zirin Gaza Yin Gudun Hijira
Published: 9th, February 2025 GMT
Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza
Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado.
A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu.
Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na tsattsauran ra’ayi na ‘yan mamaya baya daukan Falasdinu a matsayin kasar Falastinu wacce take matsayar kasar gado da tarihi da shari’a suka tabbatar da hakan, kuma ‘yan mamaya ba su la’akari da cewa tun farko al’ummar Falastinu sun cancanci rayuwa; Don haka suka rusa yankin Zirin Gaza gaba daya, tare da kashe mutane fiye da dubu 160, wadanda akasarinsu yara da mata ne, ba tare da kiyaye dokokin kasa da kasa da na hakkin dan Adam ba.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: Saudiyya ta
এছাড়াও পড়ুন:
Iran Tace Zata Kaddamar Da Sabbin Magunguna Da Ta Samar Tare Da Amfani Da Makamashin Nukliya
Shugaba hukumar makashin Nukliya na kasar Iran Mohammad Islami ya bada sanarwan cewa a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa. Yace hukumarsa za ta kaddamar da sabbin magunguna da ta samar tare da amfani da makamashin Nukliya, a dai dai na ranar makamashin Nukliya ta kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ta nakalto Islami yana fadar haka a yau Lahadi, ya kuma kara da cewa wannan ci gaban kari ne, kan ci gaban da kasar ta samu a wannan fannin, wanda kuma zai kara kyautata bangaren lafiya na kasar sannan ya zama hanyar samar da kudade ga kasar.
Shugaba hukumar makamashin nukliya ta Iran ya kara da cewa a cikin shekarar Iraniyawa wanda ya kara kadai kasar ta samar da sabbin ci gaba kimani 100 tare da amfani da makamashin nucliya, kuma tana son nan da shekara ta 2040 masana’antar makamashin nukliya ta kasar Iran zata shiga cikin masana’antun makamshin nukliya mafi girma a duniya.
Ana saran shugaba Pezeshkiyan zai halarci taron kaddamarda wadandan kayakin ci gaba da aka samu a ranar 8 ga watan Afrilu mai zuwa.
Sannan Iran ta dage kan cewa shirinta na makamashin Nukliya na zaman lafiya ne, sabanin abinda kasashen yamma musamman Amurka take zargin kasar na cewa shirin ya wuce na zaman lafiya.
Sai dai kakakin Fadar Krimlin na kasar Rasha Dmitry Medbedev ya bayyana a makon da ya gabata kan cewa shirin makamashin Nukliya na kasar Iran na zaman lafiya ne.