2025-03-09@20:14:43 GMT
إجمالي نتائج البحث: 68
«Gwamna Inuwa Yahaya»:
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta karrama Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya lambar yabo ta ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa...
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci. Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar. Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto Yadda masana’antun Arewa suka koma kufai Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin...
Shugaban Amurka Donald Trump, ya katse tallafin da yake baiwa jami’ar Columbia saboda zanga-zangar goyan bayan Falasdinu. Trump ya ce an katse tallafin na dala miliyan 400 ga jami’ar, daya daga cikin manyan a kasar, bisa zarginta da gazawa wajen fuskantar ayyukan kyamar Yahudawa a harabarta, wanda ke nufin zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Ana kallon wannan a matsayin alwashin da Donald Trump, ya sha a lokacin yakin neman zabe inda sha yin tir da yadda wasu jami’o’i ke nuna gazawa wajen fuskantar zanga zangar goyan bayan Falasdinu. Masana da dama na ganin matakin a matsayin misali na siyasantar da manyan makarantu da kuma tsoma bakin gwamnati. Shugaban kungiyar jami’o’in Amurka ya bayyana cewa matakin na gwamnatin Trump “ya haifar da...

‘Yancin Kananan Hukumomi: Gwamnatin Nijeriya Ta Ce Kananan Hukumomi 749 Sun Gaza Bayar Da Cikakkun Bayanan Asusunsu
A cikin abubuwan da aka tattauna a taron, a cikin kananan hukumomi 774, Jihar Delta ce kadai mai kananan hukumomi 25, suka mika bayanan asusunsu domin biyansu kai tsaye. “Kawo yanzu kananan hukumomin Jihar Delta ne kawai suka bayar da bayanan asusunsu. “Duk da haka, ana ci gaba da tuntubar babban lauyan gwamnatin tarayya game da yadda ake gabatar da asusun.” Da take maida jawabi kan kalubalen, Madein ta ce an tsara tsarin da za a aiwatar, amma kalubalen farko shi ne na tantance shugabannin kananan hukumomin da tsarin mulki ya zaba. Ta bayyana cewa wannan matakin ya kasance mara tabbas. “Bugu da kari, ga wadanda ke da zababben shugabanci, akwai alaman tambaya cewa wasu hanyoyin za a bi don...
Kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa a yau Juma’a yahudawa 800 sun kutsa cikin iyakar Lebanon, zuwa kabarin wani malamin yahudawa Rabbi Ashi. Sun kuwa isa wurin ne a karkashin rakiyar sojojin mamaya. Majiyar ‘yan sahayoniyar ta ce, kabarin malamin yahudawan dai yana a cikin iyakar Lebanon ne dake kallon matsugunin ‘yan share wuri zauna ta Mir Gliot. A cikin makwanni kadan da su ka gabata dai yahudawan ‘yan share wuri zauna sun rika ketaro iyaka daga Falasdinu dake karkashin mamaya zuwa Lebanon, sai dai na yau Juma’a ne mafi girman adadin yahudawan da suka ketara iyaka. Ya zuwa yanzu dai babu wata sanarwa da ta fito daga sojojin Lebanon ko gwamnati akan abinda ya faru. Amma a jiya...
An kashe mutane fiye da 70 a fafatawa tsakanin sojojin Hai’at Tahrin Assham Masu Iko da kasar Siriya ta wata kungiyar yan tawaye a yammacin kasar. Ciobiyar watsa labarai ta SOHR ta bayyana cewa an fara yakin ne bayan da aka kaiwa sojojin HIS harin ba zata a kan bakin teku a daren Jumma.a. SOHR wacce take sanya ido a kan al-amuran kasar Siriya ta bayyana haka a shafinta na X a safiyar yau Jumma’a. Ta kuma kara da cewa. a bakin ruwan garin Jabbeh kusa da lardin lardin lantaki mutane 48 aka kashe. Labarin ya bayyana cewa wannan shi ne hari mafi muni a kan sabbin masu iko da kasar Sham tun bayan sun kwace iko da kasar a...
Kwanaki 29 ke nan da wasu ‘yan bindiga suka mamaye garin Tsiga da ke ƙaramar hukumar Bakori a Jihar Katsina, inda suka yi awon gaba da Birgediya Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da wasu mutane. An yi garkuwa da Tsiga, wanda tsohon Darakta-Janar na Hukumar Yi Wa ƙasa hidima (NYSC) ne tare da wasu mazauna garin su tara, a wata ranar Laraba. An kama ’yan Pakistan biyu da laifin yin garkuwa a Legas Hukumar Zaɓen Neja ta sanar da ranar zaɓen ƙananan hukumomoni Masu garkuwa da mutanen sun tuntuɓi iyalan Janar ɗin da aka sace domin neman kuɗin fansa na Naira miliyan 250m. Wata majiya ta kusa da dangin ta shaida wa wakilinmu cewa, har yanzu ana ci gaba da...
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba. Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai. Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar. “Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar batun biyan mafi karancin albashi...

Lin Jian Ya Yi Bayani Kan Takardar Bayani Game Da Shawo Kan Sinadarai Masu Alaka Da Sinadarin Fentanyl Ta Sin
A ranar 4 ga wata, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya fitar da takardar bayani game da shawo kan sinadarai masu alaka da sinadarin Fentanyl. Takardar ta yi cikakken bayani kan yadda kasar Sin ta gudanar da aikin shawo kan bazuwar sinadarai dangin Fentanyl, da nasarorin da ta cimma, yayin da gabatar da fasahohin kasar Sin wajen gudanar da ayyukan da abin ya shafa. Dangane da wannan takardar da kasar Sin ta fidda, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya bayyana cewa, takardar za ta ba da taimako ga al’ummomi da gamayyar kasa da kasa wajen kara musu fahimtar matsayin kasar Sin kan wannan batu, da matakan da Sin ta dauka, da kuma nasarorin da...
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar rage kudaden da gwamnatin tarayya ke ba wa kwalejoji da jami’o’in da ke ba da izinin ” zanga-zangar goyan bayan Falasdinawa tare da hukunta daliban da suka shiga irin wannan zanga zanga. Trump ya yi wannan gargadin ne a wani sako da ya wallafa a dandalinsa na sada zumunta bayan da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa suka taru a harabar jami’ar Columbia da ke New York. Shugaban na Amurka ya kara da cewa “za a daure masu tayar da hankali” ko dai a daure su ko kuma a tura su dindindin zuwa kasashensu na asali.” Ko da yake bai ambaci musamman zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a cikin sakon nasa ba, amma a baya...
Ana cikin zullumi kan sake barkewan yaki a Gaza, bayan da HKI ta ci gaba da hana shigowar kayakin zuwa cikin Gaza. Sannan kungiyar Ansarull ta kasar Yemen ta yi barazanar daukar mataki a kan HKI idan ta ci gaba da hana shigar kayakin Agaji zuwa cikin gaza. Abdullatif Al-washali wani dan siyasa a kasar ta Yemen ya bayyana cewa rufe mashigar Rafah ta inda kayakin agaji suke wucewa su shiga Gaza, wata hanya ce ta wahalarta mutanen yankin, kuma yana dai dai da cilla yaki a kan mutanen Gaza. Ya ce kasar Yemen tana iya daukar matakin soje kan HKI matukar wannan tocewar ta ci gaba. Har’ila yau sojojiun kasar ta Yemen sun bayyana cewa inda HKI ta ci...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A al’adance, a duk lokacin da watan Ramadana ya ƙarato samari da ’yan mata kan yi musayar kyaututtuka domin kyautata wa juna. Misali, samari kan haɗa kayan buɗe-baki irinsu madara da ƙwai da sauran kayan maƙulashe da ake yi wa lakabi da ‘Ramadan Basket’ a turance su kai wa ’yan matansu. Sai dai a wannan shekarar da alamun abin ya sauya salo, domin kuwa ba kamar yadda aka saba ba, kafafen sada zumunta ba su baza hotuna da bidiyon Ramadan Basket ɗin ba. NAJERIYA A YAU: Yadda za ku yi girke-girken azumi da kuɗi kaɗan DAGA LARABA: Abin Da Ya Sa Wasu Maza Ba Sa Son Haihuwa Shirin Najeriya A Yau na wannan...
Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres na mika sakon gaisuwa a yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya suka fara gudanar da azumin watan Ramadan. Ramadan yana kunshe da dabi’u na tausayi, tausayawa da karamci. Sannan dama ce ta sake haduwa da dangi da sauran al’umma. Kazalika dama ce ta tuna wadanda ba su samu damar sake ganin watan ba. Ga duk wadanda suka samu ganin wannan lokaci mai tsarki cikin halin gudun hijira da tashin hankali, ina so in bayyana sakon tausayawa a gare su. Ina goyon baya ga duk wadanda ke cikin halin tsanani da wahala, tun daga Gaza da sauran yankuna, zuwa Sudan, Sahel da sauran su. Kuma ina mai ba da hadin kai da...
Farashin kayayyakin abinci kamar masara da shinkafa da gero da dawa da wake da gari da waken soya da dai sauransu sun ragu, musamman a manyan jihohin da ake nomawa, kamar yadda wani bincike da Aminiya ta gudanar ya nuna. Wannan na faruwa ne gabanin watan Ramadan, wanda aka fara yau Asabar. Yadda ake ‘Spring rolls’ Ramadan: ’Yan sanda sun tsaurara tsaro saboda azumi a Borno Haka kuma an ce, jihohin da ba sa noma suna jin tasirin rage farashin kayan abinci. Masana sun danganta faduwar farashin da aka samu a kasuwa ga karancin kudi da kuma yadda aka yi bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, wanda hakan ya haifar da faduwa farashin sosai. Wasu kuma sun ce, yawan shigo da...
Janar Mai ritaya, tsohon Darakta Janar na NYSC, ya kuɓuta bayan kwana 22 a hannun ‘yan bindiga. Wata majiya ta tabbatar da cewa an sake shi a daren Juma’a, kuma yana karɓar kulawar likita a wani asibitin da ba a bayyana ba saboda dalilan tsaro. Tsiga ya faɗa hannun ‘yan bindiga ne a ranar 6 ga Fabrairu, 2025, a gidansa da ke ƙauyen Tsiga a ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina. Lokacin harin, mutum biyu sun jikkata, yayin da ɗaya daga cikin ‘yan bindigar ya rasa ransa sakamakon harbin da wani daga cikin mutanensa ya yi. Masu Garkuwa Sun Nemi Fansar Miliyan 250 Kafin Su Saki Tsohon Shugaban NYSC, Janar Tsiga Ƴan Bindiga Sun Kai Hari A Katsina, Sun Sace...
Wani matashi ɗan shekara 32 ya soka wa ɗan uwansa wuƙa ya saboda Naira 700 a Unguwar Zara da ke Yankin Babban Birnin Tarayya. Wani shaida a unguwar ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan wanda ake zargin ya kutsa ɗakin yayan nasa ya ɗauke masa Naira 700 daga aljihunsa. Ana zargin wanda a ya yi aika-aikan ya shiga dakin ne bayan wan nasa ya tafi Sallar Isha’i Bayan ya dawo bai ga kuɗin ba, ya yi zargin ƙanin nasa da ɗaukar, ya bi sahunsa, inda ya riske shi a wata mashaya ya je sayen tabar wiwi. Ba ni lokacin cacar baka da El-Rufai —Nuhu Ribadu NAJERIYA A YAU: Azumin Ramadana: Ko Kun San Dabinon Da Kuke Shan Ruwa...

IRGC Ta Bayyana Cewa Taron Jana’izar Nasarallah Ya Yi Tisara A Duniya Gaba Daya Saboda Barazanar Da Jiragen Yakin HKI Ta Yi Wa taron
Dakarun kare juyin juya halin musulunci a nan Iran wato IRGC Sun bayyana cewa Jana’zar Sayyid Hassan nasarallah da kuma magajinsa Sayyid Safiyuddeen ya bayyana irin karfin da kungiyar Hizbullah take da shi a kasar da kuma yankin gabas ta tsakiya. A wani bayani wanda dakarun suka fitar sun bayyana cewa, taron da kungiyar ta gudanar na shahidan shuwagabanninta a jiya, ya tabbatar da cewa kungiyar tana da karfi kuma tana da karfin kawo karshen HKI a yankin da kuma kwato kasashen Larabawan da aka mamaye. Rahoton ya kara da cewa a fagen kasa da kasa kuma, mutanen da suka taru ko suka yi gangami a jana’izar ya tabbatar da yadda wannan kungiyar take da karbuwa a cikin kasar a...
Dakarun gwagwarmaya a Iraki za su ci gaba da ayyuka bisa tafarkin babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah, wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen kare wadanda ake zalunta, kamar yadda Qais al-Khazali, babban sakataren kungiyar Asa’ib Ahl al-Haq ya bayyana. Da yake magana a ranar wannan Lahadin, al-Khazali ya jinjinawa Sayyed Nasrallah, yana mai bayyana shi a matsayin babban mutum wanda ya shafe tsawon rayuwarsa a tafarkin jihadi da kare wadanda ake zalunta. Ya kara tabbatar da cewa babu makawa wa’adin Sayyed Nasrallah na samun nasara a kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila yana zuwa. “Mun yi alkawarin shrda ma Nasrallah cewa, za mu ci gaba da tafiya a kan wannan tafarki har zuwa lokacin da za a tsarkakae kasar...

Wang Yi Ya Yi Bayani Kan Ziyararsa A Birtaniya Da Ireland Da Halartar Taron Kolin Kwamitin Sulhu Da Na Tsaro A Munich Da Na G20
A jiya Asabar 22 ga wannan wata, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi bayani ga kafofin watsa labaru na kasar Sin bayan da ya kammala ziyararsa a Birtaniya da Ireland, da halartar taron kiyaye tsaro na Munich karo na 61, da shugabantar taron kolin kwamitin sulhun MDD a birnin New York, da kuma halartar taron ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar G20 a kasar Afirka ta Kudu. A matsayin kasar da take shugabantar kwamitin sulhun MDD a wannan wata, kasar Sin ta yi kira ga taron koli na kwamitin mai taken “Bin ra’ayin bangarori daban daban da yin kwaskwarima kan kyautata aiwatar da harkokin duniya”. Inda game da hakan, Wang Yi ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi...
Wani kamfani dan kasar Saudiyya mai suna Mashariq Al Dhabia, ya rattaba hannu kan wata yarjejeniyar aiki aka yi wa kwaskwarima da hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) domin hidima ga Alhazan Nijeriya a lokacin aikin Hajjin 2025. LEADERSHIP ta rahoto cewa, kamfanin a baya ya yi barazanar maka NAHCON a kotu bisa zargin karya sharudan kwangilar da hukumar ta rattaba wa hannu kan hidima ga Alhazan Nijeriya a Masha’ir a lokacin aikin Hajjin 2025. Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Al’ummar Katsina Sun Koka Da Taɓarɓarewar Hanya Da Ƙarancin Ruwan Sha Amma a wani al’amari mai ban mamaki, sai aka hangi wata tawaga daga kamfanin na Saudiyya a karkashin jagorancin shugaban kamfanin, Muhammad Hassan, ta...

Ministan Wajen Sin Ya Yi Kiran Hadin Gwiwar Kasashen G20 Don Gina Duniya Mai Adalci Da Ci Gaba Na Bai-daya
Taron na farko na ministocin harkokin wajen G20 a karkashin shugabancin Afirka ta Kudu ya kasance mai cike da tarihi, domin shi ne taron ministocin wajen kungiyar na farko a nahiyar Afirka, kamar yadda ministan huldar kasa da kasa da hadin gwiwa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola ya bayyana, yayin da yake yabawa da taron, a wani taron manema labarai bayan kammala taron, inda har ila yau ya kara da cewa, taron “mai matukar fa’ida” ya yi gagarumar tattaunawa a kan dabarun da suka shafi yanayin shiyyoyin duniya da tasirinsu a kan gudanar da ayyukansu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
“Jajircewar sa ga haɓaka ababen more rayuwa, noma da ƙarfafa matasa yana ci gaba da mayar da Jihar Neja abin koyi wajen cigaba da wadata.” Ministan ya ce yana taya gwamnan na jihar su murna, yana mai bayyana shi a matsayin jagora mai kishin hidimta wa al’umma da cigaban ƙasa. Idris ya ƙara da cewa, “Yayin da yake bikin wannan rana ta musamman, ina taya shi murna a matsayin jagora wanda jajircewar sa ga hidima da shugabanci ke nuna ainihin cigaba. “Ina roƙon Allah ya ci gaba da ba shi lafiya, hikima da ƙarfi don ya ci gaba da tafiyar da Jihar Neja zuwa matakai mafi girma.” Ya kammala da taya Gwamna Bago murna, inda ya...

Amurka Ta Ce Zata Gabatar Da Nata Shawara Dangane Da Kawo Karshen Yakin Ukraine Ga Babban Zauren MDD
A karon farko tun bayan fara yaki a Ukraine tsakanin Rasha da Ukraine a shekara 2022 Amurka bata taba goyon bayan wani kuduri dangane da dakatar da yaki a Ukraine a babban zauren MDD wanda Ukraine da kuma kasashen Turai suka gabatar ba. Amma a halin yanzu ta ce zata tsara nata shawarar dangane da kawo karshen yaki a Ukraine. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya bayyana cewa gwamnatin Amurka zata gabatar da nata kudurin dangane da tsaida yaki a kasar Ukraine ga babban zauren MDD. Labarin ya kara da cewa Rubio ya ce zai gabatar da kudurin ne a ranar litinin mai zuwa wato ranar 24 ga watan Fabrairu...
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, a karon farko ya yi Allah-wadai da kasar Rwanda kan goyon bayan da take bai wa mayakan kungiyar M23 a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin ya kuma nemi ksar ta Rwanda da ta”gaggauta” janye sojojinta daga gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango. Kudurin na ranar Juma’a “ya kuma yi kakkausar suka ga hare-haren da kuma ci gaban da kungiyar M23 ke ci gaba da yi a arewacin Kivu da Kivu ta Kudu tare da goyon bayan dakarun tsaron kasar ta Rwanda”. A wani labarin kuma sakataren harkokin wajen Amurka Marco Rubio ya yi kira da a tsagaita bude wuta nan take a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da shugaban Kenya...

Trump Yana Son Ganin Bayan Shugaban Kasar Ukraine Volodimir Zelezky Daga Kujerar Shugabancin Kasarsa
A dai-dai lokacinda shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana a fili kan cewa baya son nganin tokwaransa na kasar Ukraine Volodimir Zelesky kan kujerar shugabancin kasarsa. Al-amura suna kara tabarbarewa a Kiev. Jaridar Economist ta kasar Burtaniya ta bayyana cewa al-amarin ya bayyana kiri-kiri ne a lokacinda shugaban kasar Amurka ya zanta ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladimi Putin. Sannan aka gudanar da taro na farko tsakanin Amurka da Rasha a birnin riyad na kasar Saudiya ba tare da an gayyaci Zelesky ba haka ma, babu wani Jami’in tarayyar Turai da aka gayyata. Jaridar ta nakalto wani babban jami’in gwamnati a Kiev yana cewa tun lokacinda suka fahinci cewa Trump baya son a ci gaba da yaki...
“A watannin da suka gabata, masu ruwa da tsaki a cikin dillalan sun nuna damuwa game da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Yanzu da farashin ya ragu, kamar garin da ya fadi daga naira 81,000 a kowace buhu zuwa kasa da naira 60,000, da taliya wanda ya fadi daga naira 20,000 zuwa naira 15,000. “Adalci ne a bar masu amfani da kayayaki su amfana da wannan rage farashin abincin da aka samu,” in ji Kyari. An dai bayar da rahoton cewa, hauhawar farashin kayan abinci ya ragu zuwa kashi 24.48 da kuma kashi 26.08 a watan Janairun 2025, inda ya ragu daga kashi 34.8 bisa dari da kuma kashi 39.84 a watan da ya gabata, sakamakon sake fasalin farashin kayan masarufi...

Babban Jami’i A Kungiyar JIhadul-Islami Ya Ce: Gudumawar Marigayi Sayyid Hasan Nasrullahi Ba Zai Fadu Ba
Jimi’in ofishin siyasa na kungiyar jihadul-Islami ya bayyana cewa: Marigayi Sayyid Hasan Nasrallah ya baiwa Falastinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya siffanta shi ba Mamba a ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmaya ta Jihadul-Islami ta Falasdinu Ihsan Ataya ya yaba da irin tsayin dakan da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi a fagen goyon bayan hakkokin Falasdinawa da gwagwarmayarsu, yana mai jaddada cewa: Shahidin al’ummar Sayyed Hassan Nasrallah ya gabatar wa Falasdinu da gwagwarmaya abin da harshe ba zai iya ambata ba. A cikin wata hira ta musamman da ya yi da tashar talabijin ta Al-Alam, Adaya ya yi cikakken bayani kan yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin ‘yan gwagwarmayar Falasdinawa da yahudawan sahyoniya, yana mai jaddada cewa: Gwagwarmaya...
Kungiya mai gwagwarmaya ta Falasdinawa Hamasa ta bayyana cewa tana iya sakin fursinoni yahudawa wadanda suke hannunta gaba daya a lokaci guda a marhala ta biyu ta musayar fursinoni tsakaninta da tare da sharadin ta cika al-kawulan da ta nauyi alhakin aiwatar da shi a wannan karon. Daga cikin har da maida tsagaita wutan na din din din Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Taher Al-Nounou ya cewa idan an yi haka za’a kammala musayar fursononin gaba daya, sannan HKI ta sake duk fursinonin falasdinawa gaba daya da suke hannunta. Yin hakan ya na nuna yanda al-amarin musayar Fursinoni yake da muhimmancin ga falasdinawa. Kafin wannan sanarwan dai ministan yaki na HKI Isarael Katz ya bayyana cewa...
Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila ta fuskanci cewa dole ta mika wuya tare da amincewa da sulhu da ‘yan gwagwarmaya da ta nemi murkushe su Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya jaddada cewa: Yahudawan sahayoniyya ba su cimma ko daya daga cikin munanan manufofinta ba, kuma daga karshe ya zama tilasta su mika wuya tare da amincewa da sulhu da bangarorin da suke son kawar da su. Babban sakataren kungiyar jihadul-Islami ta Falasdinu Ziyad Nakhalah, da ya ziyarci birnin Tehran a karkashin jagorancin wata tawaga don tuntubar hukumomin kasar Iran ya gana da ministan harkokin wajen kasar Sayyid Abbas Araqchi a yammacin jiya Talata. Haka nan yayin da yake ishara da halaltacciyar gwagwarmayar...
Shugaban kungiyar Hamas Khalilul-Hayyah, ya fadi cewa; A ranakun Alhamis da Asabar masu zuwa ne za a mikawa ‘yan mamaya fursunoni rayayyu da kuma wasu gawawwaki a cikin bude wani shafin na musaya. A jiya Talata ne dai Khalilul-Hayyah ya sanar da cewa, a bisa yadda aka cimma matsaya a musayar farko da aka yi, a cikin mako na shida daga kulla yarjejeniya, za a shiga wani sabon shafin na gaba na musayar fursunoni. Khalil Hayya ya kuma ce a ranar Asabar din mai zuwa ne za a mika sauran fursunoni rayayyu da su ka saura, kamar yadda aka cimma matsaya da adadinsu shi ne 6, biyu daga cikinsu ana rike da su ne tun 2014, yayin da ‘yan mamaya...
Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran “IRGC” ya sanar da cewa; Iran za ta kai farmakin “Wa’adus-Sadik 3” a lokacin da ya dace. Laftanar janar Ali Fadwi ya kuma yi ishara da yakin Gaza, yana bayyana cewa, su kansu ‘yan sahayoniya sun bayyana cewa Hamas ta yi nasara, su kuma ba su cimma manufarsu ba. Iran dai ta kai wa HKI hare-hare guda biyu a aka bai wa Sunan “ Wa’adussadik” na daya da na biyu. Hare-haren na Iran dai sun kasance mayar da martani ne akan harin da HKI ta kai wa karamin ofishin jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kasar Syria da kuma kashe mata jami’an soja masu bayar da shawara ga gwamnatin Damascuss....
Wani matashi da aka kama kan yin gunduwa-gunduwa da budurwarsa da suka haɗu a Facebook bayan ta je ɗakinsa ya bayyana dalilinsa na aikata hakan. Matashin mai shekaru 29 da ke iƙirarin malumtar addini ya amsa a wurin ’yan sanda masu bincike cewa shi ne ya yi wa gawar budurwar tasa gunduwa-gunduwa. Ya shaida musu cewa a Facebook ya haɗu da ita, inda daga bisani ta ziyarci ɗakinsa a unguwar Olunlade a garin Ilori, bayan ta je wani biki. Sai dai ya musanta zargin da ake masa na kashe ɗalibar mai suna Hafsah Yetunde Bello domin yin tsafi. Jirgin soji ya kashe fararen hula a Katsina Malaman addini sun yi wa ’yan siyasa juyin mulki —Sule Lamiɗo Ku tona asirin...
Kwanaki 30 bayan tsagaita wutar yaki a Gaza, sojojin mamayar HKI suna cigaba da kai hare-hare a yankuna mabanbanta. Bugu da kari, sojojin na HKI suna cigaba da rushe gidajen Falasdinawa a cikin yankin yammacin kogin Jordan. Minsitan kudi na HKI Byetrael Smotrach ya ce, a kowace shekara za su rushe gidaje a yammacin kogin Jordan fiye da wadanda Falasdinawa suke ginawa. Wannan dai shi ne lokacin farko da HKI ta dawo da siyasar rusau a yammacin kogin Jordan tun a 1967. Wannan matakin na HKI yana zuwa ne a daidai lokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Marco Robio yake ziyara a Tel Aviv, kuma a lokacin da Amurkan ta bai wa HKI bama-baman MK-84 har guda 1,800.
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Bayanai daga sassa daban-daban na Najeriya suna nuni da cewa farashin kyayyakin masarufi na ta faɗuwar a kasuwanni. Kafin hakan dai farashin ya yi ta tashi, har ya kai ga duk abin da mutum ya saya a yau, idan ya koma kasuwa bayan kwana biyu zai ji an ce ya tashi. NAJERIYA A YAU: Kalubalen Da Ke Durƙusar Da Gidajen Rediyo A Arewa DAGA LARABA: Dalilan Da Al’adar Zanen Fuska Ke Neman Gushewa A Kasar Hausa Ko wadanne dalilai ne suka sa farashin kayayyakin masarufi suke ta sauka a yanzu? Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi duba ne a kan wannan batu. Domin sauke shirin, latsa nan.

Trump Ya Bukaci Ukirain Ta Bada Ma’adinanta Ga Kasar Amurka Idan Tana Son Ta Taimaka Mata Da Kayakin Yaki
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce, Amurka ta na son mallakar ma’adanan na kasar Ukiraniya, wadadensu ya kudadensu ya kai dalar Amurka biliyan 500, a matsayin mayar da kwaryar taimakon Amurkan ta fuskar soja da makamai. A wata hira da tashar talabijin ta “FOX NEWS” ta yi da shi, shugaban kasar ta Amurka Donald Trump ya ce, ya na son Amurka ta mallaki ma’anadai na kasar Ukiraniya a matsayin ladar da tallafin sojen da take bukata daga Amurka. Gwamnatin Donald Trump ta gabatar wa da Kiev shawarar yin musayar ma’adanai na musamman da irinsu sun yi karanci a duniya, da take da su, na kaso 50% da hakan zai zama abinda take biyan Amurka da su, madadin taimakon soje...
Babban sakataren MDD Antonio Guterres wanda ya halarci taron kungiyar tarayyar Afirka AU da aka bude a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, ya kira yi kungiyoyin kasa da kasa da su kai daukin gaggawa ga kasar Sudan ta fuskar bada kayakin agaji. Guterres ya nanata muhimmancin kai kayakin abinci da sauran kayakin da ake bukatuwa da su, domin taimakawa mutanen kasar ta Sudan da yaki ya daidaita. Babban magatakardar MDD ya yi ishara da rawa ta jarunta da kungiyoyin mata suke yi a cikin yanayi mai hatsari,tare dayin kira da a kare rayukan fararen hula. Har’ila yau ya yi kira da a kawo karshen shigar da makamai zuwa kasar ta Sudan da bai wa zaman lafiya dama, a cikin...
A nasa jawabin, Jatau ya bayyana cewa, duk da cewa kisan da aka yi wa wani malamin addini lamari ne mai ban tausayi, amma babu wata kwakkwarar shaida da ke alakanta lamarin da wata kungiya, addini ko kabilanci. Ya tuna irin abubuwan da suka faru a baya inda daga baya aka gano wadanda suka aikata laifin ‘yan kungiya daya ne ko kabila ko addini. Jatau ya kuma umarci jami’an tsaro da su kama wadanda ke da hannu a kisan tare da tabbatar da an hukunta su. Ya bukaci shugabanni da su kasance masu kamun kai da hakuri wajen tafiyar da irin wadannan al’amura masu muhimmanci domin hana faruwar lamarin. “Ina kira gare ku a matsayinku na shugabanni da ku yi...

Shugaban Masar Ya Dage Ziyararsa Zuwa Amurka Har Sai Bayan Zaman Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa
Majiyoyin watsa labarai sun bayyana cewa: Shugaban kasar Masar ya dage ziyararsa zuwa Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa Majiyoyin watsa labaran Masar sun watsa labaran cewa: Gwamnatin kasar ta sanar da dage ziyarar da shugaban Masar Abdul Fattah al-Sisi zai kai birnin Washington na Amurka har sai bayan taron gaggawa na kungiyar hadin kan kasashen Larabawa da aka shirya gudanarwa a birnin Alkahira a ranar 27 ga wannan wata na Fabrairu. Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Dage ziyarar ya zo ne domin shugaban kasar Masar ya shirya irin martani da zai mayar wa takwaransa na Amurka Donald Trump, bisa hangen nesa da ke samun cikakken goyon bayan Larabawa kan shirin shugaban Amurka...
Shugaban Hukumar Kwashe Shara ta Jihar Kano (REMASAB), Ambasada Haruna Zago, ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Wani ma’aikacin hukumar ya tabbatar da rasuwar Haruna Zago a asibiti, inda ya bayyana cewa marigayin ya kwanta rashin lafiya na wani lokaci kafin rasuwarsa. Gwamnan Kano Ya Bada Umarnin Kamo Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Watanni 2 Da Sauke Baffa Bichi, An Nada Umar Farouk Mukamin Sakataren Gwamnatin Kano Haruna Zago ya kasance Shugaban Hukumar REMASAB tun ranar 5 ga watan Yuli, 2023, bayan naɗin da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi masa.

’Yan Wasan Motsa Jiki Na Asiya Sun Yi Murnar Bikin Sabuwar Shekara Bisa Kalandar Gargajiya Ta Sin A Harbin
An gabatar da bikin mu’ammalar al’adu a jiya Litinin a birnin Harbin da ake wa lakabin “Birnin kankara”, yayin da ake gudanar da gasar wasannin motsa jiki na lokacin hunturu ta Asiya karo na 9 a birnin. An yi wannan gaggarumin biki ne bisa jigon “bikin sabuwar shekara ta kalandar gargajiya ta kasar Sin, wato bikin bazara karo na farko bayan shigar da shi jerin bukukuwan gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni a duniya, wanda ya zo a kan gabar gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Asiya.” ’Yan wasan motsa jiki 20 daga kasar Mongoliya da Thailand da Philipphines da Vietnam da Indiya da Nepal da dai sauran wakilan tawagogin wasannin motsa jiki da ’yan jarida...
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka. Sharhin bayan labarammu zai yi magana ne dangane da barazanar shugaban kasar Amurka ga JMI “Ko ta yarda da ta zauna kan teburin tattaunawa da ita kan shirinta na makamashin nukliya ko kuma ya tura HKI ta fermata da yaki’. Wanda ni tahir amin zan karanta. ///… A wani lokaci a cikin jirgin saman fadar shugaban kasa shugaban kasar Amurka Donal Trump ya fadawa kamfanin dillancin labaran “NewYork Post’ dangane da shirin nukliyar kasar Iran, kan cewa ya fi son ya zauna da Iraniyawa su tattauna kan shirinta na makamashin nukliya, su yarda su dakatarda duk wani abu da ya shafi nukliya, amma idan sun ki tattaunawa, kuma bai da zabi in banda...
An gurfanar da wasu mutum uku ’yan uwan juna kan yi wa wata matar aure da mijinta dukan kawo wuƙa a yankin Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar Kano. An gurfanar da su ne a gaban Babbar Kotun Musulunci ta Gazawa kan zargin yi wa matar auren karaya uku a ƙafarta da hannunta bayan sun yi mata dukan kawo wuƙa tare da ji mata raunuka. Sun kuma ƙuƙƙuje mijinta da ya yi ƙoƙarin ceton ta bayan shi ma suka lakaɗa masa duka. Ana tuhumar su laifin yin kutse da yin barazana da haɗa kai wajen aikata laifi da ji wa mutane munanan raunuka. ’Yan sanda sun ba al’ummar Sheka awa 24 su kawo sunayen ’yan daba Ɗan fashi ya yi...

Sharhin Bayan Labarai “Yadda JMI Ta bunkasa Bangaren Gine-Gine Da Masana’antu Da Kamfanonin Tare Da Fasahar Cikin Gida”
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhaka barkammu da sake saduwa a cikin shirimmu na sharhin bayan labarai, wanda zai yi magana a kan “Yadda JMI Ta Bunkasa Sana’argine-gine da da kamfanoni tare da amfani da fasahar cikin gida’ wanda ni tahir amin zan karanta. Tun bayan nasarar juyin juya halin musulunci a nan kasar Iran a shekara 1979, daya daga cikin bangarorin da aka sami gagarumin ci gaba a cikinsa shi ne, bunkasa sana’ar gine –gine da kuma samar da masana’antu, wanda ya kai ga kasar ta kai ga wadata a wannan bangaren, wani abu daga kasashen waje, sai abunda ba za’a rasaba. Har’ila yau wannan ya wadanar da mutane da dama a kasar. Kafin haka idan mun dubi...
Manchester City ta tsallake rijiya da baya a gidan Orient, bayan ta doke su da ci 2-1, hakan ya sa ta tsallaka zuwa zagaye na biyar na gasar cin kofin FA ranar Asabar. Kamar kullum, Kevin De Bruyne ne ya fitar da kitse daga wuta ana gab-da za a tashi daga wasan. Mai tsaron ragar Manchester City, Stefan Ortega ne ya ci gida tun a minti na 16 da fara wasan, sabon dan wasan City Khusanov ne ya ci kwallonsa ta farko bayan dawowa daga hutun rabin lokaci kafin Kevin De Bruyne ya jefa ta biyu. Mutanen Guardiola kuwa su na matsayi na hudu a gasar Firimiya, hakazalika za su hadu da zakarun Turai, Real Madrid a gasar zakarun Turai...
A bayan nan ne mahukunta a Ƙaramar Hukumar Agege, a ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙaramar Hukumar Agege, Alhaji Ganiyu Kola Egunjobi suka kulle babban masallacin Hausawa na garin, biyo bayan wani rikici da ke da alaƙa da na limanci ya ɓarke a masallacin a ranar Juma’a makon jiya. Rikicin na zuwa ne bayan rasuwar babban limamin garin Agege, Shaikh Sharif Habib Abdul-Majid, wanda ya rasu kwanaki biyu gabanin aukuwar lamarin. Yadda Kano ke samar da madarar Naira biliyan 2.2 An dakatar da dagaci kan zargin saran maraya da adda A wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta na zamani, an ga masallata a cikin masallacin suna kai wa junansu duka, wadanda suka haɗar da ɓangarori uku. Waɗanda suka bai wa...
An kama wata matar aure bisa zargin ta da kashe dan kishiyarta ta hanyar zuwa masa tafasasshen ruwa a kaciyarsa a garin Dawakin Tofa da ke Jihar Kano. ’Yan sanda a Jihar Kano na zargin matar ta je ta dauki yaron ne a wurin kakarsa, ida ake kula da shi bayan an yi masa kaciya, kasancewar mahaifiyarsa da mahaifin sun rabu. Bayanai sun nuna cewa duk da cewa kakar ta ki amincewa, amma sai da matar ta nace ta dauki yaron da cewa za ta kula da shi, bayan nan ne kuma sanya masa tafasasshen ruwa a gaban nasa, maimakon ruwan dumi. Duk da raunin da tafasasshen ruwan ya yi masa kuma, sai aka kai shi wurin mai maganin gargajiya...
Biyo bayan nasarar da suka yi akan Alavés a ƙarshen mako, Barcelona za ta dawo taka leda a yau Alhamis don ƙarawa da Valencia a wasan daf da na kusa da na karshe a gasar Copa del Rey a filin wasa na Estádio de Mestalla dake Valencia. Barcelona na cigaba da jan zarenta a wannan shekarar ta 2025, inda ta buga wasanni da dama ba tare da tayi rashin nasara ba tun bayan shigowar sabuwar shekara, kuma daya daga cikin mafi kyawun sakamakon da ta samu ya zuwa yanzu a bana shi ne wanda ta doke Valencia da ci 7-1 kwanaki 10 da suka gabata. Har Yanzu Arsenal Ta Na Iya Lashe Gasar Firimiya Ta Bana – Alan Shearer Ba...

Jeremy Corbyn Ya Bukaci Ganin An Hukunta Isra’ila Da Masu Ba Ta Makamai Akan Kisan Kiyashin Falasdinawa
Tsohon shugaban jam’iyyar “ Labour” ta Birtaniya Jeremy Corbyn ya yi kira da a hukunta Isra’ila, da masu daukar nauyinta akan kisan kiyashin da ta yi tun bayan ranar 7 ga watan Okotoba 2023. Cobyn ya rubuta a shafinsa na X cewa; A cikin bayan nan ne zurfin barnar da Isra’ila ta yi, yake kara bayyana, don haka wajibi ne jami’anta su fuskanci shari’a akan kowane rai daya da aka yi asararsa. Cobyn ya ci gaba da cewa; Duk wanda ma ya rika aikewa da makamai yana sane da cewa za a yi amfani da su a yi kisan kiyashi, shi ma a hukunta shi.” A cikin watanni shida da su ka gabata Birtaniya ta sayar wa da HKI makamai...

Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci Ta Iran Ya Ce; Kasashen Iran Da Iraki Zasu Kare Kungiyoyin Gwagwarmaya
Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare kungiyoyin gwagwarmaya Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf ya jaddada cewa: Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare wannan gwagwarmaya da ta hana makiya numfasawa a yankin. Shugaban Majalisar Shawarar Musulunci ta Iran Muhammad Baqir Qalibaf a wani taron manema labarai da ya yi da takwaransa na Iraki Mahmoud al-Mashhadani, ya bayyana cewa: Kasashen Iran da Iraki sun kuduri aniyar kare gwagwarmaya, yana mai jaddada cewa: Iran da kawarta Iraki sun kuduri aniyar marawa bangaren gwagwarmaya baya domin kare Musulunci da martabar al’ummar musulmi. Baqir Qalibaf ya kara da cewa: Sun ba da muhimmanci wajen raya hanyar layin dogo, musamman sabuwar...

Shugaban Kasar Amurka Ya Ce Nan Ba Da Dadewa Ba Zai Kara Kudin Fito Na Kayakin Da Ake Shigo Da Su Amurka Daga Kasashen Turai
Shugaban kasar Amurka Donal Trump ya bayyana cewa a yau litinin ne zai tattauna da shuwagabannin kasashe Mexico da Canada dangane da rikicin kudaden fiton da ya karawa kasashen biyu. Shugaban ya kara da cewa, zai tattauna da shuwagabannin biyu a yau don ya tabbatar masu da manufarsa na kara kudaden fiton. Shugaban ya kara da cewa zai dorawa hatta kayakin da suke shigowa Amurka daga kasashen Turai, nan gaba, sai dai bai sanya lokaci ba. Kafin haka dai shugaban ya bayyana cewa zai dorawa kasar Canada kashi 25% kan dukkan kayakin da suke shigowa kasar. Sai mna Desel, inda zai sanya kashi 10% kacal.
A hannu guda kuma, Gwamnan ya yi kira ga sojoji da sauran bangarorin jami’an tsaro da su kara kaimi wajen fadada yin sintiri a yankunan da ke kan iyakokin jihar, domin dakile shigowar yan ta’adda cikin jihar. A nashi bangaren, Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, ya sake baiwa Gwamnan tabbacin cewa sojoji za su ci gaba da jajircewa wajen kawo karshen matsalar yan ta’adda tare da ta yan bindiga a Nijeriya baki daya. “Babbab burinmu shi ne mu wayi gari mu ga wannan matsala ta zo karshe cikin gaggawa, kuma ina mai jaddada kira ga shugabannin siyasa da yan Nijeriya, su ci gaba da bayar da gudummawa wajen ganin mun cimma wannan buri.” In ji COAS. Hakazalika kuma, ya bayar da...
Tun bayan ’yan kwanaki da Babban Kwamandan Hisbah na Jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya sanar cewa Hukumar ta daina kamen masu aikatawa da yada baɗala, sai dai ta yi musu wa’azi, aka fara ganin yaɗuwar bidiyoyin da suka saɓa da al’ada da Addinin Musulunci suna ɓulla kafofin sada zumunta. Daga watan Disamban 2024 da Hisbah ta yi sanarwar zuwa yanzu, an samu ɓullar aƙalla bidiyoyi 10 daga jihar da suka tayar da kura a kafofin sada zumunta, musamman TikTok, ciki har da na tsiraici. Muna da ƙarfin aljihun ɗaukar nauyin Taron Al-Ƙur’ani —Sheikh Bala lau Yadda Khalifan Sheikh Ibrahim Inyass ya yi wa Tinubu addu’ar nasara Ɓullar bidiyon tsiraicin fitattun ’yan Tiktok irin su Hafsat Babaiana da Hafsat...
Kayan hadi: ”Yayan Hulba (gongoni 2, Aya (gongoni 3), Ridi (gongoni 1) Ga kuma Yadda za ku hada: Wadannan kayan hadin ku soya su duka amma sama-sama sai ku bar su su huce sanna ku daka ko ku nika ku tankade. Yadda ake amfani da ita: Za ku dinga diban cokali 2 ko 3 kusa madara cokali 2 kusa ruwan zafi ku gauraya ku shanye, sannan ana sha ne safe da rana da dare na tsawon sati 3 ko 4. Kazalika ku nemi garin hulba ku debi kadan kusa ruwan zafi ku gauraya sai ku sanya wani abu ku dinga dandanar ruwan kuna gasa shi, sannan ku samu man hulba da man zaitun da man ridi ku...
Sojojin kasar Iran sun nuna karfinsu a yankin Asiya ta kudu tare da itisayen da ta yi ta gudanarwa a cikin yan makonnin da suka gabata. Tare da nuna iya diblomasiyyar kasar tare da sauran kasashen yankin. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Rear Admiral Habibollah Sayyari mataimakin shugaban rundunar sojiji na kasar yana fadar haka. Ya kuma kara da cewa, iya diblomasiyyar kasar Iran a tsakanin kasashen yankin, ya tabbatar da karfin da kasar take da shi a fagen karfin soje. Kuma ta tabbatar da cewa zata iya kula da al-amuran tsarom da kuma tabbata shi a yankin. Sayyari yace an gudanar da atisayen na sojoji kimani rundunonin fiya da 100 inda suka yi musayar tunani...
Jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aikin soje na zamani duk da cewa wasu daga cikin jiragen tsoffin kira ne. Kamfanin dillancin labaran Sahaab na kasar Iran ya nakalto babban kwamandan sojojin sama na JMI yana fadara haka. Ya kuma kara da cewa sojojin saman kasar sun samarda wasu sabbin kayakin aikin Soje wadanda zasu nunasu nan ba da dadewa ba. Sannan ya kara da cewa dukkan jiragen yakin JMI suna amfani da kayakin aiki na zama, wanda sabbin jiragen saman yakin da ake kerasu a wasu kasashen basu yi gaba da su a wani daga cikin a kayakin aiki na zamani ba. Kamfanin dillancin labaran Sahab ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran Tasnim wanda ya nakalto babban kwamnadan...
Rundunar ‘yan sandan Babban Birnin Tarayya (FCT) tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro sun kai samame a wasu gidajen jama’a a birnin, inda suka kama wasu da ake zargin ɓarayi ne tare da ƙwato kayayyakin da aka sace. Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato da suka haɗa da: naɗin igiyoyin wutar lantarki masu yawa, an baje kolin su a yayin da rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta gabatar waɗanda ake zargin a ranar Juma’a Ga wasu hotunan kayan da aka ƙwato:
’Yan bindiga sun kashe mutane uku tare da yin garkuwa da wasu 24 a wasu jerin hare-hare a wasu kauyuka hudu a Ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara. ’Yan ta’adan sun kai hare-haren ne ranar Alhamis, a ƙauyukan Shinkafi da Jangeru da Shanawa da Birnin Yero. A garin Shinkafi, ’yan bindigar sun kashe mutum uku tare da yin garkuwa da wasu tara, ciki har da mata hudu. Mazauna garin sun bayyana cewa maharan sun bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya haifar da fargaba. Direba cikin barasa ya murƙushe sojoji sun mutu a Legas Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa A kauyen Birnin Yero, ’yan bindiga sun kai hari a wani masallaci a lokacin...
A sabon rahoton 2024 da Bankin Duniya ya fitar, ya ce a kalla ‘yan Nijeriya miliyan 129 ne suke rayuwa cikin talauci, da ke nuni da cewa an samu kari fadawar mutane cikin talauci daga kaso 40.1 a 2018 zuwa kaso 56 a 2024. Tabarbarewar tattalin arzikin da ake fama da ita tare da karuwar yawan jama’a cikin sauri, ya tsananta matakan talauci. Raguwar tattalin arziki kasar ga kowane mutum, wanda ya ragu da kashi 25.04 cikin dari daga dala 2,162.6 a 2022 zuwa dala 1,621.1 a 2023, ya kara jaddada raguwar karfin saye da kuma tabarbarewar rayuwa bisa ga rahoton PWC. Tashin farashin kayayyaki shi ne ke kan gaba wajen janyo wa tattalin arzikin Nijeriya matsaloli. Zuwa watan Disamban...

Kafafen Yasa Labaran Sweden Sun Tabbatar Da Mutuwar Selwan Momika Wanda ya Kona Alkuranai A Kasar A shekarum Baya
Kafafen yada labarai na kasar Sweden sun bayyana cewa an sami gawar Selwan Momika dan shekara 38 a duniya a wani gida daga kudancin birnin Stokhom na kasar. Selwan dai dan asalin kasar Iraki ne, wadanda yake gudun hijira a kasar ta Sweden tun, amma ya bayyana kansa a kafafen watsa labarai a shekara ta 2023 inda yake kona alkur’ani mai girma don wulakanta shi. Saboda kuma nuna kiyayyarsa ga addinin musulunci da musulmi. Gwamnatin kasar Sweden dai ta halattawa Selwan yin haka a karkashin dokar yencin fadin albarkacin baki wanda kasashen yamma musamman a turai suka amince da ita. Sai dai wannan aikin nasa ya gamu da fushin musulmi a duk fadin duniya. Yansan da a birnin Stokhom sun...
Firai ministan HKI Banyamin Natanyahu Ya bada umurnin a dakatar da musayar fursinoni da kungiyoyi masu gwagwarmaya a Gaza. Bayan da Falasdinawa sun Saki mutane 8 ya zuwa yanzu, yahudawa 3 da kuma wasu yan kasar Thailand 5. Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kafafen yada labaran yahudawan suna fadar haka. Sun kara da cewa firai ministan ya ce a dakatar da sakin fursinoni Falasdinawa 110 wadanda yakamata HKI ta sallamesu a yau. Kafin haka dai Falasdinawan sun salami wadannan fursinonin yahudawan 8 ne a zagaye uku na musayar fursinoni da kuma janyewar sojojin yahudawan daga yankunan gaza. Majiyar ofishin firay ministan ya bayyana cewa an dakatar da musayar fursinonin ne har sai abinda hali yayi. Da...
Shugabna Pual Kagame na kasar Rwanda ya bayyana cewa ba zai dakatar da goyon bayana da yake bawa kungiyar yan tawaye ta M23 ba, wadanda a cikin yan kwanakin da suka gabata sun kwace wurare da dama a arewacin Kivu na kasar DMC daga cikin har da birnin Goma babban birnin lardin. Shafin yanar gizo na ‘Afirca News’ ya nakalto kagami yana cewa ya a shirye yake ya shiga yaki da kowa saboda kare matsayinsa. A yau Alhamis dai mayakan M23 sun kammala kwace iko da birnin Goma babban birnin yankina kuma a halin yanzu sun nosa zuwa garin Bukavu babban birnin lardin Kivu ta kudu. Wannan dai shi yaki mafi girma wadanda ake yi a yankin KIvi tun shekara...
Wani jami’in fadar mulkin Amurka ( White Hosue) ya nakalto shugaban kasar Amurka Donald Trump yana fada a yau Laraba cewa, shugaban kasar Amurkan ya rattaba hannu akan wata doka ta fada da kin jinin yahudawa da ta kunshi cewa duk wasu dalibai ‘yan kasashen waje da masu ci rani a kasar, idan su ka shiga cikin Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa to za a kore su daga Amurka. Dokar da Trump din yta sanya hannu a kanta ta kuma kunshi bayar da umarni da ma’aikatar shari’ar kasar aka cewa ta bi diddigin duk masu barazanar ta’addanci, da ruruta wutarsa, da mabarnata dake cutar da yahduawan Amurka.” Haka nan Trump ya ce zai soke izinin shiga cikin kasar ta Amurka...
Babban kwamishinan hukumar kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya “UNRWA” ya bayyana wa kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa: Aiwatar da dokokin Isra’ila kan hukumar UNRWA zai zama bala’i Babban Kwamishinan Hukumar Kula da ‘yan gudun hijiran Falasdinawa ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA), Philippe Lazzarini, ya ce: Aiwatar da cikakken dokar Majalisar Dokokin Haramtacciyar kasar Isra’ila ta Knesset kan hukumar UNRWA zai zama masifa, yana mai gargadin cewa: Rage ayyukan hukumar ta “UNRWA” a wajen tsarin siyasa, kuma a daidai lokacin da kwarin gwiwa daga kasashen duniya ya yi kadan, wanda hakan zai kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza. Shafin watsa labaran Falasdinu na “Wafa” ya bayar da rahoton cewa: A jawabin da...
Babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta kasar Lebanon ya ce: Batun rusa gwagwarmaya ta zama tatsuniya kuma batun Falasdinawa ya dawo cikin fagen siyasar duniya Babban sakataren kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon, Sheikh Na’im Qassem ya jaddada cewa: Harin daukan fans ana “Ambaliyar Al-Aqsa” ta cimma burinta na mayar da al’ummar Falastinu a fagen kasa da kasa, yana mai cewa; Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta zame a matsayin kungiyar ta’addanci ta masu aikata laifuka da kisa kiyashi a idon duniya. Babban sakataren kungiyar ta Hizbullah Sheikh Na’im Qasem ya bayyana a wani jawabi da ya gabatar a yammacin jiya Litinin game da sabbin abubuwan da ke faruwa a kasar Lebanon da kuma yankin, inda ya ce: “Hare-haren wuce...
Kwamitin zaman lafiya da tsaro na Tarayyar Afirka ya sanar da cewa zai gudanar da zaman gaggawa yau Talata kan halin da ake ciki a gabashin Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango (DRC). Kwamitin na (PSC) zai gudanar da wani zaman gaggawa a yau Talata kan halin da ake ciki a yankin, wanda ke fama da yakin da ake yi tsakanin dakarun Kongo da mayakan M23″ in ji Paschal Chem-Langhee, mai magana da yawun kwamitin, yayin da al’amura ke kazanta a Goma, babban birnin gabashin DRC. Kafin nan daruruwan ma’aikatan MDD da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sun tsere zuwa makociyar kasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo din suka “mika wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan...
Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ’Yan Alluna a Jihar Kano, ta yanke wa wani matashi hukuncin ɗaurin shekara biyu, a gidan yari bayan samun sa da laifin satar wayoyin salula. An gurfanar da Aliyu Rabi’u Rijiyar Lemo a gaban kotun, bayan kama shi a kan titin Ibrahim Taiwo tare da wasu biyu, inda suke amfani da Adaidaita Sahu wajen satar wayoyin hannun fasinjoji. ’Yan bindiga sun sace matashiya bayan karɓar kuɗin fansa a Kano ’Yan bindiga sun sace mutum 22 a ƙauyukan Kaduna A wajen da aka kama shi, wasu fusatattun mtsne sun ƙone Adaidata Sahun da suke amfani da shi wajen aikata laifin. An tuhume shi da haɗa baki don aikata laifi, sata, da tayar da hankalin...
’Yan bindiga sun kai hari garin Garo da ke Ƙaramar Hukumar Kabo a Jihar Kano cikin daren ranar Lahadi, inda suka sace wata budurwa mai suna Zainab Auwalu, bayan sun karɓi kuɗin fansa Naira miliyan takwas daga hannun mahaifinta. Zainab, wadda ta kammala makarantar sakandare kwanan nan, an sace ta a gidan mahaifinta, Alhaji Auwalu. SERAP ta maka Tinubu da NCC a kotu kan kara kudin kiran waya da data Shin wannan ce kaka mafi muni ga Man-United a Gasar Firimiya? Shaidu sun bayyana cewa ’yan bindigar, kimanin su 10, sun shiga garin da babura ɗauke da muggan makamai. Sun shiga gidan Alhaji Auwalu da misalin ƙarfe 1:30 na dare, inda suka shafe awanni suna cin karensu ba babbaka, sannan...