2025-02-20@09:11:49 GMT
إجمالي نتائج البحث: 34

«Saudiyya ta»:

    Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar  gwagwarmayar...
    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya soki shugabancin Ukraine, inda ya bayyana cewar su ne suka haddasa yaƙin da Rasha ke yi da su. Trump, ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani ga shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, wanda ya ce yana mamakin yadda ba a gayyaci ƙasarsa zuwa taron tattaunawar zaman lafiya a Saudiyya ba. ’Yan bindiga sun kashe mutum 2, sun sace manoma 10 a Neja ’Yan bindiga sun Kashe mutum 2 kan jinkirin biyan kuɗin fansa A cewar Trump, Ukraine ce ta jawo wa kanta matsalar. “Da ba ku fara wannan yaƙin ba, da kun cimma yarjejeniya tun farko,” in ji shi. “Da ni ne, da na samo muku mafita, kuma babu wanda za a kashe.”...
    Kungiyar Hamas ta ki amincewa da sabbin sharuddan fira ministyan gwamnatin mamayar Isra’ila na yarjejeniyar Gaza kashi na biyu Fira ministan gwamnatin mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu a hukumance ya yanke shawarar fara tattaunawa kan mataki na biyu na yarjejeniyar Gaza, tare da sanya sabbin sharudda. A nata bangaren kungiyar Hamas ta ki amincewa da sharadin ficewarta daga yankin Zirin Gaza da kuma yin fatali da bukatar ajiye makamai a matsayin wani bangare na kowace yarjejeniya. A yayin da ake fara shirye-shiryen fara gudanar da mataki na biyu na shawarwari tsakanin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da kungiyar Hamas bisa tsarin tsagaita bude wuta da yarjejeniyar musayar fursunoni, gwamnatin yahudawan sahayoniyya yana ci gaba da yin jinkiri ta hanyar kokarin kafa sabbin...
    Jaridar Ma’ariv ta Isra’ila ta bayyana adadin wadanda suka jikkata a cikin sojojin mamayar Isra’ila da kuma miliyoyin yahudawan sahayoniyya da suka samu matsalar tabin hankali a lokacin yakin Gaza Jaridar “Ma’ariv” ta haramtacciyar kasar Isra’ila ta bayyana a jiya litinin, adadin wadanda suka mutu a cikin jerin sojojin mamayar Isra’ila a yayin mummunan ayyukan ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan Zirin Gaza, wanda ya shafe tsawon watanni 15 kafin cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da musayar fursunoni a watan Janairun da ya gabata. A cewar jaridar, sojoji 15,000 da ke cikin sojojin mamayar Isra’ila suka jikkata tun farkon yakin ranar 7 ga watan Oktoban shekara ta 2023, yayin da wasu 846 suka sheka lahira. Daga cikin wadanda...
    Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji. Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa. Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa. A wata wasika da...
    Gwamnatin Saudiyya ta bai wa babban birnin Nijeriya Abuja da kuma Jihar Kano tallafin tan 100 na dabino. Ofishin Jakadancin Saudiyya ya gudanar da gagarumin bikin bayar da tallafin dabinon ne a wani ɓangare na ayyukan agaji da yake yi duk shekara. Shirin wanda Cibiyar Bayar da Agaji da Jin Ƙai ta Sarki Salman (KSrelief) ta ɗauki nauyin gudanarwa, na da nufin tallafa wa iyalai masu ƙaramin ƙarfi a faɗin ƙasar da kuma ƙarfafa danƙon zumunci tsakanin ƙasashen biyu.
    Mujallar “Qiushi” da aka buga a yau Lahadi, ta gabatar da muhimmin sharhi na sakatare janar na kwamitin tsakiya na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping mai taken “Inganta tsarin daukar kwararan matakai wajen tafiyar da jam’iyya a dukkan fannoni”. A cikin sharhin an nuna cewa, har yanzu ana fuskantar matsanancin yanayi da sarkakiya wajen yaki da cin hanci da rashawa, kuma jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin za ta dade tana fuskantar wannan jarrabawar. Saboda haka, dole ne dukkan mambobin jam’iyyar a ko da yaushe su sa lura da nuna karfin zuci, da daukar kwararan matakai wajen tafiyar da harkokin jam’iyyar na dukkan fannoni, ta yadda za a iya raya jam’iyyar yadda ake bukata. Ban da haka, ya kamata...
    Mataimakin shugaban ya umarci shugabannin NAHCON da su gaggauta daukan kwararan matakan da suka dace domin tabbatar da kare martabar dukkanin maniyyatan Nijeriya. Da yake magana kan soke kwantiragin da suka yi da kamfanin kasar Saudiyyan, shugaban hukumar NAHCON, Farfesa Saleh Usman, ya ba da tabbacin cewa lamarin ba sai shafi kowani maniyyancin Nijeriya ba. “Ba wani abun damuwa kwata-kwata. Ba wani maniyyancin Nijeriya muddin an masa rajista da za a bar shi,” Usman ya shelanta. Ya kuma yi watsi da zargin da kungiyar Jin Dadin Alhazai ta Jihohi (FSPWA) ke yi na cewa takaddamar kwangilar na iya kawo cikas ga aikin hajjin.
    Kasar Iran ta bayyana cewa: Barazanar gwamnatin mamayar Isra’ila ga jirgin saman da ke dauke da fararen hula na Lebanon cin zarafi ne ga ‘yancin kasar Lebanon Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya yi Allah wadai tare da tofin Allah tsine kan barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, yana mai nuni da hakan a matsayin ci gaba da keta ka’idoji da dokokin kasa da kasa a fili, da kuma keta hurumin kasar Lebanon. Baqa’i ya yi nuni da cewa: Barazanar da gwamnatin yahudawan sahayoniyya ta yi wa jirgin farar hula da ke dauke da ‘yan kasar Lebanon, wanda hakan ya haifar da dakatar da zirga-zirgar...
    Alhaji Ahmad Haruna Zago da aka fi sani da Ɗan zago, gogaggen ɗan siyasa ne da ya fara siyasa tun a Jamhuriya ta biyu. Bayan dawowar Najeriya mulkin farar hula a shekarar 1999, ya shiga Jam’iyyar APP, inda ya kasance na gaba-gaba a tafiyar siyasar jam’iyyar a Kano da ma kasa baki ɗaya. Yana daga cikin waɗanda suka jawo Muhammadu Buhari shiga cikin harkokin siyasa. 2003. Gabanin zaɓen 2003, Alhaji Ahmadu Haruna zago ya taka rawa a tunja-tunjar da ta biyo bayan zaɓen fitar da gwani na Jam’iyyar APP, da ta kai ga karɓe takarar gwamna daga hannun tsohon shugaban jam’iyyar, Ibrahim Al’amin Little, aka bai wa Malam Ibrahim Shekarau. 2007 Sai dai tun ba a je ko’ina ba,...
    Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ta tabbatar da cewa an tanadar wa maniyyatan Najeriya 52,000 guraben aikin Hajjin na shekarar 2025. Wannan na cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Bayanai ta NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta fitar. An kama likita kan laifin yi wa ’yan bindiga magani a Katsina Kwastam ta lalata magungunan biliyan N100 a Ribas Ta ce hukumar ta riga ta biya kuɗin gurabe 26,287 na maniyyata, sannan ta tanadi wasu 26,000, da za a tabbatar da su gaba ɗaya kafin ranar 13 ga watan Fabrairu, 2025. Domin cika wa’adin da Hukumar Aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bayar, Shugaban NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya tafi Makka domin ƙulla yarjejeniya. Ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a...
    Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya karbi bakuncin tawaga daga kasar Saudiyya karkashin jagorancin Sheikh Nuhu Idris Fallata shugaban hukumar Saudiyya mai kula da ciyar da Alhazai. Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, tawagar ta zo ne domin ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa da dansa ya rasa. Sheikh Fallata ya yi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rasu. Tawagar ta kuma yabawa tare da karrama Gwamna Namadi bisa kulawa da jajircewarsa wajen kyautata rayuwar Alhazai. A cewar tawagar, jihar Jigawa ta yi fice mai ban sha’awa a lokacin aikin Hajjin shekarar 2024. Shi ma da yake nasa jawabin babban daraktan hukumar jin dadin alhazai ta jiha Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yabawa tawagar bisa karrama gwamnan jihar ta...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na yin watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da korar Falasdinawa daga muhallinsu Saudiyya ta jaddada cewa: Tana yi watsi da kalaman masu tsattsauran ra’ayin sahayoniyyanci game da neman tilastawa al’ummar Falasdinu yin hijira daga yankunansu, kuma ta nuna cewa ba za a samu dawwamammen zaman lafiya ba sai dai ta hanyar amincewa da tsarin zaman lafiya da zai kai ga samar da kasashe biyu na Falasdinawa dana yahudawan sahayoniyya. Hakan ya zo ne a yayin taron majalisar ministocin Saudiyya da yarima mai jiran gado kuma fira ministan kasar Mohammed bin Salman ya jagoranta, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito. Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na...
    A ci gaba da kokarinta na samun tagomashi a fannin tattalin arziki da ci gaban jihar ta hanyar kawo sauyi a harkar noma, gwamnatin jihar Jigawa na shirin hada gwiwa da wani kamfani da ke samar da dabino  da bayar da shawarwari a harkar noma, wanda ke da ofishi a Najeriya a kasar Saudiyya domin bunkasa noman dabino a jihar. Gwamna Malam Umar Namadi ne ya bayyana hakan a yayin da ya karbi bakuncin wata tawaga daga daya daga cikin manyan kamfanonin noma na kasar Saudiyya, wadanda suka kware a harkar noman dabino da sarrafa gonaki, karkashin jagorancin Abdul’aziz Abdurrahman Al-Awf, wadanda suka kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati dake Dutse. Babban makasudin ziyarar ita ce tattaunawa...
    Da marecen jiya Litinin ne aka yi tattaunawa ta wayar tarho a tsakin ministocin harkokin wajen Iran da na Saudiyya akan shirin Donald Trump na korar Falsdinawa daga Gaza,inda kasashen biyu su ka ki amincewa da shi. Ministan harkokin wajen na Iran Abbas Arakci, da takwaransa na Saudiyya Faysal Bin Farhaan, sun nuna kin amincewarsu da shirin na shugaban kasar Amurka akan mutanen Gaza. Ministan harkokin wajen Saudiyya Faysal Bin Farhan ya ce, Saudiyya tana da matsaya tabbatacciya da ita ce kin amincewa da duk wani shiri na korar Falasdinawa da karfi daga Gaza zuwa wata kasa.” Ministan na Saudiyya ya nuna goyon bayansa ga kiran da Iran ta yi na yin taron kungiyar kasashen musulmi domin tattaunawa wannan batu....
    Iran, ta la’anci kalaman foraministan Isra’ila dake cewa a kasa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya yi kakkausar suka ga kalaman na Benjamin Netanyahu da ke nuna cewa a kafa kasar Falasdinu a Saudiyya, yana mai danganta hakan da tsokana da kuma barazana ga zaman lafiya da tsaro a yankin. Babban jami’in diflomasiyyar ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da takwaransa na Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan a ranar Litinin yayin da ake ci gaba da cece-kuce kan shawarar Amurka da Isra’ila kan Falasdinu. A yayin tattaunawar shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya  ya nuna adawar Saudiyya ta tilastawa Falasdinawa gudun hijira daga Gaza ko wasu yankunan. Tunda farko...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Dakta Zainab Muhammad na daga cikin matan Arewacin Najeriya da ta jajirce tare da ƙudirin cika burinta na karantar kimiyya duk da ƙalubalen da wasu matan yankin ke bayyana cewa suna fuskanta wurin karantar fannin. Dakta Zainab ba kimiyya kawai ta karanta ba, ta karanci ɗaya daga cikin kimiyyoyin da ake ganin sun fi kowanne wahala wanda a mafi yawan lokuta ba mata kaɗai ba, har da mazan ma na ƙauracewa wannan karatun. Zainab ƙwararriyar likita ce wacce ta shahara wurin kula da marasa lafiya a asibitoci. NAJERIYA A YAU: Shin Har Yanzu Akwai Masu Rufin Asiri A Najeriya? DAGA LARABA: Yadda Al’adun Aure A Ƙasar Hausa Suka Koma ‘Event Centre’ Shirin Najeriya...
    Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon ta’aziyya ga takwaransa na Namibia, Nangolo Mbumba, bisa rasuwar shugaban kasar na farko, Sam Nujoma. A madadin gwamnati da al’ummar Sinawa, shugaba Xi Jinping ya bayyana jimami tare da yin ta’aziyya ga iyalan Nujoma da ma gwamnati da al’ummar kasar Nambia. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
    Ma’aikatar harkokin wajen Masar ta sanar cewa, kasar za ta karbi bakuncin taron gaggawa na kasashen Larabawa a ranar 27 ga watan Fabrairun nan, domin tunkarar al’amura na baya-bayan nan da suka shafi batun Falasdinu da zirin Gaza. Sanarwar ta ce, an yanke shawarar gudanar da taron ne bayan muhimman shawarwarin da Masar ta yi da kasashen Larabawa, ciki har da Falasdinu da ta bukaci gudanar da taron, tare da hadin gwiwar Bahrain. A wani labarin kuma, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ta yi kakkausar suka kan munanan kalamai da kuma rashin da’a da firaministan Isra’ila ya yi na yin kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya. A ranar Alhamis, ne Netanyahu ya ba da shawara...
    Kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran ya jaddada cewa: Kungiyar Hamas duk da iyakantaccen kayan yakinta ta kalubalanci gwamnatin ‘yan sahayoniyya Kwamandan dakarun kasa na Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Birgediya Janar Morteza Miryan ya jaddada cewa: Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta kalubalanci gwamnatin mamayar ‘yan sahayoniyya da suke samun goyon bayan Amurka da kasashen Yamma duk da iyakantaccen kayan yakin da ta mallaka na kare kai. Birgediya Janar Miryan ya ce a cikin jawabinsa a wajen bikin tunawa da shahidan harin “Wal-Fajir 8” da aka gudanar a lokacin tunawa da shahidan lardin Alborz da ke yammacin birnin Tehran: A lokacin yakin da aka yi na shekara ta 1980 zuwa shekara ta 1988),...
    Kasar Saudiyya ta jaddada matsayinta na kin amincewa da kalaman Netanyahu dangane da korar Falasdinawa daga Zirin Gaza Kasar Saudiyya ta jaddada yin tofin Allah tsine, da kuma karfafa kin amincewa da kasashen Larabawa suka yi dangane da furucin Benjamin Netanyahu kan neman korar al’ummar Falastinu daga kasarsu ta gado. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar Saudiyya ta fitar a yau Lahadi, ta jaddada cewa: Saudiyya ta tabbatar da yin watsi da irin wadannan kalamai da ke da nufin karkatar da hankali daga jerin laifukan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ke ci gaba da yi kan Falasdinawa a Gaza, ciki har da kisan kare dangi da ake yi musu. Sanarwar ta kara da cewa: Wannan tunani na...
    Falasdinawa sun fitar da martanin farko mai gauni kan kalaman fira ministan ‘yan mamayar Isra’ila dangane da furucinsa ga Saudiyya Kungiyar ‘yantar da Falasdinu ta yi Allah wadai da kalaman da fira ministan mamayar Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi game da kafa kasar Falasdinu a cikin kasar Saudiyya. Sakataren kwamitin zartarwa na kungiyar ‘yantar da Falasdinu Hussein Al-Sheikh ya bayyana cewa: Suna yin Allah wadai da matakin da mahukuntan yahudawan sahayoniyya suka dauka na kai cin mutunci da raina kimar masarautar Saudiyya da ‘yancinta, wanda suka yi kira da a kafa kasar Falasdinu a kasar Saudiyya, kuma wannan furuci na Rashin tunani ya yi cin karo da dokokin kasa da kasa da yarjejeniyar kasa da kasa. Ya kara da cewa:...
    Saudiyya Ta Yi Watsi Da Shirin Fitar Da Falasdinawa Daga Gaza
    Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar Jigawa ta ce ta mikawa hukumar alhazai ta kasa NAHCON kudaden aikin hajjin maniyyatan jihar  na shekarar 2025 kimanin naira biliyan 4.5. Babban Daraktan hukumar Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse babban birnin jihar. Ya ce hukumar ta aika wa NAHCON Naira Biliyan Huda da Miliyan Dari Biyar da Ashirin (4.520), a yayin da take sa ran za ta kara biyan wasu kudaden kafin cikar wa’adin da NAHCON din ta bayar. Ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa NAHCON ta baiwa jihar kujeru 1,809. A cewarsa, tuni hukumar ta raba kashi 40 cikin 100 ga kananan hukumomin jihar domin gudanar da aikin hajjin bana. Don...
      Yayin da Hukumar Kula da Hajji ta Kasa ta kara wa’adin biyan kudin Hajjin bana zuwa ranar 10 ga watan Fabrairu, Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna ta umarci dukkan ofisoshin da suke alhakin yin rajista su tabbatar da an yi wa duk masu sha’awar tafiya Hajji rajista kafin ƙarshen wa’adin da aka ƙara.   Shugaban Hukumar, Malam Salihu Abubakar, ya kuma yi kira ga dukkan maniyyatan da ba su kammala biyan kuɗinsu ba da su gaggauta yin hakan.   Ya jaddada cewa ba za a ƙara wa’adin bayan ranar 10 ga Fabrairu ba, don haka ya bukaci maniyyata su yi amfani da wannan damar su kammala rijistarsu kafin ko zuwa Litinin, 10 ga Fabrairu, 2025.   Rel/Adamu...
    Masana kimiyyar kasar Sin sun kirkiro wani sabon samfurin kirkirarriyar basira ta fasahar AI domin yin hasashen zuwan mahaukaciyar guguwa, wanda hakan ya ba da sabuwar fa’ida da kara haskaka hanyoyin inganta shirin tunkarar bala’o’i a duniya. A kwanan baya, masu bincike daga cibiyar nazarin teku a kwalejin kimiyya ta kasar Sin sun wallafa wannan binciken a cikin mujallar da ke wallafa harkokin kimiyya ta kasar Amurka, watau “Proceedings of the National Academy of Sciences.” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
    Shugabannin Ɗariƙar Tijjaniyya bisa jagorancin Khalifa Sheikh Muhammad Mahi Inyass, sun ziyarci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a fadarsa. A yayin ziyarar, Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass kuma ɗansa, Khalifa Sheikh Muhammad Mahi, da tawagarsa sun halarci Sallar Juma’a tare da Shugaba Tinubu a Fadar Shugaban Ƙasa. Malaman sun kuma gudanar da addu’o’in neman taimakon Allah da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba da kuma albarka ga Najeriya. Khalifa Muhammad Mahi Inyass, ɗa ga Jagoran Tijjaniyya Sheikh Ibrahim Inyass, ya jinjina wa Gwamnatin Tinubu, inda ya yi wa shugaban ƙasa addu’ar samun nasara da ƙarin basira da nasara a shugabanci domin kawo gagarumar ci-gaba a Najeriya. Masu yi wa ƙasa hidima za su karɓi N77,000 daga Fabrairu – Shugaban NYSC ’Yan...
    Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta Sanar da cewa: Ma’aikatar tsaron kasar ta kebe jirgin saman maras matuki ciki kirar “Arash-2” da ta kera ne don kai hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila A ci gaba da gudanar ranakun atisayen soji domin ayyukan tsaron kasa, da sojojin Iran suke gwajin kai hare-hare da kuma sarrafa manyan na’urorin makaman tsaro a yankin da ke yammacin kasar, a karon farko sun nuna wasu jiragen saman yaki maras matuki ciki da aka kera a cikin gida masu tsnanin karfin munanan hare-hare irin na kunan bakin wake kirar “Ababil” da “Arash-2” da dakarun sojin kasar Iran zasu yi amfani da su wajen kare tsaron kasa duk lokacin da ya dace. Jiragen saman “Ababil” ne suka jagoranci...
    Ministan Harkokin Wajen Iran ya shawarci shugaban Amurka da ya mayar da yahudawan sahayoniyya zuwa Greenland Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya yi tsokaci kan kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ya yi kan ba da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, maimakon haka Araqchi ya ba da shawarar kwashe ‘yan sahayoniyya Greenland. Ministan harkokin wajen Iran ya yi ishara da haka ne a wata hira da kafar yada labarai ta Sky News, yana mai bayyana cewa: A mahangar ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran, a bayan da Trump ya shiga fadar White House a farkon wa’adinsa ya gabatar da shawarar korar Falasdinawa daga Zirin Gaza, amma kokarinsa ba ta yi nasara ba. hakan yana nufin rashin yiwuwar korar Falasdinawa...
      Hukumar kulada jin daɗin alhazai ta jihar Kaduna ta shirya fara shirin wayar da kai da ilmantarwa ga maniyyata aikin hajjin bana.   Shugaban hukumar, Malam Salihu Abubakar, zai kaddamar da shirin ne a Cibiyar Wayar da Kai ta Alhazai da ke Dogarawa, shekkwatar karamar hukumar Sabon Gari.   “Shirin horon wayar da kai yana nufin ilmantar da maniyyata kan dukkan muhimman abubuwan da suka shafi aikin hajji,” in ji shi.   Wadannan sun haɗa da ilimin sanin ka’idojin shari’ar Musulunci da dokokin aikin hajji, da kuma warware matsalolin da ka iya tasowa domin tabbatar da sauƙi da ingantaccen hajji ga dukkan maniyyata.   Ya kuma bayyana cewa dukkan maniyyata, da waɗanda ke son yin rijista kafin ranar karshe...
    Kwamishinan ya yi ikirarin cewa ayyukan Madakin Gini na nuna rashin jajircewa ga waɗanda suka zaɓe shi. “Madakin Gini ya bayyana cewa ba ya cikin waɗanda suka goyi bayan shi da suka zabe shi. Saboda haka, babu dalilin ci gaba da kasancewarsa a wannan muƙamin idan ba ya wakiltar buƙatun mutanen Dala. Da zarar shugabannin jam’iyyar sun amince, ni na shirya fara aiwatar da aikin kiranyesa,” in ji Waiya. Taron ya samu halartar shahararrun mutane, ciki har da Alhaji Lawan Husaini Dala, shugaban NNPP na Dala; da Alhaji Dayyab Ahmad Maiturare, Kwamishinan Muhalli na Jihar Kano, da Hon. Suraj Kwankwaso, da sauransu.
    Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, ya yaba da irin gudunmawar da darikar Tijjaniyya ke bayarwa wajen samar da hadin kai a tsakanin al’ummar musulmin kasar nan.   Mataimakin shugaban kasar ya yi wannan yabon ne a lokacin da yake jawabi a wajen taron Mauludin bana 2025 na marigayi Sheikh Ibrahim Nyass, jagoran darikar Tijjaniyya a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.   Mataimakin wanda ya samu wakilcin Alhaji Babagana Fannami, Ya yabawa kungiyar musulmi bisa tsayin daka a tsawon karnukan da suka gabata akan koyarwar addinin musulunci na gaskiya.   Shettima wanda shi ne babban bako na musamman a wajen taron, ya yaba da tsarin jagoranci na darikar ‘Sufi’ ga bil’adama.   Babban bako na musamman ya jaddada...
    An gudanar da taron Maulidin ƙasa duk da gargaɗin da ’yan sanda suka yi kan barazanar harin ’yan ta’adda a Jihar Kano. Aminiya ta ruwaito cewa, ’yan ɗariƙar Tijjaniyya daga sassan Nijeriya daban-daban sun halarci taron Maulidin na Shehu Ibrahim Inyas na shekara-shekara da aka gudanar a Filin Wasa na Sani Abacha da ke ƙwaryar Birnin Dabo. An saki Falasɗinawa 200 da ke ɗaure a Isra’ila Tinubu zai tafi taron makamashi a Tanzania Sai dai tun a jiya Juma’a ce mai magana da yawun ’yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar da sanarwa mai ɗauke da gargaɗin cewa ’yan ta’adda na shirin kai hari a jihar saboda haka jama’a su ƙauracewa duk wani taro da shiga cunkoso. Daga bisani...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta yaba da kokarin ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya bisa gudunmawar da suke bayarwa ga harkokin kiwon lafiyar al’ummar jihar. Gwamna Umar Namadi ya bayyana hakan a lokacin rangadin duba aikin idanu da ‘yan Nigeria mazauna kasar Saudiyya da hadin gwiwar gwamnatin jihar ke gudanarwa a babban asibitin Dutse. Gwamnan wanda ya zagaya wuraren da aka kwantar da wadanda aka yi wa aikin idanun, ya nuna jin dadinsa da gamsuwa da yawan mutanen da aka yi wa aikin. Daga cikin wadanda suka amfana da aikin sun hada da masu matsalar ido su 500 da aka yi wa tiyata, sai kuma mutane  300 da aka baiwa gilashi. Kazalika, mutane 400 kuma suka...
۱