2025-03-26@06:45:04 GMT
إجمالي نتائج البحث: 23

«Karrama»:

    Wani rahoto da aka fitar yau Talata, yayin zaman taron shekara-shekara na shekarar 2025, na dandalin tattaunawa na Asiya na Boao, ya nuna yadda kasar Sin ke ci gaba da kasancewa cibiyar rarraba hajojin da masana’antu ke sarrafawa. Rahoton mai taken “Nazarin tattalin arzikin Asiya, da hadadden rahoton ci gaba na shekarar”, ya nuna yadda...
    Majiyar gwamnatin kasar Yemen ta basa sanarwan kai hare-hare har sau biyu kan kataparen jirgin ruwa mai daukar jiragen yaki na kasar Amurka dake cikin Tekun Red sea, wato USS Harry Truman. Inda suka cilla makami mai linzami guda da kuma jiragen yake wadanda ake sarrafasu daga nesa kan jirgin. Har’ila yau sojojin yamen sun...
    Tsohon gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya fasa baragurbin ƙwai kan zargin sace Jafaru Sani, tsohon Kwamishina a gwamnatinsa. El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna daga 2015 zuwa 2023 kafin ya miƙa mulki ga Sanata Uba Sani, wanda shi ne ɗan takarar da ya fi so ya gaje shi, ya bayyana wannan batu ne...
    Hukumar gudanarwar asibitin koyarwa na Aminu Kano ta ce ana kokarin ganin an dawo da ayyukan da masana’antar iskar Oxygen da asibitin ke yi.   A cewar Mataimakin Daraktan sashen (Biomedical/ kuma Shugaban Kwamitin Kula da Oxygen), Engr Ahmed Usman a madadin Hukumar, an sanya hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna tsakanin asibitin da...
    Ya kara da cewa an samu wasu kayayyaki a wurin, ciki har da babbar motar dakon kaya ɗauke da buhuna takwas na ‘Monazite’ da aka sarrafa, wanda nauyinsa ya kai kilogiram 1000, wanda darajar kowanne buhu ta kai naira miliyan hudu, da kuma wasu ma’adinai da ba a sarrafa ba da ake zargin an haƙo...
    Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka...
    Daga ƙarshe sanarwar ta ƙara jaddada ingantattun ƙa’idojin karatu a BUK, wanda ta ce ba za ta lamunci satar jarrabawa ko laifuffuka makamantan haka ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin...
    LEADERSHIP tana da mabiya kusan miliyan 3.7 a shafukan sada zumunta daban-daban, ciki har da dandalinta na Hausa. Tun daga ranar Lahadi, da yawa daga cikin masu bibiyar wadannan manhajoji ko dai suna ba da alamar dangwale, ko kuma taya murna kan labaran da suka shafi bikin karramawar da ke tafe. A makon da ya...
    A kasuwar Ariaria da ke Aba, NAFDAC, sun gano jabun magunguna da kudinsu ya kai na miliyoyin Naira. Bugu da kari, a kasuwar Idumota da ke a jihar Legas, NAFDAC sun garkame Shanguna sama da 3,000 bayan sun gano Shagunan shake da jabun magunguna. A kasuwar kan Gadar Onitsha, nan ma Hukumar ta sun kama...
    Parradang ya yi aiki a hukumar NIS fiye da shekaru 30, inda ya yi aiki a fadin jihohin kasar nan da suka hada da Kano, Legas, Kwara, Enugu, da Abuja. Ya halarci kwasa-kwasan ƙwararru da yawa a cikin gida da waje.   Domin karrama shi da hidimar da ya yi, an karrama shi da lambar...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area...
    Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa a ɗakin wani otel ta gano gawar wani tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Ficen Nijeriya, David Shikfu Parradang. A baya dai an ruwaito cewa wasu masu garkuwa da mutane ne suka kashe Mista Parradang bayan sun karɓe kuɗin da ya ciro a banki a yankin Area...
    Ana fargabar cewa wasu masu ta’adar garkuwa da mutane sun kashe tsohon Kwanturola-Janar na Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), David Shikfu Parradang a Abuja. Majiyoyi sun shaida wa ƙwararren mai sharhi kan yaƙi da tayar da ƙayar baya Zagazola Makama cewa ’yan ta’addan sun ɗauke Parradang a yankin Area 1 da ke babban...
    Kwanan baya, kwamitin kula da aikin lantarki na duniya (IEC) ya gabatar da ka’idar sarrafa mutum-mutumin inji mai kula da tsoffi. Ka’idar da kasar Sin ta ba da jagorancin tsarawa, ta tabbatar da yadda za a tsara da sarrafa mutum-mutumin injuna masu kula da tsoffi bisa halayen da tsoffi suke ciki, ta kuma tabbatar da...
    Hukumar bayar da gudunmawar fansho ta Jihar Jigawa da Kananan Hukumomin jihar ta kulla yarjejeniyoyi da wasu mashahuran Hukumomin Asusun Fansho guda shida (PFA) da nufin tabbatar da tafiyar da kudaden fansho na jihar yadda ya kamata. Shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K Dagaceri wanda ya jagoranci rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin...
    Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta gargaɗi shugabannin ƙananan hukumomi da su guji almundahana tare da yin amfani da kuɗaɗen jama’a bisa gaskiya da adalci. Shugaban EFCC, Mista Ola Olukoyede ne, ya bayyana haka yayin wani taro da aka shirya a Jihar Gombe kan ’yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi. Jihar...
    Gwamnatin Jihar Jigawa ta dauki matasa fiye da 6,000 aiki a fannoni daban-daban a fadin jihar, a kokarinta na ganin ta inganta rayuwarsu. A saboda haka ne ma matasan da aka dauka aikin suka karrama Gwamnan Jihar, Malam Umar Namadi, bisa kokarinsa na samar da ayyukan yi da bunkasa tattalin arzikin al’ummar jihar. Wakilinmu...
    Ya kuma bayyana cewa, a halin yanzu ayyukan hukumar bai tsaya a kan kula da tsaftace muhalli da abinci kadai ba, suna kula da tasirin sauyin yanayi da kuma fadakar da al’umma yadda za su amfana da trallafin sauyin yanayin da ake samu daga Majalisar Dinkin Duniya.   A nasa jawabin, Babban Manajan Daraktan kamfanin,...
    Jiragen Yakin HKI Sun Kashe mutane 3 da kuma jikada wasu 4 a kudancin kasar a jiya Asabar. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto majiyar kafafen yada labara na yankin kudancin kasar ta Lebanon suna fadar haka. Labarin ya kara da cewa HKI ta yi amfani da makamai masu linzami wanda jirgin...
      Gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta sanar da cewa za a gudanar da taron Karrama Sir Ahmadu Bello karo na 11 a ranar Asabar, 22 ga Fabrairun 2025, a Bauchi.     Wannan taron, wanda ke tunawa da rayuwa da gado na Sir Ahmadu Bello KBE, Sardaunan Sokoto da Firaministan tsohuwar Yankin Arewa,...
    Albarkacin bikin bude gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 dake gudana a birnin Harbin na Sin, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa, Thomas Bach ya ziyarci cibiyar yada labarai ta gasar a jiya Juma’a, kuma ya yi hadin kai da shugaban rukunin gidajen rediyo da talibijin...
    Saka sunan Taye Taiwo a cikin jerin zakakuran yan wasan kungiyar ya nuna yadda dan wasan ya nuna bajinta da kuma yadda ita kanta kungiyar ta Marseille ta yaba da irin kokarin da ya yi a baya.
    Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karrama wasu mutum 35 ’yan asalin Jihar Kano waɗanda suka yi fice a fannoni daban-daban na rayuwa. Daga cikin waɗanda gwamnan ya karrama akwai janar-janar ɗin soji 19, Farfesoshi 6 da wasu fitattun Kanawa 10. Asibitin Malam Aminu Kano ya hana motoci masu baƙin gilas shiga harabarsa Mahaifin ma’aikacin Aminiya...
۱