Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-03-25@18:00:29 GMT

Jihar Bauchi Zata Tarbi Taron Karrama Sir Ahmadu Bello Karo Na 11

Published: 11th, February 2025 GMT

Jihar Bauchi Zata Tarbi Taron Karrama Sir Ahmadu Bello Karo Na 11

 

Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi.

 

 

Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa, zai hada da jerin tattaunawa da ayyukan da zasu mayar da hankali wajen magance kalubalen tattalin arzikin yankin.

 

 

Taken taron na bana, “Alherin Duniya: Sauyw Albarkatun Halitta na Arewa zuwa Cigaba Mai Dorewa”, na zuwa ne a lokacin da ake fuskantar karin damuwa kan talauci da rashin aikin yi da rashin ci gaba duk da kasancewar Arewa na da yalwar albarkatun halitta.

 

 

Za a tattauna yadda yankin zai iya amfani da gonakin noma da ma’adinai da albarkatun ruwa wajen samun ci gaban tattalin arzikin da zai dore.

 

 

Wannan taron na tsawon mako guda zai hada da horo na kwarewar zamantakewa ga matasa a Jihar Bauchi da gabatar da tallafin karatu ga dalibai ‘yan asalin jihohin Arewa a makarantu na gaba da sakandire da kuma ba da kyaututtuka ga mutanen da suka cancanta a fannonin al’umma.

 

 

Tsohon Daraktan Gudanarwa na Bankin Duniya, Dr. Mansur Mukhtar OFR, zai gabatar da jawabi, yayin da His Excellency Senator George Akume, Sakataren Gwamnatin Tarayya, zai kasance matsayin baƙo na musamman.

 

His Excellency Alh. Muhammadu Inuwa Yahaya CON, Gwamnan Jihar Gombe ne wanda zai jagoranci taron, tare da Gwamnan Jihar Bauchi, His Excellency Sen. Bala Mohammed CON, a matsayin babban mai masaukin baki.

 

 

Ana sa ran manyan baki a wurin taron su hada da gwamnonin jihohi da ‘yan majalisar dokoki da ministoci da sauran manyan masu ruwa da tsaki, wanda ke nufin haɓaka tattaunawa mai ma’ana da dabaru masu amfani domin bude damar ci gaban tattalin arzikin Arewa.

 

Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello tana ci gaba da aikinta na inganta ilimi da cigaban ɗan adam, da cigaban tattalin arziki a Arewa, a cikin girmamawa da gado na marigayi Sardauna.

 

Daraktan gidauniyar, Engr. Dr. Abubakar Gambo Umar, ya bayyana farin cikinsa dangane da wannan taron, yana mai jaddada muhimmancin albarkatun halitta na Arewa wajen tsara makomar yankin.

 

“Yankin Arewa na da yalwar albarkatun halitta da noma da ma’adinai da ruwa wanda zai iya zama babban dama don haɓaka ci gaban dake dorewa,” in ji shi.

 

“Amma wannan damar za a iya cimma ta ne kawai idan muka ɗauki hanyar gudanarwa ta haɗin gwiwa da cikakken tsarin kula da albarkatu, domin tabbatar da cewa ci gaban yana faɗaɗa ga dukkanin masu ruwa da tsaki,” ya ƙara da cewa.

 

Dr. Umar ya kuma bayyana muhimmancin taron Karrama Sir Ahmadu Bello a matsayin dandalin tattaunawa a kan waɗannan kalubale.

 

Ya kara da cewa, “Wannan jerin taron yana cikin muhimmancin gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello na ƙarfafa tattaunawa mai ma’ana a kan shugabanci da cigaba mai dorewa da haɓaka tattalin arziki.

 

 

Ya ce, “yana da muhimmanci mu haɗa muryoyi daban-daban daga gwamnati da ɓangarori masu zaman kansu, da ƙungiyoyin farar hula don ƙirƙirar dabaru masu amfani wajen ci gaban yankin.”

 

 

Khadija Kubau

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jihar Bauchi Zata Tarbi Taron Karo Karrama

এছাড়াও পড়ুন:

Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani

An ruwaito cewa, shirin aikin noman ranin da aka kaddamar a yankin na Lallashi, zai karade hekta 10, wanda kuma sama da kananan manoma 80, za su amfana da shirin kai tsaye.

Bugu da kari, shirin zai taimaka wajen kara samar da girbin amfanin gona mai yawan gaske tare kuma da kara bunkasa tattalin arzikin jihar baki-daya.

Malam Aliyu Musa, da yake yin jawabi a madadin sauran manoman da ke yankin ya bayyana cewa, samar da shirin a yankin da gwamnatin jihar ta yi, tamkar zuba hannun jari ne.

A cewarsa, al’ummar yankin za su ci gaba da yin addu’a, domin shirin ya dore tare kuma da ganin an kara fadada shi, don su ma sauran yankunan jihar su amfana.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Masu neman yi wa Natasha kiranye ba su cika ƙa’ida ba — INEC
  • An Gudanar Da Taron Karawa Juna Sani Kan Karfafa Rawar Da MDD Ke Takawa A Beijing
  • ‘Yansanda Sun Cafke Mutum 2 Kan Zargin Kashe Ɗan Achaɓa Da Sace Babur Ɗinsa A Bauchi 
  • An Yi Taron Tattaunawar Kasa Da Kasa Kan Damammakin Da Sin Ke Gabatarwa A Rasha
  • Sule Lamido Ya Soki Rabon Abinci da Seyi Tinubu Ya Yi A Arewa
  • An Bude Taron Shekara-Shekara Na Dandalin Tattauna Raya Kasa Na Sin Na 2025
  • Iran Tace Zata Kaddamar Da Sabbin Magunguna Da Ta Samar Tare Da Amfani Da Makamashin Nukliya
  • Za’a Gudanar Taron Tattaunawa Tsakanin Rasha Ta Amurka A Karo Na Biyu 2 A Birnin Rayad na Kasar Saudiya
  • Gwamnonin Arewa sun yi wa Radda ta’aziyyar rasuwar mahaifiyarsa
  • Hikimar Gwamnatin Jihar Jigawa Na Kaddamar Da Shirin Gina Rijiyoyin Burtsatsan Noman Rani