Ƙungiyar Malaman Tsangaya Ta Naɗa Gwamna Inuwa Sarautar ‘Khadimul Qur’an’
Published: 9th, March 2025 GMT
Ƙungiyar Malaman Tsangaya a Jihar Gombe ta naɗa Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’ a matsayin girmamawa ga goyon bayansa maras misaltuwa ga ilimin Alƙur’ani da kuma matakan da ya ɗauka wajen kyautata tsarin Almajiranci.
Ƙungiyar Malaman Tsangaya ta miƙa wannan girmamawa ga Gwamnan yayin wani taron buɗa-baki na musamman da aka shirya musu a Fadar Gwamnati da ke Gombe, wanda ya tattaro shugabannin malaman Tsangaya daga faɗin jihar.
Wannan taron na cikin tsarin shekara-shekara na Gwamna Inuwa Yahaya na shirya shan ruwa tare da jama’a, wanda hakan wani mataki ne da yake ƙara haɗin kai, zaman lafiya, da hulɗa a tsakanin al’ummar Musulmi.
A jawabinsa bayan buɗa-bakin azumi, Gwamna Inuwa Yahaya ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na kyautata jin daɗin malaman Tsangaya da kuma yara Almajirai.
Ya bayyana muhimmancin ilimin Alƙur’ani ga al’umma tare da jaddada bukatar samar da yanayi mai ɗaukaka ga koyo da koyarwa.
Gwamnan ya yi bayanin yadda gwamnatinsa ta yi gagarumin ƙoƙari wajen gina manyan makarantun Tsangaya da ƙananan makarantun Almajirai a faɗin jihar, tare da haɗa ilimin Alƙur’ani da na zamani cikin tsarin karatu.
Haka kuma, ya yi nuni da cewa yara Almajirai an sanya su cikin shirin lafiya na Go-Health, wanda ke ba su damar samun kulawar lafiya kyauta domin tabbatar da lafiyarsu.
“Mu a matsayin gwamnati mun fahimci muhimmiyar rawa da makarantun Tsangaya ke takawa wajen tarbiyya da cigaban ilimi ga yaranmu.
“Wannan ne ya sanya muka fifita jin daɗinsu ta hanyoyi daban-daban, ciki har da gina makarantun Tsangaya da kuma shigar da su cikin shirin Go-Health domin samun ingantacciyar kulawar lafiya ba tare da wata matsala ba,” in ji Gwamna Inuwa.
Da yake magana a madadin malaman Tsangaya, Goni Mai Babban Allo ya yaba wa Gwamna Inuwa Yahaya kan goyon bayan da yake bayarwa ba dare ba rana.
Ya kuma bayyana cewa Gwamnan ya ɗauki matakai na musamman, ciki har da gina makarantun Tsangaya, sanya fitilu masu aiki da hasken rana a makarantun, da haɗa Almajirai cikin shirin kula da lafiya na jihar Gombe.
“Ba mu taɓa samun gwamnati da ta damu da jin daɗin malaman Tsangaya da ɗalibanmu kamar wannan ba,” in ji Goni Mai Babban Allo.
A cikin girmamawa ga ƙoƙarinsa da kuma sadaukarwarsa, Ƙungiyar Alarammomi ta naɗa Gwamna Inuwa Yahaya sarautar ‘Khadimul Qur’an’, alamar kasancewarsa bawan Alƙur’ani mai sadaukarwa.
Tun da farko, a jawabinta na maraba, Sayyada Amina Sheikh Dahiru Bauchi, mai bai wa gwamna shawara ta musamman kan harkokin Tsangaya da Ilimin Almajiranci, ta yi kira ga Alarammomi da su ƙara yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban Jihar Gombe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gwamna Inuwa Yahaya jihar Gombe malaman tsangaya Gwamna Inuwa Yahaya makarantun Tsangaya malaman Tsangaya a makarantun Tsangaya da
এছাড়াও পড়ুন:
Faransa, Masar da Jordan sun yi kira da a tsagaita wuta cikin gaggawa a Gaza
Shugabannin kasashen Faransa da Masar da kuma Jordan sun fitar da wata sanarwa ta hadin gwiwa inda suka bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa a Gaza, tare da sukar Isra’ila kan gazawarta wajen tabbatar da ayyukan jin kai a zirin.
Kiran tsagaita wuta ya nuna bukatar samar da agajin jin kai cikin gaggawa a Gaza kuma ya nuna damuwar da kasashen duniya ke ci gaba da yi kan tashe-tashen hankula da rikicin jin kai a Gaza.
Haka kuma sanarwar wadannan kasashe uku ta nuna muhimmancin hanyar diflomasiyya na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A baya dai shugaba Macron ya nuna adawarsa da mamaye yankunan Falasdinawa da Isra’ila ta yi.
Macron ya kuma kira sabbin hare-haren da Isra’ila ta kai a yankin bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita bude wuta a tsakiyar watan Maris da cewa wani babban koma baya ne.
Sarki Abdallah na biyu na Jordan, shugaban Faransa Emmanuel Macron, da shugaban Masar Abdel Fattah el-Sisi na Masar sun bayyana cewa, “Dole ne a dakatar da yakin Gaza duba da bala’in da ya haifar a yanzu.
Tashin hankali, ta’addanci, da yaki ba za su iya samar da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba.
Sanarwar ta yi nuni da bukatar gaggawa na kara kai kayan agaji a Gaza, inda tuni aka fara samun matsalar yunwa, da kare hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da ma’aikatan jin kai da ke aiki a yankin.