Ƙungiyar Malaman Tsangaya Ta Karrama Gwamna Inuwa Lambar Yabo ta ‘Khadimul Qur’an’
Published: 9th, March 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci.
Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar.
Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin al’ummar Musulmi.
A jawabinsa bayan buɗa-bakin azumi, Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata jin daɗin malaman Tsangaya da kuma yara Almajirai.
Ya bayyana muhimmancin ilimin Alƙur’ani ga al’umma tare da jaddada buƙatar samar da yanayi mai ɗaukaka koyo da koyarwa.
Gwamnan ya yi bayanin yadda gwamnatinsa ta yi gagarumin ƙoƙari wajen gina manyan makarantun Tsangaya da ƙananan makarantun Almajirai a faɗin jihar, tare da haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani cikin tsarin karatu.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa yara Almajirai an sanya su cikin shirin lafiya na Go-Health, wanda ke ba su damar samun kulawar lafiya kyauta domin tabbatar da lafiyarsu.
“Mu a matsayin gwamnati mun fahimci muhimmiyar rawa da makarantun Tsangaya ke takawa wajen tarbiyya da cigaban ilimi ga yaranmu.
“Wannan ne ya sanya muka fifita jin daɗinsu ta hanyoyi daban-daban, ciki har da gina makarantun Tsangaya da kuma shigar da su cikin shirin Go-Health domin samun ingantacciyar kulawar lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Gwamna Inuwa.
Da yake magana a madadin malaman Tsangaya, Goni Mai Babban Allo ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya kan goyon bayan da yake bayarwa ba dare ba rana.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya ɗauki matakai na musamman, ciki har da gina makarantun Tsangaya, sanya fitilu masu aiki da hasken rana a makarantun, da haɗa Almajirai cikin shirin kula da lafiya na jihar Gombe.
“Ba mu taɓa samun gwamnati da ta damu da jin daɗin malaman Tsangaya da ɗalibanmu kamar wannan ba,” in ji Goni Mai Babban Allo.
A cikin girmamawa ga ƙoƙarinsa da kuma sadaukarwarsa, Ƙungiyar Alarammomi ta naɗa Gwamna Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’, alamar kasancewarsa bawan Alƙur’ani mai sadaukarwa.
Tun da farko, a jawabinta na maraba, Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan harkokin Tsangaya da Ilimin Almajiranci, ta yi kira ga Alarammomi da su ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Yahaya jihar Gombe malaman tsangaya Gwamna Inuwa Yahaya makarantun Tsangaya malaman Tsangaya a makarantun Tsangaya da
এছাড়াও পড়ুন:
Saudiyya Za Ta Karbi Bakuncin Tattaunawar Amurka Da Ukiraniya
Shugaba Zelensky na Ukiraniya zai kai ziyara kasar Saudiyya a ranar Litinin, gabanin bude tattaunawar da za a yi tsakanin kasarsa da kuma Amurka da zummar kawo karshen yaki da Rasha.
Shugaban na kasar Ukiraniya ya wallafa wani sako a shafinsa na X cewa; Manufar ziyarar tashi ita ce haduwa da yarima mai jiran gado Muhammad Bin Salman, sannan kuma tawagar da zai je da ita, za ta ci gaba da zama a can Saudiyya din saboda yin aiki tare da mutanen Saudiyya da kuma Amurka.”
Zelensky ya kara da cewa; Kasarsa Ukiraniya tana son ganin an sami zaman lafiya mai dorewa.
Bugu da kari shugaban na kasar Ukiraniya ya ce; Matakin farko da kasarsa ta gabatar a matsayin shawarar kai wa ga zaman lafiya, shi ne dakatar da yaki a lokaci mafi kusa, da hakan zai zama share fage ne na warware sabanin da ake da shi baki daya,kuma Ukiraniya a shirye take ta yi aiki da Amurka a turai domin shimfida zaman lafiya”
Dangane da taron da za a yi a kasar Saudiyya, wani babban jami’in gwamnatin kasar ta Ukiraniya ya ce, a ranar Talata mai zuwa za a yi ganawa a tsakanin tawagar kasarsa da kuma ta Amurka a Saudiyya.
Jami’in na Ukiraniya ya ce ganawar za a yi ta ne a kokarin kyautata alaka a tsakanin kasashen biyu, bayan abinda ya faru na cacar baki a tsakanin Donald Trump a Zylenisky.
A gefe daya ministan tsaron Birtaniy John Healey ya furta cewa; Da akwai kyakkyawar dama ta tarihi domin shimfida zaman lafiya a Ukiraniya” sannan ya kara da cewa: “ Shugaban kasar Ukiraniya a shirye yake ya rattaba hannu akan yarjejeniya da Amurka, amma yana da bukatuwa da a ba shi lamuni.